Showing 3001 words to 6000 words out of 37025 words

Chapter 2 - JININ ABBANA BOOK COMPLETE TXT By Zainab Habib Mom Islam.txt

25 Jan 2025

2101

menene damuwarki dashi ? tunda ba san mutane yakeyi ba , murmishi Momy tayi tace ”ai yakoma makaranta da zama rabona da ganinsa nima na dad'e , Fauziyya ce ta tace Momy bani number sa , mik'a mata wayar Momy tayi ta d'auki number Harun ta mik'e tayi bedroom d'inta , fad'awa gado tayi tafara k'ok'arin kiran sa , Harun dake kwance yana kallo a TV kasancewar yau baije ko ina ba , janyo wayarsa dake ring yayi , wata murya yaji amma yana tunanin kamar yasan mai muryar ,kawar da tunanin shi yayi yana saurarar mai kiran , cewa tayi d'an saurayi yakk kasan jiya nayi missing d'inka ? zaro ido Harun yayi yace ”ina tunanin kinyi wrong number ne , k'ara mak'ale murya tayi tace ”katsaya ka saurareni , anjima dai ina zuwa , Harun ne yace ”karki kuskura kikara ran wanan number ni ba kalar y'an iskan nan bane , dariya Fauziyya tasa ta katse wayar , tafara rawa tana cewa wlh sai na jefaka cikin masifa shege mai farin jini kawai ."






Asma'u ce zaune a gida tana tsincewa umman ta shinkafa wani amai ne ya taho mata da gudu ta mik'e taje ma kwarari tayi tasami ruwa ta d'auraye bakinta ta dawo ta zauna , umma dake yanka latas ta kalle ta irin kallon tuhuma , sunkuyar da kai Asma'u tayi , umma ce tace ”dama bakida lafiya ne ?"gaban Asma'une ya fad'i tafara in ina tana cewa um am ...dakatar da ita umma tayi , tasa aka siyo mata abin gwajin ciki saboda , ganin haske dakuma nononta dasuka ciciko ga k'iba datayi tashi daya , umarni umma tabata akan taje tayo fitsari a wata k'aramar kwalba , seda umma tasata yin fitsarinne tafara dana sanin zargin y'arta datakeyi da abinda ko a mafarki bazata aikata ba , sun san sunbata tarbiyar mai inganci , kawar da tunanin Umma tayi ganin Asma'u tadawo da fitsarin , gwadawa umma tayi ganin result din yasata....






Yau Harun yafara zuwa aiki ba laifi gurin yayi sosai kuma akwai albashi mai tsoka wanda dan danan mutum zai tara arzik'i na ban mamaki , kullum yana busy bashida lokaci , yana gurin aiki kasancewar shi mutum ne mai maida hankali a abinda yasa , a gaba wata k'ya k'yawar yarinya ce ta shigo sanye da hijab mai hannu ba k'aramin kyau tayi ba , k'are mata kallo Harun yayi zatakai shekara sha bak'wai , karo na farko daya tsaya ya k'urawa budurwa ido kenan mamakin kansa yakeyi , can kuma yaji k'irjinsa na bugu , dawowa wanan budurwa tayi , tacewa ”Harun barka ,dady na ya gayamin munsami sabon ma aikaci , washe fararen hak'waran sa yayi yace ”barka sister , dariya tayimasa tana yimasa wani irin kallo mai wuyar fassara , Harun baisan wanan budurwar ta tafi ba saboda ya fad'a kogin tunanin ta lol , kodai kodai🧏‍♀️..




*WASHE GARI*
Da safe yayi wanka sashen su momy ya nufa da sallama ya shige samunsu yayi a dining suna breakfast , momy ce ta washe baki tace ” a 'a my son zoman kaima ka karya , durk'usawa yayi ya gaida dady ciki ciki dady ya 'amsa kana ya juya ga momy , cikin fara'a ya amsa ,jiyayi ance brother barka da safiy, ywwa kintashi lpy sis cikin shagwa6a tace ”lafiya lau , a d'a rare ya zauna a dining chair d'in yayi karin kumallo ,tunda ya zauna fara'ar fuskar dady ta gushe , shigowar Bash ce yasanya Harun juyawa , sanye yake da gajeren wando iya guwai warsa sai singlet fara a , k'arasowa yayi yace ”good morning dad ,good morning mom, amsawa sukayi cike da kulawa suna yimasa ya aiki ,dady ko janyo Bash yayi kusa dashi yazuba masa farfesun kaza , Fauziya ce tace ”ya Bash inason muyi wata magana saboda is very important to me and yau lol , kashe mata ido yayi yace ”oky yanzu dai kibari na gama sai muje muyi ko , suna had'a ido da momy ta galla mata harara , Harun ne ya dubi gefen da Bash yake zaune yace ”brother babu magana ne , cikin zafin rai Bash yace ”bana magana da y'an iska irinku , yana magana yana nuna Harun , hankalin su momy ne yakoma gurinsu , yacigaba da cewa wlh dady ciki yayiwa wata yarinya yanzu gashinan iyayenta suna nemanshi ido rufe yama samu na rufa masa asiri , a razane ido yai ja Harun ya d'ago yana kallon Bash yace k'iyayyar mu harta kai ga kayimin sharin zina ?"nine fa d'an uwanka , dariyar mugunta Bash yayi yace ”a da kake d'an uwana amma yanzu an sauya bani babu abota da mazinaci !! kalmarnan ba k'aramin dukan Harun tayi ba ,har lokacin idon Momy da dady da Fauziya na kanshi ,wasu hawaye ne masu zafi suka kwaranyo daga idonsa ya had'a hannuwansa biyu yace ”na rantse da Allah dady da momy ku yarda dani ko kula y'ammata banayi walhi , wani mari dady ya wanka masa yana cewa d'an iska dama shiyasa kake shigo mana gida ?"to kull kar in sake ganinka a ginanan kaje can 6angaren ka amma nayi maka iyaka da iyali na so get out ko bakaji ba , Harun na kuka yana cewa dan Allah ku amince da magana ta, haka ya fice zuciyarsa babu dad'i ."






Dady ne ya kalli momy yace ”kinga abinda yaronnan ze janyo mana ko ? sunkuyar da kai momy tayi hawaye na zuba a fuskarta ta d'ago ta dubi Bash tace ”Bashir kaji tsoron Allah kuma kasan zaka mutu kaje ka tarar da Allah shin gaskiya ne ko k'arya ? Bash ne yatashi yana mita , ni dama ai ba'a yarda da maganata ya fice , a hanya ya had'u da Harun ya tsuguna ya dafe kansa , dariya Bash yasa yace ”d'an samari kana lokaci , bai sami damar maidawa Bash martani ba ya mik'e jiki na rawa yanufi part d'inshi , gado ya fad'a tare da sakin kuka mai ban tausayi .






Rurin dayaji wayarsa na yine yasashi cirota a cikin aljihu bai mai number ba 'amma tunda yafara zuwa sabon gurin aiki bari dai ya d'aga ,yana d'agawa yaji ance Malam Harun nine ma manjan ma aikatar ku , kasancewar baisan ko waye manaja ba yasashi gaisheshi cikin ladabi , mutumin da yakira sunanshi a matsayin manaja , yace ”inason mu had'u a gidan Zoo sabo wanda kasani ,hak'ika Harun ya firgita amma tunda umarnin manaja ne dole yabi , haka ya share hawayen fuskarshi ya mik'e yashiga toilet yayi wanka yana fitowa ya shafa mayukansa masu k'amshi ga turaruka ,yasanya ya d'auki k'ananun kayansa ya sa ya d'aura agogo , ya dauki wayarsa da key d'in motarshi ya fice , yana shirin shiga motar yaji wani kiran yasake shigowa , d'agawa Harun yayi cikin rawar jiki yace ”manaja ga ninan zuwa , cikin sauri ya shige motar yatada ta yanufi titi tafiya yakeyi amma gabanshi na fad'uwa ...✍️.






Vote me on wattpad
♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.


_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_




*Story and writing*
*By*


*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_


Zainabhabibu713 @gmail.com


Wattpad momislam2020




Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk




Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2






________________________________




*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com




https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w


_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


EPISODE 9 & 10


____Bash ne shida Fauziya a bedroom d'insa kwance take yana wasa da gashin kanta ,kanta ta d'aga tayi masa rad'a a kunne , mik'ewa naga sunyi ta zura hijab suka fice , Allah ka karemu da rayuwar dabbobi🤦‍♀️,zama yayi a cikin mota yana jiran fitowar Fauziya ,bedroom d'in momy taje ta sameta a zaune tana goge mirror , gefen gadon tasamu ta zauna ta rik'o hanun momy ta shagwa6e fuskar ,momy ce tace ”to shagwa6u ,meyafaru ?" cikin shagwa6a tace ”momy zanbi ya Bash shopping , momy ce ta dubeta tace ”mezakije siyowa , turaruka cewar Fauziya , to Allah ya tsare ki kula da kanki please ,oky momy natafi , tashige mota suka wuce , suna tafiya suna hirarsu wacce ni kaina banajin abinda suke fad'a ."




Umma na fito da abin gwajin cikin taga ya zana mata layi biyu , waro ido tayi cikin tuhuma tace ”Asma'u tsiyar da zaki janyo mana kenan?"shikenan na shiga uku cewar umma ,Asma'u dake zaune ta sunkuyar da kanta k'asa ,idanunta na kan shinkafar da take tsincewa tace ”Umma dan Allah kiyi hak'uri dan girman Allah , wani wawan mari umma tabata yayi dai dai da shigowar Malam , cikin alamun tambaya ya zauna yana ”cewa meyafaru kike dukan budurwa kamar wanan gaskiya bai kamata ba , hawayen da Umma take k'ok'arin 6oyewa ne sukayi nasarar zubo mata , Malam daya kasa gane me yafaru ya dakawa Umma tsawa yace ”bana san sha shanci ina tambayar ku meya faru amma duk cikinku babu mai bani amsa ? juyawa malm baya umma tayi tare dacewa ”to cikin shege Asma'u tayo , mik'ewar da Umma zatayi ta yanke jiki ta fad'i , Asma'u dake cikin tashin hankali ta nufi d'akin umma a d'an madai_daicin fridge d'insu wanda yad'an ji jiki ta d'auko ruwa a gora ta yayafawa Umma , ajiyar zuciya umma ta sauke tare da cewa wlh kinyi asara a rayuwarki duk tarbiyar da muka baki bin mazan waje yafi yemiki komai ko? Malam da zuciyarshi ta hassalo ya mik'e yashiga d'akinsa da yake ajiyar bulalai ya d'auko mai baki biyu yakuma d'auko mai baki d'aya ya had'asu yashiga , zabgawa Asma'u , saida yayi dukan ya gaji dan kansa yaga idanuwanta ne masu k'iftawa alamar taji jiki , zama yayi ta gefenta ya yarfe gumin goshin sa yace ”Asma'u yanzu irin tarbiyar da na baki kenan ?"sakaiyyar da zakiyimin kenan wlh bakiyi mana adlci ba kin cucemu kin 6atawa gidannan suna , saita bulalar yakumayi yana shirin zabga mata yace ”ubanwa yayi miki ciki ?" rufe bakinta tayi tana shirin yin amai , takasa mik'ewa dole ta kwararo amai a gurin , Malm ne yace ”tambayarki nakeyi kokuma kinason ink'ara miki bulalar ne , shiru tayi tak'i magana , Malam ko kamar jira yakeyi tak'iyin mgna ya zuga mata bulalar yana shirin k'ara kaimata na biyu ne tace ”malm kayi hak'uri zan fad'a maka , to ina saurarar ki cewar Malam ,Asma'u ce tayi jimm can kuma tace ”Harun ne , gyara zama Malam yayi yace waye Harun??? ,d'ane ga Alhaji Muntari yayan Alhaji Yusuf mahaifin Bashir ,Malam ne yace ”kina nufin kintsatsen yaronnan dashi kukayi watsewar ?"sunkuyar da kai k'asa tayi Malam ko saida yakuma yimata lilis sanan yafice domin yin sallah la'asr."








Da isar Harun gidan Zoo d'in ya hango wani bak'in mutumi ya rufe fuskarshi , yana shirin ciro waya yakira wanda yace ”yazo aka shak'e masa wuya aka sanyashi a mota sukabar gurin ."






Washe gari malm ta saka Asma'u a gaba wai saita kaishi gidan wanda yayi mata abin kunya , saida suka hau a dai daita sahu ta kaisu har zuwa anguwar , Malam ne yatsa a nesa da get d'in gidan yacewa Asma'u , taje ta k'wan k'wasa , tafiya take cikin sanyin jiki ta nufi get d'in , k'wan k'wasawa tashiga yi , megadi ne yace waye ?"Asma'u dake waje tace ”nice munzo gurin masu gidanne , to bari a sanar musu cewar mai gadi , dawowa yayi yace ”alhajin yana ciki wai kushiga , Malam ne yataso da sanyin jiki , shigewa sukayi tundaga k'ofar dazata sadaka da cikin gidan Malam jikinshi yayi sanyi dubada ganin yanayi dakuma tulin nerar da aka kashewa gidan yasashi tafiya kamar mai k'irga k'asa , suna isa k'ofar da zata sadaka da baban palorn gidan sukaja suka tsaya , jin alamun bud'e k'ofa ne yasa su Malam razana Fauziya ce ta fito cikin riga k'arama mai siririn hannu sai wando gajere fari tass , da ganinsu tasan ko suwaye , cewa tayi gurin dady kukazo ne ?"Malam na rawar jiki yace ”eh jagora tayi musu suka shiga k'ayataccen parlorn da yakuma tsinkawa Malam zuciya dan yana ganin idan yace ”Harun ne yayiwa ,Asma'u ciki tabbas bazasu yarda ba , da shigarsu suka tarar da momy zaune ta pillow a ciyanyarta zama sukayi a k'asa suka gaida momy , amsawa tayi cikin sakin fuska tace ”daga ina kuke ”ban ganeku ba , malm ne yace ”dama nazone akan maganar Harun ,Harun momy ta mai maita cikin fad'uwar gaba , me Harun d'in yayi ,kalon Asma'u Malam yayi yace ”wanan tarinyar ita k'adai Allah yabani a duniya , munbata tarbiyar dai dai gwargwado kuma tayi karatun islama tayi na boko tana sakandire , to ni inacan gurin neman abinda zamusa a bakin salati nadawo nasamu mahaifiyarta tana yimata fad'a yanzuma munbaro ta a gida tayanke jiki ta fad'i , dady dakejin komai yana daga saman step yace ”malm ban gane ba?" Malam ne yace "Harun ne yayiwa y'ar wajena ciki !!momy da taji gabanta yayi mumunan fad'uwa ta nuna Malam da yatsa tace ”kull Harun ba d'an iska bane walhi , Malam ne yace ”to gatanan dai insharri nayimasa Allah yasaka masa ,itace tagayamin , dady ne ya k'arasa saukowa yace is okay , kome akace Harun yayi bazanyi musu ba , amma kuyi hak'uri insha Allah dole ya aureta what!!! momy tace ”hankali a tashe wanan bazai yuwu ba wlh , haka kawai bawan Allah beyi Abu ba ace yayi ?" haka su Malam suka mike ,dady ne yaciro dubu ishirin 20k yabasu suka fice daga gidan."








Mom ce taketa gwada number Harun amma switch of yau kwana biyu kenan , Hajiya ce tace ”ki kwantar da hankalinki tunda yasami aikinnan baicika zuwa a kan kari ba , badan mom tayi na'am da maganar hajiya ba ta sai saita yanayin fuskarta , amma tanajin gabanta na yawan fad'uwa , alwalh tayi tazo ta tayar da sallah , addu'oi tadin kuwararo wa Harun na bud'i dakuma na kariya ta dad'e akan sallahya daga nan ta mik'e tanufi bed ta kwanta da tunani kala kala a cikin ranta."






Basma ce kwance tarasa meke kimata dad'i rabonta da ganin Harun a makaranta harta manta ko muryarshi bataji , momynta ce tazo ta zauna kusa da ita tana rarrashinta akan taci abinci koda ad'anne ,haka dai Momynta ta tilasta mata tutura abincin...✍️.


♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.


_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_




*Story and writing*
*By*


*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_


Zainabhabibu713 @gmail.com


Wattpad momislam2020




Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk




Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2




*_SALON ALK'ALA MINTA DA BANNE✍️_* 💃






________________________________




*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com




https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w


_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_




*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




EPISODE 11 & 12




____Wani d'aki aka shiga dashi mai duhu , magunguna kala² mutanen suka d'irka masa dan zasukai su hud'u , kwanciya Harun yayi bacci mai nauyi ya kwashe shi , bayan 30mins ,ya mik'e alamar jikinnasa yana yimasa wani iri sha'awa ce ko kuma buk'atar mace a kusa dashi ne yakasa ganewa , mutanen ne suka shigo jikinshi babu k'wari dan bazai iya magana ba bare har ya ta6uka wani abu , wanka suka masa suka ciro masa wani sabon kaya wando ne iya guwai wa sai riga irinta nigogi , haka harun ya koma kamar d'an arna , wani jan abu suka shafa masa a kansa tare da mik'o masa cup da Vijumilk a ciki da wani abu da suka sanya, jiki na rawa Harun ya kar6a yasha mik'ewa yayi yana layi yana cewa beb kizo gareni man , wata budurwa da alamu ba musulma bace "wani gaye da gefen , Harun yayi mata alamu da ido , tafiya tayi da wasu shegun kayan jikinta da kana ganinsu kasan shed'an yasami mazauni , kwanciya tayi a cinyar Harun tana shafashi had'i da sakar masa zazzafan kiss , daganan lamarin nasu ya k'azanta harta kai ga Harun ya cire kayan jikinshi sun yi zina shida wanan budurwa , nishi yake saukarwa kamar wanda yayi gudu , itako shu'umar cigaba tayi da kwanciya a jikinsa , a lokacin Harun bai dawo hayyacin sa ba , yana kwance a gurin tsirara ,haka suka d'aukeshi suka kaishi toilet suka yimasa wanka , kayansa wanda yazo dasu suka sanya masa ,mik'ar dashi sukayi suka sanyashi a mota , direct gidan su suka nufa dashi ,ganin babu kowa a tsakar gida suka turashi cikin d'akinshi suka kullo k'ofa ."








Zaune Asma'u take tana da ddna wayar da Bash ya siya mata , tuno hud'ubar da bash yayi mata tayi akan cewar ko me za'ayi mata karta sake tace shine yayi mata ciki tace ” Harunne , tausayin Harunne ya kamata , dukda bata sanshi ba amma yanada kya kyawan hali lokaci guda hankalin ta ya tashi tana tunanin anya tayiwa Harun adalci kuwa , amma kuma ai bata isa tace ” ba Harun d'in bane tunda maganar farko da ita ake amfani ,wani hawaye ne yazubo mata mai tattare da nadama ."






Bacci yakeyi ko motsi bayayi , sallamar da akayi ne tasa shi k'ok'arin farkawa , jin idanunsa sunyi masa nauyi yayi dak'yar ya bud'e idon ya d'orasu a kan wacce ta shigo , mom ce fuskarta sha6e sha6e da hawaye , tace ”Harun ina kashiga ?"Harun babu magana sai dai yana binta da ido , kiran drivern daya kawota tayi. yana shigowa tace ”ya temaka mata tasa Harun a mota , babu musu ya kama Harun mom ma ta rik'eshi suka nufi mota , direct hospital suka wuce da azama aka kar6e su sbda nan asibitin su momy ke zuwa kulawa aka fara bashi ta gaggawa , mom banda kuka babu abinda takeyi , wani doctor ne yafito hancinsa sanye da abin rufe hanci yace ”hajiya wanan yaron akwai matsala 'a tattare dashi , yasha abin da zai gusar masa da tunani , bayannan ba a bisa k'a ida yasha ba sbda abubuwan dayasha na maye dakuma na tada sha'awa suna neman salwantar da rayuwarsa, rik'e baki momy tayi tana kallon likitan harya gama jawabinsa ya fice .*








Dady ne yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login