Showing 9001 words to 12000 words out of 37025 words

Chapter 4 - JININ ABBANA BOOK COMPLETE TXT By Zainab Habib Mom Islam.txt

25 Jan 2025

2107

wata yarinya wace ake yayi y'ar India samari ke rubibi a kanta , kasancewar ta lula a soyayyar Bash yasata dena kula kowa sai shi gida ya kama musu mai kyau amma madai daici , sunkoma kamar mata da miji sosai suke k'aunar junan su ."






Yau watan bash uku yana cikin na hud'u ,a India , zaune suke shida baturiyar sa suna holewa a wani katafaren gurin wasa , daga shi sai gajeren wando iya cinyarsa babu riga , lol baturiya kuwa skirt ne dashi da babu duk d'aya sai wata riga mai shara_shara , Bash ne ya janyo hanunta tare da cewa "zomuje mu huta , bai gama rufe baki ba , abinda ya hango ne yasashi mutsike idanunsa ....






Asma'u tashiga watan aihuwa umma ce da malm a asbitin, dan babu wanda ya rako su , mutane sai tsegumi sukeyi , umma dai bata kula kowa ba ta me aihuwa takeyi , tun karfe takwas na safe Asma'au ke nak'uda gashi yanzu k'arfe hud'u na yamma shiru wuya kam Asma'u tasha , doctors ne suka cewa su umma inhar Asma'u ta wuce biyar na yamma to tiyata zasuyi mata , cikin tashin hankali malm yace ” wa umma to yanzu a ina zamu samo kud'in tiyatar nan , umma dake share hawaye tace ”wanan yarinya ta janyo mana abinda yafi k'arfinmu wlh...✍️.








Wow my pans mom Islam tana yinku kamar inda kuke yinta wlh kuna matuk'ar ji dani to nagode 🥰Allah yabar love muje zuwa 🤙.




♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.


_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_




*Story and writing*
*By*


*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_


Zainabhabibu713 @gmail.com


Wattpad momislam2020




Whtsapp group. https://chat.whatsapp.com/CehHXDP6kjk9GTiqw3BVfk




Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2






________________________________




*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com




https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w


_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




EPISODE 17 & 18




____Bahijja Bash ya hango ita da Emanuel ga k'aton ciki a gaba , rik'e suke da hannun juna suna tafiya suna dariya , daka gansu zakasan suna cikin farinciki , kasa kawar da fuska Bash yayi yana dad's k'arewa Bahijja kallo ,shin ta yarda ta d'auki ciki da wanan k'aton arnen tabb Bash yace ”yayinda ya mik'e ya nufi gurinsu , da zuwanshi yace ”Bahijja ?"ko kallon sa Bahijja batayi ba ta maida kai gefe tana rik'e da hanun Emanuel , Emanuel da hankalinshi yayi gaba ya sunkuceta suka bar gurin , Bash kuwa yashiga tashin hankali , sosai ,a ranshi yana cewa tare mukazo ta gujeni taje ta d'auki ciki da k'aton arne , budurwar shi ce ta matso kusa dashi tana shafa masa kai tace ”meya faru ne my man , idanunsa da sukayi Ja jawur yace ”bb komai zomutafi , after dree budurawar tasa suka wuce gidan nasu , da shigarsu bashi ya bud'e kwalbar beer sha yakeyi kamar an aikosa , sanda ya cika cikinsa tabb da giya sanan ya kwanta yafara surutai marasa kan gado ,budurwar sa ce ta rungumo shi tana tambayarshi meyasa zesha over ?"ina Bash yayi nisa bayajin kira ,wata gyatsa yake fitarwa mai wari sosai , da haka ta gyara masa gurin kwanciya ta barshi a gurin ."








Ana shirin shiga da Asma'u d'akin tiyata ,tafara yunk'urin aihuwa , malm da umma ko sai adu'oi suke jero mata suna daga waje dan ba'a barsu sun shiga ba , cikin ikon Allah ta haihu nurses ne suka gyra jaririn tare da yimasa wanka , jin kukan jin jiri yasa umma nufo d'akin ,lokacinma angama gyara komai saura mai jego tayi wanka ."








Malam ne zaune a masallaci yana adu'ar Allah yabasu kud'in biyan asibiti , ya shafa adu'ar gami da mik'ewa , ya nufi cikin asibitin , samun Asma'u yayi tana kwance ,lokacin tayi wanka ."




Harun ne kwance a hospital likitoci sun rasa gane kan ciwon sa anyi gwajin anyi amma duk shiru babu sakamako , kuma har yanzu jini zuba yakeyi kuma ana k'ara masa jini , mom tayi kukan harta gaji , hajiya ko kullum adu'a take kwara rowa Harun na Allah yabashi lafiya , suna zaune a kan tabarma sukaji sallamar momyn Bash cikin fara'a Hajiya da mom suka tareta ,ledace k'atuwa a hanunta cike da kayan mar mari , gakuma food flaks na abinci na farfesun kifi , gaisawa sukayi momy ta tambayi jikin Harun suka cemata da sauk'i , kasancewar doctors sunrufe k'afarsa babu wanda zai gane sai an gaya masa , momy ta d'an dad'e a hospital d'in daganan tayi musu sallama tare da ajiye musu ledoji ."




Kwance take tana bacci ,wani gun guni da taji ne yasata yin azamar mik'ewa da tsohon cikinta , agogo ta duba k'arfe 3pm na dare ,duba gefenta tayi babu Emanuel , a tsorace ta mik'e saboda jin wani gurnani dake tashi a gidan , wata k'ofa da tunda tazo gidan bata ta6a shigarta ba anan tajiyo gurnanin , tafiya yakeyi sad'af sad'af har ta iso k'ofar ,ta jikin wani huji na k'ofar ta lek'a , hango Emanuel da jajayen kaya tayi da wani k'o k'o a hanunsa bakinsa duk jini , jin kanta tayi yana juyawa saboda tsabar firgici , da sauri ta dawo ta kwanta cike da firgici ."






*GIDAN BASH*


Ya watsake sosai ,wanka yayi yasa kayansa masu kyau ya fito parlor ganin baiga budurwar tashi bane yasashi k'wala mata kira , ko ina ya duba babu ita babu alamar ta , wayarshi ce tafara ring ganin number Asma'u yasashi jan tsaki yace ”to kuma menene ?"cikin shagwa6a tace ”na haihu ina asibiti kuma gobe za'a sallamemu babu kud'i , Bash da yanzu haushinta yakeji , yashi cewa nawane kud'in ,dubu d'ari biyu cewar ,Asma'u , kan uba ubanwa kika mayar mai gonar kud'i bakida hankali ne baki da tunani ne , kokuma wani naki ya ta6a ciyar dani ? Asma'u da muryarta bata fita sosai tace ” Bash ,wlh kayi yunk'urin wula k'antani wlhi zan tona asiri , cikin zafin rai yace ”ki tona mana , y'ar talakawa kawai , wanan furucin ba k'aramin k'onawa Asma'u rai yayi ba , cikin hassala tace "wulak'ancin ya isa haka whattt, ki san dawa kike magana ,inace dai kud'i ne to zan turo turomin account , hmm (halinka da babu zuciya) tace ”toh ."








*NIGERIA*


Zaune suke su biyar kowa da bak'in kaya a jikinshi , wanan budurwar da sukayi sex da ita , duban wani mutumi tayi tace ”oga yakamata a kawo min wanan saurayin , wata muguwar dariya sukasa cike da jin dad'i oga yace ”lokaci muke jira karki damu nan bada jimawa ba ,wani mutum ne yashigo da jar hula yana tafiya yana dariya yace ”nifa na matsu nima yaron make jira , suka kuma shek'ewa da dariya tare da nuna video d'in da sukayi masa lokacin da suke sex ,fuskar Harun tafi fitowa sosai , oga ne yace ”duk da wanan videon da mukeda shi zamu k'ara had'awa da namu ."




Sumaiya ce zaune a parlor tana kallo a TV , Abbi ne yafito daga d'akin momy yace ”daughter ya kukayi da Mubin ?"sunkuyar da kai tayi k'asa tace ”Abbi yace ”baya sona, ehe shida bakinsa ya gaya miki hakan ?"eh Sumaiya tace ”tana girgiza kai alamun tabbatarwa , Ammi ce ta fito sanye da wani dakakken less mai adon duwatsu , zama tayi gefen Abbi tace ”ni a ganina yakamata mu bata za6i ko ?"Abbi ne yace ”tunda wancan yaron ya watsa mana k'asa a ido ai ba naman kai mukeyi da ita ba , ita dai Sumaiya na zaune bata k'ara magana ba , Abbi ne yace ”daughter ya kamata acikin mane manki ki fitoda mijin aure , Sumaiya ce ta shagwa6e fuska tace ”Abbi wlh sekuma ta mik'e ta ruga da gudu tana dariya , suma su Abbin dariya sukeyi ."






Momy ce zaune ita da dadyn Bash suna hira , kwanciya tayi a kan cinyarsa tace ”dan Allah kaje ka gaida Harun a hospital bashida lafiya , wata uwar harara ya daka mata tare da cewa shid'in kun had'a dangi ne dashi , kokuma ,yaron d'an uwanki ne ?"momy da ranta ya 6aci tace ”koba yaron d'an uwana bane ai mahaifinsa amana yabar maka , cikin fusata dady yace ”to bazan jeba ya mutu ,wayasani ma ko a yawon zinace zinace ya kwaso cutar , momy da hawaye ke ambaliya a fuskarta tace ”yakamata kasani Allah ne yayi mutuwar Muntari kuma kai.....wani mahaukacin mari dady ya wankawa momy tare da k'ara mata wani , da gudu ta shige bedroom d'inta tasa key ,takifa kai a gado tana kuka ,mai tsuma zuciyar mai sauraro ."






Harun dai na nanan inda yake sauk'i sai na Allah , dare babu bacci sai da rana amma daga Hajiya har momy babu mai bacci da daddare , adu'oi kan ana yinsu sai dai har yanzu Allah bai nufa yasami lafiya ba amma akace mai rai baya fidda rabo da samun rahamar ubangiji."






Alert ne ya shigo wayarta na dubu d'ari , tana dubawa ta buga tsaki umma dake gefe tace ”keda waye ?"Asma'u tace ”nida wancan shegen ne , Bash , umma ce tasa dariya da alamu dariyar takaici ce tace ”ai tare kuke kuma wlh Allah ki kiyayi had'uwarki da ubangiji ,nidai nayimiki tarbiyar iya iyawata amma dare d'aya kin watsar da komai , umma ta fashe da kuka , Asma'u ko ta6e baki tayi ta kawar da kanta gefe ....✍️.




Vote me on wattpad


Please share👏
♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.


_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_




*Story and writing*
*By*


*ZAINAB HABIB*
_(Mom Islam)_


Zainabhabibu713 @gmail.com


Wattpad momislam2020




Telegram
https://t.me/joinchat/IaKr804dfndik1e2




My whtsapp group
https://chat.whatsapp.com/J7cmS5wP5fBHAnF0ut8905


Bakandamiya Mom Islam Habib


Facebook Mom Islam




*✨GODIYA TA MUSAMAN GA YAR MALAM NAGODE DA NUNA SOYAYYAR HAK'IK'A INA YINKI OVER WANAN SHAFIN NAKINE NABAKI SHI KYAUTA ✨*




________________________________




*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com




https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w


_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




EPISODE 19 & 20




____Emanuel ne zaune da jayen kaya yana kur6ar abu wani jan abu , ya dubi shugaban su yace ”nidai ayimin rai kar a kashe ni ,zanyi k'ok'ari inga na kashe jaririn da Bahijja zata haifa ,shugaba ne ya shek'e da dariya yace ”kasan yanzu saura mutum uku ka gama koh ?" cikin rawar jiki Emanuel yace ”haba kuyimin rai a ina zan sami mutane kuma na jikina guda biyu yanzu , banida uwa banida uba duk nabawa dodo jinin su yanzu kuma kuce sai na k'ara muku ina , wata tsawa da shugaba ya daka masa ne yasashi tsorata , shugaba yace ”kasani kafin ka shiga k'ungiyar mu sai da kayi mana alk'awarin bada jinin mutum biyar yanzu kana so kace ,zaka yiwa dodo k'arya ko kuwa , a tsorace , Emanuel ya ce ”a 'a zan baku nayi alk'awari ."




Fans jinin wa Emanuel zai bada bayan jinjirin Bahija da yace ”zai bada muje zuwa.


Anbiya kud'in hospital dubi goma , su Asma'u sun dawo gida cikin k'oshin lafiya itada jaririn ta , ranar suna malm ya rasa wane suna zai sanya masa kwai ya Sanya masa Muhammad ,ranar suna mai jego ta tara k'awayenta , umma ko rasa wazata gayyata tayi sbda bata gaiyaci kowa ba kuma babu wanda ya lek'o gidan haka akayi sunan babu wani kaya da Asma'u tasamu dama umma tace ”mata duk mai cikin shege bazai ga dai_dai ba ."






Hutun Bash ya k'are yau jirginsu ya d'aga zuwa Nigeria , babu wanda ya gayawa gashinan zuwa kawar surprise ya shirya yiwa su dady , da saukar su ya trolley d'insa ya ya fita daga airport d'in ya nufi titi , motar haya ya hau ya nufi gidan su , mai gadi najin k'arar mota ya wangale get ya d'auka ko anyi bak'i ne , hango Bash yayi ya fito daga mota yana mik'awa mai mota kud'i , gyara zaman jakar dake rataye a bayansa yayi ya nufi cikin gidan , mai gadi ne yaketa jera masa sannu amma ko kallonsa bai yi ba ya shige ciki , da shigarsa ya bud'e k'ofar d'akinsa da take waje nesa da ta momy , samun d'akin yayi fess dashi babu datti kasancewar momy ba mace mai son k'azanta bace , kayan jikinsa ya fara cirewa yana gamawa ya shige toilet bayan yayi brush ya kunna ruwan d'umi yayi wanka , ya fito d'aure da tawul a jikinsa , yafara rawa , mayukansa masu k'amshi ya sa sanan ya fesa turarukansa had'i da ciro kayansa a drowa , riga da wando tsadaddu masu kyau , taje gashin kansa yayi ya sa takalmi ya fito zuwa part d'in momy ."






Samunta yayi zaune ita k'ad'ai a parlor tana kallo ta zuba tagumi , k'arasawa yayi babu salama yace ”my momy oyoyo ya rungumeta , momy ce ta share hawayen da suka kwaranyo mata , Bash sam bai lura da halin da momy ke ciki ba , bubuga bayansa momy tayi tace ”my son babu sanarwa ?"dariya yayi yace ”momy surprise nayi muku , murmishi momy tayi tace ”kazo lafiya ya karatu , alhmdulilh my momy nasha karatu bakiga na rame ba ? kallonsa momy tayi tace ”naga dai kayi k'iba kuma ka k'ara fresh sosai , dariya yasa yace ”momy yunwa nakeji sosai , mik'ewa momy tayi ta je kitchen tasami y'ar aikinta na soya doya ,tace ”please had'awa son shayi karkisa madara , kasancewar bayaso , to Hajiya ,cewar y'ar aikin , dafa shayin tayi da citta da kaninfari da na'ana da lemon grass ,da lemon tsami kad'an ta d'auki jug da tirai da small spoon ta nufi parlor , samun Bash tayi a zaune kansa na kwance a jikin momy tayi sallama ta ajiye a dining , mik'ewa yayi ya nufi dining d'in yasa zuma yafara sha ."






Yau jikin Harun da sauk'i sbda adu'oi da mom da Hajiya ke kar6o masa daga gurin wani malami ,amma har yanzu jinin nanan yana zuba kad'an , yanzu kam yana cin abinci sosai kuma suna hira da mutane , sallama aka kuma rubuta musu suka koma gida , wani doctor yana zuwa yana wanke masa ciwon , yanzu ba laifi mom ta rage tunani sbda ganin jikin Harun yayi sauk'i , momyn Bash kuwa bata sake zuwa ba ."








*********************
Mom da Hajiya ne zaune a kusa dashi suna hira ,Harun ne yace ”barin tashi yau in zaga ,Hajiya ce tace ”mutumin da bashida k'afa ina shi ina yawo , kwai gani sukayi Harun ya mik'e k'afar tadena zubar da jini , farinciki da nishad'i a zuciyarsu mom da Hajiya ba'a magana , kowane na cikinsu sai masha Allah yakeyi , Harun kuwa dariya ya kama yi yace ”yaukan naji sauk'i zuwa gobe zani ma aikata ko makaranta , mom ce tace " no kabari zuwa next week in ka kuma jin sauk'i saika tafi ,baya San yiwa mom musu haka ta hak'ura , jinya ta k'are ."




Anya warkewar Harun babu lauje cikin nad'i🧏‍♀️.


Dady ne yayi sallama , momy dake zaune ta amsa da wa/alaikumusalam sanu da zuwa , ywwa dady yace ”a tak'ai ce , har yanzu fushi kikeyi dani ?" cewar dady , hawayen da momy ke 6oyewa ne suka zubo ta kawar da kanta gefe , rungumota dady yayi tare da rik'o hanunta ya mik'ar da ita suka haura sama 😉base na bisu ba."






Fauziya ce ta dawo daga hutu driver ya d'aukota sbda a boarding school take , tana hango Bash yayi shirin fita ta fito daga mata ta rungume shi , suka shige ciki , dady da momy da suka sauko yanzu suka fara dariya suna cewa oyoyo daughter , shiko dady cewa yayi shikuma Bash yaushe ya dawo?" momy ce tace ”jiya nima ko gayamin baiyi ba , dady dake dariya yace ”to muje dining muci abinci , Bash dake rik'e da mukullin mota yace dady nidai zani anguwa yanzu zan dawo , okay to sai ka dawo , momy ma Allah ya tsare tace ”masa , anguwarsu Asma'u ya nufa , da isarsa anguwar ya tsaya can nesa da gidan kiranta yayi a waya , cikin mamaki da sauri ta d'aga , tace ”Bash yaushe a gari number Nigeria nagani , cikin rashin fara'a yace ”in kinada lokaci kizo yanzu gani a waje , to tace ”batare da ya k'ara magana ba ya kashe wayar ."


Yamma ce kuma umma na zaune a tsakar gida , fitowa tayi da abin kwashe shara a hannunta , tana tafiya kamar mara gaskiya , umma ce tace ”bance kidena fitowa ba?" cikin in ina tace ”zan zani zan zubar da shara ne ,ko kallonta umma batayi ba Asma'u ta fice ,da hijab a mara ,tana fitowa ta saka hijab d'in , duk lek'en da takeyi Bash na kallon ta har lokacin da tasa hijab , cikin zuciyarsa kuma ranshi na k'una sosai wanan kucakar yake kulawa jibeta talauci yayi mata yawa kash , gyara zamanshi yayi yana shafa sumar kanshi , ganin bai fito a motar ba yasata bud'e murfin ta shige ,da fara'arta tace ”sanu da dawowa ka dawo lafiya?"lafiya Bash yace "tare da cewa ”nazo gurinki ne akan maganar da mukayi dake dakuma wace dadyna ya gayawa mahaifinki , so yanzu sonakeyi asan inda za'ayi , ki auri Harun , Asma'u ce ta dafe k'irji tace ”Harun!!! eh Bash yace ”alamun babu wasa a tattare dashi , gaskiya bazan iya ba haba ,Bash kamar ba musulmi ba ?" har Bash ya d'aga hannu zai kaimata mari sai kuma ya fasa ya dunk'ule hanunsa , Asma'u ki fahimceni karkiyimin mumunan fahimta indai kud'i ne karki damu ko nawa ne zan baki , Asma'u da jikinta yayi sanyi ta ce zanyi tunani , ta bud'e murfin motar zuciyarta babu dad'i ta fice ...✍️.








Kufayi hakuri da salon alk'alamin nawa sbda duk mai karanta book dina yasan salon sa 🥰 so da sababbi dakuma masu bibiyarsa kuyi hak'uri Ku biyoni insha Allah zanyi kokarin dena Ja muku rai 🤙.






comments and sharhi👌
♦️♦️😭JININ ABBANA!!😭♦️♦️.


_Labari mai d'auke da tsan tsar zalunci cin amana dakuma nishad'i_




*Story and

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login