Showing 27001 words to 30000 words out of 59211 words
sarauniya. Sonki ne kawai ke neman zubar dani amma ke kina ɗaukar komai wasa”.
Shiru ta masa bata tanka ba. Shima sai ya bar zancen ya kama wani daban. “Ni kam banga Zizaah da Aneesa ba, ko basu san baki da lafiya bane?”.
Kansa ta jinjina masa alamar eh.
“A gaskiya ya kamata su sani. In sha ALLAHU anjima zan kirasu na sanar musu kuwa”.
“Ni dai ban saka ba”.
Idanu ya ɗan waro waje. “Saboda mi?”.
“Ba saboda komai ba, kawai dan mutum na ciwo sai anta talla da shi. Yanzu miyyasa ka kai Nene gida ma?”.
“Saboda taje ta huta. Ba su Didi na zuwa ba”.
Hararsa ta ɗan yi, kafin tace, “To idan kuma ina buƙatar wani abu fa kafin su suzo?”.
“Ba gani ba sai ki sakani nai miki. Ai shiyyasa nazo nan na zauna a madadin Nenen. Faɗi mi kike buƙata gimbiyar Rafeeq?”.
Baki ta buɗe zatai magana tsulum sai ga sallamar Yazeed. Kafin ma su gama amsashi ya riga ya shigo. Kallon kallo sukaima juna shi da RK ɗin sai kuma kowa ya janye cike da basarwa. Takowa yazeed ɗin ya ƙarasa yi ta ɗayan side ɗin. Saboda neman magana sai ya zauna a bakin gadon kusa da ƙafafun Maanal. A hankali ta matsar da ƙafafun nata dake cikin bargo, dan RK ya wani zubama ƙafafun nata ido kamar mai kallon television duk da a lulluɓe suke a bargon. Cikin dauriya ta gaida Yazeed. Ya amsa mata idanunsa kafe a kanta....
“Yaya jikin naki?”.
“Na samu sauƙi Yaya. Ya aiki?”.
“Alhamdullahi. Tunda kin samu sauƙi sai sallama kenan ko?”.
Maimakon amsa saita sakar masa ɗan murmushin yaƙe kawai. Abinda ke hannunsa ya miƙa mata. “Ga abinda kikace kina so, shine maimakon ki sanar min kika kama faɗama su Shahidah ko? Bana gaya miki duk abinda kike buƙata yanzu ki sanar min ba. Domin nine da hakkin yimiki shi ai, kwana nawa ya rage mana zama ma'aurata”.
Kanta kawai ta jinjina masa da faɗin, “Nagode”. Yayinda RK ya saki wani ɗan iskan murmushi yana sake yin balance a kujerar. Sai kuma ya wani laɓe baki yana kauda kansa. Duk Yazeed na lure da shi, dama kuma yayi furucin domin shi ne.
“Ina Nene?”.
“Taje gida bata jin daɗi”.
“Ayya ALLAH ya bata lafiya. Ai tana ƙoƙari ma ga jikin girma. Su su Shahidah fa?”.
“Basu ƙaraso ba, suna hanya dai sukace”.
“Okay yayi”.
Ya faɗa yana zaro wayarsa da ake kira. Ɗagawa yay tare da kaiwa kunne, sai kuma ya miƙe saboda masifar da Mamma ke masa daga can, dan har ita Maanal ɗin taji furucinta na farko ma. Sassanyar ajiyar zuciya Maanal ta sauke ƙasa-ƙasa dai-dai Yazeed ɗin na fita. Hakan yasa RK tuntsurewa da wata dariyar wulaƙanci. Kallonta ta maida garesa cikin mamaki. Shiko ya wani ɗage mata gira cike da neman rigima ya ce, “Amma dai kina matuƙar tsoron wannan yayan naki fa. Irin wannan sauke ajiyar zuciya haka”.
Ƙin kulashi Maanal tayi, sai dai maimaita kalmar tsoron daya ambata tanama Yazeed ɗin take a zuciyarta. Shima bai sake cewa komai ba ya kawo hannu zai ɗauki abinda Yazeed ɗin ya bata tai saurin ɗaukewa tana ɓata fuska.
“Wai kai idan baka shiga rayuwar mutum ba da abinda ba'a sakaka ba baka jin daɗi ne halan?”.
“Oh haka kike fassarani ashe?”.
“Hummm”.
Kawai tai shiru. A ransa yace miskilatu kenan. Magana fal cikinta amma bata son yi. A fili kam zaiyi magana sai ga Yazeed ya dawo. Bai fasa ba ya cigaba da faɗin, “Birthday na ya kusa mi zaki bani as gift?”.
“Humm”.
Maanal ɗin ta faɗa idonta akan Yazeed daya iso gaban RK ɗin rai a ɓace. Shi kuma yayi kamar bai gansa ba. Cikin fusata ya ce, “Malam ina son magana da kai”.
Sai lokacin RK ya dubesa. Sai kuma ya nuna kansa cike da rainin wayo wai shi? A kausashe Yazeed ya ce, “Eh”.
“Okay to Bismillah ai gani. You are free zaka iya maganarka kawai”.
“Ba'a nan ba”.
Yanda yay maganar a fusace ya saka Maanal dake saurarensu kallon Yazeed ɗin a karo na farko. Sai kuma ta kalla RK dake wani shegen murmushi baida alamar motsawa balle aje ga batun tashin. A hasale Yazeed ya sake buɗe baki zaiyi magana Shahidah da Amaal sai mijin Shahidah ɗin sukai sallama. Dole ya haɗiye maganar yana mai furzar da huci, sai kuma ya juya suka fara gaisawa da mijin Shahidah. Shima RK miƙewa yay yana amsa gaisuwar su Amal, kafin ya juya ga mijin Shahidah ɗin shima suka fara gaisawa. Daga haka ya fice a ɗakin. Hankalin Manaal naga su Amal Yazeed shima ya sulale ya fita, sai da ta ɗago da nufin yin magana dashi kawai taga wayam. Waige-waige ta fara cikin mamaki, cikin tsokana Mijin Shahidah ya ce, “Oh in dai samarinki ne ai sun fice auta”.
Fuska ta ƙwaɓe kamar zatai kuka ta ce, “Kai Uncle Sadeeq”.
Dariya suka sanya mata su duka....
★★★
Sam RK bai san Yazeed na bin bayansa ba. Dan hankalinsa ma nakan wayarsa fuskarsa da murmushi saboda saƙon da yake karantawa. Jin ansha gabansa ya tsaya cak tare da ɗagowa. Kallon ido cikin ido sukaima juna shi da Yazeed ɗin kaikace zakuna ne jirace da juna a filin daga.
“Doctor ina son maka gargaɗin farko da ƙarshe akan yarinyar nan”.
“Saboda mi?”. RK ya faɗa yana tsatstsare Yazeed da ido. Shima Yazeed ɗin cikin dakiya ya bashi amsa da, “Saboda ita ɗin matar dazan aura ce. Akwai ranar aurena akanta. Kasan kuma nema akan nema haramun ne sai dai idan kana da ƙarancin ilimin addini ne kuma na maka ƙarin bayani yanda zaka fahimta”.
Maganar Yazeed ta ƙarshe-ƙarshe ta zafi RK, amma sai ya danne yama saki murmushi da ƙoƙarin raɓashi alamar zai wuce abinsa. Cikin zafin nama Yazeed ɗin ya sake shan gabansa. Kallonsa RK ya sake yi yana ƙoƙarin danne ɓacin ransa, dan shima fa ya iya zuciyar nan, dalili ne kawai ke sakashi danne tasa ba tsoro ba.
“Yazeed why???”.........✍️
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_
ب
ِ
س
ْ
م
ِ
الل
َّ
ه
ِ
الر
َّ
ح
ْ
م
َٰ
ن
ِ
الر
َّ
ح
ِ
يم
_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖1️⃣5️⃣
........“Why kake son mu dinga kasancewa a wannan yanayin ni da kai?. Ina fa ganin girmanka ne matuƙa shiyyasa kaga ina barin komai a yanda yake. Please respect your self mana. Kai namiji ne, nima namiji ne kowa ya cigaba da gwada sa'arsa mai rabo sai ya ɗauka a cikinmu. Dan har yanzu banga dalilin da zaisa na iya janyewa ɗin ba”.
“Haka kace?”.
Murmushi RK ya sakar masa da kashe ido ɗaya kawai ya zagayesa ya bar wajen. Hakan ya sake hasala Yazeed matuƙa. Tabbas shi ɗin mutum ne mai haƙuri da dattako. Amma yana da tsananin kishi akan abinda yake so shiyyasa yake zafafawa akan al'amarin Maanal matuƙa. A zuciyarsa yake tunanin dolene ya koyama guy ɗin nan hankali, dan haka a daren yau zai wuce Kaduna dan gara ya zauna ayita ta ƙare shi da Daddy. Mamma dai ce matsalar zai rumtse ido kawai komai ma ya faru daga baya yasan zata sakko ta yafe masa.....
Kiran daya shigo masa a wayane ya katse tunaninsa. Ganin ƙanwarsa Badiyya ce kamar zai share sai kuma dai ya ɗaga. Yana kai wayar kunnensa ya janye da sauri saboda abinda ta sanar masa.. Yana sauke wayar daga kunnensa sai kuma ga text massage ɗin Ammie itama ya shigo masa. Ai bai tsaya sauraren komai ba yabar asibitin......
_____________
“Wai Daddyn Yazeed mikake nufi da ni ne a gidan nan? Katafi kai da matanka holewarku bance komai ba, ka dawo ranar girkina kace baka buƙatar komai daga gareni. Na zuba maka ido nan ma, washe gari Basariyya tai girki ita jiyama haka. Yau kuma ƴar sonka ta amsa”.
Idan kujerun dake falon sun motsa Alhaji Usman ya motsa kenan. Tamkar ma bai san da zaman Hajiya Yaya a falon ba yake kallon labaransa yana shan fruits da Ammie ta haɗo masa. Hakan ne ya sake sakata fusata, cikin matuƙar ɓacin rai ta ja remote ɗin dake a Centre table ta kashe tvn gaba ɗaya. Karo na farko ya juyo ya kalleta fuskarsa a matuƙar haɗe. Itama kallon nasa take tana huci.
“Sadiyya bar falon nan kafin ranki yafi haka ɓaci”. Har cikin ranta taji tsoron fitar kakkausar muryarsa. Amma sai ta dake dan gara dai ayita ta ƙare. Itama a fusacen ta ce, “Babu inda zanje wlhy. Dan nifa na gaji da abinda ake min a gidan nan. Ubana ya dasa inuwa wasu banzaye suzo su zagayeta domin sha suna min gadara.”
“Hummm”.
Ya faɗa kawai yana miƙewa. Bedroom ɗinsa ya shige tare da rufo ƙofar ya barta a falo tana jidali ita kaɗai. Haka dama yake mata, ita kuma sai take ɗauka kamar tsoronta yake ji ko tafi ƙarfinsa ne. Bata san yana hakan bane kawai saboda wani dalilinsa daban, amma badan gorin da take masa ba akoda yaushe. Tsautsayi rabon faɗan nan ya koma kan Ammie sai gata ta shigo sashen batare da tasan Hajiya Yaya na nan ba. Aiko ina wuta Hajiya Yaya ta saka Ammie, nanfa ta shiga mata gori da cin mutunci. Ita dai Ammie komai batace da ita ba ta ajiye basket ɗin hannunta dake ɗauke da kayan abincin maigidan a saman d/table. Rashin tankawar da batai ba itama sai ya sake fusata Hajiya Yaya, a matuƙar zafafe ta nufi d/table ɗin da niyyar kifar da kayan abincin Ammie ta tare tana girgiza mata kai.
“Kiyi haƙuri Hajiya kar kiyi haka dan ALLAH. Koba komai shi ɗin abincine, yana da darajar da wulaƙantashi kuskurene takowace irin fuska”.
“To mama Asiya shawara kike bani ko umarni?”
“Babu ko ɗaya da nake baki a ciki kiyi haƙuri”.
“Anƙi ayi haƙurin munafuka kawai, kullum sum-sum ita a dole ta ALLAH amma dafinki yafi na baƙin kumurcin maciji. Kin mallake min miji da bin bokaye, kin cika mana gida da agololi har kina shirin ganin kin mannawa ɗana. Wlhy Asiya sai naga bayanki a gidan nan”.
“Idan ta juya ba.....”
Alhaji Usman daya fito ya faɗa a zafafe. Juyowa sukai su duka suna kallonsa. Fuskarsa a ɗaure ya cigaba da faɗin, “Idan ta juya kam zakiga bayanta Sadiyya. Amma kiga bayanta akan zama dani har gaban abada bazakiga hakan ba da iznin UBANGIJI. Asiya ajiye abinci, idan kin isa dan ALLAH ki zubar da shi ni kuma wlhy yau sai na baki mamaki irin wanda baki taɓa zato ko tsammani ba. Ke Sadiyya bafa wai ina tsoronki bane a gidan nan. Karki ƙureni a wannan karon wlhy idan ba hakaba zakiyi matuƙar dana sani.”
“Dana sani na nawa kuma ai nayi dana sani tun daga randa na amince na aureka....” sai kuma ta fashe da kuka “Kai dai burinka kullum ka wulaƙantani a ƙasan ƙanwar bayana koma nace sa'ar ɗana ko, shike nan ga gidan nan na bar maka, ka kwaɗata ka cinye dan ALLAH” fuuuu ta fice daga falon. Tsaki yaja kawai tare da juyawa zai koma bedroom ɗinsa. Hankalin Ammie ne ya tashi, cikin sauri tabi bayansa, kusan a tare suka shigo bedroom. Jin yanda ta faɗo masa ya sashi juyowa yana kallonta.
“Dan ALLAH ka bita karta tafi ɗin da gaske, na roƙeka Abban Hameed. Bana fatan kowacce matsala ta kasance tsakaninka da matanka a dalilin.....”
“Asia!”.
Ya faɗa cikin katseta. Kanta ta shiga girgiza masa sai ga hawaye. Zata sake magana kawai ya jawota jikinsa ya rungumeta. Sosai take bashi tausayi, mace ce mai haƙuri da juriya akan komai na rayuwa. Tana da kawaici da saurin sallamawa koda abu zai cutar da itane ko zuri'arta. Duk abinda kaga ta masa musu a kai to ka duba wannan abun kuwa. Komai yace ita mai biyayya ce a gareshi ko bai dace da ita ba. Wannan halayen nata ne suka mamayesa cikin ƙanƙanin lokaci yake jinta ƙololuwa a saman matan da ya aura tun yana da jajayen sawunsa. Hanata duk wata damar sake magana yayi, ba kuma ta sake yi ɗin ba ta haƙura saboda ita ɗin mai biyayyace a garesa. Fitowarsu falo babu jimawa tana zuba masa abinci sai ga Asalamiyya ta shigo tana kuka ita da Basirah.
“Daddy dan ALLAH ka kazo ka hana Mamma tafiya. Gata can ta haɗa kaya zuwa mota zata tafi Daddy”.
A birkice Ammie ke kallonsu, sai kuma ta yunƙura jikinta na rawa zata nufesu. Cikin bada umarni Daddy da tun kallo ɗaya da yay ma su Asalamiyyar bai sake ba ya dakatar da ita. “Asia koma ki zauna”.
Kallonsa Ammie tai kamar zata fashe da kuka. “Daddyn Hameed kana fa jin abinda suke faɗa”.
“Cigaba da zuba min abinci nace. Ku kuma ku bar falon nan!!!”. Ya ƙare maganar a tsawace. Zabura sukai saboda tsawar ta shigesu. Har rige-rigen fita suke daga fallon. Kallonsa Ammie ta sake yi zatai magana ya ɗaga mata hannu. Dole tai shiru ta cigaba da zuba masa abincin hannunta sai rawa yake. Tsaf yake kallon yanda hannun nata ke rawa amma sai bai tanka ba. Tana gama zuba masa abincin yaja ya fara ci hankalinsa kwance.. Abu ya ishi Ammie ta rasa ina zata kama, sai kallon Daddy kawai take. Can dai ta jawo wayarta ta shiga rubutama Yazeed text massage.....
______________★
Yau da wuri Nene ta dawo asibitin. Dan haka ta kora su Amaal gida suma saboda mijinta daya shigo Abuja. Daga nan ma asibiti da yazo ya duba Maanal ɗaukar Amal ɗin yay suka wuce masaukinsa. Itama Shahidah da mijinta yazo sai suka wuce kawai. Hakan yasa Maanal ta kasance daga ita dai Nene a ɗakin. Sai kuma duk kaɗaici ya isheta. Dan Nene da zaran tayi sallar isha'i zakaga ta fara gyangyaɗi abinta. Gashi babu waya a hannun Maanal ɗin, tana Kaduna aka barta, bakuma a kawo mataba har yanzu. Shiyyasa ma taima Shahidah maganar a sayo mata kayan zane-zanen ta dan ta iya sosai, shine Yazeed yaji ya hana Shahidah siyowa shi ya sayo mata. Tun ɗazun daya kawo mata su ta ajiye bata sake bi takansu ba. Sai yanzu ta jawo ledan ta fiffito da su. Komai da take buƙata akwai, harma da wanda batace a sayo ba ya sayo. Dan haka sai ta gyara zama kawai ta fara zanenta dan shine hubby nata tun tana yarinya. Maanal ta masifar iya zane ta yanda idan ta zana abu sai ma ka ɗauka ba itace ta zana ɗin ba. Da farko ɗakin jiyyar tata ta fara zanawa harda Nene dake zaune a kujera tana famar gyangyaɗi, sai ita kanta a yanayin da take zaune. Koda ta gama taga komai ya mata sai ta tsinta kanta kuma da fara zana agogo. Abinda ta jima batayiba a rayuwar zanenta kenan. Ta zana guda biyu tana akan na uku RK da Doctor Ranjet suka shigo ɗakin. Firgigit Nene ta farka, yayinda Maanal tai ƙoƙarin rufe zanen nata amma sai caraf RK ya rikesa.
“Woow!, this is amazing”. Ya faɗa yana kallon zanen cike da matukar mamaki. Sai kuma ya kalleta. “Dan ALLAH da gaske kece kikayi Baby?”.
Kafin ma Maanal ta bada amsa Nene ta cafe cikin taɓe baki. “Yo in dai Manaalu ce ai baka rabata da zanen aljanai Rafeequ. Tun tana yarinya uwar tayi tayi amma ina harma an barta taitayi itace zata ƙare da mafarkinsu ai ba wani ba”.
“Nene ai abune mai ƙyau wannan ɗin.....”
“Ɗan nan a al'adar yahudu da nasara ba. Amma mudai a musulunce banjin cewar abune mai ƙyau duk da ni ɗin ba malama bace”.
Dariya RK yayi, sai kuma ya miƙama Nenen zanen yana faɗin, “Amma Nene kinyi fa ƙyau a wajen nan kamar wata sarauniya a kujera”.
Ba ƙaramin zare ido Nene tayi ba tana kallon kanta an zane ras harda yanayin atamfarta. Duka ta kaima Maanal itako ta kauce tana ƙara ɓata fuska. Aiko ta shiga zazzaga jaraba shi dai RK da Dr Ranjet na dariya abinsu. Manaal dai ta miskile fuska kamar ba ita tai tsiyar ba. Sai da Nene tayi mai isarta sannan ta fice dan idan anzo duba Maanal ɗin fita takeyi. Bayan fitar Nene Dr Ranjet na duba Maanal RK daya kasa ajiye zanen ya dubi Maanal cikin serious ya ce, “Amma basirar nan naki bai kamata ya tafi a banza ba kawai, yana da ƙyau mutane su amfana da shi”.
“Kamar ya?”.
Ta faɗa a ƙasan maƙoshi. Bai damu ba, dan zuwa yanzu ya sake fahimtar miskilancinta mai lasisi ne.
“Akwai Companyn da nasan suna matuƙar buƙatar aiki da mai irin wannan basirar taki”.
A daƙile ta furta,