Showing 36001 words to 39000 words out of 59211 words

Chapter 13 - AJIYA A DUHU Book Complete Original billy.docx

04 Feb 2025

26270

idan abinda kike tunani kenan ki ciresa kuwa....”

    Hajiya Yaya ta katse Ammie a harzuƙe. Shima Daddy a harzuƙen ya katseta da faɗin, “Ashe kuwa zaki mutu bayan anyi, dan Maanal ita na zaɓama Yazeed kuma shima itace zaɓinsa aure tsakaninsu babu fashi da izinin UBANGIJI ko da Asiya data haifeta bata yardaba kuwa. Baba ku ƙyaleta, tunda ita bata san masalaha ba dan ALLAH mu zuba aga ni da ita waye keda ƙarfin iko akan Yazeed ɗin.....”

        “A'a Usman duk baza'a kai ga haka ba”. Baba Kalla ya faɗa. Batare da ya jira cewarsu ba ya cigaba da faɗin, “Ku duka ku kwantar da hankalinku kuji. A matsayinku na iyayen Yazeedu duk kuna da iko a kansa, amma fa ku sani shima yanada hakki a kanku. Aure dai ba wasa bane, ba kuma jeka ka dawo bane ba. Dan haka ku masa adalci ku barshi ya zaɓi wadda ransa ya kwanta da ita koda a cikin zaɓin naku ne. Idan kuma babu a cikinsu itace ma babbar masalaha ya auro daga can gefe shike nan matsala ta kare. Saboda haka kai Yazeedu kana da wadda kake so ne?”.

       A hankali kuma karo na farko Yazeed ya ɗago idanunsa da suka kaɗa sukai jajur saboda damuwa. Cikin danne ƙuncin daya mamaye masa zuciya ya ce, “Baba idan har auren duka zaɓin nasu zai zama masalaha na karɓa. Zan auri Maanal ɗin da Nazeefa....”

    “Baka isa ba sai dai ka auri Nazeefa ita kaɗai....” Hajiya yaya ta katsesa cikin daka tsawa. Babanta ne shima ya katseta a tsawacen. “Sadiyya bana son shashanci fa. Yaro ya kawo mafita kinama mutane rashin hankali, ko kunyar idona baƙyaji bare nauyi. Shin kokin manta mune a gabanki bashi mijin naki kaɗai da kika raina ba. Ana binki ta lalama kina wani botsarewa saboda wulakanci. To wlhy ki shiga hankalinki. Idan kuma ba hakaba zan hanashi auren Zazeefa ɗin naga yaya zakiyi. Shashancin banza kai”.

       Haƙuri ta fara bashi ranta a matuƙar dagule. Tayi hakanne kawai dan ganin yanda ransa ya ɓaci, ta kuma san halin mahaifin nata idan yay magana baya canjawa. Gara ta lallaɓashi suje a haka ita tasan duk ma hanyar da zatabi dan ganin ta tarwatsa wannan aure.... Shima Daddy haƙurin yaba baban, dan haka ya cigaba da faɗin, “Shike nan magana ta ƙare zai auresu su dukan. Dan haka sai kuje ku fara shiri dan nan da watanni biyu za'ayi a wuce wajan. Rana ɗaya za'a ɗaura auren.”

        Wani irin motsawa zuciyar Ammie tayi da ƙarfi. Hakama Hajiya Basariyya da tun da aka zauna bata tofa komai ba zuciyarta wani irin raɗaɗi take mata. Ina bazai yiwu ta bari ai wannan haɗin ba, sannan bazata taɓa yarda aima Yazeed auren gata shi kaɗai ba wlhy, Gara a cigaba da wannan fitinar hakan yafi sakata nishaɗi, zai kuma fi bada armashi idan yazam anyi auren Nazeefa da Yazeed ne farko. Ammie zatai magana tai saurin katseta ta hanyar fara yi. “Baba mun gode ALLAH ya saka da alkairi ya kuma sanya albarka a al'amarin. Sai dai nakega maganar ɗaura auren rana ɗaya kamar akwai damuwa musamman ga ita Maanal. Tunda likitoci sunce abarta ta ɗan huta mizai hana a fara yin na Yazeed da Nazeefa daga baya sai ayi da ita Maanal. Komai ma zaifi tafiya a cikin masalaha ni dai anawa ganin, zuwa lokacin itama Maanal ta murmure dan yarinyar ta fyaɗu sosai a wannan karon, wlhy abin tausayi kamar bazata rayuba ma. Sai itama Huznah ta samu miji, Inaga sai a haɗa dana Yazeed ɗin kawai ko yaya kukace”.

        A maganar farko Hajiya Yaya wani irin daɗi da godema Hajiya Basariyya ta shigayi a zuciyarta. Daga ƙarshe kuma sai taji zafi danta fahimci hassada Hajiya Basariyya ke son nunawa. Amma zata bita a hakan dan itama ta ribantu. Itama dai Ammie har ranta taji daɗin zancen Hajiya Basariyya, duk da tasan tayi hakanne badan ALLAH ba sai wata manufa tata. Shiko Daddy wani irin ƙuna zuciyarsa ta shigayi, saboda ya jima da fuskantar wacece matar tasa. Cikin takaici kawai yake mata wani kallo mai kama da harara. A ɓangaren Yazeed kuwa wani irin tsanar matar uban tashi ya fara ji a karo na farko a rayuwarsa. Duk da ya jima da fahimtar halinta na munafunci dan ta sha haɗashi da Daddy a baya bai taɓa maida hankali ko damuwa da lamarinta ba. Amma a yau ji yake kamar ya maketa dan baƙin ciki. Shifa ya amshi auren Nazeefa ne kawai dan ya samu dai Mamma ta haƙura ya auri Maanal. Amma shine munafukar matar nan zata kawo wannan ƙauli da ba'adin. Kasa daurewa yayi cikin sanyin murya ya ce, “Ummi anawa tunanin ai ba komai bane. Idan ta dawo ƙarƙashina zama tafi samun kwanciyar hankalin da su likitocin ke buƙata. Maanal na buƙatar hutu ne da kulawa. Kuma ina sha ALLAHU duk bazan gaza yin hakan akansu su duka ba”.

      Ganin kamar zancen ya shigi baba yasa Ammie saurin tare numfashinsa. “Hakane Yazeed, amma dan ALLAH nima ina roƙonka da abi shawarar Hajiya. Saboda ya kamata aje neman auren Maanal wajen dangin mahaifinta. Ita kanta kuma sake samun nutsuwar zaisa komai ya tafi mana dai-dai yanda ya kamata. Idan akayi na Nazeefar kamar da wata biyar haka itama sai ayi natan. Kamar yau ne ai ka kwantar da hankalinka kaji Yazeed”.

     Ji Yazeed yay kamar ya fashe da ihu. Dan idanunsa har wani ɗan tara ƙwalla sukayi. Baba Kalla ne ya ce, “To da gaskiyarsu kuma ta wani fanin idan muka kalla. Tabbas mai irin wannan ciwo mai haɗari ya kamata abi dokar likitocin domin samar mata da nutsuwa. Sannan kamar yanda mahaifiyarta ta faɗa yana da ƙyau aje neman aurenta wa mahaifinta. Dan haka kayi haƙuri Yazeedu kamar yau ne in sha ALLAHU. Kaima idan akai haka zaifi baka nutsuwa da kwanciyar hankali. Ai rabon baima zoba ballantana ya wuce”.

      Albarka duk suka saka da fatan ALLAH yasa haka shi yafi alkairi. Sai dai a ɓangaren Yazeed zuciyarsa a matuƙar ƙuntace take. Haka shima Daddy sam wannan tsarin bai masa ba. Kawai dai dan anfi ƙarfinsa ne. Amma ya ƙullaci Ammie da Hajiya Basariyya. Da haka dai taron ya watse.....

     _________★

     Bayan wucewar su Baba Ammie ta samu Daddy akan zataje gaishe da Nene tai mata godiya da ban gajiya. Amma sai yace bai yarda ba. Abin ya bata mamaki, saboda a fusace yay maganar. Zata roƙesa kuma ya ɗaga mata hannu da nuna mata ƙofa alamar ta fita. Tsantsar biyyarta garesa yasa bataja zancen ba ta fitan, dan ta fahimci a fusace yake da ita ne, sai dai bata san ainahin laifin nata ba ita kam. Koda ta kira Nene ta sanar mata ya hana, sai tace ta jirata gata nan zuwa ita....

   ________★

      Hajiya Basariyya kam dariya ta dinga sheƙawa. Sai kuma tai kiran aminiyarta ta lambarta mata komai. Dariyar suka haɗu sukayi tayi su duka. Sai da sukai mai isarsu cike da zolaya Hajiya Kamila daga can tace, “Aminiyata ke kwalba ce wlhy uwar sharri. Cikin ƙanƙanin lokaci kinsa dole anbi yanda kike so. Ho tawajena kina wuta fa”.

         “To ni ɗin ta wasa ce aminiya ai idan sun san wata basu san wata ba. Idan har ina raye Asiya bata isa samun abinda ni ban samu ba. Ita kanta Hajiya Sadiyya da take ganin kamar na mata aiki ne ta saurari shirina akanta.”

      “Kai ta wajena mi kike shirya mata ita kuma?”.

   “hhhhh karki damu sai mun haɗu zaki ji komai da komai. Ke dai yanzu kice da Malam Nagode. Zuwa gobe kuma zan turo miki Huznah ya mata dukkan abinda yace dan ina son shap-shap yaron nan ya kawo kasa tunda har na gumtsa musu zancen kada a fara ɗaukata maƙaryaciya”.

     “An gama ai karki wani damu kanki”.

   “To shike nan sai tazo.”

Daga haka sukai sallama kowa ya yanke wayar. Hajiya Basariyya ta faɗa saman gado tana mai jin kanta a sama can ƙolokuwa da tabbatar ma da kanta yau sa'a tata ce........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)

2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)

3 DUNIYAR MU (Huguma)

4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500

Book 2:-1000

Book 3:-1500

Book 4:-2000

0022419171

Access bank

Maryam Sani Gumi

Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷

1000CF

89825722

Nousaiba Lawali Maradi

Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_

ب

ِ

س

ْ

م

ِ

الل

َّ

ه

ِ

الر

َّ

ح

ْ

م

َٰ

ن

ِ

الر

َّ

ح

ِ

يم

_*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖1️⃣9️⃣

.......Sosai ƙannen Yazeed sukai farin cikin dawowar mahaifiyarsu gidan. Gaba ɗaya sun zagayeta anata cakai-cakai kowa na bata labarin abinda ya faru da bata nan. Itako sai murmushin jin daɗi take yi musamman akan abinda suka dinga ma Ammie. Suna a hakan Aunty Sabuwa ta samesu. Tashi Hajiya Yaya tai suka shige ƙuryar ɗaki suka rufe kansu. Dama itace tai kiranta tunɗazun bayan wucewar su Babansu. Sai da Aunty Sabuwa tasha fresh milk ɗin data ɗakko daga falo sosai sannan ta dire tana sauke ajiyar zuciya da faɗin, “Kai nafa kwaso rana da yawa. Kin ganni nan daga tudun wada nake. Kin san munata shirye-shiryen bikin ƴar ƙawata Sailuba. Ko sanda kika kirani muna tsaka da meeting ne ma dan tun sassafe na baro gida”

       “Kai kar dai kice min bikin yarinyar nan har yazo?”.

   “Wlhy kuwa yazo Yaya ai abin babu wuya...”

    “Gaskiya ba wuya kam. Abin mamaki wai Sailuba da aurar da ƴa”.

   “Hhh kai yaya da abin dariya kike. Yo ALLAH na tuba komu badan yaran nan sun tsaya ruwan ido ba ai da tuni jikoki sun cika mana ko'ina.”

     “Ai dan ubansu dole kam suzo su fito da mazajen aure dan na gaji da ganinsu ɗirka-ɗirka a gida sai yawo bikin wasu da taron birthday party. Ba maneman nan suka rasa ba amma narasa mi sukema hange-hangen”.

     “A'a to yadai kamata wlhy Yaya. Yanzu abin sha'awa bakiga yarinyar nan yanda mijin ya haɗo lefe na nunama sa'a da tsara ba. Jiya mukaje muka duba gida komai yaji gidansa kamar ka zauna kaita kallo. Kuma karki daɗa karki raga yaron shagone wlhy. Amma komai babu raini”.

        “To Sabuwa ai dama abin zuciya ce ba dukiya ba. Sai dai kuma kana gudun inda yaronka zai je ya ƙasƙanta ne. Ko ka saida akuya ta dawo tana ci maka danga.”

    “Da wannan kuma dan wannan. Yanzu dai zakije min baici ko?”.

   “A mizai hana, ranar yinin biki insha ALLAHU zan zo, ai Sailuba nada mutunci da girmamawa. Yarinyar nan ko sanda kike zaune a Kano indai tayo tanan anguwar dai ta shigo mun gaisa”.

     “Sailuba ai bata da damuwa Yaya. Damma ALLAH ya bata shegen miji ne kawai. Wai shi uztazu. Ko akan bikin nan sai da muka bisa ta ƙasa sannan fa ya amince da wannan shagulgulan amma da duk ya hana”.

      “Oh kice dai kuna nan da halin bin malam nan maƙaryata ko Sabuwa?”.

   “Ko ɗaya aunty kawai dai sai ta kama. Wani lokacin ne halin mazan nan sai ka haɗa da dabaru. Yanzu ko ke abinda Yaya ke miki a gidan nan da zaki bari ai masa ɗaurin huhun goro ai da kin wuce wajen. Ko su su Basariyyan haka nan suka zauna ne kike gani. Ai wlhy ba banza ba yake wannan rawar jikin akansu har shi ma Yazeed ɗin”.

     “Zan iya yadda dake wlhy Sabuwa, dan yau naga abu a gidan nan. Kai Basariyya makirar mata ce. Tabbas na tsani Asiya kuma bana sonta amma wani lokacin gara min ita sau dubu akan Basariyya..........”

   Tsaf Hajiya Yaya ta labartama Sabuwa yanda komai ya faru yau a zaman da akayi, har hukuncin da su Baba suka yanke. Sosai Aunty Sabuwa ta sauke ajiyar zuciya da har sai da Hajiya Yaya ta ce, “Lafiyarki kuwa irin wannan ajiyar zuciya haka?”.

       “Wlhy ƙalau Yaya. Naji kawai abubuwan duk sun zo da sauƙi ne. Koba komai ai mu munafuncin Basariyyan yaman rana yau, dan in dai an rigada anyi na Nazeefar Asiya kuma sai dai ta nema ma ƴarta wani mijin amma ba Yazeed ba”.

     “Nima haka nace ai, shiyyasa ma na ƙyalesu aje a hakan. Amma kuma kin san Basariyya maciji ce bata ramin kanta. Mi kika fahimta a wannan salon nata?”.

    “Hassada ce kawai wlhy Yaya. Tasan auren Yazeed sai ya zama na nunama tsara a gidan nan shiyyasa take so ta cusa na ƴarta ayi tare. Kuma tayi na banza dan babu abinda zamu fasa sai ma mu ƙara in sha ALLAHU. Ita waye ƴar nata zata aura ma shin?”.

          “Yo waya sanan musu bata faɗa ba. Ai kin santa ita komai nata ƙunshe-ƙunshe saboda munafunci bata so a sani. Amma nidai tunda nake a gidan nan ban taɓa ganin wani fitaccen baƙon mutunci da za'a kirashi mijin aure yazo wajen Huznah ba. Sai dai idan ba'anan gida ake taɗin ba”.

     “Eh ai munafuka ce zata iya tsara komai. Shiyyasa wlhy Yaya ki zagargari yaran nan suma su fiddo mazan aure, in ba hakaba zataita kutsawa ne dan taga ta gama aurar da nata yaran duk ɗan abin arziƙin su wawashe a barsu su da saura. Kina dai gidan nan agololi biyu sukai aure Yaya ya dinga ɓarin kuɗi kamar babu gobe. Badan mun daƙile wannan ba ma dana uku kenan. To shi dama aurar da yara haka yake na farko-farkon nan sunfi morewa, dan anfi kashe musu dukiya”.

        Sosai zancen Aunty Sabuwa ya shigi Hajiya Yaya. Cikin juyayi ta ce, “Oh dama haka abin yake Sabuwa? Amma shine baki fargar dani ba tuntuni”.

     “Ba fargar dake ne banyi ba Yaya. Kin san auren agololin can munafuntarmu akai akaita komai kamar talakawa zasu aura shiyyasa bamu bama abin muhimmanci ba. Sai daga bayan nan muke ganin ashe lulluɓin biri akai mana da fatar kura. Kuma ko rantsuwa nayi banyin kaffara Yaya ne ya samawa yaran nan mazansu. Shegu da yake suma burin su kenan gasu nan har da ƴaƴa bibbiyu”.

       “Humm ai Daddyn Yazeed ya jima yana zaluntata a gidan nan ban farga ba. Kiga fa Asiya ta bayan bayana wai itace da waɗan nan nasarorin. Babu komai zamu ɗauki mataki”.

    “Babban ɗaukar mataki ALLAH Yaya kuɗi zaki fiddo ko ki shirya ma dake muje ayo miki aiki ɗan gaske. Mufa ba bokaye muke bi ba. Malamai ne na zaure, kin ga ko kaje wajen malami ba bokaba ai babu batun rasa sallar da ake cewa ta kwana arba'in ko?”.

      “Hakane kuma. Inaga dai wannan karon zanje ɗin”.

    “Haba koke fa yaya”.

    (Humm ALLAH ai ba'a masa wayo ko dabara Sabuwa. Idan abu ya dameka ka miƙa lamarinka ga UBANGIJI shi baya barci kuma baya mantuwa. Fafi yawan wasu abubuwan da muke ɗaukarsu damuwa a rayuwarmu hassada ke mana jagora akansu. Amma mu sani rabonkafa rabonka ne. Sannan wani baya canja maka ƙaddararka. Duniyar nan cike take da arziƙi, ka tsarkake zuciyarka ka nema naka kaima in dai nakan ne wani bai isa tare maka wannan samun ba ko ya ƙarama kansa. Shima iya nasa kawai zai ci. Ya rabbi ka yafe mana kurakuranmu😭🙏 ka gafartama iyayenmu 🙏).

____________★

       “Tabbas da manufa kam ta ƙarfafa maganar taki Asiya. Amma kada ki wani damu. Mu ALLAH yasa haka shine mafi alkairi. Dan nima ta bakinki zuwa yanzu auren Maanal da yaron nan ya fita a raina. Duk kuwa da shi ɗin mutumin kirki ne. Amma halin uwarsa da ƴan uwansa bazai bar Maanal zama lafiya ba. Gata ita mai rauni. Ni yanzu abinda nake gani kawai mu lallaɓa Maanalu ta bama yaron nan Rafeeq dama ya shigo sosai, shi kansa Yazeed ɗin ba lallai idan sun aura masa tasu ba su barshi haka ai”.

     Tabbas hakanne Nene, ni kaina wlhy yaron nan Rafeeq yamin. Yaron a haka dai kamar baida wata damuwa. Gashi kuma ɗan uwan Majdiya uwa ɗaya uba ɗaya. Majdiya mutuniyar kirkice ga addini. Dan hatta yaranta tarbiyyarsu ta banbanta da sauran ƴaƴan gidansu. To dan dai yaran yanzu ne kai kana hango musu alkairi su suna wani hange daban. Amma dai yanzu zanyi duk yanda zanyi ta cigaba da zama can Abujan dan bana sha'awar dawowar Maanal gidan nan a yanzu kuma sam Nene wlhy”.

      “Wannan ma tunani ne mai ƙyau. Gara ta zauna a can ɗin kusa da ƴar uwarta. Tunda shima can yake Rafeeq ɗin sun ma fi samun shaƙuwa. To amma shi maigidan naki bazaiga an masa ba daidai ba?. Kinga dai yanda yake matuƙar ƙaunar yaran nan da musu hidima. Tunda kuka dawo hannunsa bai taɓa bambanta al'amarin su dana ƴaƴansa ba”.

     “Tabbas hakane Nene. Nima idan na tuna hakan jikina yana sanyi. Dan ya musu abinda mahaifinsu da ƴan uwansa suka gagara musu. To amma yaya zamuyi, matar nan wlhy ta wuce duk yanda kike tunani. Nata ma mai sauƙi ne, dan babbar matsalarta itace ƙanwar nan tata. Saboda mashawarta ne bata moreba kawai, amma duk masifarta ta wani fannin tafi Basariyya sauƙi”.

          “To mu cigaba da addu'a, ALLAH ai bai manta da kowa ba. In sha ALLAHU komai zai kasance da sauƙi. Yanzu dai sai kisan dabarar da zaki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login