Showing 54001 words to 57000 words out of 59211 words

Chapter 19 - AJIYA A DUHU Book Complete Original billy.docx

04 Feb 2025

26273

na zagaye dake ki manta da baya, ki saka a ranki ƙaddarar data gitta rayuwarki bazata hanaki aure ki zauna a gidan mijin ba har kuma ko samu farin ciki fiye da zatonki. Dan ALLAH shine shaida baki je kin aikata dan son zuciyarki ba. Dan haka ki manta komai, dan ALLAH ki manta komai kije ki fara aiki, abu nagaba kuma kiyi ƙoƙarin fidda mijin aure tsakanin Rafeeq da Yazeed kodan ki tabbatar ma Ajwaad kina rayuwane domin kanki. Dan kuwa cikakkiyar amsa kika samu a jiyanki game da shi, idan a baya hasashe kawai mukeyi bisa dalili yanzu ya tabbatar miki shi da kansa”.

      Sosai Maanal take kuka yanzu kam, Amal ta jawota jikinta ta rungumeta itama tana kukan, sam basa son tunawa da bata, basa son tunawa da ƙaddarar data ratsa rayuwar autarsu, basa so ba sa so. Cikin rawar murya da son ture komai Amaal ta ce, “Duk abinda Didi ta gaya miki shine gaskiya wlhy Auta. Ki dake zuciyarki kiyi abinda ya dace da rayuwarki a yanzu. Ki manta da abinda ya wuce kamar ma ba'ayi komai ba. Koda wasa kada ki zubda daraja da kimarki ta ɗiya mace. Ki amshi ƙaddarki kamar yanda muma muka rungumi tamu. Hakan da zamuyi sai ya ƙara ƙarfafa Ammien mu, ki duba kiga rayuwar data baro, mai cike da tarin gwagwarmaya amma a yanzu ALLAH ya mata canji, canjin kuma baisa ace babu wasu jarabawoyin ba kuma. Tunda anan ɗin ma tana fuskantar ƙalubalen bawai sun ƙare bane. To haka rayuwa take duk yanda ka kai ga samun sauyi da nasara da jin daɗi dole ƙaddararka aminiyar NUMFASHINKA ce Maanal. Tare suke tafiya a jefe ƙafa da ƙafa. Aminan juna ne tamkar gangar jiki da numfashi. Hakama jarabawarka abokiyar gangagar jikinka ce. Kinga ko har abada babu ɗayan da zai rayu babu ɗaya a tsakanin gangar jiki da numfashi ko?”.........✍️

🏃🏃🏃Hummmmmmmmmmmmmmm🥲

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)

2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)

3 DUNIYAR MU (Huguma)

4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500

Book 2:-1000

Book 3:-1500

Book 4:-2000

0022419171

Access bank

Maryam Sani Gumi

Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷

1000CF

89825722

Nousaiba Lawali Maradi

Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_

ب

ِ

س

ْ

م

ِ

الل

َّ

ه

ِ

الر

َّ

ح

ْ

م

َٰ

ن

ِ

الر

َّ

ح

ِ

يم

_*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖2️⃣6️⃣

.........“Hakane ƴan uwana, na gode da shawarwarin ku, kuma in sha ALLAHU zan yi aiki da su. Dan ALLAH kuyi haƙuri da ɗaga muku hankalin da nakeyi a koda yaushe. Har yanzu ni mai RAUNI ce a cikinku, ina da matuƙar rauni ƴan uwana na sani....”

      Kuka ya sarƙeta, rungumeta sukai su duka tausayinta na sake ratsasu. Tabbas gaskiya ta faɗa ita ɗin mai rauni ce a cikinsu. Dan ko lokacin ƙiruciyarsu kadai faɗama Maanal tsiwa da rashin kunya ga shegen tsokanan faɗa. Amma akwai tsoro kamar farar kura. Sai kuma da jarabawar tasu ta fara ita ta ninku mata sau biyu, duk da kuwa suma sau bibbiyu ne, amma ita tata tafi tasu ƙarfi ne. Ba komai yasa hakan ba sai dan sun fita ƙarfin zuciya, sannan su dama basu samu kansu a irin yanayin data samu kanta ba a wancan lokacin kasancewar sun fita hankali da wayo sosai. Sannan su komai dama anyinsa a wasa-wasa ne bakamar ita ba.

    Kusan raba wannan daren sukai zaune. Suna sake bama Maanal ƙwarin gwiwa da nasiha data sake ƙarfafata ta kuma ji ta gamsu zataje tayi aikin. Hakan yasa washe gari yanda kowa yay shirin zuwa office itama tayi, yayinda Amaal tun asuba ta kama hanyar Kaduna tunda dama da mota tazo. Sun fito Maanal na ƙoƙarin shiga motar Shahidah sai ga motar RK ta shigo gidan. Dole ta ɗan dakata yayinda Uncle Sadeeq ke dariyar ƙeta cike da tsokana ya dubi Maanal ɗin yana faɗin, “Ga majnoon nan lailah sai ki dakata”.

    Dariya Shahidah tayi itama tana amsa masa, “Aifa sai Majnoon ɗin, Rafeeq sam baya gajiya shi kam”.

   Maanal dai batace komai ba har RK ɗin ya daidaita parking ya fito a motar. Yayi matuƙar ƙyau cikin farar shadda ɗinkin tazarce. Sai dai babu hula a kansa. Wajen Uncle Sadeeq ya fara zuwa suka gaisa cike da mutunta juna da kulawa. Dan ta ko'ina fa RK ya kafa jam'iyyar sa. Sai kuma ya juya ga Shahidah itama ya gaisheta da mutuntawa. Itama ta amsa masa da kulawa tana tambayarsa yaya aikinsa. Idanunsa akan Maanal ya amsa mata da Alhamdullah.

      Ganin irin kallon da yake mata ta ɗan hararesa sannan ta gaishesa a cinkushe. Maimakon amsawa sai ya kalla agogon dake a tsintsiyar hannunsa yana faɗin, “Ashe da banyi sauri ba dana makara?”.

     “A gaskiya kam daka makara. Amma ALLAH ya taimakeka, bari kaga muma muyi nan karmu makaran wajen kallon lailah Majnoon”. Uncle Sadeeq ne da wannan magana cike da tsokana yana kallon Maanal. Yayinda Shahidah ke ƴar dariya itama dai hankalin nata akan Maanal ɗin. Motocinsu suka shiga suka fice abinsu aka bar Maanal tsaye sororo, wani irin daka zuciyarta ke mata yau a kansa. Sotake ta ƙarfafa kanta game da shi ta bashi damar kamar yanda ƴan uwanta suka bata shawara a daren jiya. Sai dai ina ji take anya kuwa zata iya hakan? Amma sai wani sashe na zuciyarta ke sake ƙarfafata....

       “Good morning my queen”.

   RK ya faɗa yana ɗan duƙowa kaɗan saitin kunnenta. Wani irin numfashi taja tare da jan jikinta baya duk da bawani ya matseta bane akwai tazara a tsakaninsu. Murmushi yayi da ɗan ɗage mata gira sama ita kuma ta hararesa tana kauda kanta. Sai kawai ya fashe da dariya. “Oh ni ɗan Mamana irin wannan harar da akemin sai na sace amarya ai ko a sallar isha'i a ɗaura mana auren daga baya. ALLAH ki daina mun wannan hararar rikita min lissafi kike gimbiya. Balle irin yanda nai kewar nan taki kwana biyu dubeni har wata rama nayi marayan ALLAH abin tausayi”.

      A yanda yake maganar batama san sanda taji murmushi na neman suɓuce mata ba. Amma sai ta dake abinta ta danne tare da ɗan girgiza kanta ta ce, “ALLAH dai ya shiryeka”.

         “Amin matar Rafeeq Kasheem Kura”.

    Manaal bata kulashi ba, dan wayarta dake neman agaji, ƙoƙarin cirota ta shigayi a bag shi kuma ya amshi ɗan lunch box ɗinta na abinci data haɗa. Yazeed ne ya bayyana ɓaro-ɓaro akan screen ɗin. Hakan ya saka RK taɓe baki cike da basarwa yabar wajen. Da kallo kawai ta bisa ƙasa-ƙasa tana mai kai wayar kunnenta a nutsenta tai masa sallama. Da kulawa ya amsa mata da ga can tare da tambayarta jikinta tace Alhamdullah ta samu sauƙi.

     “Masha ALLAH nima zuwa anjima zan shigo duk kin bi kin tadamin hankali da rashin ganinki tunda nazo aikin ma yaƙi yuwumin yanda nake so. Amma yanzu na ɗan ji ƙarfi tunda na jiki Alhamdullah”.

          Shiru tai ta kasa cemasa komai. Shima sai kawai ya saki murmushi daga can, tare da faɗin, “To sarkin kunya bari na barki nima zan fitane ma na kiraki”.

   “ALLAH ya tsare ya bada sa'ar abinda za'aje nema”.

       “Amin ya rabbi mar'atussaliha”.

Ya faɗa can ƙasan maƙoshi cike da shauƙin so da ƙara jin tarin ƙaunarta har ƙarƙashin zuciyarsa. Wayar tai ƙoƙarin maidawa cikin bag ɗin dai-dai da isowar RK wajen da mota. Fitowa yay ya buɗe mata mazaunin gefensa ta shiga ta zauna ya rufe sannan ya zagaya ya shiga shima yay ma motar key suka fice. Yanata dai ɗaɗɗaurewarsa bata kulashi ba. Dan ta fahimci yana masifar kishin Yazeed. Koyaya yaga wani abinda ya shafi Yazeed a tattare da ita zai fara fushi. Itako sai dai yay tayi, dan Yazeed dai tare ya gansu, yazeed kuma abin girmamawarta ne dan ya taka rawar gani a rayuwarsu a lokacin da kowa ya guje musu. Shiko fa daga sama ya tsinceta.

     Sunyi nisa a tafiyar motar shiru dan kansa ya yanke shirun nasu ta hanyar ɗan juyowa ya kalleta fuskar dai babu walwala. Sai kuma ya maida kansa ga titi yana faɗin, “Har yanzu baki sanarma su Zulaiha kina Abuja ba ne?”.

     Shiru kamar bazata tanka masa ba sai kuma a can ƙasan maƙoshi ta ce, “Sun sani wani abu ya faru ne?”.

         “No babu komai, nagane basu zo dubaki ba har yanzu”.

      “Ni nace su barshi basai sunzo ba.”

“Okay”.

Ya faɗa yana ƙara damƙe steering da ƙyau. Daga haka suka sake yin shiru har suka iso Mawaad Company. Yauma kamar wancan ranar komai a tsaftace a kuma nutse yake a companyn. Sai da ya daidaita parking da ƙyau tana ƙoƙarin ɓalle murfin motar ta fita ya dakatar da ita. “Na musu reporting akan baki da lafiya shiyyasa baki zo jiya ba kamar yanda suka buƙata. Dan haka ko sun tambayeki sai kisan amsar da zaki basu. Please dan ALLAH ki kula, wajen nan cike yake da ƙartin banza kar'a tsinceni a titi muna raba hali da al'umma”.

      Ɗan kallonsa tai a karo na farko sai kuma ta janye lokaci guda tana mai girgiza kanta. Maimakon amsa masa batunsa ta buɗe kawai ta fice abinta. Ta ɗan fara tafiya taji alamar ana binta a baya, juyowa tai da taga shine riƙe da ƴar lunch box ɗinta. Tsayawa tai tare da miƙa masa hannu, amma sai ya girgiza mata kai yana nuna mata hanya alamar suje. Babu yanda ta iya haka suka jera har cikin Companyn...

      Wani irin lumshe idanu AA Darma dake zaune cikin motarsa daga baya dan driver ne yau ya kawo shi Office ɗin tare da datse leɓensa ba ƙasa da ƙarfi. Sai dai sam bazaka taɓa fahimtar hakan ba kasancewar jarida a hannunsa yana dubawa. Shima isowarsu kenan, kuma tun a hanya a wajen fitilar bada hannu yaga motar RK ɗin, ya hango mace a motar amma baiga wacece ba. Sai dai haka kawai zuciyarsa ta bashi wacece ɗin, dan haka koda suka iso kasancewar sun riga su RK ɗin shigowa Companyn sai bai fita a motar ba. Komai daya faru a kan idanunsa ne dake sakaye a cikin glass mai matuƙar haske daya ƙawata ƙyawun nutsatstsiyar fuskarsa. A hankali yay wurgi da jaridar hannun nasa a sit ɗin gefensa.

       Shi dai driver bai san mike faruwa ba, amma yana tunanin ko wani abin ogan nasa yake shiyyasa. Suna a haka RK ya fito fuskarsa cike da walwala kamar ba shine ya gama fushin kishin Yazeed ba. Motarsa ya shiga abinsa yabar harabar companyn, securitys ɗin gate suka ɗage masa karfe da aka gitta a ƙofar bayan gate ya fice. Wani siririn tsaki AA Darma ya saki a can ƙasan maƙoshinsa. Sai kuma ya ɓalle murfin motar aɗan fusace ya fito batare daya ɗauki komai nasa dake a motar ba. Sanye yake cikin ash color ɗin suit masu haske da sukai masa shegen ƙyau. Daga ciki black rigace mai wuyanta har saman wuya. Yanda yake taku cike da bada faɗi da cika waje ma kawai abin kallo ne. Securitys sai gaidashi suke amma hannu kawai yake iya ɗaga musu batare da ko kallonsu ba. Koda yazo ga ƙofar shiga da sauri aka buɗe masa ya shige drivern sa biye da shi da tarkacensa. Tsitt kake ji ma'aikatan dake wajen sakamakon shigowar tasa. Sai kuma kowa ya shiga faɗin, “Good morning Sir!”. Hannu kawai ya ɗaga musu sau ɗaya yay wucewarsa batare da ko kallon kowa ba anan ma. Hakan ya sakasu fahimtar yau fa gizagon boss ɗin yafi na kullum, sai kowa ya ƙara kama kansa.

     Elevator ya shiga tare da danna floor ɗin ƙarshe 6th da office ɗinsa yake, shima drivern nasa ya shiga. Ƙofar zata fara rufewa Maanal da AS da yay mata rakkiya office tai singing da ake buƙatar tayi suka iso wajen. Shigowa sukai da sauri batare da hankalin AS ɗin yakai ga wanda ke cikin elevator ɗin ba kasancewar ya ɗan juyama ƙofar baya yana danna waya. Balle kuma Maanal da itama gaba ɗaya nata hankalin ke akan wayarta. Sai da suka gama shigowar AS ya shaƙi ƙamshin turaren boss. Sai kuma sukai ido huɗu da driver. Ya juya da sauri nan ma sukai ido huɗu da AA Darma.

        Cikin ɗan rawar baki ya ce, “So...sorry sir good morning. ALLAH bamma lura kaine a ciki ba. Zan kai new staff ɗinmu office ɗinta ne bisa umarnin Director Mustapha”.

      Kai kawai AA ɗin ya jinjina masa, yayinda Maanal da zuciyarta ke wani irin bugawa da sauri-sauri ta sake dakewa abinta dan tunda AS ya fara magana ta ɗan ɗago ta gefen ido ta saci kallon wanda yakema wannan rawar bakin sai ta ɗauke kanta. Ɗan duƙowa yayi kaɗan ƙasa-ƙasa ya furta, “Boss ne kiyi gaisuwa”.

      Shiru tai kamar bazata kulashi ba sai kuma a hankali a can ƙasan maƙoshi batare data kalla kowa ba ta furta, “Morning”. Daga haka taja bakinta tai shiru. Ita tai abin amma AS ta bari da ruɗani, sai wani irin haɗiyar yawu yake yana kallon AA ɗin ta gefen ido ko zaice wani abu akan gaisuwar rainin wayon sabuwar ma'aikaciyar tasu....

__________★

        Fuska cike da murmushi Hajiya Basariyya ke kallon kayan da ƴar Tata Huznah ta baje a gabanta. Ba kayan ci bane ba kuma na sakawa ba kayan da malam ne na Zaria ya haɗoma Huznah ɗin bayan ta ɗauki tsawon kwanaki tana acan ana tsumata da wasu aikin. Ba kuma akan kowa akai hakan ba sai sabon saurayinta data samo a birnin tarayya Abuja lokacin bikin ƴar ƙawar Hajiya Basariyya ɗin. Sam kayan babu wani ƙyan gani ko birgewa a kallonsu. dan kuwa tarin guraye ne da ruwayen magani da layu sai garin magungunan da turarruka na shafawa harda su hoda da kwalli na idonka idona. Sai da ta gama mata bayanin komai dalla-dalla kafin ta ta fuska ɗauke da murmushi ta ce, “Kin daiga komai Ummi, bayan kuma wanda yay mun a jikina dan na aikata iya aikatuwa. Yanzu dai babu zama dole na shirya na wuce Abuja. Dan ya tabbatar min da in dai nayi komai yanda ya dace babu fashi auren mu zai kasance tare da na Yazeed ne a gidan nan”.

       “Kai Alhamdullah Masha ALLAH. ALLAH dai ya sakama malam da alkairi wlhy. Shiyyasa bana baƙin cikin biyansa duk abinda ya buƙata dan shima ana samun biyan buƙatar daga nasa aikin. Tafiya Abuja kam dole ne. Sai dai Daddynku nake tsoro dan yana gari. Dama da yaya ya bari kika tafi Zaria ɗin nan. Yanzu ko akace Abuja nasan da rigima”.

     Cikin matuƙar damuwa Huznah ta ce, “To Ummi yanzu yaya zamuyi kenan, dan ni dai ko ana ha maza ha mata sai naje Abujar nan wlhy??”......✍️

     

      _Tofa, maji ma gani wai an bizne tsohuwa da ranta jama'a 😂🏃._

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)

2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)

3 DUNIYAR MU (Huguma)

4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500

Book 2:-1000

Book 3:-1500

Book 4:-2000

0022419171

Access bank

Maryam Sani Gumi

Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷

1000CF

89825722

Nousaiba Lawali Maradi

Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_

ب

ِ

س

ْ

م

ِ

الل

َّ

ه

ِ

الر

َّ

ح

ْ

م

َٰ

ن

ِ

الر

َّ

ح

ِ

يم

_*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖2️⃣7️⃣

........Maimakon Hajiya Basariyya taji haushin furucin ƴar tata sai ta tuntsure da dariya tana faɗin, “Ja'ira wato ke ƴar daɗi soyayya ko? Kwantar ma da hankalinki komai zaizo da sauƙi bani lokaci dai nayi tunani.”

     “To Ummi nidai dan ALLAH kar tunanin naki ya wuce yau da gobe dai. Dan a matse nake gashi nayi kewarsa ina son ganinsa.”

     Anan ɗin ma dariya Hajiya Basariyya ta sanya abinta.

__________★

      A can ɓangaren Aunty Sabuwa ma shiri takema ƴarta na mugayen mallaka, dan hatta da Hajiya Yaya aba'a ƙyaleba tuni sunanta na wajen boka. Kai shi kansa Daddyn ba tsira yay ba da sauran ƙannen Yazeed mata. Dan tace tako ina sai ta bama ƴarta garkuwa. Tako bayar ɗin gwagwargwadon abinda take ganin ya wadaceta. Ga maganin mata ana ɗirkama Nazeefa kamar babu gobe, gefe kuma fetsararrun ƙawayen uwarta su Hajiya Malika na koya mata kissa da kisisina harda salon kwanciya da miji.

     A tacan ɓangaren Mahaifinta kuwa yana nasa shirin ne akan Daddy. Dan a wannan karon yaci alwashin samawa kansa nasara akan Daddyn. Sai kuma shirin biki na ƴar gata da sukeyi da ga shi har Aunty Sabuwa ɗin.

     Ata nan ɓangaren Hajiya Yaya shirin suma suke na garari, dan a satin nan zata wuce Dubai ita da Baraka da Asalamiyya su haɗo lefe da nasu kayan cin bikin. Da farko Daddy ya hana tafiyar, saboda ya fahimci ana komai ne dan ƙuntatama Ammie. Amma sai Ammien ta dinga masa roko da magiya dan tasan hanawar wata sabuwar rigima ce, kuma dai laifin a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login