Showing 48001 words to 51000 words out of 59211 words
bai taɓa ganinsa a wannan yanayin na yau daya gansa ya fito daga conference room ba. Ya kuma tabbatar ba ƙaramin abu bane zai sakashi cewa kada abar kowa ya shigo inda yake ɗin.
Daga shigowar RK harta AS ɗin nasa da abinda yake ƙoƙarin faɗama RK ɗin duk a kunnensa ne, dan yana tsaye jikin ƙaton ƙayataccen gilashin da akai ma kusan kowanne bango na Companyn gaba ɗaya ado da shi hannayensa duka biyu a cikin aljihun suke ya zubama harabar wajen Companyn idanu koma ace ƙayatattun gine-ginen birnin na Abuja. Sai da ya basu kusan mintuna uku kafin ya ɗan juyo kamar mai fama da ciwon wuya ya zuba musu ido su duka biyun, sai kuma ya wani watsa musu ɗan iskan kallo ya ɗauke kansa.. Hakan yasa AS ƙoƙarin fara kare kansa cikin rawar murya da damuwa. Amma sai yay masa alamar yaje da yatsunsa biyu cike da salo. Kai AS ɗin ya jinjina masa cike da girmamawa yana mai haɗiye abinda yaso faɗar. Koda ya fice ya rufe musu ƙofar sake maida kansa yay ga kallon wajen batare da yayi magana ba kamar yanda shima RK ɗin baiyi magana ba har lokacin.
Iska mai ƙarfin gaske RK yay wani irin fesarwa ta alamar tsantsar takaici. Sai kuma ya sake takowa cikin Office ɗin sosai har inda yake shima ya tsaya kamar yanda yake a tsayen, batare daya kallesa ba ya furta, “Miyasa tun farko ka yarda zaka ɗauketa aiki cikin girmamawa da darajtawa! Amma ka saɓa hakan? Kasan matsayinta a wajena kuwa AA!?”.
Idanunsa da suka kaɗa sosai ya lumshe. Sai kuma ya saki wani ɗan siririn tsaki mai ɗan sautin da har RK ɗin yaji. Shiru na tsawon mintuna fin huɗu har RK ɗin daya sake ƙuluwa da haushi ya fidda ran amsawar tasa sai kuma ya ɗan karkato da kansa ya duba RK ɗin. Shima juyowar yay ya kallesa sukaima juna kallon ido cikin ido kowanne ƙwayar idanunsa na bama ɗan uwansa dai-dai da amsar da yake buƙata ko nemar mata fassara da fashin baƙi. AA ɗin ne ya fara janyewa yana sake sakin wani lalataccen murmushi a karo na farko mai kama dana rainin hankali ko tsantsar takaici. Sai kuma ya maida fuskarsa ya tsuke tamkar ba shiba, a dakensa a kuma karo na farko cikin muryarsa mai zurfi da amo ƙasa-ƙasa ya furta, “Calm down first, let's talk when you're ready. Right now I need to be alone”.
Wani irin zuba masa ido RK yay cikin takaici, sai kuma ya saki murmushi mai ciwo shima daya sake bayyana tsantsar bacin ransa. Juyawa yay yana kallon AA ɗin daya sake maida hankalinsa gaba ɗaya ga kallon garin. Taunar lips ɗinsa ya shiga yi da ƙarfi kafin ya juya ya fita a Office ɗin batare da ya sake cewa koman ba. A yanda ya ɗan bugo ƙofar ya sake saka AA lumshe idanunsa daga inda yake bai kuma juyo ba.
RK daya fita baiko kalla AS ba ya shige elevator. Har zai danna sai kuma ya fasa ya fito. Dogon hanya ɗin yabi sai gashi ya fito wani wajen da jerin Offices duke har kusan guda biyar. Office na biyu yay knocking. Kai tsaye aka bashi izinin shiga dan duk wanda ke'a cikin Office ɗin yana kallonsa ta hanyar camara. Ɗaya daga cikin wanda sukama Maanal interview ne. Fuskarsa ƙawance da murmushin daya bama RK ɗin mamaki ya tarbesa. Bayan ya nuna masa wajen zama zai miƙe ɗauka masa wani abun ya dakatar da shi.
“Director Mustapha thanks you basai ka kawo komai ba muyi magana kawai mana”.
“To ALLAH yasa dai lafiya?”.
Director Mustapha ya faɗa yana komawa ya zauna a mazauninsa.
“I'm sorry nasan dokane a companyn nan abinda zan tambayeka. Amma ina neman alfarmar sani ne sakamakon wani dalili mai ƙarfi. Please yarinyar nan da kukama interview yanzu wani abu ya faru da ita ne a wajenku ko aikin ne bata samu ba?”.
Ajiyar zuciya mai haɗe da murmushi Designer Director Mustapha ya saki, sai kuma ya girgiza kansa. “No Doctor babu wani abu daya faru gaskiya. Hasalima an bata aikin dan har CEO ya bata damar fara zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu. Yanzun nan R&D Director ya fita anan na gama bashi list ɗin abinda office ɗin ta zai buƙata a yau komai za'a gama haɗa mata shi. Shin wani abu ya faru ne?”.
“No! No! Babu wani abu daya faru. Nagode sosai”.
“Ai babu zancen godiya a tsakaninmu, yarinyar ta cancanci samun aikin dan gaskiya she is very smart and amazing because she demonstrated excellent problem-solving skills and an innovative approach during the interview. Tunda kaga babu wani ja'inja Boss ya bata dama da wuri haka ai kasan bata wasa bace. Haka muma kowa ya gamsu da brain ɗinta wlhy”.
Murmushi RK ya masa cikin jinjina kai, sai kuma ya miƙa masa hannu yana miƙewa da faɗin, “Thanks you Director”
“No worries doctor. I am on my job”.
Daga haka yay masa sallama ya fito a office ɗin dukkan damuwarsa da AA ya dasa masa na guduwa daga cikin ƙirjinsa. Sai dai kuma hankalinsa nakan dalilin halin da Maanal ɗin ta shiga........✍️
_Tofa ƙaƙa raƙa ƙaƙa. Shin minene alaƙar Maanal da AA?, sannan minene alaƙar RK da AA kuma. Dan tabbas alamu sun nuna akwai sanayya mai ƙarfin gaske a tsakaninsu. Hhhh badaƙala kenan, mi kike son ji?😂 Ga wuri ga waina. To kawai mu haɗe a comments section 🤣🤣🤣🤣🏃._
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_
ب
ِ
س
ْ
م
ِ
الل
َّ
ه
ِ
الر
َّ
ح
ْ
م
َٰ
ن
ِ
الر
َّ
ح
ِ
يم
_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
*_WhatsApp channel_*
https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖2️⃣4️⃣
.........Wata irin ajiyar zuciya director Mustapha ya saki. Sai kuma ya saki murmushi a ransa yana mamakin kansa da ɓoyema Doctor Rafeeq ɗin sauran gaskiyar abinda ya faru da yay... Kirane ya shigo daga landline ɗin office ɗin, ganin daga office ɗin CEO ne ya sashi saurin ɗagawa. AS ne ya sanar masa CEO na buƙatar ganinsa yanzun nan, kuma ya taho da file ɗin sabuwar staff ɗinsu. Bai wani tsaya wasa ba ya miƙe yana dariya. A fili ya furta, “Anya babu wata a ƙasa akan yarinyar nan kuwa? To madai ji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta”.
Sai da AS ya shiga yay masa iso sannan ya shiga. A yanzu kam AA ɗin na zaune ne a kujerarsa ta aiki saɓanin a yanda RK ya samesa ya kuma barshi. Gaisuwa Director Mustapha ya miƙa daga tsayen batare daya zauna ba. Shima AA ɗin da hankalinsa ke kan computern desk ɗin batare daya amsa ba yay masa nuni da vesitors chair ɗin gaban desk ɗin kawai. Zama yay, kafin cikin girmamawa ya ce, “Gani Sir. Dama ina ƙoƙarin ƙarasa haɗa komai ne na kawo sai kuma ga kiran AS akan kana son ganina”.
Shiru bai amsa masa ba, yanata aikin gabansa kawai har lokacin hankalinsa nakan screen ɗin computer ɗin, sai da yaja kusan mintuna uku kafin ya ajiye tare da maido hankalinsa kan Director Mustapha ɗin. “Am sorry ina wani abune”. Ya faɗa cikin muryarsa mai zurfi. Da sauri Director Mustapha ya ce, “Babu komai Sir”.
Kansa kawai ya jinjina masa. Sai kuma ya miƙa masa hannu alamar ya basa file ɗin. Miƙa masa yay da sauri cikin girmamawa. Yayinda shi kuma ya shiga buɗesa yana duba komai daki-daki. Sai zuwa can ya ɗan ɗago. “Baku ƙarasa bane?”.
“Eh sir! Saboda kana fita itama ta miƙe ta fice muna ƙoƙarin tsaidata amma bata sauraremu ba. Mun cigaba da abinda ya dace ne kawai saboda ka bada umarnin hakan. Dan mu harma mun fara tunanin ko tanada wani c......”
Muƙutt ya haɗiye zancen saboda wani shegen kallo da AA ɗin ya jefa masa. Sai kuma ya duƙar da kansa yana shashshafa ƙeya. Shiru office ɗin ya ɗauka na kusan minti biyu kafin yay masa nuni da hannu alamar yaje. Miƙewa yay tare da ɗan rissinawa na girmamawa sannan ya fice a office ɗin.....
Duk yanda yaso cigaba da aikin zuwa lokacin break hakan ya hagaresa. Dan wani irin zazzaɓi ne ma ke neman rufesa. Ga ciwon kai. Dan hatta fararen idanunsa launinsu ya canja zuwa jaa sosai alamar akwai wani abu dake damunsa. Sai dai sam fuskarsa bata nuna komai.
Kwanciya yay a office ɗin bayan dawowa sallar azhar, kamar wasa zazzaɓi mai azabar zafi ya rufesa, ga wani irin sanyi da yake ji. Ya kulle kofar tare da ma AS gargaɗin baya buƙatar kowa. Hakan yasa ko lokacin Asr AS bai masa knocking ba dan yasan ogansa baya wasa da salla. Ganin har biyar na yamma lokacin ma'aikata sun fara tashi babu alamar zai fito hankalin AS ɗin ya fara tashi, ya dai daure dan yasansa da iya yin over work. Kamar wasa har magrib companyn yayi shiru sai securitys. Dole fa yaje ya fara masa knocking amma shiru kake ji wai malam yaci shirwa. Hankali tashe AS yay kiran wata number, bayan an ɗaga yayi gaisuwa cikin girmamawa ya sanar da halin da boss ɗin nasa ke ciki. Banji mi aka sanar masa ba, sai dai ya amsa da girmamawa yana sauke wayar. Yana nan yana faman kai-kawo a bakin ƙofar sai ga wani nutsetstsen mutum da zai iya kaiwa shekara arba'in haka. Sosai yake kamanni da AA ɗin, hatta da rashin yawan fara'ar fuska kamar AA ɗin dai. Gaisheshi AS yay da girmamawa. Ya jinjina masa kai yana amsawa, sai kuma ya fiddo wani ɗan card a aljihun jallabiyarsa fara ƙal ya goga a jikin handle ɗin ƙofar. A take kuwa ta rabe gida biyu ta buɗe. Gaba ɗaya an kashe wutan office ɗin, hakan ya saka gabansa faɗuwa, dan sun san minene ganin AA a duhu yake nufi, wayarsa ya zaro ya kunna fitilar, hakan ya bashi damar ƙarasawa ga makunan fitulun office ɗin ya kunna. A take haske ya gauraye ko'ina. Idanunsa suka sauka akan AA dake kwance a kan sofa. Cike da sassarfa ya ƙarasa garesa yana kiran sunansa, amma shiru babu allamar zai amsa, har ya zauna a saman table ɗin gaban sofa ɗin tare da kai hannunsa saman na AA daya dafe kai da shi, hannun ya janye a hankali ya maye gurbinsa da nashi, sai da gabansa ya faɗin jin wani irin hucin zafi, sanyin hannunsa yasa AA buɗe manyan oily idanunsa gently, sunyi wani irin mugun kaɗawa jazur, sam babu hasken nan mai kama da madara a cikinsu yanzu, sai ƙyallinsu daya sake saka jan yin bauuu. Ga kuma jijiyoyin kansa da suka sake fitowa ruɗu-ruɗu....
“Ya arrahaman Auta! Baka da lafiya amma kazo nan ka kwanta? Are you mad da baka san muhimmancin lafiyarka bane?”.
Maimakon amsa masa sai AA ɗin ya maida idanun nasa kawai ya sake lumshewa. Tsaki mutumin yaja tare da miƙewa ya tada AA ɗin shima. “Oya get up and go home?”.
Bai masa musu ba ya miƙe ɗin, haka ya kamashi suka fito yana bama AS da hankalinsa ya tashi da ganin halin da boss ɗinsa yake ciki umarnin tattaro abubuwan AA ɗin. Cikin sauri ya amsa shi kuma ya wuce da shi......
_____________★
A hankali yake juya steering kamar baya so. Yayinda gaba ɗayan hankalinsa ke akan al'amarin Maanal. Yama rasa yaya zai fassara lamarin, musamman a yanzu daya koma Maawad yaji komai daya faru. Shin murnar samun aikin ce ta sakata kukan? Ko kuwa mike faruwa?. Rashin mai bashi amsa ya sashi ɗaukar hanyar gidan Shahidah, dan gaskiya yana buƙatar ganin Maanal ɗin. Ya ɗan yi nisa da tafiya kira ya shigo masa. Kamar bazai ɗauka ba sai kuma dai ya ɗauka saboda ganin abokin aikinsa ne na asibiti. Neman gaggawa ake masa zuwa asibiti yanzun nan, dole yay reverse zuwa asibitin dan yanda yaji Doctor ɗin a rikice yasan akwai babbar matsala. Kafin ya isa kiran wasu doctors biyu ƴan uwansa ya sake shigo masa. Dole ya ƙara gudu cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi ya iso.....
_________★
A ɓangaren Maanal kuka taci sosai na tashin hankali. Dan har yamma ta kulle kanta a ɗaki taƙi ta fito. Yara da suka dawo makaranta sunata buga mata bata kulasu ba. A haka shima baban nasu ya dawo ya tarar da al'amarin. Linda ce ta sanar masa iya abinda ta sani na shigowar Maanal ɗin da gudu tana kuka ta wuce ɗaki ta kulle kanta...
Hankalinsa ne ya tashi shima. Ya shiga knocking ƙofar yana kiran sunanta amma shiru. Sai ya fara tunanin kodai batama rayene? Gata tare da ciwo mai haɗari. Wayar Shahidah ya kira yace ta dawo gida yanzun nan. Hankali tashe ta shiga tambayarsa lafiya? Dan ita bata tashi a nata aikin ba. Amma sai yace ba komai tazo dai kawai. Daga haka ya yanke kiran ya fita neman maigadi dan yazo su gwada ɓalla ƙofar. Babu jimawa suka dawo, zuwa lokacin yaran nata kuka suna sake buga ƙofar. Sunta ƙoƙarin buge ƙofar amma bata ɓallun ba, dole maigadi ya ce, “Yallaɓai sai dai fa a nemo wanda yasan aikin karma ayi ɓarna. Bara muga na kira wani yaro dana sani”.
Kai kawai Uncle Sadeeq ɗin ya iya ɗaga masa. Dai-dai nan Shahidah ke shigowa a ruɗe. Cikin tashin hankali take tambayarsa abinda ya faru. Bayani ya mata kamar yanda Linda ta masa. A take jikin Shahidah ya kama rawa. Itama ƙofar ta fara bugawa muryarta na rawa tana kiran sunan Maanal ɗin amma shiru. Wani tunani ne yazo mata, ta fita cikin sassarfa zuwa can baya inda windows ɗin ɗakin suke. Binta shima mijin nata yay. Kwance suka hango Maanal sharɓan a gado babu alamar rai a tare da ita. Ai Shahidah bama tasan tayi wani irin yin baya ba tana neman faɗuwa sai da mijinta ya tarota. Cikin rawar baki data murya ta ce, “Honey ta rasu ko? Da alama Maanal bata numfashi”.
“In sha ALLAHU bata rasu ba Honey cool down. Zata iya yiwuwa suma tayi ko barci take”.
“Barci! Ina badai barci ba Honey.....”
Isowar su maigadi ya hanashi bata amsa. Kamata yay suka koma cikin gidan. Cikin abinda bai wuce mintuna goma ba aka ɓalle ƙofar ɗakin. Daga Shahidah har mijinta da yaran a guje suka afka ciki. Lokaci ɗaya ita da yaran suka zagaye Maanal ɗin. Koda ta cacumota sai tai mata wani jagab alamar babu rai tare da ita. “ Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un”. Ta shiga ambata jikinta na rawa. Yayinda yaran suka fara ihun kuka suna kiran Maanal ɗin. Shi kam mijinta ƙoƙarin neman number RK yake yi, sai dai sam taƙi shiga. Dole ya koma neman Dr Ranjet. Cikin Sa'a kuwa sai ita ta shiga. Bayani ya masa a taƙaice, hankali tashe Dr Ranjet yace gashi nan zuwa gidan RK ya shiga theater ɗin gaggawa ne tun ɗazun shiyyasa bazai samesa ba.
Alhamdullah Dr Ranjet ya iso akan lokaci tare da wata abokiyar aikinsa. Dandanan ya saka kowa ya fito suka kasance su biyu kawai a ɗakin. Taimakon gaggawa suka shiga bama Maanal ɗin, sunfi awa ɗaya kafin cikin amincin UBANGIJI ta farfaɗo. Dama ya tabbatar musu su kwantar da hankalinsu bugun zuciyarta ne yay ƙasa sosai shiyyasa numfashinta ya dakata ma amma tana da rai. Basu bari kowa ya shigo ba sai da suka gama dai-daita komai suka saka mata ruwa da allurai sannan.
Bayanin da Dr Ranjet yamusu ya saka su dinga sauke ajiyar zuciya a tare. Shahidah ta dinga share hawaye. Su duka suka shiga tare da yaran da mijin nata, ganin Maanal ɗin na barcinta hankali kwance ya sake saka musu nutsuwa. Bayan fitowarsu ne Dr Ranjet ke sanar musu dolene su kula sosai da shan maganin Maanal ɗin, dan yanzu ma yana tunanin sakacin hakanne ya kawo wannan matsalar, duk da ya fahimci akwai damuwa tattare da ita bai faɗa musu ba dai. Hakan kuwa ɗin ne kamar yanda yay hasashe, dan yasa an kawo masa magungunan ya duba ashe kona safe bata sha ba ta fita. Ya sake tabbatar musu da kula da shan maganin nata da shigarta kowacce matsalar damuwa komai ƙanƙantarta sannan suka wuce.
Dole yau Shahidah tare ta kwana da Maanal. Alhamdullah ta tashi cikin aminci kuma. Dukkan wata kulawa Shahidah ce ta bata a wannan safiyar, harda yara kowa tattalinta yake yi, hatta da abinci tara suka bata a baki, hakan ya sakasu makarar fita dan sai da ta sake komawa barci sannan. Bayan ta farka Linda tai ƙoƙarin taimaka mata tai wanka taci abinci tare da sanar mata zuwan RK gidan har sau biyu, amma sai Maanal ɗin taƙi cewa komai tana zaune kawai tana hawaye. Ana haka RK ya sake dawowa. Babu lallashin da Linda batai mata ba akan taje su gaisa ko shi ya shigo amma taƙi, tanata kukanta kawai. Hankalinta sai ya sake tashi tai kiran Shahidah dake a wajen aiki ta sanar mata. Cikin