Showing 15001 words to 18000 words out of 59211 words

Chapter 6 - AJIYA A DUHU Book Complete Original billy.docx

04 Feb 2025

26262

kai wa duƙe ya ɗauki abinda idonsa ya sauka a kai tun fitowarsa dake yashe a ƙasa. Agogo ne silver na mata mai ƙyau sosai, juyawa yay ya kalla motar daya jingina batare da yayima agogon wani kallon tsaf ba. Har ya kai hannu zai aza agogon saman motar da tunanin maybe masu motar ne suka yadda sai kuma ya fasa. Tunanin ajiyewa yay a hannunsa dan maybe su haɗu da masu motar sai ya basu, kada ya ajiye kuma wani ya ɗauka dan a ɗan kallon fisha da yay ma agogon ya fahimci mai daraja ne da za'a iya sayensa da kuɗi masu yawa. Motar da suka fito ya buɗe ya jefa agogon sit ɗin mai zaman banza daya zauna dan ɗayan ne yayo driving ɗin.  Daga haka ya juya abinsa kawai....

    ______________★

   Duk da yawan taron jama'a bai hana ai musu tarba ta musamman ba da girmamawa da mutuntawa. Dan can ƙuryar ɗakin amaryar gidan aka kaisu tare da musu sauka ta musamman da abinci da kayan ciye-ciye irin na biki. Sai nan nan Hajiya Majdiya keyi da Ammie dan tuntuni take son su jone su zama ƙawaye Ammien ce dai bata maida hankali ba. Ita kuma ba komai yasa hakan ba sai sanin uwargidanta jone suke da Hajiya Yaya 5&6, ko bikin nan ma dan na yarinyar matar tsakkiya ce shiyyasa Hajiya Yayan bata zo ba saboda suna matuƙar adawa da juna. Ita kuma aminiyar Hajiya Basariyya ce dan ita tun sassafe ma tana nan Zaria ɗin da duka yaranta kuma kwana zasuyi dan har Abuja inda za'akai amarya zasuje ma.

        Ƙorafin da take tayi yasa Ammie bama su Maanal umarnin cin abincin. Amrah ce ta zuba ma Ammie sannan ta zuba musu. Maanal na cewa ta ƙoshi Hajiya Majdiya tace, “Haba ɗiyata kada kimin haka mana, idan kuma baƙya sonshi na canjo miki wani ko na dafo miki yanzun nan”.

     Da sauri ta ɗauki spoon ta saka cikin abincin, hakan ya saka Amra kwashewa da dariya. Sunci abincin Ammie da Hajiya Majdiya na hira sai ga wata budurwar yarinya ta shigo ɗakin. Zasu iya zama sa'anni dasu Maanal, tayi ƙyau cikin lass da nake ƙyautata zaton ankonsu kenan dan ƴammata da yawa na dashi a wajen bikin. Tafawa suka ɗan yi da Amrah alamar sun san juna sosai sai kuma ta ɗan zunguri Maanal cike da tsokana ta furta, “Kurman Ammie”. Hararta Maanal ta ɗan yi duk da ba wani sabo sukai ba gaskiya, dan ko gidan sukaje iyakar Maanal ɗin da su gaisuwa ne. Cikin dariyar da suke ta gaida Ammie, yayinda Amrah ke faɗin, “Amma fa sunan nan ya dace da ita sosai, Najwa kin iya saka suna ALLAH”.

     Dariya Ammie da Hajiya Majdiya suka sake yi. Nan dai suka cigaba da tsokanar Maanal ita da Amrahn. Bayan sun tsagaita ta dubi Maman nata tana faɗin, “Ummy Uncle Rafeeq fa ya iso”.

       “Oh Masha ALLAH har ya ƙaraso, da'alama gudun nashi na tsiya yayi kenan. Yana ina?”.

      “Na kaisa ƙaramin falonki wai yunwa yake ji, sai yaci abinci zai fita wajen ɗaurin aure”.

   Ƴar dariya tai da faɗin, “Acici kenan mala'ikun tauna. Ga key dama na haɗa masa abincin ai. Idan kin ɗauka ki rufe min kitchen ɗin, sai ya gama sai nazo mu gaisa”.

       Amsa tai tana miƙewa, sai kuma ta kalli su Amrah, “Ku taso muje kunzo kun ƙunshe a nan. Amrah karfa ki bari Maanal ta koya miki halinta”.

       Da sauri Amra ta ce, “Da naga takaina. Maanal fa ko maijego bazata faɗa mata zaman ɗaki ba, magana kuwa yakan iya sati batayi da kowa ba”.

     Hararar su Maanal tayi batare data motsa ba ko yin magana. Ganin haka suka fahimci bazanje ba. Dan haka Najma tai saurin kai ƙararta wajen Ammie. “Ammie kinga wai bazata ba”.

   Kallon Maanal Ammie tayi dole ta miƙe badan taso ba suka fita. Kitchen ɗin ta shiga ta ɗauka basket ɗin da aka shirya kayan abincin sanan suka bi wani ƙofa, roƙonsu take akan suje kai amarya Abuja dan ALLAH. Yayinda Amrah ke bata amsa da basuzo da wasu kaya ba. Dai-dai zasu shiga take cewa baga nata kayan ba tasan zasu musu ai, kokuma idan zasu wuce Abujan su tsaya kd ɗin su ɗauki kayan. Shigarsu tasa babu wanda ya bata amsa. Falone ƙarami amma yayi ƙyau sosai cikin tsari.

      “I'm sorry Uncle na barka kana jira”. Ta faɗa dai-dai tana ƙarasawa gaban mutumin dake zaune ya ɗan juya ma ƙofa baya ta yanda basa ganin fuskarsa da ƙyau. Juyowa yay ya kallo ta inda suke cikin sigar harara, sai idanunsa cikin na Maanal.

Cak kuwa ta tsaya kamar wadda aka buge mata ƙafafu da sanda, hakama numfashinta sai da yay rawa. Shima ɗin da wani kalar mamaki ya zuba mata idanunsa har yana ɗan warosu waje na kasa ɓoye mamaki. Sai yanda yay ɗin ya saka su Amrah kallon Maanal ɗin suma cike da tambayoyi.

        Lips ɗinsa ne suka ɗan motsa a hankali ya faɗi abinda ita da su duk basu ji ba. Yayinda Najma ta furta, “Uncle ko ka sansu ne?”.

   Maimakon amsa mata sai ya saki wani ƙayataccen murmushi kawai da kai hannu ya ɗan shafo sajensa siriri yana lumshe idanu da kauda kansa gefe. Itama Maanal janye nata idanun tayi a hankali daga garesa, sai kuma ta juya da nufin fita. Najma ce ta riƙota da sauri tana faɗin, “Kimma isa madam. Dawo ku gaisa. Ai mu wannan abin farin ciki ne agaremu Uncle Rafeeq da budurwa a yau”.

     Da sauri Maanal ta harareta da faɗin, “Aka faɗa miki”.

        “Basai an faɗa mana ba komai ya bayyana kansa ko Amrah?”. Tai maganar da kallon Amrah da jikinta duk yay sanyi. Murmushin yaƙe ta mata da faɗin, “Ai kam dai gara mu sani”. Maanal zatayi magana suka ja hannunta suka ƙarasa cikin falon dole badan taso ba. Zama sukayi ita da Amrah, yayinda Najma ta duƙa gabansa tana haɗa masa abincin. Shiko ya zuba ma Maanal ido ko ƙyaftawa baiyi. Ita kuma data ɗago taga ita ɗin yake kallo sai ta ɗan hararesa, shi kuma ya sakar mata murmushi. A haka Amrah ta gaishesa. Ya amsa mata cike da basarwa kafin ya maida dubansa ga Najma, cikin sigar tambaya yay mata nuni da Maanal. Juyawa tai ta kalleta itama da ƴar dariya a fuskarta ta ce, Ƙawayena ne kuma ƴan uwana.”

      “Uhm yayi ƙyau” ya faɗa yana maido kallonsa kan Maanal dai. Hakan yasa cikin dauriya da sake tsuke fuska ta ce masa “Ina yini”.

     Kansa tsaye ya amsa da, “Ya gajiyar tafiya? Da ƙin amsa min waya?”.

          Jitai kamar ta ja abu ta wulwula masa bisa kai amma dai ta daure kodan su Najma, batare data kallesa ba ta ce, “Hummm”.

      Shima Humm ɗin ya faɗa yana ɗaukar spoon ya fara cin abincinsa.

     “Oh oh mukam an sakamu a duhu, Uncle Please ka mana bayani”.

    “To uwar gulma anƙi ɗin. Ga ƙofa maza kama gabanki idan na gama zan nemoki. Auntyn ma kice ta hutar da kanta ma gaisa bayan an ɗaura auren”.

          “Oyooooo!! Korarmu ma ake, kinga Amrah taso mu ware to”. Tai maganar tana kama hannun Amrah suka nufi ƙofa. Miƙewa itama Maanal tayi dan bazata yarda a barsu su biyu ba, sai taga shima ya miƙe idanunsa a kanta kamar zai cinyenta da su.........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)

2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)

3 DUNIYAR MU (Huguma)

4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500

Book 2:-1000

Book 3:-1500

Book 4:-2000

0022419171

Access bank

Maryam Sani Gumi

Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷

1000CF

89825722

Nousaiba Lawali Maradi

Shaida:-09033181070

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_

ب

ِ

س

ْ

م

ِ

الل

َّ

ه

ِ

الر

َّ

ح

ْ

م

َٰ

ن

ِ

الر

َّ

ح

ِ

يم

_*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖🔟

______________

Abubuwan da nake saidawa

Atamfofi

Laces

Shadda

Materials

Takalma

Jakunkuna

Mayafai

Trolley

Sarka da dan kunne

Oil perfumes

Numbers

08034469681

08135142610

Handles

Instagram @ummu_mahnoor_luxuries

TikTok username @ummu_mahnoor_luxuries

Facebook ummu_mahnoor_luxuries

____________

........Fuska ta ɓata sosai kafin ta kallesa babu wasa. “Kasan fa bana son irin haka ko?”.

        Kansa ya ɗan rausayar gefe yana murmushi da raba idanunsa a kanta. Cikin raɗa-raɗa ya ce, “Sam ban sani ba sai dai yanzu da kika faɗa min”.

   Harararsa ta sake yi zata raɓasa ta wuce yay saurin shan gabanta yana ƙara faɗaɗa murmushinsa. “ALLAH idan kika ce sai kin fita tare zamu fita ne, kuma duk inda kika shiga sai na biki a gidan nan kin dai sani”.

      Ɗagowa tai da mamaki ta kallesa, “Ka bini fa?”.

     “Yes gwada kuma ki gani, kin dai sai ni nafi mayen ƙarfe ai garama ki koma ki zauna kawai”.

     Kanta kawai ta ɗan girgiza, a zuciyata tana faɗin (Kai guy ɗin nan bala'i ne). A fili kam sai kawai ta koma ta zauna a kujerar dake kusa da ƙofar dama anan ta tashi. Ajiyar zuciya ya sauke shima tare da komawa ya zauna a inda ya tashi. Sai da ya ɗiba abincin zai kai baki sannan ya ɗago ya kalleta. “Bismillah”. Kanta ta girgiza masa kawai batace komai ba. Shima sai bai damu ba ya cigaba da faɗin, “Ina su Aneesa?”.

        “Gida”.

     Ta faɗa a taƙaice.

Kansa ya jinjina kawai shima. Sai kuma falon yay ɗan shiru, a can ƙasan zuciyarsa wani irin farin cikine ke ɗawainiya da shi. Har dai ya kasa dannewa sai da ya furta, “Ashe ma ni a gida nake farauta amma naita wahalar da kaina. Ya kuke da su Najma?”.

       Ɗagowa tayi na ɗan kallesa, ganin shima ita yake kallo sai ta maida kanta ga wayata kawai.

     “Humm zama da miskilin mutum dai sai haƙuri, shike nan tunda bazaki sanar min ba. In tai wari naji. Ni bara na faɗa miki nawa alaƙan da su to. Mahaifiyarta Yaya tace uwa ɗaya uba ɗaya. Nine autan ɗakinsu, shiyyasa kikaji Najma na kirana Uncle”.

         Har cikin rai sai da taji tashin hankalin alaƙar tasu. Amma sai ta dake a taƙaice ta ce, “Masha ALLAH”.

  Murmushi yayi da ɗan girgiza kansa. Dai-dai nan Hajiya Majdiya tayi sallama. Amsawa yay yana mai maida dubansa ga ƙofar tare da bata izinin shigowa. Koda ta shigo idonta a kansu, fuskarta kuma ƙawace da murmushi. “Auta na kasa haƙuri ne ALLAH, yanzu Najma taje mana da wani daddaɗan labari”.

      “Kai wannan yarinya da gulma take aunty”.

    Cikin dariya Hajiya Majdiya ta ce, “Aini gulmar tata ta biyani. Kai idan hakan ta kasance zanyi matuƙar farin ciki Rafeeq. Kaga tuwona maina kenan, ALLAH ya tabbatar da alkairi dai”.

         Ko kunya Babu ya amsa da, “Amin aunty. Sai kita tayani addu'a dan gimbiyar har yanzu taƙi bani babban fili koda na zuwa gidane a sanni. Kuma shekara ɗaya kenan muna tare”.

      “Kai haba shekara ɗaya fa? Wai kodai dama itace kake faɗa mana ni da Aunty Babba kwanaki wadda kuka haɗu a jos?”.

     “Tabbas itace aunty”.

   “Ikon ALLAH, ni ashema abu a kusa dani yake haka. Karka wani damu kanka Maanal yarinyar kirki ce kamar yanda kake mutumin kirki. Na tabbatar itama zata soka”.

           Ko kunya babu ya kalli Maanal yana wani ɗage gira da faɗin, “Wai haka?”.

     Da sauri ta ɗauke kanta zuciyata na wani irin gudu da sauri-sauri. Yayinda take jin wani irin takaicinsa na yanda ya ɗaureta gaba ɗaya a wajen matar da take matuƙar ganin girma da kimarta. (Ya ilahi, RK kuwa nada hankali?) Ta ayyana a zuciyarta tana jin kamar ta saki kuka. Ita sai ma taji tausayin Hajiya Majdiya ɗin yanda taketa farin ciki kamar ma ance an aura masa Maanal ɗin.....

   

        Bayan ficewarta ta kallesa da idanunta da suka kaɗa dan masifar dake cin ranta. Sai dai tana motsa baki zatayi magana ya mike yana dariya. “Koma mi kike son faɗa haɗiye abinki ni na tafi wajen ɗaurin aure, ALLAH yasa muma azo namu nan kusa”. Yay ficewarsa yana kashe min ido ɗaya ga dariyar rainin wayo yana yi. Yana fita baifi da mintuna biyu ba, kafin Maanal ta gama tattaro abinda ya dunƙule mata nunfashi Najma da Amra suka dawo. Rungumeta Najma tai tana farin ciki wai zata zama matar Uncle ɗinta. Surutanta take amma ita Maanal sam bata wani fahimtar komai....

     _____________★

        “Wai nikam lafiya duk kin zama wata sukuku ko duk gajiyar bikin ce haka Auta?”.

    Didi Shahidah ce mai maganar tana zama kusa da Manaal dake kwance a doguwar kujera idanunta a lumshe. Tunda suka shigo gidan ta zube a wajen tana bitar abinda ya faru a Zaria. Ƙaramin murmushi ta sakar ma ƴar uwar tata. Sai kuma ta yunƙura ta tashi zaune sosai. “Babu komai Didi. Kawai na kwanta ne dai”.

    Murmushi Didin tai mata, sai kuma ta kai hannu ta ɗan shafi fuskarta. “Auta gyaran jikin nan na amsarki sosai. Idan kika yosa duk sai ki canja kamar wata amarya dake”.

        Da sauri Maanal ta ɓata fuska. Zatai magana aka buga ƙofar falon da ƙarfi har duk sai da suka razana. Hajiya Yaya ce sai yaranta biyu biye da ita. Cikin hargagi da masifa ta shiga ƙwala kiran ainahin sunan Ammie. Duk miƙewa sukayi, dan yanda take a birkice zakasan babu lafiya. Ita kanta Ammie da sauri ta fito ɗankwalinta a hannu.

      “Ya salam Hajiya miya faru?”. Ammien ta faɗa tana ƙarasowa cikin falon da sassarfa.

   “Oh tambayata ma kike miya faru? Wai Asiya nikam kodai ke kika haifar min Yazeed a gidan nan ne?”.

        A hankali Ammie ta sauke ajiyar zuciya tana mai girgiza kanta. Sai kuma a nutsenta ta bata amsa da “Hajiya kiyi hakuri ban san akanmi kike magana ba. Yazeed ai kowa yasan kece kika haifesa”.

      “To kuwa tunda kin san ni na haifi abina ki fitar min sabgar yaro. Dan wlhy idan ma kina mafarki ne ki farka. Ki kuma je ki sanarma bokanki anan anfi ƙarfinki anfi ƙarfin tsafinsa. Alhajin dai da kika iya mallaka har kika aura kinci nasara, wataran kuma ruwa zai ƙarema ɗan kada shima. Amma Yazeed har gaban abada bazai auri wannan ƴar taki ba, wancan ya samu ya gudu da ƙyar ko nace uwarsa ta miƙe tsaye a kanku shine ni za'a ƙaƙudubar min yaro da tsafi da asiri a haɗashi da sauran ciwo. Kuma wlhy daga yau sai yau, kika sake ɗaukar min yaro ya kaiki anguwa duk abinda nai miki kece kika jashi a gidan nan, mayyar mata kawai.......”

      “Haba Mamma nafa miki bayani Daddy ne yace muje ba laifin Ammie bane ba”. Yazeed daya shigo falon ya katseta cikin sarƙewar murya. Kansa ta juya da masifa kamar zata cinyesa. Harda faɗin idan har bai rabu da Maanal ba ALLAH sai ta ɗaga masa mama. Sai kuma ta juyo ga Ammien ta cigaba da mata zagi na rashin mutunci da gori. Gaba ɗaya rayukansu Shahidah sun gama ɓaci, yayinda Amal ta kasa haƙuri ta yunƙura zata tanka mata Ammie ta hanata. Dole tai shiru. Da gudu Maanal tabar falon kuka mai ƙarfi na ƙwace mata. Hakan yasa Amal bin bayanta itama zuciyarta kamar zata kama da wuta. Sam bata so Ammie ta hanata ba. Amma koba yau ba ta ɗauki alwashin sai ta gogema matar nan abinda ke kanta. Haba wanna abin ya isa haka mana. Tasara miyyasa mutanen nan basu da adalci sam, kowa dai Ammiensu kowa Amminsu sai kace itace kaɗai kishiyarsu. Taga dai suma kishiyoyin juna ne, amma basa fitinar juna sai Ammie, shin sai yaushe ne Ammiensu zataji daɗin rayuwar aurenta?. A gidan mahaifinsu bata zauna lafiya ba, fitinar miji data uwar miji, aka dawo ta kishiya har sai da ta bar musu gidan, yanzu kuma anan ta kishiyoyi har biyu....

      Sosai Hajiya Yaya ta diga jidali da tujara wa Ammie kamar ta samu ɗiyarta. Ammien kuma bata tanka ba bata bar ƴaƴanta sun tanka ba. Hakan kuma shine mafi mata ciwo, kai su duka su wannan shirun da Ammien ke musu akoda yaushe na ƙona musu zuciya da ruhinsu. So da yawa suna mata abu dan ta tanka amma sai ta basar. Da ƙyar Yazeed ya lallaɓata ta fita. Suka bar Ammie da su Manaal cikin matsanancin ɓacin rai. Ga Ammie ta hana kowa maganar har dare sashen nasu babu daɗi. Hakan yasa duk suka kwanta da wuri. Sai can cikin dare Maanal ta bar ɗakinsu da ayanzu yake nata ita kaɗai sai idan sauran ƴan uwan nata sunzo gidan ne ta koma na Ammien. Ta sameta tana salla, dan haka itama ta fasa kwanciyar tayo alwala tabi sahunta. Sai da sukai sallar asubahi suka ɗan sake kwanciya Maanal ɗin dai nata daurewa dan bata jin daɗi......

  ____________

    “Wai Auta bazaki tashi a barcin nan naki ba haka nan. Jibafa lokaci ko kari bakiyi ba, ga ƴan uwanki na jiranki ki rakasu gidan mai gyaran jiki. Suna fara damunki kuma nasan zaki manta da yunwar cikinki ne

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login