Showing 57001 words to 59211 words out of 59211 words

Chapter 20 - AJIYA A DUHU Book Complete Original billy.docx

04 Feb 2025

26272

kanta da baya so zai ƙare. Dan tuni Hajiya Basariyya tayi uwa tayi maɗaukiya a bikin shiyyasa ita ake kiranta ƴar baƙin ciki. Haka dai dole Daddy ya bari dan yana matuƙar jin kunyar Ammie ta roƙesa abu ya kasa mata saboda dattakonta itama, sai dai da sharaɗin karsu wuce sati ɗaya, idan kuma hakan ta faru zasu sha mamakinsa. To a hakan ma dai Ammie bata tsira ba dan sai da tasha zagi da habaice-habaice. Ita dai bata kulasu ba kamar yanda ta saba. Sai ma ta maida hankali akan shirin Daddy da shima yake yi dan wannan shine karo na biyu da zai aurar. Na farko ya aurar da su Shahidah da Asalamiyya a rana ɗaya, duk da dai an kwashi matuƙar rikici a wannan aure dan Hajiya Yaya cewa tai baza'a haɗa mata auren ƴa da agololi ba. Shiko yace tayi kaɗan tayi tsororo ma.  Bayan dai an sha fama dole ta haƙura akayi yanda ya tsara ɗin. Sai dai ita Asalamiyya ma nata auren bamai jimawa bane. Dan a gida ma ta haifi ƴarta. To yanzu ko Yazeed kaɗai za'a aurar. Babban ɗansa kuma namiji, sannan ɗa mafi soyuwa a garesa da Hajiya Yaya. Damma ALLAH ya ragewa aya zaƙinta auren ba wanda yake so bane ba. Saboda har yanzu sam Daddy baya son wannan haɗin kawai dai babu yanda zai yi ne ya haƙura. Amma yaci alwashin sai ya bama kowa mamaki a auren Maanal da Yazeed in sha ALLAHU.

    To daga can gidan Alhaji Mamman ma dai shirin suke. Dan jikokin duka biyu nasu ne, dan haka dole suma su taka tasu rawar da aljihunsu da kuma matsayinsu. Dan haka suka kasance cikin irin nasu shirin su da sauran ƴaƴansu da dangi. Dan ko tafiya Dubai ta zama kamar za'ayi ta a tare ne bisa ɓangarori biyu. Ba Hajiya Yaya da Asalamiyya da Baraka bane kawai a tafiyar harda mahaifiyar su Hajiya Yaya ɗin da kuma wasu ƙannensu Hajiya Yayan su biyu, da harda Aunty Sabuwa amma ta zamewa tafiyar dan akwai binne-binnen da suke son zuwa suyi a inda za'a saka amarya duk da ma Daddy ya ɓata musu tafiyar da buri wai anan gidan su Yazeed ɗin zasu fara zama a tare da su. A yanzu hakama ana kan gyara sashen samarin gidan da dama shine dai zaune a ciki kasancewarsa namiji tilo a baya sai yanzu da Ammie ta haifi Waleed da Hameed. Suma acan ɗin suke amma yanzu Daddy yasa ana musu nasu ginin ata can bayan na Yazeed ɗin kasancewar akwai fili sosai. Sai suka dawo sashen Ammie yanzu tunda ita kaɗaice. A wannan gini ma dai sai da akai ɗan rikici, ɗan daga Hajiya Yaya har Hajiya Basariyya nunawa sukai basu yarda ba. Sai da Daddyn yay musu kaca-kaca yace idan akwai wadda ta haifesa a cikinsu kota saya masa gidan ko suka haɗa kuɗi suka saya to tazo ta hanashi yima yaransa wajen zama sannan suka kama kansu. Amma hakan bai hanasu komawa gefe suna zagin Ammie ba da aibantata.

___________★

       Shine ya fara fita a elevator ɗin, hakan yasa AS da driver rufa masa baya cikin hanzari. Cikin takaici da ƙunar zuciya Maanal ta raka bayansu da harara kafin itama ta fito tana jan tsaki. Maimakon tabi bayansu sai kawai ta samu waje ta zauna anan wajen elevator ɗin. Tsahon mintuna goma sai ga AS ya dawo wajen. Da mamaki yake faɗin, “Ina can inata tunanin inda kika maƙale ashe kina nan.”

    Ɗan ɗagowa tai kawai ta kallesa batare da tace dashi komai ba. Shima sai ya kama kansa dan ya fahimci Maanal irin mutanen nan ne masu masifar miskilanci da kame kai. Har office ɗin Directors Mustapha ya kaita, sai dai sun samu baya ciki da alama ya ɗan fita. Wajen zama ya nuna mata yana faɗin, “Ki jirasa anan duk inda yake nasan baiyi nisa ba”.

Kanta kawai ta iya jinjina masa. Shima sai ya juya ya fita abinsa. Bayan futarsa ajiyar zuciya ta ɗan sauke da numfashi mai ƙarfi. Dai-dai lokacin idanunta suka sauka akan hotuna huɗu da aka saka daga can saman saitin inda kujerar mai office ɗin take. Hoton farko shugaban ƙasa ne a jiki, sai Ministan Abuja. Hoto na biyu AA Darma ne da yay wani kalar masifar ƙyau, sanye yake cikin wasu shegun suit baƙaƙe da adon gold a jikinsu mai matuƙar ƙyalli, yaɗan zauna a saman kujera mai tsaho ɗin nan, sai ya kasance kamar ya zauna a karkace ƙafarsa ɗaya ya sakko ƙasa sosai ɗayar na daga jikin ƙarfen da akaima kujerar kwalliya. Takalminsa baƙi da kwalliyar gold shima. Bai saka rigar suit ɗin ba, yana riƙe da ita ne kawai da hannunsa na dama dake sanye da agogo kalar gold a saman kafaɗarsa, sai farar long sleeve shirt ɗin data sauna ɗaran a jikinsa ta fiddo da girman jikin dake a buɗe. Ya saki wani mayataccen murmushi daya sakata ƙurama cikakkiyar fuskarsa mai kwarjini da adon gashi ido. Idanunsa sanye da farin gilashi da tun ƙuruciya tasan yana sakawa. Sun wani haska oily idanun nasa da suke farare tas kamar an watsa musu madara tsabar yanda suke ƙyalli da ɗaukar idanu....

Kaɗan Director Mustapha ya ɗan bubbuga desk ɗin, dan sai sallama yake amma babu alamar tasan da shigowarsa. Numfashi ta ɗan ja ta fesar cike da kame kanta da vasarwa ta dawo hayyacinta. Murmushi ya ɗan yi a ƙasan ransa yace (Boss Sarkin sa'a. Akoda yaushe cikin kama zuciyar ƴammata yake).

    Ita kam kicin-kicin ta sake yi da fuska sannan ta shiga gaishe da Director ɗin. Ya amsa mata da kulawa tare da mata barka da zuwa. Kanta kawai ta jinjina masa shi kuma yakai zaune yana ɗaukar file ɗinta ya shiga dubawa. Sai lokacin ta sake bin office ɗin da kallo daki-daki, idonta ta ƙarasa saukewa akan hoton AA ɗin, sai kuma ya janye ta maida kan ɗayan hoton dake kusa da nasa da bata kalla ba. Mace ce sanye cikin baƙin hijjab da niƙab, hatta idanun nata ana iya ganinsu ne kawai ta cikin sirrin farin gilashin data sanya. Hakan yasa baka isa tantance wacece a hoton ba duk iya kallon ƙurullarka da bin ƙwaƙwaƙwafi, dan hoton yasha editing ta yanda aka ɓadda kamanin komai.

      A hankali ta taɓe baki da sake kauda kanta zuciyarta na ayyana ma maybe matarsa ce. Tunkuɗe tunanin tayi gefe ta maida hankalinta ga Director Mustapha dake mata magana. Umarnin biyosa ya bata, babu musu ta miƙe tare da ɗaukar hand bag ɗinta tabi bayansa. Wani office dake kusa da nashi suka shiga. Nan ma sun sami mai office ɗin daya kasance ba bahaushe ba. Bayan sun gaisa ya amshi file ɗin hannun Director Mustapha ya saka hannu. Daga haka suka fito. A ƙofa suka haɗu da wani matashin saurayi, cike da girmamawa ya shiga gaida Director. Shima ya amsa masa da kulawa yana nuna masa Maanal.

“Itama Watch Designer ce, kaje da ita department naku, sit ɗin da aka shirya jiya nata ne”.

Fuskar saurayin da murmushi yana kallon Maanal ya amsa ma Director da girmamawa. Ita ko sai wani basarwa take. Bai damu ba ya fara gaidata, sai ta amsa kamar wadda taji kunya. Shi dai director kallonsu kawai yake yana sake jinjina miskilancin yarinyar.

Saurayin daya kira sunansa da Yaqub tun'a cikin Elevator ɗin ya gabatar mata da kansa matsayin Watch Designer shima. Ɗan murmushi kawai Maanal ta masa. Dan ta fahimci yana da nutsuwa. Koda suka fito anata kallonsu, bata damu ba dan ita babu wanda take kallo har suka iso rukunin su daya kasance matsayin office. Su takwas ne, kuma duk artists ne suma ɗin, sai dai abin damuwar ita kaɗai ce mace a cikinsu. Amma sai ta dake, dan tasan zata iya zama da kowa. Ta gaishesu tana sake ɗaure fuska ganin yanda suke kallonta. Yayinda Yaqub ya gabatar da ita a wajensu shi dai. Suma ya shiga gabatar da su da sunayensu ɗaya bayan ɗaya. Kafin ya nuna mata wajen zamanta dake a farko. Sun mata maraba da zuwa cikin farin ciki, itama sai ta ɗan musu murmushi kaɗan. Daga haka takai zaune tana dudduba komai nata dake a wajen. Batare data damu dasu ba kuma wayarta ta ɗauka ta shiga ɗaukar komai na iya wajenta hoto, Ammie ta turamawa, alamar wayar a hannun Ammie take mintuna biyu ba'a ƙullaba sai ga video call ɗin Ammien ya shigo. Murmushi mai sanyi Maanal ta saki tana mai gaggawar amsa kiran sai ga Ammie tar-tar ta fito. Cikin murmushin farin ciki Maanal tace, “Uhm kaga amaryar Daddy”.

     Daƙuwa Ammie tai mata itama tana murmushin ta ce, “Ungo naki nan ja'ira yau kuma nice bar tsokanrki”.

       Karo na farko Maanal ta sanya dariya, abinda kakan daɗe a yanzu baka gani ba a tare da ita. Duk ko sai samarin suka shagala suna kallonta duk da su basa ganin Ammie sabo a desk ta ɗaura wayar. Ita ko cikin rashin damuwa da wanzuwar su a wajen tace da Ammie, “Tom yi haƙuri Hajiya Ammie na. Ina fatan kin tashi cikin aminci da ƙoshin lafiya tare da farin ciki a wannan rana ta laraba ranar samu inji Nene”.

       Sosai murmushin Ammie ya sake ƙawatuwa. Da kulawa ta ce, “Alhamdullah Auta. Ya ƙarfin jikinki? Ya kuma sabon office?”.

     “Alhamdullahi Ammie na warke abuna. Sabon office kuma gashi ki sanya masa albarka daga bakinki mai tsarki”. Tai maganar tana miƙewa da wayar a hannu ta maida back camara tana haska mata ko'ina na office ɗin, sai dai koda wasa bata yarda ta hasko samarin nan ba. Sosai Ammie ta shiga yabawa da sanya albarka. Ta kumayi addu'oi sosai ga autar tata. Sannan suka ɗan yi hira sukai sallama tace ta fara aikinta. Fuskarta da murmushi ta ajiye wayar, ita kaɗai tasan irin tari-tarin ƙaunar da takema wannan baiwar ALLAH. Mahaifiyarsu dabance a cikin daban ɗin da bazai ƙididdigu a zukatansu ba. Fatansu dai ALLAH ya ƙara mata lafiya da nisan kwana masu albarka. (Tare da iyayenmu baki ɗaya. Ka gafartama wanda muka rasa ka yafe musu KURAKURANSU😭🙏 damu da muke raye baki ɗaya).

     Jan kujerar tata tai har zuwa gaban kantar da aka ajiye musu a office ɗin dan kusan da ita ma aka zagaye wajen. Komai na kayan zane-zanen da zasu iya buƙata akwai a wajen. A haka ta zazzaɓo duk abinda take buƙata a lokacin ta sake burko tayoyin kujerar ta dawo da ita mazauninta. Sosai ta ringa ƙoƙarin ture komai a ranta ta maida hankalinta ga fara abinda ya kawota duk da tana ji a jikinta sauran abokan aikinta hankalinsu na a kanta ta wani sharesu tamkar ita ɗaya ce a wajen.

Wani zanen Designs na agoguna data ƙirƙira yanzun nan a kanta ta fara cike da ƙwarewa. Cikin ƙanƙanin lokaci ya haɗa su tsaf su biyu kamar ka saka hannu ka ɗauka daga takardan. Bayan ta gama zana su a dunƙule sai kuma ta koma zana ɓangare-ɓangare ɗin jikinsu kowanne tana saka masa suna da amfanin da zai yi a cikin agogon. Hakanne ya ja mata lokaci sosai dan har ƙarfe ɗayan rana. Jin ana kiran sallar zuhur daga masallacin cikin companyn ya sata sauke ajiyar zuciya da ajiye kayan aikin nata ta miƙar da hannunta da ya ɗan sage da ambaton sunan ALLAH.

      Miƙewa tai zuwa window ɗin office ɗin ta leƙa batare data ma kowa magana ba, dan daga wajen ana hango masallacin. Hango ma'aikata tayi nata fita zuwa ƙatuwar harabar companyn. Ganin mazansu da matansu ne yasa ta fahimci masallacin harda mata kenan. Dan wasu ma na ƙoƙarin shigane yayinda wasu suka kasance rukuni-rukini suna hirarsu. Sai wasu dake alwala ta can ƙarshen katangar inda aka tanada domin hakan. Huci taɗan furzar daga bakinta tare da barin wajen, dai-dai suma su Yaqub na miƙewa. Sauran fita sukai gulma fal bakinsu, yayinda shi kuma Yaqub yazo inda take.

Shine ya sanar mata tazo suje salla. Kanta kawai ta jinjina masa ta baro wajen ALLAH ya sota ta taho da hijjab kasancewar yau ma shigar Abaya ce a jikinta ƙirar Dubai ruwan ƙasa. Hijjab ɗin ta buɗe ta saka bayan ta zame hularta da ɗan kwalin abayar data naɗo a kanta ta ajiye saboda hijjabin ya rufe mata gashinta sosai. Hankalinta kwance kuma kanta tsaye ta fito a office ɗin daga ita sai wayarta kawai a hannu. Kusan duk an fice ma, dan wajen yayi tsitt, dan haka a gaggauce ta nufi elevator jin za'a tada sallar kasancewar su suna a 4th floor ne. Bata gama dai-daita tsaiwarta ba kawai taji shigowar mutum babu ko sallama. Dan haka ta ɗago manyan idanunta domin ganin wane sallamemmen ne haka........✍️

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)

2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)

3 DUNIYAR MU (Huguma)

4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500

Book 2:-1000

Book 3:-1500

Book 4:-2000

0022419171

Access bank

Maryam Sani Gumi

Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷

1000CF

89825722

Nousaiba Lawali Maradi

Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login