Showing 51001 words to 54000 words out of 59211 words

Chapter 18 - AJIYA A DUHU Book Complete Original billy.docx

04 Feb 2025

26275

ƙanƙanin lokaci kuwa sai gata ta dawo gidan...

     ★ “Haba Maanal wai mike faruwa ne duk kinbi kin ɗaga mana hankali. Jibafa office na baro saboda kiran da Linda taimin duk da tarin ayyukan dake a gabana. Amma inata magana kinyi shiru sai kuka kikeyi. Idan jikin naki ne kuma muje asibiti. Ko na kira Ammie ne dai?”.

      Da sauri Maanal ta shiga girgiza mata kanta tana sharce hawayen da suka gagara tsaya mata. “Didi kar ki kirata dan ALLAH. Ba wani abu baneba fa”.

        “Haba Maanal ya zakice bawani abu bane gaki kinata faman kuka. Idan baki son na kira Ammien to ki faɗa min mike faruwa ne? Wani abun Rafeeq ɗin ya miki jiyan da kuka fita? Ko aikin ne basu ɗaukeki ba?”.

     “A'a Didi babu ɗaya daga ciki, ina son yai zan koma KD”.

“Okay mune mukai miki wani abu kenan?”.

“Kai Didi ni mi zaku min. ALLAH ki kwantar da hankalinki babu komai”.

      “Batun kwantar da hankali kam bazai kwantu ba Maanal, yanzu fa kike cewa zaki tafi KD. Amma dai bara na kira Ammien ni kam, ƙila ki sanar mata ko Nene. Ga Rafeeq can Linda tace yayi mayawa takai huɗu tunda safe amma kinƙi fita, kinƙi cin abinci, kinƙi wanka Maanal why? Gara nai kiratan dai zai fi”.

  Caraf ta riƙe mata hannun tana girgiza kanta. Yayinda idanunta suka cika da ƙwalla tab. “Please Didi karki kirata zan gaya miki”. Kai Shahidah ta jinjina tare da sauke numfashi sai kuma ta sakar mata wayar da faɗin, “To ina saurarenki, mike faruwa?”. Sai da Maanal taja kusan mintuna biyu kafin da ƙyar ta iya furta, “Didi sun ɗaukeni aikin amma bazanyi ba”.

     “Baza kiyi ba kamar ya? To saboda mi?. A wannan lokaci da aiki ke wahala Maanal. Kin samu cikin sauƙi haka amma kice baza kiyi ba. Ko auren Yazeed ɗin kike so to? Ko kuma dan kinji jiya ankai kuɗinsa gidan su Nazeefa ne har kika nema tadana kanki ciwo?”.

         “Didi mizai sa na damu da auren Yaya Yazeed tunda ba'a kaina zata zauna ba.”

    “To mike faruwa? Wajen aikin ne ya miki alamu na marasa ɗa'a ko me?”.

    “A'a Didi kawai dai”.

“Miye kawai dai. Maanal ki fito kimin bayani mana yanda zan fahimta na kuma gamsu”.

       Rasa yanda zataima Shahidah ɗin bayani tayi, ta fito fili ta sanar mata abinda idanunta suka gani a jiyan ko kuwa ta shanye al'amarin a cikinta kawai ta dage akan aikinne bazatayi ba. To amma tasan nacin RK, shima bazai barta ba ai. Sannan ita kanta Didi ba barinta zatai ta huta ba har sai ta san gaskiyar al'amarin. Sanin gaskiyar kuma na nufin abinda zata ɓoye a yanzu dan sai sun san komai. (Ya arrahaman) ita ina ya kamata ta kama ne?.....

     “Maanal!!”

Shahidah ta kirata tana mai girgizata. Firgigit ta dawo hayyacinta kamar wadda aka tada daga barci, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tare da kai hannunta saman goshi tana murzawa a hankali.

       “ALLAH Maanal tambaya ta ƙarshe zan miki daga nan zan kira Ammie ne kawai tunda ni baki son nasan damuwarki”.

  Jin yanda Shahidah tai maganar a hasale tana ƙoƙarin miƙewa yasa Maanal saurin kamo hannunta ta dawo da ita. Idanunta cike da ƙwalla ta ce, “Didi ba ɓoye miki nake ba wlhy, kema kin sani bana taɓa ɓoye muku komai a rayuwata. Kawai dai na fasa yin aikin ne saboda companyn na Bes...” sai kuma ta canja ta ce,  *_“AA Darma_* ne?”.

     Cikin matuƙar razani Shahidah ta miƙe zumbur hannunta dafe da ƙirji ta ce,  “What!! Kina nufin *_Ajwaad!!_* Maanal!”.

        “Shi Didi, shi! Shi! ɗin dai.” Maanal ta faɗa wasu hawaye masu zafi na sake gangaro mata.

   Jagwab Shahidah ta koma ta zauna tana mai dafe kanta da duka hannaye biyu, ita kanta jikinta tsuma yake, sai kuma ta ɗago tare da jawo Maanal ɗin jikinta ta rungume dan kuka take mai ban tausayi da tsuma zuciya. Cikin sarƙewar murya ta ce, “Maanal kuma kin gansa ya ganki? Kin tabbatar shi ɗin ne dai?”.

     Kai Maanal ɗin ta jinjina mata, “Ya ganni sosai, amma ya nuna kamar ma bai taɓa sanina ba tamkar a wancan ranar da yay......” nan dai ta labarta mata duk yanda komai ya faru. Gaba ɗaya mamaki ya gama kashe Shahidah, amma sai ta danne ta shiga Lallashinta har sai da tai shiru. Daga haka ma ta ciro maganinta ta bata kasancewar lokacin shan na rana yayi. Tana sha babu jimawa ta ɓingire wani barcin. Lallaɓawa Shahidah tai ta gyara mata kwanciya, sannan ta saka mata ac kaɗan ta kashe mata fitilar ɗakin ta fice..........✍️

_Tofa, wanene *AA Darma* a rayuwar Maanal Habeeb Giro?. Karku gajiya kumuje zuwa dan yanzune labarin AJIYA A DUHU ma zai fara. Labarin nan fa akwai cakwakiya ta musamman mutane na. Ni bamma san team ɗin wa zan kasance ba bana. Karna zaɓi AA ace min mayyar kuɗi🥲🥱🤪🏃_

✨ZAFAFAN DAI ✨

1 ƘALBIM (Mamu gee)

2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)

3 DUNIYAR MU (Huguma)

4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)

Book 1:-500

Book 2:-1000

Book 3:-1500

Book 4:-2000

0022419171

Access bank

Maryam Sani Gumi

Shaida:- 09033181070

Kati MTN:- 09032345899

Ƴan NIGER 🇮🇷

1000CF

89825722

Nousaiba Lawali Maradi

Shaida:-09033181070

*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*

*_Typing📲_*

*_💞AJIYA A DUHU....💞_*

*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*

*_

ب

ِ

س

ْ

م

ِ

الل

َّ

ه

ِ

الر

َّ

ح

ْ

م

َٰ

ن

ِ

الر

َّ

ح

ِ

يم

_*

_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._

*_My TikTok account 👇_*

https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1

*_Instagram👇🏻_*

https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv

*_Arewabooks_*

Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30

*_WhatsApp channel_*

https://whatsapp.com/channel/0029Vb1UKNuGk1FwLVPMgu2R

_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_

🅿️➖2️⃣5️⃣

........Nata ɗakin ta nufa tanata faman sauke ajiyar zuciya. Yayinda abubuwa masu yawa ke mata kaikawo a cikin rai tamkar sun faru sun wuce ne a cikin film. Tana shiga ɗakin wayarta ta ɗauka domin kiran Ammie. Har tayi dailing no ɗin nata sai kuma ta katse da sauri, dan kuwa ziciyarta ta tsawatar mata akan ba ita ya kamata ta kira ba. Cikin gamsuwa da hakan ta maida alaƙar kiran ga Amal duk da tasan itama dai tana wajen aiki yanzu haka. Sun gaisa kamar yanda suka saba cikin so da ƙaunar juna. Tare da tambayar yara da bayan rabuwa. Sai kuma Amaal ta ciga da faɗin, “Didi ya naji muryarki duk ta canja kamar wadda ke'a cikin damuwa? Kuma kamar ma a gida kike bakije office bane?”.

       “Him ke dai bari Amaal, abin duniya ne ya isheni wlhy dawowa nayi. Akan Auta ne fa”.

    “Ya ilahil'alamin miya faru kuma?. Kin saka gabana faɗuwa badai jikin nata bane kuma?”.

    “Bashi bane duk da dai jiya taso rikita mana lissafi gaskiya. Amma Alhamdullah yau ta tashi normal. Sai dai abinda yaso zama sanadin tada ciwon nata har yanzu yana tare da ita.”

      “ Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un. Didi kimin bayani dan ALLAH yanda zan gane. Mi kuma ya sake faruwa da Autar?”.

    Komai daya faru Shahidah ta labartama Amaal kamar yanda Maanal ta sanar mata ita da kuma wanda ya faru anan gidan. Ai Amaal batama san ta rikito a kujerar office ɗinta ba tana zunduma wata ƙatuwar ashariya da maimaita sunan “Ajwaad fa? Na gidan Oum?”.

       “Shi kuwa wlhy Amaal.”

   “Kan babbar b... uba. Ke nan dama suna ƙasar nan Didi?”.

“To bazamu ce ba Amaal ALLAH kaɗai ya sani, amma nayi mamaki matuƙa nima, dan banyin zaton haka daga Oum ba. Shin miya hanata neman mu?.”

      “Humm Didi wannan maganar ta wuce ta waya. Ki saurari zuwana anjima kaɗan koda sassafe ne na dawo saboda office. Kin gayama Ammie?”.

     “A'a ki rufan asiri kin santa dai ai. Ke kaɗai na gayamawa. Ko Abban su Barrah ban sanarma komai ba ma. Amma Daddyn Munaya zai barki?”.

  “In sha ALLAHU zai bari barima kiga”...

_____________★

       Sosai Hajiya Yaya da Aunty Sabuwa da ƴaƴansu suka haɗa wata ƴar ƙwarya-ƙwaryar walima a gidan Aunty Sabuwa ɗin wai na murnar saka rana. Abin ma sai ya baka dariya da mamaki. Dan dj aka ɗakko ya saki speakers iya maƙura aka cashe akaci kaji da lemuka. Ga taron ƙwayen Aunty Sabuwar ƴan duniya, dan mafi yawansu zawrawa ne. Dan ita dai Hajiya Yaya tun abin na birgeta tana murmushi har ya fara tsikarin zuciyarta. Amma sai ta danne ta basar. Kasancewar tasan Daddy na gari anayin la'asar ta tattaro su Asalamiyya sukayo gida ransu a ɓace. Dan so sukai ta barsu su kwana acan su ƙara ɓararrajewa da ƙyau.

     To ashe wasa farin girki, dan kuwa tafiyar su Hajiya Yaya kamar an buɗe wani sabon babin shagalinne a gidan. Tsabar taɓara da zubewar mutunci sai ga mahaifin Nazeefar ya shigo fili wai shima ya taka rawa, liƙi Sabuwa ta fara masa sauran ƙawayen ma suka rufu a kansu suna liƙesu ana dariya da shewa da shaƙiyanci tunda shima ɗan duniyar ne. Sai daga baya ya fita ya barsu ya shige ciki, su kuma suka cigaba da shagalinsu. Yayinda guri yay guri Sabuwa tama manta da wanzuwar miji a gidan, babban aminiyarta ta zame jiki tai wuff tabi bayansa. Dama sun jima tare ita Sabuwa ce bata sani ba. Aiko ya sama ƙofa key suka hau shagalinsu suma.

     A taƙaice dai wannan taro bai tashi ba sai kusan sha biyun dare. Duk sun bi sun hana ƴan anguwa barci anata musu ALLAH wadarai. Koda suka nutsu Sabuwa ke tambayar Hajiya Malika aminiyarta ina ta shige, sai cemata tai ai gida taje saboda oga ya dawo neman wasu takardu bai gansu ba. Sai da ta koma ta bashine ta dawo. Cike da shaƙiyanci suka hau tsokanarta wai bawasu takardu kodai-kodai. Dariya ta dinga tuntsurawa ita dai. A haka Mijin Sabuwa ya sakko daga sama. Suna haɗa ido da Hajiya Malika suka wani kashema juna idanun cike da salon shaiɗanci batare da kowa ya lura da su ba.

      (Humm ALLAH ya ƙyauta. Hajiya Malika dai matar abokin Alhaji Sajid ce, kai yama wuce ace aboki sai dai amini ɗan uwa. Hakan yasa suka ƙulle matansu suma suka zama aminan Sabuwa da Malika ɗin kenan. Sosai suke aminta dan babu wani sirri na Sabuwa da Malika bata sani ba, hakama duk wani sirrin Malika Sabuwa ta sanshi. Abota ce tun ta ƙuruciya. Ko lokacin da Sabuwa ta rabu da Alhaji Sajid ɗin Sabuwa da Malika na tare, kusan ma za'ace da taimakonsu ne aka maida auren bayan Sabuwar taje tayi auren kisan wuta saboda saki uku ne. Shi mijin Hajiya Malika sam ba mazauni bane ba, ɗan kasuwa ne da kullum yana wacan ƙasa gobe yana waccan kamar wani ɗan sama jannati, da wannan damar Mijin Sabuwa ya samu kan Hajiya Malika suke sheƙe a yarsu. Dan a yanzu haka ƴaƴan Hajiya Malika ba duka bane ɗiyan mijinta idan za'a tantance, akwai gauraye dana mijin Sabuwa saboda yanda suke tare matuƙa kamar wata matarsa. UBANGIJI kuma yay musu talala har yanzu babu wanda ya taɓa sanin wannan alaƙa tasu duk da tsahon shekaru sai wata mai aikin da Hajiya Malika ta taɓa yi, ita kam ta kamasu dumu-dumu cikin aikata al'amarin ta tsorata, itama hankalin Hajiya Malikan ya tashi amma sai Mijin Sabuwa yace karta damu ta jira taga mi zaiyi. Aiko taga abinda zaiyi ɗin, dan a gabanta yayma yarinyar nan ƴar aikinta fyaɗe, daga nan yaja mata dogon gargaɗi akan idan ma taje ta tona musu asiri saita haɗa da kanta, ya nuna mata video ɗin daya saka Hajiya Malika ta ɗauka sanda yake tare da yarinyar. Hankalinta ya tashi, ta dinga kuka tana ramtsuwar bazata faɗa ba wlhy. Basubi takanta ba sukace ya haɗa kayanta washe gari aka maida ta ƙauyensu. To tundai daga nan babu abinda ya sake faruwa sai dai UBANGIJI na kallonsu, ba kuma su san ya musu talala bane ba)

   🏃 ALLAH ka tsaremu da ikonka da rahamar ka😭🙏.

_________★

    Kamar yanda Amaal tai alƙawari ta iso Abuja kusan takwas na dare. Alhamdullah zuwa sannan Maanal ta farka. Dan shigarta wanka kenan Amaal ɗin ta iso. Ta fito taci karo da ita a ɗakinta sai tayi turus. Dariya Amaal ta sanya mata tare da buɗe mata hannayenta alamar tazo gareta. A yanzu kam babu musu Maanal ɗin ta nufota suka rungume juna, kai kace ba kwanan nan suka rabu ba.

    Sai da Maanal ta shirya tai sallolin dake kanta sannan ta dawo tsakiyar yayun nata maganin kukanta ta zauna. Abinci suka fara ci, yayinda Maanal ta shagwaɓe musu wai ita hannunta na ciwo bazata iya ci da shi ba. Aiko su biyun duk suka dinga bata a baki. Hakan da sukai mata ma sai taci abincin sosai. Dagan nan ne suka nutsu akan abinda ya tarasu.

      Da farko dai sun fara lallashinta akan batun aiki tace ita fa ta fasa bazatayi ba. Hasalima tana son komawa Kaduna ne kawai wajen Ammie.

    Baki Amal ta taɓe cikin ɗan ɓacin rai dan dama tafi Shahidah zafi ta ce, “Oh Kaduna ko? Kenan auren Yazeed ɗin kike son yi?”.

       “Yazeed kuma? Didi ni na taɓa cema wani zan auri Yazeed?”.

   “Ai basai kin faɗa ba gashi yanzu kin nuna mana. Wai Manaal mike damun kanki ne dan ALLAH?. Ke gaba ɗaya tunaninki a bauɗe yake dana mutane, sai shegen taurin kai da kafiyar tsiya. To wlhy bari ma na fito miki a mutum ki tattara hankalinki waje guda ki maidashi jikinki. Har mi akai akayi wani Ajwaad can da zai hanaki samun cikar burinki....”

   Hannun Amaal Shahidah ta jimƙe a nata tana girgiza mata kai alamar tayi shiru. Hakan ya saka Amaal ɗin jan ƙaramin tsaki. “Didi ki barni da ita. Na kula sam Maanal bata tausayin kanta bata tausaya mana mu ƴan uwanta. Wace irin rayuwace wannan ace mutum da taurin kai....”

      “Kinga ya isa haka. Maanal bani hankalinki nan muyi magana ta gaskiya”. Shahidah ta faɗa tana kamo hannun Maanal data tsurama Amaal idanu cikin nata. Dole ta janye daga kan Amaal ɗin ta maido kan Shahidahn. “Maanal kiyi haƙuri bazamu takura miki ko tirsasaki akan abinda baƙya ra'ayi ba. Amma ina son ki fahimci wani abu, mufa a yanzu bamu da maraba da marayu da suka rasa mahaifi da dukkan dangi. ALLAH ne gatanmu sai Ammien mu sai kuma Nene kawai sai kammu. Dolene fa mutattara komai daya faru a baya mu zubar da shi muyi mantawa irin ta AJIYA A DUHU duk da nasan akwai tabo da bazai taɓa goguwa ba a zukatanmu amma komai na ALLAH ne. Sannan dole musan kammu mu kuma gina gobe yaranmu masu tasowa. Maanal Daddy ya riƙemu babu banbanci da ƴaƴan daya haifa a cikinsa tunkan Ammie ta haifa masa Waleed da Hameed. Kuma muma a yanzu babu wanda mukema kallon uba sama da shi. Sai dai fa mu sani iyakarmu kiransa uban ne kawai a iyakar kayinmu, amma a wajen al'umma sunanmu AGOLOLI a gidansa. Maanal ba fata nake ba, amma ki sani a yanzu ALLAH ya ɗauki rayuwar Daddy wlhy ko Amminemu bazasu bari ta rayu a wannan ahalin ba. Saboda su Waleed ƙanana ne, basu kai girman da zasu ƙwata mata ƴanci ba. Mu kuma komu yarda ko karmu yarda munada iyakarmu a gidan nan. To mikike tunanin ya kamata muyi? Wannan aikin tuƙuru domin gina gobemu da goben yaranmu. Bazamu so mu sake maimaita rayuwar baya ba Maanal, bazamu so mahaifiyarmu ta sake maimaita wahalhalun data sha a kammu ba a shekarun baya, idan sannan muna da ƙuruciya yanzu munkai girman share mata kukanta, mun girma Maanal mun girma”.

    Kuka ya sarƙeta. Suma duk sai suka fara kukan, koda yake dama Maanal ita tuni ta fara hawaye. Kusan mintuna biyu Shahidah ta share hawayenta da cigaba da faɗin, “Maanal bamu san mi gobe zatazo mana da shi ba. Dan muma mata ne. Idan har Ammie zata iya riskar kanta a irin rayuwar da mukai a shekarun baya bai kamata mu mushagala da tunanin komaima bazai faru ba saboda a yanzu rayuwarmu ta inganta. Karfa mu manta da irin labarin gata da rayuwar Ammie tasha a hannun iyayenta, amma hakan bai hanata fuskantar ƙalubale ba a hannun mijin aurenta da kowa ke gani hakan bazata faru ba. To muma bai kamata ganinmu a cikin irin waɗan nan manyan gidajen yasa mu shagala ba. Bai kamata mu cigaba da zaman jiran kullum a mana ba. Saboda haka ki dawo cikin hankalinki Maanal, ki tuna su waye mu a yanzu. Ki ajiye abinda ya wuce baya ki manta da shi, ki kaishi cikin duhuwa ki ajiyesa tamkar ma ba'a taɓa yin komai ba. Yanda Ajwaad ya nuna bai sanki ba ki zama JARUMA kema ki nuna baki sanshi ba, ki manta da shi, ki manta da abinda ya shafesa, ki tsaya da ƙafafunki, kisa a ranki shi bai isa hanaki kaiwa ga cikar burinki ba, karki wani damu da zamowarsa shugaban kamfanin ko matsayin nasa ke aiki ya kaiki domin kanki. To kiyi kuma aiki tuƙuru a companyn nasa domin kanki da cigabanki. Maanal ki duba yanda Rafeeq ke hidima dake da son ganin farin ciki ki, hatta Yazeed ma ni wlhy ban taɓa ƙin kasantuwar aurenku ba saboda mutumin kirki ne. Koba komai yasan mutuncin mahaifiyarmu, ya taimakemu a lokacin da muka rasa taimako daga jininmu ma. Kawai mahaifiyarsa ce matsala. Idan kuma da alkairi a zamanku sai ALLAH ya ɗauketa ku zauna ɗin babu yanda zatayi. Amma dan ALLAH ki amshi al'amarin Rafeeq ki gwada ki gani shima. Ki kwantar da hankalinki addu'ar mu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login