Showing 24001 words to 27000 words out of 59211 words
zuciya ya sauke. Sai kuma ya zari handkhachief ya goge zufar goshinsa. “Hakane kam Aunty, ina jin tsorone kawai kar ya kasance itama Maanal ɗin tana sonshi, wannan kam kinga bazan iya jayayya da kowa ba tunda itace mai zaman auren.”
“Eh tabbas kam, amma nidai ban taɓa jin akwai wata alaƙar soyayya a tsakaninsu ɗin ba gaskiya. Tunda da akwai na faɗa maka mahaifiyar Yazeed sai a hankali ce, da sam bazata bari a zauna lafiya ba. Amma yanzu ma inda wata shawara, ka samu lokaci ka shigo Zaria wajen Abbansu Najma. Ka masa bayani a matsayin kana son ya maka iso wajen Alhaji Usman ɗin akan maganar mana, ni kuma kafin kazo zan sake bincikawar kamar yanda nayi maka alƙawari”.
Ajiyar zuciya mai haɗe da ƙayataccen murmushi RK ya saki, sai kuma ya kama hannun ƴar uwar tasa ta sumbata yana faɗin, “ALLAH ya saki a aljanna Aunty na mai share kuka na”.
Dariya tayi tana mai kai masa ɗan rankwashi a kai, hakan ne ya sakashi shima yin dariyar sannan ya tada motar suka cigaba da tafiya......
✨✨✨✨✨✨✨
Alhamdullah wannan zuri'a suna cikin farin cikin farfaɗowar Maanal a yau, duk da ba'a barsu sun ganta ba har zuwa yanzu saboda likita dake tare da ita hakan bai hana bayyanar murmushi a fuskokinsu ba. Sai da su Dr Ranjet suka gama mata dukkan abinda ya dace kafin su ka buƙaci Nene dake goge mata jiki kullum ta shiga ta goge matan. Shahidah da Amal kuma sukai shirin komawa gida haɗo mata abincin da Doctor yace zata iya ci. Bayan kammalawar Nene Daddy da Ammie ne suka fara shiga. Tana kwance fayau da ita saboda ramar da tayi na ciwo. Gaba ɗaya na'urorin da aka sanya mata a kwanakin da suka gabata an janyesu, sai igiyar daketa jikin hancinta kawai. Jin ƙamshin turaren Daddy kusa da ita sosai ya sakata buɗe idanunta da suka ɗan kumburo, daga cikinsu sun ɗan yi ja sun kuma ƙara girma. Daga shi har Ammie dake tsaye ta zubama idanun, sai kuma a hankali ta saki murmushi mai sanyi tare da miƙa musu hannunta. Ammie dake murmushi tana hawaye ce ta kama hannun tana kaiwa zaune bakin gadon kusa da ita. Yayin da shi kuma Daddy ya ɗan duƙo ya shafa kanta yana murmushi shima, kafin yakai zaune a kujerar gaban gadon.
“Sannu kinji Daughter. ALLAH ya baki lafiya yasa kaffara ne”.
Kanta ta ɗan jinjina tana sakin murmushi, sai kuma ta motsa lips ɗinta a hankali ta furta, “Amin Daddy nagode”.
Murmushi ya sake mata, tausayin yarinyar da ƙaunarta na sake gauraye zuciyarsa. Maanal ta maida kallonta ga Ammie dake sharar hawaye. Nan ma a hankali ta ce, “Ammie ki daina kuka na samu lafiya fa”. Kai Ammie ta shiga jinjina mata tana share hawayen da sakin ƴar dariya. “Na daina Maanal kinji, ALLAH ya ƙara miki lafiya da nisan kwana. ALLAH yasa kaffara ne, ALLAH ya rabaki da wannan ciwo gaba ɗaya”.
“Amin Ammie nagode. Ina su Didi fa?”.
“Sunje gida yimiki abinci yanzu zakiga sun dawo. Ko kina son cin wani abune a kirasu su yi miki?”.
Ɗan shiru tayi alamar tunani, sai kuma ta kalla Daddy dake ta kallonsu yana murmushi, itama ɗan murmushin ta masa sannan ta sake maida dubanta ga Ammien. “Ammie sumin faten dankali, sai kunun gyaɗa”
“To shike nan bari na kirasu karsu taho”.
Kai Maanal ta jinjina mata, yayinda Ammie ke ƙoƙarin kiran su Amal. Dai-dai nan Yazeed ya shigo ɗakin da sallama Waleed riƙe da hannunsa, sai Hameed biye da su. Daddy ne ya amsa masa. Yayinda ita kuma ta zuba musu raunannun idanunta. Da sauri Hameed da Waleed sukayo inda take cike da farin cikin ganin idanunta a buɗe. Hannunta duk suka kama suka riƙe suna kaiwa durƙushe daga ƙasa ta yanda fuskokinsu zasu daidaita da tata.
“Alhamdullahi Didi ta samu lafiya”. Cewar Hameed yana sake ƙanƙame hannunta. Shima Waleed cike da ɗoki ya furta, “ALLAH mun gode maka yau muna cikin farin ciki Daddy Didi ta buɗe ido”.
Ƙaramar dariya Daddy yayi da faɗin, “Alhamdullahi” shima. Maanal cikin magana a hankali tace, “Ƴan turai kamarku daban”. Dariya duk suka ƙyalƙyale da shi. Itama saita maida kallonta ga Yazeed dake tsaye kawai yana kallonsu fuskarsa ƙawace da murmushin farin ciki. Kallon da take masa ya sashi ƙarasa ƙarasowa gaban gadon sosai. Sai kawai ta lumshe nata idanun a hankali ta kuma sake buɗewa duk a lokaci guda.
“Alhamdullahi. Sannu Maanal ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffarane kinji”.
Murmushi ta sakar masa a karo na farko, murya can ƙasa ta ce, “Amin Yaya nagode”.
Amsa mata yay cike da farin ciki, jiyake tamkar ya rungumeta a jikinsa sai dai babu damar hakan. Balle ma ga Ammie a wajen ga Daddy. Suna a hakan dai kuma sai ga RK. Tunda ya shigo idanunsa akan Maanal ɗin ne shima, itama dai shi ɗin take kallo da ɗunbin mamaki. Yayinda zuciyarta ke raya mata (shi wannan duk inda naje sai ya bini ne shin?) Rashin mai bata amsa yasata janye idanunta a zahiri daga kansa. Shima sai dai janye nasan yayi tare da ƙarasowa ya gaida Daddy da Ammie cike da girmamawa. Maanal ta sake shan mamakin ganin yanda duka amsa masa da kulawa da alamar sanayya sosai kuma. Dubansa ya maida a kanta yana mai ɗan kashe mata ido, hakanne ya sakata yimasa ƙaramar harara. Murmushi ya saki mai faɗi da ƙoƙarin ɗaukar file ɗinta dake a drower ɗin gefen gadon yana faɗin, “Gawa taƙi rami yaya jikin?”.
Dariya Daddy da su Waleed sukayi, yayinda Ammie tai ɗan murmushi kawai. Yazeed kam fuska ya sake tamkewa kamar bai san minene dariya ba. Yayinda Maanal ta ɗan tsuke fuska itama tana hararar RK ɗin yanzu ma. Yi yay kamar bai ganta ba ya miƙama Yazeed hannu cike da shaƙiyanci yana faɗin, “Babban Yaya barka ƙanwa ta miƙe. ALLAH ya ƙara lafiya yasa kaffara ne ya kiyaye gaba”.
Rasa abinyi Yazeed yayi, sai mamakin RK ɗin ke sake mamaye masa zuciya. Wani gefe kuma na tunanin RK fa bawai yasan ainahin alaƙarsa da Maanal bane, dan kuwa kallon yayanta uba ɗaya yake masa kenan. Daurewa yay ya ɗan sake fuska ganin Daddy na kallonsu ya bashi hannun shima suka gaisa yana amsawa da, “Amin doctor muna godiya, kuma kunyi ƙoƙari ai sai fatan alkairi a gareku”.
“Doctor!”.
Manaal ta faɗa a hankali cikin suɓutar baki idonta akan RK. Kafin ma RK yay wani yunƙurin bata amsa Waleed yabata amsar da “Eh mana Aunty shine likitanki tare da Dr Ranjet. Kuma yana da kirki kullum sai yaje damu yawo ya saya mana abubuwa, yana kuma cemana mu dinga miki addu'a a dallarmu ALLAH ya baki lafiya ko warke gaba ɗaya ki daina wannan ciwon ”.
Sake dai kallon RK ɗin Maanal tayi kawai, zuciyarta na wani irin motsawa a ƙirjinta da sauri-sauri kamar ma ciwon nason dawowa sabone komi. Ganin kallon da Ammie ke mata ta sata lumshe idanu kawai tai shiru dan ita kam bata kuma san abin faɗaba bayan hakan. Ɓoyayyen murmushi kawai RK yayi yana cigaba da dudduba abinda ya kamata, sai kuma ya fara mata tambayoyi a hankali. Dole ta buɗe idanunta a kansa dan yanda yake magana can ƙasa-ƙasa tsigar jikinta har tashi take. Kasa amsa masa ko ɗaya tayi da baki, sai jinjina masa kai kawai da girgizawa. Wani irin kishi ne ya turniƙe Yazeed, dan shi mutum ne mai kishi sosai. Rai a ɓace ya ɗan duƙo shima gareta murya can ƙasan maƙoshi ya furta, “Kina son cin wani abu Miss?”.
Idanunta ta ɗan maida garesa, “Yaya su Didi na zuwa da abinci ai”. Ta faɗa a hankali dan muryan baya fita sosai. Cikin jinjina mata kansa ya ce, “Na sani, ko ɗan fruit haka baƙya so? Ko wani abu bayan abincin?”.
“Zanci apple to, amma green”.
“An gama Baby”. Ya faɗa cikin raɗa ta yanda ita kaɗai taji sai RK dake kusa da su sosai. Saurin kauda kanta tayi, sai kuma ta kalla sashen da Ammie da Daddy suke. Ganin hankalinsu na kan su Waleed yasa ta sauke ajiyar zuciya. RK ta ɗan kalla, sai taga shima yay wani kicin-kicin da fuska yanata rubutu a file ɗin ta. Tana ƙoƙarin janyewa ya ɗago nasa idanun sai caraf a nata. Wani miskilin murmushi ya sakar mata tare da sake duƙowa kusa da ita gab, cikin raɗar shima ya furta, “Apple yana cikin abinda bazaki ci ba a yanzu wife to be, dan haka kada ki ma wahalar da Yayanmu”. Ya ƙare maganar da kashe mata ido ɗaya sai kuma ya kalla Yazeed ya sakar masa wani ɗan iskan murmushin rainin hankali.
(Nikam mike damun waɗan nan?) Maanal ta faɗa a zuciyarta dan tama rasa yanda zata masalta al'amarin nasu. Tana fama da kanta sunzo sun sakata tsakkiya da shirmensu ya ilahil alamin. Shigowar su Shahidah ne ya taimaketa. Cike da farin ciki sukazo suka rungumeta suna hawayen daɗin ganinta. Itama farin cikin take ji a ranta matuƙa. Nanfa suka shiga nan nan da ita. Sai kawai Daddy da Ammie suka fita tare da su Waleed. Dan ba'aso suyi yawa a ɗakin sam. A hakan ma dan RK najin nauyinsu shiyyasa baiyi magana ba. Ganin Yazeed bashi da niyyar fita a ɗakin RK ya dubesa cikin danne kishinsa ya furta, “Yauwa babban yaya inama son magana da kai. Dan akwai alluran da za'a mata zuwa 6pm naga kamar babu shi anan ya ƙare, ko zaka samo mana shi a pharmacy please?”. Yayi maganar ne idanunsa a kan takardun hannunsa yana kuma ɗan tafiya, dan haka baka isa gane ainahinsa ba kai tsaye. Bin bayansa Yazeed ɗin yayi batare da yace komai ba. Maanal ta bisu da kallo ƙasa-ƙasa.
Da taimakon yayun nata biyu ta ɗan ci abincin, nurse ɗin dake kula da magungunan ta ta shigo ta bata. Babu wani jimawa barci mai nauyi yay awon gaba da ita. Dama haka doctors ɗin suke buƙata ta dinga barci isashe dan zuciyarta da brain ɗinta su samu nutsuwa.........✍️
_🥱Team RK & Team Yazeed ina miƙo gaisuwar ban girma😌👌._
✨ZAFAFAN DAI ✨
1 ƘALBIM (Mamu gee)
2 ƘIRJIN MAI HANKALI (Miss xoxo)
3 DUNIYAR MU (Huguma)
4 AJIYA A DUHU (Bilyn Abdull)
Book 1:-500
Book 2:-1000
Book 3:-1500
Book 4:-2000
0022419171
Access bank
Maryam Sani Gumi
Shaida:- 09033181070
Kati MTN:- 09032345899
Ƴan NIGER 🇮🇷
1000CF
89825722
Nousaiba Lawali Maradi
Shaida:-09033181070
*_ALLAH ka gafartama iyayenmu 😭🙏_*
*_Typing📲_*
*_💞AJIYA A DUHU....💞_*
*_Bilyn Abdull ce 🤙🏻_*
*_
ب
ِ
س
ْ
م
ِ
الل
َّ
ه
ِ
الر
َّ
ح
ْ
م
َٰ
ن
ِ
الر
َّ
ح
ِ
يم
_*
_Da sũnan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai._
*_My TikTok account 👇_*
https://www.tiktok.com/@bilynabdull?_t=8mfvWuXADVF&_r=1
*_Instagram👇🏻_*
https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv
*_Arewabooks_*
Read My Book "AJIYA A DUHU" on ArewaBooks::https://www.arewabooks.com/book?id=675067e55c3130f457527f30
_Duk wanda bai fallowing ɗina ba ALLAH yasa kada yaga AJIYA A DUHU har a gama😂😂🏃🏃_
🅿️➖1️⃣4️⃣
.......A ɓangaren Yazeed da RK kam suna fita Yazeed ya tsaya cak. Kallonsa RK ya juyo yanayi, sai kuma ya saki lalataccen murmushi yana dawowa da baya inda Yazeed ɗin yake. “A'a babban Yaya yaka tsaya kuma? Ya kamata muje ko”.
Murya a sarƙe Yazeed ya amsa masa da, “Rubuta sunan alluran ka bani anan. Sannan ka daina wani kirana Babban yaya dan ban san alaƙar data maidani yayanka ba”.
Hannu RK ya kai ya shafo bayan ƙeyarsa yana murmushi irin na ƴan duniya shi a dole irin yaji kunyar nan. “Haba bazan iya kiranka da sunanka ba gaskiya. Ko a bayan ma kafin na fahimci kai Yayan Maanal ne yasa nake kira. Yanzu kam dana sani sam bazan iya hakan ba”.
“Ni ba yayan Maanal bane kawai mijin da zata aura ne”. Yazeed ya faɗa a gadarance. Wani irin mugun dukan zuciyar RK furucin yayi, amma sai ya dake cike da basarwa ya furta, “Irin wannan wasan ai saika saka zuciyata ta buga babban yaya, kona ɗauka baka son aura min ita ne. Please mubar zancen haka ga sunan allurar”.
Yana miƙa masa ƴar takardar da yay rubutun yabar wajen da sauri dan baya buƙatar sake jin wani furuci daga Yazeed ɗin bayan wanda yaji. Shifa wlhy san Maanal yake. Kuma baya jin zai iya barma Yazeed ɗin koma mi za'ayi. Sai dai suyi yaƙi mai rabo ya ɗauka. Babu ruwansa da ƙarfin alaƙarsu kowa ya iya allonsa kawai ya warke.
Da wani irin kallo Yazeed ya bisa kawai batare da ya sake cewa komai ba shima yabar wajen...
_________★
Ganin jikin Maanal Alhamdullah Ammie ta matsama Yazeed komawa kan saboginsa. Shima Daddy ta damesa da roƙon ya koma Kaduna kada su shiga hakkin sauran matansa. Yazeed dai ya jitane kawai. Dan ya ƙudura a ransa bafa zai tafi ya bar Maanal a hannun wannan kuren likitan ba RK. Dan haka ƙafarsa ƙafarta idan ta samu lafiya. Shi kam Daddy sai da sukai ƴar rigima sannan ya yarda zai wuce Kaduna ɗin, amma kuma dole sai tare da ita, yace nan da kwana biyu ta dawo ta sake dubata tunda dai ga Nene gasu Shahidah. Ita dai Ammie tace hakan yafi mata duk da bata so hakan ba, dan tana son kasancewa da Maanal ɗin itama amma babu yanda ta iya haka ta haƙura suka tafi bisa shawarar Nene dan itama tafi son yaje ga sauran matansa kar abin ya zama wani daban kuma. Yazeed dai ya nuna mata akwai aikin da yake anan ɗin dan gobe ma zaiyi zama da masu Companyn Mawaad ne.. Wucewar Daddy da Ammie kamar ya buɗema Yazeed da RK wani filin TAKUN SAƘA ne, dan kuwa kowa ya riƙe wuta yana baje kolin hajarsa. Yayinda ita kuma take nuna bama ta fahimci inda suka dosa ba su duka. Tun suna abin a kaikaice har ya fara bayyana kansa sosai, dan takai da Yazeed ya shigo duba Maanal tsalam zakaga RK a ɗakin ya shigo kamar wanda aka jeho. A wajen su Amal taji duk yanda akai aka kawota Abuja. Nan ta fahimci RK yaje gidansu ne sai ya kasance a dai-dai lokacin da take a halin taimako. Hakan ya kwaranye mata mamakin ganin nasa anan. Sai dai kasancewarsa likita bai bar bata mamaki ba. Dan har sukai zamansu a Jos suka gama bai taɓa nuna musu ga aikinsa ba. Kai ita tama sha yin gulmarsa da jifansa da kalmar mara aikinyi, sannan a tunaninta shi ɗin ɗan Jos ɗin ne ma ai.
Yau Nene ta ɗan tashi da ciwon kai, dan haka ta wuce gida dan ta ɗan huta. Dama itace ke kwana da ita anan, da safe zuwa goma sai ta wuce gida idan su Amaal sun zo, sukuma suke yini da ita anan har sai dare idan Nenen ta dawo sukuma sai su wuce. Daga Nene har Amal suna a gidan Shahidah ne yanzu, dan bayan wucewar su Ammie sai itama Nene ta koma can gudun karta zauna ita kaɗai anan ɗin duk da ma ƙarfin zaman nata a asibitin ne dai. Bayan wucewarta Maanal ta tashi a barci, da taimakon Nurse tai wanka, kafin ta fito an gyara ɗakin, tana ƙoƙarin zama a bakin gado take tambayar Nurse ɗin, “Nene fa?”.
Amsa ta bata da, “Doctor Rafeeq ya kaita gida ta huta kanta na ciwo”.
Shiru kawai Maanal tayi, mamakin RK na sake kasheta, gaba ɗaya fa yabi ya kanainaye mata ƴan uwa kowa ya sanshi. Yanzu haka kullum Waleed da Hameed na manne da shi har sai da suka wuce aka samu lafiya. Haka idan su Didi sunzo zaizo ya zauna wai yazo gaishesu duk hararar da take masa baya ma nuna ya gani. Itako yaya zatai da wannan bawan ALLAH. Babu ma abinda ke damunta sai zaman marina da suke tsakaninsa da Yaya Yazeed, hatta gaisuwa sama-sama sukeyinta yanzu ma ta rasa mike damun kawunansu haka.... Shigowarsa ɗakin shi da Doctor Ranjet ya katse mata tunaninta, da sauri taja hulanta ta saka tana ɓata fuska. Ɗauke kai RK yay kamar bai ganta ba yama hau duba magungunanta. Shi dai Dr Ranjet matsowa yay kusa da ita yana tsokanarta, haka yake mata dan shi mutum ne mai wasa sosai. Dole ta daure ta ɗan masa murmushi dan turancinsa na sata nishaɗi, kullum gaya mata yake ita ɗin mai sa'a ce. Ruhunta nada tauri sosai, saboda da wahala kaga mai irin matsalarta ya shiga irin yanayin data shiga kuma ya tashi ya cigaba da rayuwa, dan shi kansa a randa aka kawota asibitin baimayi tunanin zata kai washe gari a raye ba. Dai-dai Dr Ranjet na ƙoƙarin mata wata allura da kullum a irin wannan lokacin ake mata RK ya ƙaraso wajen. Kujera yaja ya zauna yana mai zuba mata ido dan sai ɓata fuska take tana kallon allurar. Amma tana juyowa suka haɗa ido da shi sai ta ɗaure fuska ta fiske abinta. Kansa ya kauda kawai yana murmushi baice komai ba. Allurar akai mata, ana gamawa ta kwanta saboda jiri take sakata. Idonta a rufe har fin mintuna biyar Doctor yay mata sauran abinda ya rage har ya fice da kusan mintuna biyar sannan ta iya buɗe idanunta da suka kaɗa sosai. A kansa ta saukesu, sai kuma ta janye da sauri ganin shima ita yake kallo.
“Nifa bana son haka, azo a tasa mutum gaba ai haramunne ma wannan”.
Murmushi ya saki mai faɗi yana mai janye idanun nasa daga gareta. Sai kuma ya furzar da huci kaɗan a hankali ya furta, “To amin afuwa