Showing 1 words to 3000 words out of 39246 words

Chapter 1 - YAR FILLO COMPLETE DOCUMENT BY Nabilancy Love 😘.txt

07 Feb 2025

5321

[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:*"YAR FILLO...*
_Dijen k'auye_








*True life Story*




*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)






Hankalinta kwance take damun furarta tana "yan wakokinta ckn harshen fillanci




Saiji tayi Anrufe mata idanu ta baya


Ta tsaya cak! Da damun tana shakar kamshin turarenshi a tafin hannun nashi


Tasan ko waye ta haddace kamshinsa Abokin tane wato Abdul hamid wanda take kiransa da Abokin birni




Murmushi tayi tareda cewa "walh naganeka Abokin birni ne...




Yacire hannunsa daga fuskarta ahankali yana fara,a yadawo gabanta ya durkusa yana kallon kyakykyawar fuskarta


Ta ajiye kwanan shan robar datake damun takalleshi da mamaki tace "abokin birni yaushe ka dawo?




Yace yana dry "Yanxu yanxu muka shigo kauyen naku jaka kawai na jiye agidan gona nataho gunki.



"Amma dai kai kadai kazo ko???


Ya girgixa kansa ya nuna bayanta yana fadin "kalli can kiga '


ta juya ahankali tana dora idonta akansa take taji wani k'ululu aranta ranta yai mugun b'aci da wannan bak'in toxali da tayi wannan shi ake kira da mugun gamo ………








_Coming Soon_




*Auntyn S&S* ce[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:😂👌🏼
🐄 *"YAR FILLO...*🐄
_Dijen k'auye_
🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕









_Dasunan Allah mai Rahama mai jinkai Ina godiya Ga Allah Daya Bani ikon Sake Rubuta wannan Sabon Novel Din nan nawa Fatana Allah Yasa Nagamashi Lfy Allah yasa Masoyansa Suji Dadinsa Sukuma Amfana Dashi Amin_





*SADAUKARWA GAREKU MASOYANA MASU MUHIMMANCI DA AMANA*

*Sis Nerja,art YARIMA SUHAIL*
&
*CLASSIC FEEDO SUHANA*
&
*FRESH UMMIEY XEEY*
&
*Itz B Y ebrerheem*
&
*Maman Gausiyya*
&
*Sis Snaanerh*












*True life Story*








*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)






Hankalinta kwance take damun furarta tana "yan wakokinta ckn harshen fillanci




Saiji tayi Anrufe mata idanu ta baya


Ta tsaya cak! Da damun tana shakar kamshin turarenshi a tafin hannun nashi


Tasan ko waye ta haddace kamshinsa Abokin tane wato Abdul hamid wanda take kiransa da Abokin birni




Murmushi tayi tareda cewa "walh naganeka Abokin birni ne...




Yacire hannunsa daga fuskarta ahankali yana fara,a yadawo gabanta ya durkusa yana kallon kyakykyawar fuskarta


Ta ajiye kwanan shan robar datake damun takalleshi da mamaki tace "abokin birni yaushe ka dawo?




Yace yana dry "Yanxu yanxu muka shigo kauyen naku jaka kawai na jiye agidan gona nataho gunki.



"Amma dai kai kadai kazo ko???


Ya girgixa kansa ya nuna bayanta yana fadin "kalli can kiga '


ta juya ahankali tana dora idonta akansa take taji wani k'ululu aranta ranta yai mugun b'aci da wannan bak'in toxali da tayi wannan shi ake kira da mugun gamo taki jinin
Taganshi takuma tsaneshi kamar yadda shima yatsaneta






Abdallah kenan yaro matashi dan kwalisa me ji da kansa me takama da arxikin da Allah yabaiwa ubansa gashi shi mutum ne marason son talaka akusa dashi yanada shariya gashi miskilin gaske


Cousing ne ga Abdulhakim wanda jininsu ya matukar haduwa very close suke tun suna yara suke kwana daki guda har yanzun da suka girma basu raba dakiba Halayyarsu ta bambanta don kuwa shi Abdulhakim mutum ne meson mutane bashida wata matsala ga wasa da dariya baida wulakanta jama.a


Abdallah yanada boyayyen halin da bai taba bari Abdul hakim ya ganoshiba wato shan giya wanda tun suna malesia yakoyi sha shida abokansa na sheke aya harda neman mata wanda aboye yakeyi bai taba bari Abdul din yaganeba don sigari kawai daya kamashi yanasha saida yayi wata uku bai masa magana ba shima dan Abdallan yayi kwantan bauna ya nuna masa cewar yadaina shane shiyasa ya sauko daga fushin dayai dashi




Abdul hakim yatsani mutum mai halin banxa balle me shaye shaye shiyasa bai taba yin abokiba sbd baya son tension






Dije ta hade girar sama data kasa takalli Abdul hakim tace "abokin birni me yasa kaxo min gunnan da wannan me bakin halin?


Abdul hakim yayi dry yace "haba khadija yaxakicewa d'an uwana me bakin hali dan Allah kada kisake aibata masa suna kinji.




Tace "amma kasan dai jinin mu bai haduba ko? Kasan baya sona yatsaneni gaskiya bana son nasake ganinsa..,Abdallah daya karaso gun yatseta da sauri "ke kaxamar yar kauye ba gunki naxoba kuma nima ba qaunar ganinki nake ba gun dan,uwana naxo


Ya nuna Abdul hakim "kai kuma ko kataso kazo muwuce muyi abinda yakawomu kokuma walh indauki mataki dan yanzu zanyiwa dadi waya inshirya maka sharri walh.




Abdallah yahade rai "kaga mallam banason rashin mutumci kabar gunnan ko muyi fada




"Mun dade bamuyiba dama gara muyin indai akan wannan bakauyiyar ce kuma kasani ba inda zan motsa walh kafara kafarka banza mara aji.




Abdulhakim yadawo da kallonsa gun dije da take hada kayanta zata bar gurin yahau bata hakuri dan yaga kuka takeyi




"Dakata khadija kiji nawane duka furar zanbiya ki koma gida ki huta kawai.




Tace ckn kuka "kabarshi kawai nagode ko iya cin zarafin dan,uwanka ya isheni ayau.


"Oh my god khadija banso ranki yabaci akan wannan inda sabofa yaci ace kinsaba,




Ta rike kugu takalli gefe tace "abokin birni yakamata kaima kabarni kamar yadda dan,uwanka yabukata tunda mutumci ne ajunanmu ba soyayyaba.




Yace ""naji amma kinsan Allah ne yahadamu bashi ba ballan tana yarabu kuma kinsan nayi sabo da shan furarki duk sanda naxo kauyen nan dan haka kizubomin aleda natafi da ita kokuma walh inkai kararki gun Addaji ince yau kinmin rowar furarki me ddi.




Ta duka ahankali ta juye masa furar data gama damun aleda takulle tabashi


Yakarba yana cewa "nagode ga kudin.




Ta sunkuci kayanta tayi gaba bata kulashiba shida kudin nasa




Tsaki Abdallah yaja yace "banxa kaxami meshan kayan kaxamai kai dai walh kalar zaren ba kalar yadin bane.




Harara ya maka masa "kashiga hankalinka zan b'atar maka walh ina ruwanka cikinka ko nawa?






Abdallah yai gaba yana masa dryr mugunta


shikuma Abdulhakim yabi bayansa yanata yi masa mitar abinda yayiwa dije




~~~~~~~~~~~~
Koda suka isa Gidan gonar dadyn nasu kowa safgarsa yashiga ran Abdulhakim abace yake kokula Abdallah baiyiba na tsahon wasu awanni yana fushi dashi


Shiko Abdallan
Yanuna ko ajikinsa hakan saida yaga da gaske Abdul din yake kana yaje yasameshi awata yar rumfar shakatawa yaxauna akusa dashi yace "Abokina har yanzun fushi kake dani ko?




Abdul hakim yai biris dashi yaci gabama da karatun news paper dinsa




Abdallah yakwace news paper din yace "kai dan iska nizaka juyawa baya akan waccen yarinyar da bata kai takawo ba kana nufin har anxo lokacin da wata zata shiga tsakaninmu lallai kuma nan gaba bansan yazakaimin ba inkanunata amatsayin wacce zaka aura inna hana.




murmishi Abdulhakim yayi yace "kana bani mamaki Abdallah kanayin abinda bai cancantaba kuma ba halin gidanmu bane wannan wulakanta dan adam din da kakeyi sam momy da dady basu koyarmu hakanba sunbamu tarbiyya kuma sun nusarmu da gane cewa talaka da me kudi da dan kauye da dan burni duk daya yake agun ubangiji.




"Amma ai ba matsayinsu daya aduniya ba. Abdallah yafada da zafin rai da daga murya




"Kai kake ganin hakan kuma lamarin Allah baida wuya xai iya maida me kudi yadawo talaka haka zai maida talaka yadawo me kudi kokuma dan kauye ya dawo dan burni harma yafi dan burnin bude ido da iya mu,amula ta wayewa






"Walh karya kake duk inda dan kauye yaje baxai taba wayewa ba dole saiya xauna amatsayinsa kaidai kawai sbd yarinyar can nne yau kaxama me wa,azi




Dariyar maganar Abdallah taso sille masa amma saiya dake yace "to kaima fa asalinka dan kauyenne koka manta anan aka haifi mahaifin dady nan ne asalinmu dan dai duk mun rasa kakannin namune da sun rikeka agunsu.




Wani naushi yakawo masa dan jin haushin lafazinsa


Abdul hakim yagoce da sauri yana dariya




Shikenan suka shirya




😂😂😂 aka shiga hira amma saida yatursasa Abdallah akan wai saisunje yabaiwa dije hakuri na yanda yasata kuka




Abdallah yaja tsaki yace "Allah yakiyaye inbaiwa sa,ar kanwata ta biyu hkr haba aiwalh ko za.a kasheni baka isa ba bakuma ta isaba sbd kana sonta saika bakanta min.




Abdallah yace "nifa babu soyayya atsakaninmu kawai amintace da haduwar jini.






Tsaki Abdallah yakara ja yace "hhhmmm kaji dashi duk yaran cikin gidanmu bakai aminta dasuba sai na kauye haba mutumina nafi kowa sanin halinka.




Abdulhakim yace "Amma dai kasan inada tunani bakamarka nakeba




Abdallah ya mike yabashi guri yana zaginsa "aikin banxa akwai mara hankali irinka dan,iskan kauye. 😅😅




Da yammaci sakaliya Abdulhakim yashirya tsaf yatafi gidansu dije yadade akofar gidan kafin yasami dan Aike yaturashi gidan yayo masa sallama da ita




Bata d'au lokaciba tafito tana ganinshi ta hau dariya tana fadin "walh nadauka ko baxaka biyo bayaba dana kara fushi akan wanda nayi.




Abdulhakim yayi dry yace "au dama fushi kk da abokinki bai saniba?




Ta murguda baki tace "eh mana bayan agabanka dan shigegen can yagama cimin zarafi amma baka dake shiba koka rama min koda da wata kalma ne me zafi dashima zaiji haushi




Abdulhakim yace mata "khadija kinga narasa yadda zanyi da Abdallah akan yadaina mk hakan amma abinda naga yafi kawai inhar yaimin kiringa ramawa kada kidubeni kawai nina saki domin innafiye shigar mk zamu ringa samun sabani dashi




Ta gyada kanta tace "to shikenan aiko walh baxan taba raga masaba dama albarkacinka yakeci


Abdulhakim yace mata "shigarni cikin gidan ingaida Addaji.




Tace " to muje.






har cikin dakin addaji takaishi suka gaisa ckn mutumci da Addajin sannan suka fito kofar gidan




Sunyi hirarsu ckn raha yabata janta da wasa da dari


Lallai wannan haduwar jini tanada ban mamaki




Zakuyi mamakin jin cewar sbd dije kawai Abdulhakim yake zuwa gidan gonar tasu




Toshi kuma Abdallah sbd wa yake xuwa knn?




Alh Mustafha hamshakin me kudine yana zaune da matarsa a unguwar shagari kwatas dake Zoo road


Matarsa daya mesuna hjy Samira mace me kirki da son jama.a kamar dai mijinta ga alkairi




Yaransu biyar aduniya banda uku da suka rasu


Aunty Maryam itace babba tana Auran wani tsohon dan,majalisa a jam,iyyar APC me kudine shima


Abdallah shine me binta shekararsa talatin da biyu Bashir shine na uku yana karatunsa a KUT wudil bording shi ba.a futarsa wajeba Shida kannansa mata Zannurat da Mubina " yammatane kusan sa,annin juna shekara biyune tsiransu zannurace babba tana Nouthwest sai mubina data gama secondry dinta yanzun zata fara karatun gaba da sec.din




Mahaifin Abdulhakim shine Alh Mahmud kanin Alh mustafha ne Allah yai masa rasuwa tun Abdulhakim na yaro sukayi accident shida matarsa hjy shafa,atu suka rasu dama shikadai ne dasu daganan bayan rasuwarsu rikonsa yadawo hannun dan uwan baban nasa




Rikon tsakani da Allah yasamu agidan basa nuna bambanci akansa duk abinda akaiwa Abdallah shi xa.ai masa wani xubinma har nashi gatan yanafin na Abdallah dayake akwai dukiyarsa ma agun Alhajin gadonsa knn.




Abdulhakim yabaiwa Abdallah shekara uku Amma sai anfada dan Abdallah yafishi bargon jiki yanayinsu ba daya bane Abdulhakim dan jikine dashi shiko Abdallah kakkaurane




Abdallah da Abdulhakim kud da kud suke basu taba fda ba inba na wasaba kuma Abdallah yana bashi girmansa suna mutumta juna sosai wani baya zartas da wani abun saida shawarar dayansu




Zannurat tana matuqar son Abdulhakim Amma takasa gaya masa saidai alamu da take nuna masa amma yakasa fahimtarta




~~~~~
dijen kauye marainiyace Asalin iyayanta sun rasu itanma tun mahaifiyarta na haifarta ta rasu aranar mahaifinta kuma saida ta fara girma yarasu Rikonta na hannun yayarsa da suke uba daya dan baida kowa sai yaruwarsa da kaninsa akauye su biyu ciki daya shikuma uwarsa da ban amma sai in anfada kansu ahade yake




Addaji itace marikiyarta tanason dije sosai bata taba haihuwaba shiyasa tamaisheta tamkar ta cikinta fulanine su usul ma kuwa






Dije yarinyace me karancin shekaru amma tanada girman jiki shekararta goma sha shida amma saika zaci tayi 20




Sai intabuga sokonci zakagane yarinta natare da ita




Kyakykyawa sosai gashi har baya saidai ba gyara gata dason tayi gayun kuma akullum tanaso taga mutum dan gayu shiyasa Abdulhakim yake burgeta gashi tana burin taga taje birni tayi rayuwa acan saidai kuma batada kowa acan ta yaya knn zataje birnin ???
Yaushe burinki zai cika……?😂








*Auntyn Sayyada da Shahida ce*[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:👌🏼
🐄 *"YAR FILLO...* 🐄
_Dijen k'auye_
🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕
















*True life Story*












*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)










5-10




Kwanansu daya akauyen Dan Rogo suka kammala abinda sukeyi suka hau shirin komawa gida




Akwai ma,aikatan dake kula da kaji da Ragunan da shanun dake ckn babban kangon da yaxama gidan gona domin garke guda aka ajiye shanu da raguna ga bangaren kaji masu kwai daban marasa kwai daban




Duk da akwai ma,aikata amma sukanxo su duba Suga komi yayi sukuma ga babu matsala sannan su ware kwai kret-kret agefe kafin axo adauka






Saida suka fito suka shiga mota sannan Da sauri Abdulhakim yai zumbur kamar Anmin tsineshi ya mike yafito daga ckn motar




Abdallah yace masa "dalla mallam ina zakaje kuma muna sauri muwuce ?




Abdallah yace dashi da fara,a "pls kayimin alfarmar naje muyi sallama da Kawa kada nayi laifi.




Wani mugun tsaki Abdallah yaja kana yace masa " walh baka isaba babu inda zakaje inko katafi to katabbatar ma baxan xauna jirankaba xantafiyata




Abdulhakim yasan hali zai iya dan haka saiya dawo motar da dacin rai yadubeshi yace "kasan Allah duk abinda kakeyi taraka nakeyi kaci gaba




Abdallah dake sit din dreba yayi tsaki yace "kaji dashi nidai nahana soyayya kuma dole ahakura.




Abdulhakim yabuga masa wata harara yace "oya futo kabani na tukamu dan baxan yarda kayi gudu damuba nasanka da wutar ciki da azalzala banaso ayi gudu dani atiti.


Salin alin Abdallah yafito yabashi sit




Shikuma yadawo yatashi mota yacillata kan titi




Yanaji yana gani suka futa daga kauyen bai biya gidansu kawar saba domin inyace xai wuce dasu amota to duk abinda Abdallah yayiwa dije baxai futa aguntaba xata xaci ko yakaishine dan yaci mata xarafi kuma yasan xa,ai hakan




Shiko Abdallah dariyar mugunta yake masa kwai don yaga yadura yacika yayi tam




Suna tafe suna sauran wakar celindion music ne


Abdallah ne yakunna tunshigarshi motar


Abdulhakim yakaihannu yakashe wakar adaidai lokacin da Abdallah ke lumshe idonsa yanajin ddin wakar yana sonta gashi anxo daidai baitin dayafiso ackn wakar sbd kalamin da akai amfani dashi shi masoyiyarsa *lowest* ke yawan yi masa intasaka wakar ko insuna tare alokacin suna turai _i still have feelings for you.Not enough to want you back.but enough to make it hurt_ … wannan kalami na cikin waken natayar masa da hankali da tuno masa abar kaunarsa lowest wacce da ita yafara yin soyayya aduniya har yanzu kuma baiga wata kamartaba saidai tayi masa nisa Auransu kuma baxai yiwuba tunda ba musulma bace amma tana son ta musulunta adalinsa Amma yana tsoron iyayansa inhar yace musu ita zai Aura yasan da kamar wuya sbd Asalinta




Har suka shiga kano babu wanda yacewa dan,uwansa kanxil


Wayar Abdulhakim tayi ruri yadauka yaga sunan Aunty Babba ce wato yayar Abdallah kenan Aunty Maryam babbar yayarsu




Yadaga da sallama suka gaisa tace masa "Ina nemanku yanxu kaida Abdallah maza ina jiranku agidana.




Yace mata "to " kawai yakashe wayar yakarya akalar motarsa sai gidan Aunty maryam datake zaune a Sultan Road GRA ne unguwar silenly




Abdallah yasha mamakin ganin sunyo unguwar GRA batareda anyi masa bayaniba to amma saiya xuba masa idanu baice kalaba tunda shima baice masa ba amma dai yafahimci cewar da Aunty maryam knn yayi waya shiyasa yayi gidanta




Yayi horn me gadin gidan ya bude suka shiga ya daga musu hannu suma suka daga masa




Tana zaune afalonta tana kallo suka shigo




Da fara.a ta taresu tana cewa "Ga "yan kanne na ga kanne na.




Suka xauna akan kuje suna cewa "wash! Atare




Tace musu "ikon Allah ina kukaje haka kuke kiran wash kamar wanda kukasha Aiki?




Abdulhakim yace "walh Aunty daga gidan gona muke yanzun haka ko gida bamujeba tun jiya muna can muna hanya kk kiranima.




Tace "Sannunku bari akawo muku abin motsa baki.


Abdallah yace "nikam ruwa kawai nake bukata.


Takwallawa me aikinta kira




Dataxo ta umarceta akan takawo musu ruwa da lemo.




Saida suka sha abu me sanyi kana suka gaidata




Abdulhakim yace mata "Aunty gamu kince kina neman mu meya faru?




Ta gyara zama tace "wato daxu dadynau Safna yakawon wani zance dayai min dadi wai yanaso yahada Ni,imah da Abdallah Aure amma in yaga yana sonta sbd yana sha,awar asake kullah halaka mekyau da ahalinmu...


Aibata kai karshe ba Abdallah yatari yawun bakinta yace "tsaya haka aunty kada ayi nisa da zancen wacece Ni,imah kuma?




Tayi murmushi tace " Kanwar Dadyn Safna mana saikace baka san taba kawar Zannurace fa kud da kud.




Yaja tsaki yace "batayimin ba plz aunty abar zancen nan iya nan dan Walh bata ckn kalar jerin matan da nakeso na aura




Abdulhakim yagalla masa harara yace "aiko dai walh baka isa ka watsaya dadyn Safna kasa a idoba kama sani kamar anyi angama.




Yayo kan Abdulhakim da fada "to aishikenan ubana inka isa dani kadaura auren ingani.




Aunty maryam ta daga masa hannu ranta abace tace "kai mara mutumci nixaka bawa kunya ni xaka wulakanta …
"Aunty ba wulakantaki nayiba gaskiya na fada




Tace "wane gaskiya kodai rashin mutumci meye da Ni,amah na rashin kyau da xa.a k'ita gata da ilimi gata da kyau gasu da arxiki to me kake nufi da nuna kin aurenta ? Ko ka nunan ban isa ba kokuma ka wulakanta min miji kasa kuma inji kunya ko? To walh baka isaba wannan maganar saita zama babba dan saina kaita har gun Dady






Abdallah ya mike afusace yafuce yabarsu afalon




Ranta yabaci Abdulhakim yahau bata hkr "kada ki damu Aunty tunda har dady na kasar kawai kije kisanar masa kinsan kuma dole za.aiwa tufkar hanci.


Yai mata sallama yafuto yatarar da Abdallah ackn mota yanata kumbure kumbura




Baikulashiba yashiga yajasu suka futa




Abdallah yace masa "kaga mallam kafuta daga ckn maganar kada kasa baki ack dan walh banga me yimin doleba




Abdulhakim yace "Aure dai dole kayishi duk gudunka ……




"To inga meyiminshi ban shiryaba kokai dole akai maka naga kabani shekara uku atleast yanzu kanada 35 kaine ma yakamata asawa ido afarawa yiwa Aure baniba.




Abdulhakim yaharareshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login