Showing 15001 words to 18000 words out of 39246 words

Chapter 6 - YAR FILLO COMPLETE DOCUMENT BY Nabilancy Love 😘.txt

07 Feb 2025

5326

🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕
🏕








*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)








PG 100-105


Dan Allah ayi min uxirin posting din yau baxaku samuba sai gobe ko jibi ina fama da mura da ciwon kaine ………














*sorry fans*


_tommorow insha Allah zamu jone_
🐄 *YAR FILLO*🐄
_Dijen kauye_
🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕








*Alhamdulillah Masoya "Yar fillo kunnuna min Soyayya gashi Allah yabani lfy nasami sauki ina godiya na nunamin kulawa masu sako da bugo waya najin Dijen kauye shiru nagode sosai Allah yabar kauna Amin*








*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)






-PG
50-55


Dije dan bakin ciki harda hawaye tarasa ya zatayi dashi yau


Itadai ba iya daukarsa zatayiba balle takaishi dakinsa kuma bata tabah shiga gun Ni,imaba balle ta shiga tagaya mata don tazo ta taimaka tunda ko banxa ai mijin sune tare


Tahau tunanin ko dai me gadin zata je tagaya masa halin da ake ciki


Ganin Abdallahn ya mike tsaye taga taga zai fadi yasa tayi saurin rikeshi da karfin tsiya ya jingina da jikinta


Batasan tanada wannan karfin ba sai yau domin jansa tayi jikinta ta sakalo hannuwansa kafadunta suka hau tafiya ahankali zuwa dakinsa


Takwantarshi akan gadonsa


Ta bude siff dinsa ta dauko wata jallabiyar ruwan toka ta cire ta jikin nasa datasha amai ta canxa masa da mai kyau




Sosai taringa juriya takauda kanta gefe don ganin tarin gashin kirjinsa lallai shi din dan baiwane


Jikinsa ya burgeta tana son namiji me fadin kirji da gargasa saidai kash! inama jikin Abdalla ne haka domin har kullum tana saka ran wataran zata auri Abdulhakim din


Saida tasaka masa rigar sannan takai me aman toilet tareda jiko tawul taxo ta goggoge masa fuskarsa da hannuwa da kafafunsa ganin amai ajiki taringa toshe hancinta tsami yacikata


Taduba mirro dinsa ta dauko Air freshner zata fesa dakin saikuma wata zuciyar ta hanata "kul kada ki fara salon inya farka ya yaba miki ko kuma ya zageki ya gwasale ki, sanin kankinefa ba.a yiwa wannan banxan gwaninta


Ta maida Air Freshner din amazauninsa tareda fucewa dg dakin jiki asanyaye


Saida tagyara falon tas ta feshe shi da turaren k'amsasa daki kana ta tafi takwanta ranta cunkushe da bakin ciki na gano halayyar Abdallah tashan giya tabbas agobe zata gayawa Abdulhakim komi,tasan bazai goyi bayan taxaunawa dan giya ba kuma tabbas zata gayawa iyaye don araba Auren domin baxata zauna da dangiya ba




Da bakin cikin Abdallah cunkus aranta takwanta


Shiko gogan baifarkaba sai safiya tangararan


Giyar ta sakeshi yamike yana mika tareda mamakin ganin inda yake da kuma ganin jallabiya Ash, ajikinsa shidai yasan fara qal yasaka daxai fita kuma mamaki yake shin waye yadawo dashi gida dg cluv?


Ya shige toilet yasallo wanka yayo Alwala sannan yafito yayi makararriyar Sallarsa


kicin din Dije Yanufa domin ya dora ruwan zafi shayi yake son yasha


Ransa yai matuqar baci naganin babu gas cikin cilinder din




Yaza.ai ckn sati biyu ace Gas yakare to uban me take dafawa akullum haka?


Idonsa rufe yanufi dakinta da ayaune karo na farko daya fara shigarsa

Yana shiga yabuga kofar tareda kwalla mata kira "ke "yar kauye kina ina?fito kigayamin gidan uban wa kk kai gas din kicin?


Afurgice Dije ta tashi tana mitstsika idanu don bacci takeyi yatayar ta


Ya tsaye mata aka ya nunata da yatsa "wato kinganshi bitalmanu shine kika saka aka zuk'e aka siyar mk kika aikawa tsoffin kauye kudin ko?


Dije bata gane nufin saba saitahau zare idanu


Yaci gaba da masifa "bari kiji ingaya mk nan ba gidan da akeyin almubaxaranci bane don da kudi muke siya ba.a ruga muke debowa ba


Harya juya zaifita yakuma dawowa yatsaya akanta yace "zanje yanzu nayi refelling sbd bukatar kaina ba takiba don hk kikula kada inkara ganin gas yagaxa wata inko ba hakaba zansiyo mk ice domin dashi dama kk saba,


Waima ya akai kika iya kunna gas ne ma? Yatambayeta da wulakanci yana harararta


Ta bude baki da tsiwa itama tace "tambaya kakeyi? Intambaya kakeyi kaje aji malam yabaka amsa aikin kawai.


Tana gama fadin haka ta sauko daga gadon ta wullar da bargon data rufe jikinta saigata daga ita sai gajeran wando da yar shimi data kamata bigil




Ita tama mance meye ajikinta to bata saba ba dama jiya da dare tafara saka irin shaidanun kayan nan Mubina ce ta dage saita fara koyar sawa


Saida ma taje bandakin data ganta a mirro tahau jinkunya tana cewa "wayyo nashiga uku yanxu ahaka yaganni? Aradu na mance a yanayin danake amma banso wancen banzan gardin yaganewa Abdulhakim jikin danake masa tanadi ba😭😭


Shi ko gogan ai baku saniba idan ba jikin Dijene ya furgitashi tab! Fatarta dake sheki kadai ta shagaltar dashi ga nashanunta daya fito waje sukai tozali 😱 lallai haka abin yake ashe ?


Koda tazo shiga toilet ma bin bayanta yai da kallo yaga maxaunai na motsawa gwanin sha.awa ckn 3 kwata me mannewa afatar jiki


Ya dade adaki yanata zarya yana dukan hannaye abango kyakykyawan jikin Dije yana masa gixo a idonsa


Shaff yamanta ma zaije yai refelling gas


Saiyaji yanaso yakara ganinta akaro nabiyu


Kai tsaye yashiga dakin dayake yasami tacewa


Yatararta gaban mirro da daurin kirji tana shafa


Yatsaya daga kofa ya harde hannaye ransa abace yace "ke waye yashigo ya ciren riga ya canzan wannan?.ya nuna ta jikinsa


Takalleshi awulakance tace masa "kafara zuwa katambayi me gadi kaji cewar ajiya da dare awane yanayi kadawo tukunna saikaxo inkarasa maka amsarka.


Yace "ainasan da me gadin amma naxo na tambayeki ko?


Ta rausayar da kanta tace "Eh nasan da haka amma shima yataimaka maka kamar yadda nima nataimaka maka yadda yashigo dakai ckn gidanka ya rufa maka asiri haka nima nataimaka maka alokacin daka bata jikinka da amai nacanxa maka data jikinka amma kasani idan me gadi yai maka rufin asirin kada wani yaji irin abinda kake aikatawa nashan giya toka tabbatar ni DIJEN KAUYE baxan taba rufa maka asiriba domin ayau ba sai gobe ba walh zanje nafadawa iyayanka komi....."kinada kai kuwa?had'ani dasu zakiyi knn to walh babu inda zakije


Tayi dariya tana tattare gashinta ckn ribons (dijefa akwai gashi bakikkirin har bayanta yasauko)


Tace masa "kana wasa da dijen kauye yau zakaga tsagwaron kauyanci domin baxan hanuba ko akafa saina fita walh agidan nan.


Yadauka ko wasa take yaja tsaki yafita




Itako tanata kiciniyar shirin fita don lokacin tara da rabi nasafe


Acan bangaren Ni,ima kuwa tananan tashaqa tayi fam kamar tafashe najin shiru Abdallah baishigar mataba alhalin jiyan .ma kwanan tane sai zcyrta tahau wassafa mata cewar sunacan suna soyayya da dije aiko dai kishi yataru fal ranta


Baishigo mataba sai goma daidai alokacin ta shirya tsaf tana jiransa yashigo tanemi izinin futa




Koda yashiga ckn ladabi tagaidashi


Ba laifi ya amsa mata da sakin fuska


Taso tayi masa complain saikuma tafasa tunda tasan halin nasa kada yabutsare mata suyi rigima yahanata fita itako ayau ko satar futa saitayi domin tajewa da boka bukatunta


Cikin ikon Allah, Allah yadorata akansa tana tambaya zata gaidasu momy yabarta yace tafito yakaita don can yanufa


Suka fito suka tafi


Kafin dije ta fito harya fice amotar shida Ni,imar


Itako dije dayake da kudi ahannunta bata kulaba dajin karar motarsa balle taga shida ni,imar nema


Tana futa ta tsaida dan sahu tafadi inda xai kaita dayake mubina ta tisa mata kwatancen gidan nasu baya b'uya bame wahala bane dady sananne ne


Dama sbd hakan ko xai hanata zuwa wataran yasa ta nemi kwatancen gun mubinar


Kafin ashiga layin
Aka ajiyeta don zata gane gidan


Adaidai kwanar shiga gidan nasu shikuma Abdallah yakaryo motarsa yafito yaja burki da karfi ganin dijen tazo gidan nasu yasha mamaki matuqa yakuma kadu tsoronsa ko zata ida nufinta ayau din tagayawa su momy zancen giyar dayasha jiya domin kuwa dadyn yananan yanzun ma sako zai karbowa dady awani waje


Da sauri yafito amotar yatari gabanta yana fadin " yanxu saida kk fito yarinyar nan ashe dama ba.a koya mk bin maganar miji ba?


Taja tsaki tace " waye mijin?tab ai walh har yanxu banda miji don wanda nakeso shi nake fatan yazamo mijina amma kaikuwa ban more miji dan shaye shayeba tirr!! Ta tofar da yawu


Ransa yai masa quna na kalaminta amma sai ya maze don lallabata yakeso yayi yace


"To naji dan Allah ina neman Alfarmar ki rufamin asiri iya yau kawai ma kada ki gayawa dady da momy dan Allah baxan sake shan barasa ba nayi mk alqawari kinji.


Ta matsa gefe guda tana masa gatsine "wannan kuma kai tashafa bani ba ji kuma kamar sunji sungama.


Ya harxuka yace "to kifada mana sai me inkin fasa keba "yar halak b ace kuma kisani walh inkika fada musu yau sai jikinki ya gaya miki.




Yashige motarsa yai gaba


Itama tanufi gidan ranta abace fuska ba fara.a


Tana shiga suka gaisa da me gadi




Dayake bai ganetaba saida tayi ms bayanin kanta sannan suka Sake gaisawa mutumce again


Tun shigowarta gidan
Abdulhakim yahangota tashigo itakadai saiya cika da mamaki tunda yaji xuwan Abdallah shida Ni,ima take yasha jinin jikinsa tabbas ba lfy


Ckn sauri yasauko yaje yatareta a korido


Saiganin mutum tayi diff! Agabanta taja ajiyar zcy tareda sauke kwayar idonta akansa


yaji Kamar yakama hannuta saikuma yafasa yace "Khadija lfy?meyafaru naganki haka fuskarki ta nuna alamun ba lfy khadija me akai mk?


Dije akwai raguwar zuciya take tafashe da kuka


Yace "kinga yi shiru rufe bakin kada wani yajiki taho muje can bayan gida wajen boys quarters kigayamin


Yashige gaba tana binsa abaya har gun wasu kujerun roba


Suka zazzauna


Bata daina hawayenba


Yakara tambayarta ko lfy?


Nan tahau gaya masa abinda takama Abdallah yayi jiya nashawo giyar da yayi yaxo mata abige


Jikin Abdulhakim asanyaye yaji mamaki to yasan dai khadijan bata karya to amma ai baitaba kama dan uwan nasa da kwalbar giyaba koda empty ce anya kuwa ba shiryawa khadijan tayiba don bata sonsa.


Yace mata "khadija Abdallah ba mashayin giya bane don bantaba kamashi da kayan maye bama kodai wani laifin yayi mk zaki fakaice da k'ak'aba masa shan giya


tayi rau rau da ido tace "walh da gaske nk kaje ma katambayi me gadi shine shaidata.


Ya gyada kansa "to !to naji goge hawayen banso ki sake zubda hawayenki akan wannan zanje nayi bincike akai amma yanzu inaso wannan yakasance secret kada wani yaji yaxamto kinxama me boye sirrin mijinki kinji.


Ta zob'ara baki tace "tabdijan ai walh kadaina kiranshi da mijina ma
.
Yayi dariya yace "to waye mijin naki inba shiba.?


Tayi shiru kanta akasa


Yace "khadija bakinki akwai magana ko?


Ta gyada masa kai


Yace "to ki boyeta zanzo gida gobe muyi maganar amma yanzu ki tashi kije kigaida su dady gacan kishiyarki ma taxo gaidasu


Ta mike tana fadin "To nidai muje kashigen gaba


Ya mike shima yana fadin "ho !!khadija "yar daruna


Tayi masa wani kallo daya kasa fassarashi


Masu karatu ko zaku iya fassara masa ,…………????
😂😂😂




_Muje Zuwa_




*Auntyn Sayyada da Shahida ce*
🐄 *"YAR FILLO* 🐄
_Dijen Kauye_
🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕







*True Life Story*











*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)








PG
55 - 60


Dije taringa bin Abdallah abaya har cikin gidan saida yasadata da falo inda momy take da muqarrabanta sannan yahaye sama Abinsa sbd idan har Zannura tana guri baya zama agun sbd yanda take shishshige masa baya so sam jininsu bai haduba


Shigowar Dije dakin Bakaramin bakantawa Ni,ima da Zannura rai yaiba hira suke suna fara.a amma lokaci guda suka tsaya cak!da hirar sannan suka hade rai


Ita kuwa mutuniyarta Mubina aguje tayi gunta tana mata oyoyo tajata ta xaunarta a sit tazauna kusa da ita momy ma ta nuna murna da ganinta tasa mubina takawo mara abin sha


Zannura tahau harare harare da tsaki tana fadin "Momy naga sai wani farin ciki kk dan kinga gayyar kauye saikace kinga abin Arxiki.


Duka sosai momy takai mata ranta abace tace "kishiga taitayinki nizaki gayawa haka? Matar yayan naki kk cewa gayyar Kauye? Toki sani khadija me muhimmanci ce aguna kuma abar arxiki ce tunda makaunaciya tace tun kafin tasanni azahiri take min aiken fura kuma inajin dadi kuma har akullum innatuna nakanji dadi araina don hk ki iya bakinki walh tallahi baxan yarda ki wulakanta taba inko kk sake mata hakan zan hadaki da dadynki ato.


Zannura tacika tayi dam ganin yanda momy ta hakikance ta rufe idanu tana mata fada akan yar kauye dije


Ta mike afusace takalli Ni,ima tace "tashi mutafi unguwar da zamu nikam baxan iya xaman falon nan ba.


Ni,ima ta mike tace da momy " momy bari muje dubiyar friend dinmu mudawo.


Momy tace mata "to kada dai ku dade kudawo da wuri.


"To momy .


Suna fita momy takalli Dije dake takure tace mata "khadija kisaki jikinki kinji kada kiga hakan tafaru dake ki tsangwami kanki wannan ba wani abu bane indai ina nan babu wanda zai takaki inkyaleshi kidauki nan tamkar agidanku kk haka ma ki daukeni kamar nina haifeki in akwai wani abun kixo kisameni da shawara zanbaki inma wani abun kkso zan mk haka kuma in wani abun Abdallah yai mk kada ki boye aranki kije ki cutu abanxa kigayamin kinji?


Dije ta daga kanta tana dan murmusawa saitaji dadi aranta taji qaunar momyn takaru aranta taji inama batayiwa Abdulhakim alqawarin boye shan giyar data kama Abdallahn keyi ba da tabbas yanzun zata fadawa Momy saidai bazata iya karya Alqawarin Abdulhakim ba sbd son da take masa




Dije taji dadin zuwanta gidan momy ayau domin taringa nan nan da ita domin da ranama saida ta tambayeta abinda takeso agirka mata sannan akayi alale tace tana so kuma shi momyn ta umarci me aikinsu tayi yaji kwai aciki




Haka da dadyn yafito falon ba karamin nuna farin cikin ganin ta yayi ba


Dije bata tabbatar da irin qaunar da dadyn ke matabama saida taji yayi waya da Abdallan yace yataho masa da waya karama mekyau sabuwa keypard da layin mtn.


Da Abdallahn yadawo kuwa yana baiwa dady wayar dadyn yamiko mata kyautarta yace mata "khadijatu ga tukuicin furar da nakesha akauye yanda kika faranta min inaso naxama me faranta mk sannan inaso in tambayeki kan cewar kinada ra,ayin karatu anema miki kifara daga farko ko kuwa bakyaso abari?




Khadija data kankame waya tana faman farin ciki tahau naxari anya kuwa zatayi karatu kuwa?


Tanadason taga yau itanma tanajin turanci saidai tasan zatasha wahala sosai kafin ta iya wasu abubuwan takalli wayar hannunta tasan ita kadai darasine akan rashin ilimi domin inbakada ilimi ma hatta waya gagararka take ka iyata koda calculata ce


Tanaso kuma ace itama tazama wayayyiya kodan yan iskan mata yan rainin hankali irinsu Zannura


Dady ne yakatseta da cewa "khadija inkinga bakya ra,ayin karatu bazan takura mk kiyi adoleba dama ra,ayinki nake sonji tunda kokin aminta sai in mijinki ya amince sannan zansa ya nema miki.


Dije ta dago kanta asukawane takalli Abdallah dayake ta danne danne awayarsa kamar bayajin abinda dadyn ke cewa ma


Takalli dady tace masa "na amince dady inaso


Dady ya gyada kansa yace "yayi kyau to Kai Abdallah kaji khadija nason karatu ta amince innema mata kaima ka aminta?


Kansa akasa yana amfani da waya yace da dady "wannan ba matsala bane na amince tayi karatunta.




Dady yace "to ai shikenan saika nema mata akusa da gidanka kuma mekyau nakeso ta fara daga primary yakamata tafara


Abdallah yakarkace kai yakalli dije yace "yanzu dady wannan godeden ce zatayi primary ackn yara ? Lallai amma zata zama maman yara kenan


Momy ta tareshi da fadin "to inbanda abinka Abdallah nawa khadijan take da baxata shiga ckn yara ba itada natabbatar ko sha bakwai batayiba sannan kuma ai tanada fuskar yara girman jikin me kawai kaidai kawai kayi mata fatan Alherin.


Dady yace "koma dai meye banaso asami matsala nabar maka komai ahannunka indai private ce zasu karbeta ko aji nawa ne tunda kudi za.a kashe don haka banaso asami matsala katabbatar kuma kai zaka ringa kaita makaranta kanaji


Ran Abdallah abace ya amsa da to kawai badan yasoba


Abu dayane yafaranta masa rai dayaji har zuwa wani lokaci iyayan nasa basui masa magana akan ko dijen takawo kararsa ba sai hankalinsa ya dan kwanta don ya zaci ko yanda tace masa zata fada din ko ta fada.


Duk yanda ta wakana afalo akan zancen saka dije makaranta Abdulhakim yaji tas dayazo saukowa amatatttakalar benen ransa bai masa dadi ba sbd bayaso ace khadija tana futa kullum sbd yasan inhar akace yau khadija ta waye ta bude idonta to za.a sami matsala yatabbatar baxata zauna da dan,uwan saba.


Daki yakoma yazauna akan gado yadafe kai yahau tunanin mafita


Abdalla yashigo dakin nasu yana fadin " dan,uwa wai dama kana cikin gidan Amma banji motsinka ba?


Abdulhakim yadago kansa yakalli Abdallah yakakaro murmushi yace dashi "ina cikin gidan banfita ba banajin ddi ne.


Abdallah yabashi hannu suka gaisa yace masa "sannu friend ko akwai damuwa ne?


"Babu wata damuwa kawai dai baccine da bai ishe niba jiya nakai dare sosai ina ciccike files dinnan da za.a fita dasu gobe


Abdallah yace masa " ok sannu dan,uwa Allah yasauwake.




Amin


Harya juya zai futa Abdulhakim yakirashi yawaigo yace "akwai wani abunne?


Abdulhakim yace "kwarai xoka zauna muyi magana me muhimmanci ma kuwa.


Yaxauna kusadashi


Abdulhakim yagyara zama yace dashi "uhhmm akan maganar Khadija ne dama.




Gaban Abdallah saida yafadi domin yasha ko zancen dasukai na shan giyar dayai ne da ita ko dama Abdul din tagayawa aiko yana shakkar Abdulhakim yaji sbd baya masa ta dadi zai iya juya masa baya su bata




Abdulhakim yace "wato naji maganganunku dasu dady daxu akan batun saka khadija makaranta da za.ayi nikam banso hakan ba banso kuma naji ka aminta ba sbd khadija bata san kowa ba akano saimu inajiye maka halin matan birni da maxuga kaga lafiyar Allah take kada tazo ta shiga sch tahadu da muggan kawaye su canxa mata ra.ayi akanka taxo tafi karfinka dan haka ina me kiranka da babbar murya akan kadakatar tun wuri sbd....


Abdallah yadaga masa hannu "dakata Abdulhakim wato inna fahimta so kake kace min nan gaba zata iya fin karfina lenan?


Gyada kai kawai Abful yayi


'"Ta dade batafi karfi naba walh ni da hakan zata kasance zanfi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login