Showing 30001 words to 33000 words out of 39246 words
Chapter 11 - YAR FILLO COMPLETE DOCUMENT BY Nabilancy Love π.txt
kawunansu kamar wasu yara suka hau kuka babu mai rarrashin wani ackn su
Dady ne yazo inda suke yaji tausansu ya zauna kusa dasu yana gyaran murya suka dago ganinsa ma yasa suka kara wani kukan aransu
Abdallah yahau sambatu "dady kaga zannura ta mutu tabarmu ko?yanzu yaya zamuyi?
Dady yatoshe masa baki "kayi shiru Abdallah kayi mata Addu,a shiyafi ba kuka ba shixai tabbatar da kuma kana kaunarta bawai kuka ba hawayenka masiface agareta kuringa daurewa ranku mana kune fa yakamata ku hana amma bawai ku kebe kuna mata kuka ba
Nan dai yaita musu nasiha da ban baki har sukai shiru
Likita ya aiko kiransu dukansu
Bayan sunje sukaji wani bayani agunsa mai tada hankali domin jakunkuna yabasu wai atare dasu Ni,ima aka gani da alamar tasuce tunda aciki akasami wayar da aka kira daddyn
Sannan yasanar musu cewar Dole sai anfuta da Ni,ima waje don lamarinta yafi karfinsu awajen ne zasuyi mata aiki haykan da zata iya tashi tayi tafiya amma zasusha caji na kudade.
Dady kansa saida yayi hawaye yaji tausayin Ni,imar bayama daya ganta kamanni sun canxa hatta hancinta yayi fosss! Bakinta ya kumbura lebunanta sun tashi
Abin tausayi walh
Koda suka bude jakunkunan nasu sunsha mamaki ganin abinda ke ciki
Momy tana kuka tana dubawa tana fadin "Allah yajikanki zannura bansan meya kaiku gun malami ba harya baku wadannan layuka da magungunan walh danasan haka zata faru daban barkuba.
Aunty maryam tace "momy kiyi mata addu,a kawai mubar wani bude bude aje ma azubdasu kafin wasu su fahimta Allah yajikanta.
Sauran dake gun sukace Amin.
Mubina da Dije suna baranta sunata kuka
Dady da mijin Aunty maryam suka nemi asallami Ni,ima aranar domin su zasu kaita egypt d kansu
Aranar aka kai zannura makwancinta Allahu akbar Allah ya yafe miki ZANNU. Yasa kin huta
Ana zaman makoki su dady suna can wani babban Asibiti akasar wajen ana baiwa Ni,ima taimako donta sami lfy sbd ta bugu sosai acknta kota farfado ihu kawai take tana kuka tana dukan cikinta tamkar ta tabu
Koda sukai mata hoton cikinma sun gano mahaifarta ta tabu sosai ga jini daya taru ackin amma suna bakin kokarinsu akanta don acikin sati ta fara samun lfy ckn yai mata sauki ammafa ankashe kudi hatta Abdallah saida yaturo kudi ta account din dady wanda dadyn bai saniba da baxai barshiba tunda shima yanada kudade wadatattu abankuna har 5 haka shima yayan Ni,imar yana iya bakin kokarinsa ganin yayi abinda yar,uwarsa zata warke shima da anbukaci kudi zai bayar sbd yana son Ni,ima yanaji da ita uwa daya uba daya suke amma iyayansu sun rasu dama agunsa ta taso shiya Aurarta ga Abdallah shiya dage tsayin daka akai Auren.
*******
Bayan sadakar bakwai din Zannura suka dawo kasa Nigeria cike da sa.ar samun saukinta tana motsa jikinta fiye da da sannan anyi mata aiki akashin guiwa amma baxata taka da wuriba saiya warke fuskarta tasamu don kamanni sun dawo kunnenta anmata dinki yahade tsaf saidai mahaifarta ta sami matsala ba ita ba haihuwa sannan ansai mata keken guragu akai dole zata ringa tafiya amma da sandunanta da zata ringa dan yawo inta warke
Ba karamin tausayinta Dike taji ba domin da aka dawo da ita ma ita ta tare ida mubina adakin da aka warewa Ni,imar suna bata kulawa duk motsin a zatayi akan idon Dije nan da nan zata hau tambayarta "lafiya ? Me kk bukata? Me za.ai mk.
Ni,imar tanajin dadin hakan har kwalla take fuddawa inta kalli dijen ta tuno abubuwan data ringa mata abaya.
Sau dayawa tana son ta nemi yafiyar amma takan kasa ganin mubina na gun saidai kawai intaga irin kulawar da dijen ke mata saitahau mata murmushi kawai
Momy najin dadin yanda diken keyi tamkar ba kishiyarta ba shiyasa ma taji takara kaunar dijen itama
Abdallah yakan shigar mata ya dubata yai mata addu.ar fatan samun lfy daya shigo dijen ke futa fuskarta babu fara.a yana lura da hakan saiyaji ba dadi aransa don azatonsa ko tsanar datayi masa ne yasa bata son taganshi
To amma anata ran ba haka bane guri kawai take bashi shida matarsa ko zasuyi magana tunda tasan yana son Ni,imar sosai itace ta gaban goshinsa.
Sati biyu knn da faruwar wadannan Al,amuran dady yanemi da Dijen tafara zuwa sch din da aka nemar mata.
Amma sai dijen tace masa "Dady daka bari sai anyi arba,in tukunna domin kada aga wautata anyi mutuwa agidanmu amma ina futa makaranta.
Dady da momy suka dara sukace "wannan ba wani abu bane khadija mutuwa anriga anmutu babu me mk wata magana akan hakan Zannura ta tafi knn addu.a kawai zakiyi mata inkin tunota.
Abdallah da Abdulhakim sukace hakan da tayi daidai ne kawai abarta din sai anyi arba..in
Duka wannan ra.ayun sune kuma dadyn yabi
Sunga hankalin dijen
To yau da gobe ta Allah ce saigashi anyi sadakar arba,in har Dije tafara zuwa sch ansakata daga pri.2 gwanin sha.awa inka ganta ackn unifoam tamkar balarabiyar misra driver ke kaita yaje ya daukota
Da taimakon mubina take samu kwakwalwarta ke budewa duk abinda akai mata tana kwashewa duk wani home work mubina na nuna mata yadda zatayi kuma intayin tana cinyewa da sannu yazamo itake daukar na daya,zuwa na biyu ammafa tayi girma da ajin saida takai anmaidata pri.5 danganin kokarinta cikin shekara uku tagama primary cike da sa.a kowa agidan ya jinjina mata dady yabata kyautar sabuwar waya android alokacin data shiga secondry ne jss one akasaka ranar Auran mubina da Abdulhakim wanda kuma ckn ikon Allah suka hada kansu suke tsaftaciyar soyayyarsu tana bashi girma haka shima yanaji da ita sosai
Alokacin da dije tagamo suna soyayya tasha kuka adaki ita kadai takuma dangana taringa addu.ar Allah yacire mata sonsa tunda iskace ke wahalar dame kayan kara Amma kuma kullum kara tsanar Abdallah takeyi bata son ganinsa ko kusa ko alama balle taji sonsa aranta
Shikansa Abdallahn gidan yadawo kacokan tunda can din gyara akeyi asashin dijen kuma bazai iya zama abangaren Ni,imar shikadai ba
Abinda yanxu yakeji aransa yana damunsa abin Son ganin dije da son jin muryarta yarasa dalili domin yanajin wani nishadi inya ganta koda bazatayi masa mgn ba har tsirar sata aiki yakeyi ko mubina da me aikinsu na gun
Inyace mata takawo masa ruwa ko abinci saita bushi iska take yi danma kada tajawa kanta maganane yasa takeyi amma ta tsani Abdallah yakasa ganewa
Haka shima yakan yi mata kallo naso da kauna amma takasa gane hakan yarasa mafita yarasa yanda zaiyi ya bayyana mata son da yake mata Gashi son nata zai masa illa ina mafita β¦β¦β¦??
*To fans din Abdallah saiku nemar masa mafita*π
tunda yafada tarkon dijen kauyeπ€π
π *YAR FILLO* π
_Dijen kauye_
πππππππ
πππππ
ππππ
ππ
*True life story*
*Nabilancy Luv*π
(Auntyn S&S)
PG 100-105
Abu kamar wasa saiga Abdallah ya susuce akan son dije wanda takai takawo inbai gantaba yaringa tambayar mubina knn kokuma yadami momy da zancenta insuna falo momy takance masa "hhhmmm kai Abdallah bama kayin ta matarka Ni,ima dake fama da lalura saita dije wacce ita ba kaine agabanta ba.
Narkewa momyn yakeyi yace "to momy inba nine agaban taba wanene?tanada kama tane?
Momy ckn zolaya take ce dashi "akwai mana.
Da tsoro karara akan fuskarsa yakece da momyn "haba momy dan Allah kidaina fadin haka ina aka taba hakan mace da Auranta tasa wani agabanta inba mara tarbiyya ba.
Momy tana dariya tace dashi "to dai khadija me tarbiyyace tunda har tayi biyayya ta Aureka a baka sonta ta iya xama dakai har kuka kai ga hakan baka taba bata hakkin taba saima halin ko inkula da kk yi da ita alokacin kuma matarka Ni,imace kawai agabanta dan haka yanzu itama ta sami wanda yafika saika kyaleta ta huta ko
Tsare momy yake da ido yace da ita "wanene wanda yafi ninnan ne momy?
"Karatunta mana! Atakaice momy tabashi amsa
Yahade rai yace "ai walh momy kinsa ma naji kishin karatun nata dolene ma akansileshi tunda naga ta iya rubuta ta hada harufan abubuwa masu sauki gara abarshi hakan kada gaba taxo tafi karfina.
Momy tace dashi "wannann ne baka isaba tunda tun farko ka amince kayarda ta fara to kamakaro khadija saitayi jami,a agidan nan
Yadafe kai "wayyo momy ki ceceni akan wannan batu walh baxan yarda taje ga jami,a ba ina ganin alokacin idonta yagama budewa zata iya gagarata..."saidai kai ta gagareka tunda baka sonta amma mu baxata gagaremuba tunda ita din mai tarbiyyace.
Ya gyara zama yana fadin "walh momy ina sonta !ina son khadija har raina...
Dije ta sawo kai kenan falon taji kalaminsa na karshe yana gayawa momy wai yana sonta
Taja tunga da sauri harda dafe kirji !"ni kuma yau Abdallah keso? Ta tambayi kanta
"Lallai zanyi maganinka saina gasa maka aya ahannu wato yagama wulakantani shine yanzu xai zagayo yace yana sona sbd yaudara don yaga matarsa Ni,ima awani hali baxata mora masaba shine zaiyi munafurci yafake dani yakeso toko abinda yake nema baxai samuba.
Ta karaso falon tazauna kusa da momy tana fadin "wash !"
Momy ta dafa ta tana fadin "diyar momy gajiya kkyine kike kiran wash?
Dije tayi murmushi tace "walh nagaji dayawa na aikatu yau.
"Me kikayi dakika gaji hakan?
Dije tahau matsa yatsunta tana kallon Abdallah tawutsiyar ido wanda sai kallonta yakeyi
tace "walh kayan Ni,ima na wanke nakuma zazzagaya da ita a can filin bayan gida.
Momy tace "kema ina hanaki dorawa kanki kinki ki daina ga me aikinan gakuma injin wanki can meye naki nagajiyar da kanki haba khadija yakamata ki sassautawa kankifa.
Dije ta dara tace "to momy ai injin yau yatsaya bansan meyasa ba kuma nikam dakin barni naringa mata duk wani abu daxan wahala babu komi lada nake nemafa kuma ai yiwa kaine kishiyace aguna kuma yar,uwa
"Allah sarki khadija sannu khadija Allah yayi mk albarka. Cewar momy
Shiko zukud'i yayi yana kallonta yanda take maganarta anitse da shagwaba saita burgeshi dama haka take da hali me kyau amma bai taba ganiba,lallai yayi dacen mata ya godewa Allah tareda godiya ga dan Uwa Abdulhakim da dady da suka hada Auransa da khadijan.
Momy ta tashi tabar falon
Dije naganin momy ta tashi itanma ta mike da sauri sbd batason wannan kallon dayake tsareta dashi
Kafin ta ankara saiji tayi yajanyota jikinsa yana shinshinata kamar wani maye
Tabude baki zatayi ihu yarufe mata da hannu yana fadin "ke mijin naki zaki tarawa mutane.
Tayi kicin kicin tace "ni ka sakeni mallam kokuma walh inkwallawa momy kira tazo taga abinda kake yi.
Ya kyalkyale da dariya yace "to saime matata ce fa .walh kina kiranta saina baki kunya don agabanta zan cire mk kaya nayi duk abinda nakeso nayi dake.
Ta zumburo baki domin ta yarda anufinta din zai iya batason wayo yai mata ba kokusa bai isaba inashi ina hakan
Tace "toni kasakeni nakoma daki kada wani yaganni ajikinka ace min yar iska... yatoshe mata baki yana fadin "kada ki sake kirankanki yar iska domin da aurena akanki komai inmukai lada zamu samu dan haka ina bukatarki ayau.
Tagalla masa harara tace "Allah yakiyaye ka bukaceni to ni ina ruwana dakai.bafa sonka nakeyi ba kuma kaima ba sona kakeba koka manta kataba cewa katsaneni? Tai masa tambayar tsare ido
Ya dabarbarce yana fadin "a,a a, ina sonki khadija ki mance da zantukan baya sharrin shaidan ne _plz i need you my wife_
da karfin tsiya ta janye jikinta daga nasa ta tofa masa yawu tana masa gatsine ta xura dakinsu aguje
Amaimakon yaji haushin hakan saima murmushi daya hau yi yana gogo yawun afatar fuskarsa yana lashewa yana fadin "i love you my khadija
Kamar wani wawa hak yaxama yaita bin momy duk lokacin dayazo da zancen shikam adawo masa da matar sa khadija gida yagaji haka da zamanta agidan nasu
Momy tace masa kabari sai Ni,ima tawarke sai sukoma tare.
Baiji dadin wannan hukuncinba shikam yana son khadija over yasan kuma jarabtanr dg indallah shiyasa akeao inxakayi ki kayishi kadan sbd samun irin hakan yanzu gashi yaraineta da kiyayyarsa gashinan ta taso akan hakn itama tana kinsa yanzu wa gari yawaya dana sani da nadama yayi tafi cikin kwando
Saida ya kebe ma da Abdulhakim yana gaya masa halin daya shiga akan khadija shima Abdul din fada yaita masa yana cewa "komai kaga khadija tayi akanka batada laifi ai tun akauyensu nasha fada maka ka sassauta yi mata wannan tsanar kaki ga irintanan gashi yanzu kaike sonta ita kuma bata son ma meye son ba dan haka yarage naka kaje kasamo mafita.
Abdallah yadurkusa gaban Abdulhakim yana masa magiya akan yataimaka masa yatayashi shawo kan khadija ta yarda dashi ta karbeshi amatsayin miji mai sonta bamai kintaba
Tausayi yabaiwa Abdul matuqa nan yadagoshi yace "bakomai na yarda kana sonta zantaimaka maka brother fatana dai kada akwata anan gaba nasan khadija tanada saukin kai kuma innafadi mata abu zatabi
Abdallah yaita masa godiya yaji dadin hakan
Godiya ma yaiwa Allah dayasa baitaba batawa da Abdulhakim dinba akan sharrin shaian din daya taba masa xuga arai akan ganinsa dayai da khadijan afalonsa
Abu fa yai tsamari in dije taji yazo yana falo bata fitowa saidai ta wuni adaka itada Ni,ima wacce yanzun jininsu yahadu suita hira abinsu
Alokacin antsaida ranar Auran Abdulhakim da Mubina saura wata daya
Dady ne yatarasu dukansu afalo har Ni,ima da jiki yafara sauki alokacin tana takawa da sandar karfe
Dady yace "Kai Abdallah nanda wata guda zaka debi matanka ka koma gidanka dasu tunda ankammala gyaran gidan dama so nake in anyi bikin Abdulhakim saiku koma kafin nan Ni,ima tagama wartsakewa kai kuma Abdulhakim akwai gidana dake sharada nabakashi kyauta kaje kaduba in kana bukatar canza masa fasali to yarage naka.
Yadubi matan yace dasu "kowaccenku nasa ayomin odar kayan daki daga dubai za.a saka mata adaki Naki Ni,ima nakwashe za.ai mk canji saikayan kicin shima kafin kukoma za.a kawosu dan haka saiku fara shiri.
Dukansu sukaita yi masa godiya
Karatun Dije ya mika yi takeyi haikan bata wasa ko kawayen kirki batadasu ita ke daukan na biyu ko uku tanada kokari sosai
Abdulhakim yaso su zauna Don yayi mata zancen Abdallah Amma batabari ko kusa su hadu
Harya fara zargin koyayi mata laifine bai saniba?β¦β¦β¦β¦β¦β¦
*Auntyn Sayyada Da Shahida ce*ππΌ
π *YAR FILLO* π
_Dijen kauye_
πππππππ
πππππ
ππππ
πππ
*True Life Story*
*Nabilancy Luv* π
(Auntyn S&S)
*Wannan page din Nakine kyauta Sukutum nabaki shi babbar masoyiyar Dijen kauye wanda take matuqar kokarin yin sharhinta akai dabada gudummawa tare da tayani posting ina godiya Nafi Nijar* Alherin Allah yakai miki har NijarππΌπβ€ππΌππ»
PG 105-110
Kwanakin da dady yadebar musu na shagalin biki da komawarsu gida yanata tafiya har saura kwana takwas amma dijen bata yi wani shiri ba domin har ranta bata son takoma gidan Abdallah tafi son zaman gidan dady tanajin dadin yanda momy ta maidata "yar lelenta tamkar "yar cikinta abinda zataiwa mubina shitake mata don har magungunan matan datasaka aka kawowa mubina da tsimi itama dijen ta bata abu daya zuwa biyu ke sakata fargaba yanda inta tuno zata rabu da kawarta masoyiyarta mubina wacce zaman Aure zaikaita har garin bauchi zatayi mata nisa batason ta tuna sbd sun shaqu matuqa baxata taba mantawa da mubina ba domin itama ta taka rawar gani wajen ganin rayuwarta tayi kyau da haske tabar jahilci da duhu tashiga haske don har malamin islamiyyarsu mubina ke xuwa gida yana biya maa karatun qur,ani da hadisai tana godewa Allah daya nufeta da zama abirni tunda gashi *TA TASHI DAGA DIJEN KAUYE TADAWO DIJEN BIRNI*
tasan da cewa ma Abdulhakim shine silar faruwar komai daya hada auranta da Abdallah taji aranta hakan dayayi mata yakyauta tunda gashi tasamu ci gaba arayuwarta ta dalilin hakan da Abdul din yai mata da tuni yanzun tanacan kauye ckn jahilci da duhun kai tunda batayi arabi ba balle boko sai a birnin
Dije tana zaune akan sallayarta ranar juma,a bayan ansauko daga masallaci tana tilawar karatu Ni,ima tana can kwance akan katifa tana bacci saijin shigowar Abdulhakim taji yafado dakin nasu da sallama
Ta dubeshi duba na tsanaki yayi kyau fiye da kullum yasha farar shadda tazarce kansa dauke da hula tagaidashi ya amsa ckn xolaya tace dashi
'"Su ango ansha kamshi kamar andaura aurenma saikamshi da kyallin angwanci kakeyi.
Yayi murmushi yace "hhhmmm khadija knn kema ai amaryar ce kyallin kkyi kamar yadda nakeyi ai.
Takama baki tace "Ni! π€ waceni me ido ba dan ciki ba wani kyalli danakeyi
Yazauna akan stool din gado yadubi Ni,ima yace "wannan bacci takeyine?
Dije tace "eh,tasamu yin bacci yanzun nan
"To ya jikin nata amma da sauki ko?
" da sauki sosai tana tfy ita kadai ma saidai tana dingisa kafar kuma bata dadewa tana tafiyar sbd gajiya take da wuri saita huta takeci gaba.
Ya gyada kansa yana fadin "to da haka da haka dai saukin zaizo gaba daya Allah dai yakiyaye gaba yabata lfyr baki daya.
Tace "Amin.
Yace mata "ya banga madam dina ba tana ina?
Tagane mubina yake nufi saitayi dariya tace "tayi tafiya au bata gaya makaba knn?
Yasan zolayarsa take saiya basar yace "ok,ok ta fada amma ai tare mukaje muka dawo dan haka yanzu dai ina tashiga inje in lalubo kayana.?
Ta kyalkyale da dariya wato bai shigaba knn dataso ta shigar dashi
Ta karkata kai tace "dazu suka fita da kawayenta rabon invitation.
Ya gyada kai yana fadin "to ke kuma wane shiri kikeyi don komawa gidan mijinki tunda dai kinji abinda dady yace kuma har an gama muku gyara yau saura 8 days.
Ta hade rai harda raurau da ido ta narke masa zatayi kuka
"Nidai walh bana so inkoma gidan mugun nan walh tunda yakai hannu yadakeni nakara tsanarsa dan Allah katayani baiwa dady hkr yataimaka mini yaraba Auran nan nagaji da xama dashi.,...tafara kuka
Yaga abun nata da gaskene yahau bata hkr yana rarrashi "kinga yi shiru abin baikai hakaba share hawayenki ingaya mk yanda za.a yi kurabu ckn sauki.
Ckn sauri tahau goge hawayen danta yarda abinda xai rabasu zai fada.
"Kinaji ko banaso kowa yasan irin tsanar da kikayi masa kinga daga dady har momy baxasuji dadiba tunda suna sonki kuma dan sune me zaisa baxakibi abin asannu ba tunda kinga yanzun shi yadaina tsanarki yana sonki kinga inkin koma saikiyi tayi masa wayo kina dabara yakamu dayawa asonki ta