Showing 6001 words to 9000 words out of 39246 words
Chapter 3 - YAR FILLO COMPLETE DOCUMENT BY Nabilancy Love 😘.txt
kansa
*****A can bangaren Amarya dijen kauye kuwa batasan wainar da ake toyawaba har ana gobe daurin Aure itadai taga iyayanta maxa sai shige da fice suke ackn gidan sunayin kus kus da Addaji.
Taga kuma yan garinsu Addaji da wasu yan uwan sunxoxxo gidan wai biki sukaxo har ana ce mata amarya! Nan tahau tuhumar kanta wacece amaryar?! To bikin wa akeyi haka da batada masaniya abu har ckin gidansu akeyi?
Da dare ta tisa Addaji a daki ita kadai ta sata agaba da tambaya
"Addaji wai bikin wa akeyi ackn gidan nan dahar ban saniba? Waye adangi ake bikinsa kuma ackn gidanmu?
Addaji takalleta da tausayi tace "Dije Aurenki ne mana kina nufin baki ganeba? Ko bake kk kawo mijin ba??
Da sauri dije ta ja baya tarea dafe kirji idanu awaje ckn rawar jiki tahau fadin "Aurena kuma Addaji!? Dawa za.ai min Aure ban saniba?? Yaushe nakawo mijin walh bansan wani mijiba nikam bansan zancenba dan Allah kiyi min bayanin daxan fahimta.
Nan Addaji ta warware mata magana tace mata Alh mustafha me gidan gonane yaxo dakansa gidan yanemi Aurenta ga dansa kuma iyayanta suka amince kuma ance kina son yaron Ko Abdul sunansa ko miye ma na manta.
Dije ta tsaya cak tunaninta yadawo tahau tunanin wani abu tayi shiru domin tunaninta bata yayi wato dady yaxo yanemawa Abdulhakim Auranta knn har An bashi amma bata saniba to meyasa Abdul yai mata hakan meyaa baizo yasanarta ba har suka tafin. Ita ai dama shi takeso wannan ai abin farin cikin tane.
Ta mike asanyaye tafuta taje dakinta takwanta tana tunanin Abdul
MurmuShi tahau zabgawa tana farin cikin wannan lamari
Wai gobe iwar haka taxama mata agun Abdulhakim tabbas dole tayi godiya ga Allah daya cika mata burinta yabata Abdul A salin Alin batareda tasha wahala wajen bayyana tana sonsa ba.
Kwana tayi tana farin ciki tayi baccin dadi sosai harda makara wajen yin sallah
Allah Allah taringayi axo adaura tayita kasa kunne son taji ana daurin aure amma har hantsi bataji anxo daurin Aurenba tace Allah yasadai bafasawa sukaiba
To acan birni kuwa saida "yan daurin Aure suka fara zuwa Aka dauro Auren Ni,ima sannan Aka rankayo kauyen rogo domin Daura aure na biyu
Ango dai yadawo gidansu Amma baisami zuwa kowanne daurin Aurenba domin rashin lfyr karya yakwanta dasukazo da uncle wai duk don dadynsa yatausaya masa kada yai masa fadan barin gidan dayai hhhmmm shiko dady kallonsa kawai yai ba magana me tsayi sai Allah ya sawwaqe
;
Abdallah yabi ayari zuwa kauyen rogo daurin Aure
Sai shabiyu daidai suka isa
Ba b'ata lokaci aka daura Aure aka kawo musu fura taji nono da sukari suka hau sha suna yin santi harda masu qulla zasuyi guxuri da ita
Kafin sukoma Abdulhakim yasamu kebewa da Amarya asoro
Taxo tasha kwalliya kanta lullube ruf da mayafi kowa yai xaton shine angon ackn gidan domin yasha babbar riga yai kyau ainun
Yarasa da wane lafazi zaiyi mata bayanin komi
Saida tadago idanunta takalleshi da wani kayataccen murmushinta take yaji wani yarrr!
Abinda bai tabaji atattare da itaba sai yau
Tagaidashi tace "Ango na ina wuni.
Jin hakan yasa yadaure yafara mata bayani " khadija ina me bakin cikin sanar miki cewa ba dani aka daura mk Aure ba nasan zakiyi tunanin ko nine mijin naki to bani bane dan,uwana ne Dady shi yayi sha,awar yahada auranki da jininsa sbd kyan halinki da yayi dan haka kiyi hkr kiyi hkr khadija Abdalla ne mijinki baniba ……
Xumbur ta mike tsaye ta yaye gyalen ta jingina da bango jin zata fadi ta nunashi da yatsa tana kuka takasa ma maganar donta makale amakoshinta
Tuno fuskar Abdallah datayi yasa taji wani jiri tareda ganin wani duhu aitake taxube agun
Suma tayi na awa biyu anata shafa mata ruwa don matane suka fito suka dauketa aka kaita dakin Addaji
Shiko duk yarike yashiga damuwa sai alokacin yahau nadamar abinda yayi
Wayyo khadija kada ki mutu baki yafenba.nayi nadamar wannan hadin domin ji yayi xcyrs na mata wani mugun tausayi fiye da yanda xai tausayawa kansa.
Yan taron daurin aure basusan komi daya faru da amaryaba suka hau shirin komawa
Abd dady yace sai sati yazagayo za.a dawo daukar amarya kafin nan aun gama bikin al,adunsu suma na kauye
Jikin Abdulhakim Asanyaye yabisu suka koma birni ransa ba dadi.
Dije tafarka taganta ajikin Addaji jikinta sharkaf da ruwa da alamar shafa mata akai tayi don tafarfado
Subiyune adakin u u
Tana farkawa tahau kuka ckn harshen fillaci tahau fadin " *Wallahi mi yid'a mo Addaji mi wanyi ma lara yeso mako* (walh banasonshi Addaji,natsaneshi bana qaunar inbude ido inganshi)
Addaji tahau bugun bayanta ahankali " *wadu munyal dije, Allah su'bine ko lati khairu* (kiyi hakuri dije kada kibujire Allah yasa hakkane mafi Alkairinki)
Dije tahau kuka tana share kwalla
Addaji tace "kada kinunawa jama.a cewar bamu isa dakeba tunda kuma anriga andaura hkr xakiyi kixama me biyayya don kiga dakyau arayuwa kiyi shiru kinji dijena kixama me bin iyaye da miji.
Maganganun addaji sunshigeta nan tayi lakwas ajikinta tana faman matse kwalla tana fidda numfarfashi
Addaji taci gaba da bata baki cikin fillanci " *jedu accu vojji, d'o on jarabu ma ambo* (kiyi shiru kidaina kuka jarabawarki kenan)
dije ckn sanyin murya tace " to *Addaji wannam do'a, Allah wadu hanjum on khairu me* (addaji kiyimin Addu,a Allah yasa hakan yaxamar min Alkairi Arayuwata)
"Allah yasa dijena.Allah hokkumo sa.a.
Itakanta Addaji saida tayi mata kuka abayan idonta don ta bata tausayi data nuna hkr lokaci guda
Tunani yaiwa dije yawa yaya zatayi da son da takewa Abdulhakim knn?bazata iya cireshi arai ba
Ta wani bangaren kuma ai burinta yacika naxuwa birni
To amma wane irin rayuwa zatayi a birni da wanda bataso baya sonta ????? ………
_muje zuwa_[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:🙆🏼
🐄 *"YAR FILLO…*🐄
🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕
*True life story*
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S&S)
PG 20-25
Cikin kwana guda da yin daurin Aure Dije ta rame ta futa hayyacinta danma tanada garin jiki dama batayo jikin siraran fulanin rugaba
Addaji taringa matsa mata akan saitaci abinci dole ga "yan taron biki basu watseba domin sai anyi sati ana biki ana shad'i dayin bikin mard'on na fulanin kauye wanda "yammata ke hadawa a dandali da daddare
Bikin mard'on bikine nashan damammen gero dafaffe yasha nono da sugari
Kwarya kwarya ake hadoshi daga gidan amare akawo "yammata susha suda samarinsu ana hira ana nishadi me kida nayin kidansa afili wasu na liki
To ita dije dama bawani kawaye take dasu wararruba
Kawayen kara dai sunzo mata "yan unguwa da sa,o,inta "yan uwa ancika anyi bidi,a ta al,ada
Ba laifi ta saki jikinta ackn yan biki wanda ba kowanema yafuskanci tanada damuwa ba
Akwai "yar gidan kawunta sa,ar tace wato indo itace ma tasan abinda ke wakana atare da ita insun kebe takan tausheta da bata baki harda ce mata "aike ki godewa Allah ma da zakiyi rayuwar Aure a birni don wasu hakan suke nema ma kuma mijinki dan gayu ga kudi dan Allah kicire damuwa aranki kiyita Addu,a Allah yasaka mk sonshi kawai.
Dije bata ce mata komi saidai tace mata "hhhhmmmm
Ita kadai tasan me takeji aranta mekuma take hange agaba don ko tayi addu.a Allah yasa mata sonshi aranta to shikumafa yazatayi da tsanar dayai mata, itakam har Abada zuciyarta Abdulhakim take kauna kuma baxata dainaba abinda ma yasa taji hankalinta yadan kwanta tuno kalaman Abdul din datayi nayanda ya bata hkr da kuma nuna mata cewar akullum acan zai kasance tare da ita xaikuma taimaka mata baxai bari Abdallah yacuce taba.
To wadannan kalami inta tuno takanji sanyi aranta.
**** *****
Daga can bangaren ango Abdallah kuwa baitashi saniba sai dare yaji Abokansa ta koina suna masa waya ana masa Allah yasanya Alkairi wasuma harda nuna fushinsu akan bai gaya musu ba
Mamaki yamamaye shi farko yaringa musu dry don yazaci ko zolayace to inbanda tsokanarsa suka shiryi yi yama xa.ai ace yai aure arana guda ya auri mata har biyu kuma daya a kauye daya abirni duk shi kadai
Bai gaskatasu ba saida Uncle dinsa yatashi tfy yakirashi daki agaban mahaifinsa ya shiryasu yai masa fadan gudu yabar gidan dayayi yakumace masa shima yatabbatar yabar maganar Lowerst domin ayanzu shi din me Aure ne akansa Aure ma harna mata biyu.
Ya zabura yarikice yace da uncle "Aure kuma uncle? Ni?!! A,a badai niba walh bansan maganar ba
Uncle din yace dashi "Abdallah kanutsu kazauna inyi maka bayanin yanda akai aka daura maka Aure da "Yammata biyu ayau.
Wato Abdallah kai me hankaline amma kanaso kazama wawa manufa ka girma amma gakanan ne kamar yaro sbd wauta iyayanka na duniya amma kana neman kabata dasu baka son kaxama meyi musu biyayya yanzu abinda kayi na nuna fushi ga mahaifinka daidai ne? Daga gaya maka gaskiya akan yarinya saika gujeshi wannan abu yakona masa rai da baka nuna kabi maganarsa ba kuma yayarka takawo maka magana kasa kafa ka shurs sannan ance akwai yarinyar da a can kauyen rogo kake wulakantawa akan tana nuna maka SO to sune dadynka yadaura maka Aure dasu ita waccen khadija da kanwar mijin maryam ni,imah dan haka inaso kazama jarumi kaxama me hkr da bin iyayae kada kanuna jin haushi ko fushinka kada kace zaka bujire ka kunyatasu tunda anriga andaura maka Aurs dasu.
Wasu zafafan hawaye yaji sun sauko masa akunci dama ashe haka aka shiryi yi masa lallai yau annuna masa rashin kauna kuma saiya nuna shi Abdallah ne
Yakalli mahaifinsa yana kuka kamar wani yaro karami yace "dady Amma wannan matakin da hukuncin naka sunyimin tsauri dayawa walh duka yaran bana sonsu araina kuma baxan iya zama dasu amatsyin matanaba kayiwa Allah dady kasa inwarware wannan Auren Akan nasu walh indai akan yarinyar can dana kawo maka zancen tane to na hkr kabani kowacce ackn "yan uwa amma banda wadancan
Dady yahade rai tamkar bai tab'ayin murmushi ko dariya ba yace da Abdallah
"Kuma ni dasu nake son kazauna kakuma basu babban matsayi ackn gidanka inkuma kanuna min ban isa ba insallama ka
Dan haka kaxaba koni ko ra,ayinka.
Abdallah yayi shiru yana jan ajiyar zuciya ransa na masa quna
Uncle yadafa shi yace masa "Abdallah kaxama namiji gwarxo jarumi mana kadauki wannan tamkar kaddararka knn kayi godiya da Allah dataka jarabawar ma taxo cikin sauki tunda kai da kanka zaka iya daidaita lamarinka wajen karbar taka jarabawar ahannunka manufata karike matanka batare da nunawa ubangijinka cewar baka son zabinsa ba domin zabin Allah ne su kuma zabin mahaifinka dan hk kada kaki amincewa sbd kada kasami sabani akan wannan kaida mahaifinka kaji,
Cikin sanyin jiki yahau gyada kansa da alamar yadauki maganarsa
Dady yadubi uncle da zafin rai da daga murya yace "kasan Allah Alh inhar bai bi wannan abinda na shirya masa ba bai karbi zabin danai masa ba to walh yasani bani bashi bakuma "yan,uwana bashi hakama dangin mahaifiyarsa kada yasa ran xuwansa gunsu dan zan hana su karbeka kuma tsinuwace zata biyo bayanka
Wani abu ne yatsaye axcyrsa lallai dady yadauka da xafi ba dashi xa.ai hakanba ckn kwantar da murya yace da dady
"Allah yahuci zuciyarsa dady na amince zan zauna dasu amatsayin matana
Uncle yace "to aikaji Alh saikasa masa Albarka tunda ya amince da abinda kayi masa.
Dady yasaki rai yace "to naji Allah yayi mk Albarka tashi kaje.
Yatashi asanyaye yafuta
Kai tsaye dakinsu yanufa yatarar da Abdulhakim yafito daga wanka yaxira jallabiya
Da bacin rai yatunkareshi yanunashi da hannu "kai tsohon munafuki ashe Aurena kukaje shine baka gaya minba kuke ta boyaemin kaketa kumbiya kumbiya to walh nasan ma akwai hadin bakinka ack
Abdulhakim yace "hhhmmm koma me zakace kace naji amma kasani cewar kai kaja komi tunda da ace kana daukar shawarata da hakan baxata faru dakai ba
Yanxun da akai hakan wa gari yawaya? Tokasani duk abinda yafaru dakai ka tuhumi kanka
Abdallah yakufula yace "Au haka kace ko?
Abdullhakim yaxuciyo shima yace "nafada din me zaka iya?
Abdallah ya buga masa tsaki yafuta yana xaginsa
Saida yafuta shikuma yaxauna gefen gado yadafe kansa domin yanajin tausayin abokinsa dan,uwansa sosai bayaso yanuna masa ne
Adaidai lokacin da abin duniya yaiwa Abdallah yawane ita kuma Amarya Ni,imah Abin duniya yai mata dadi domin Allah yacika mata burinta yabata wanda ta dade tana kauna
Bata taba zaton wannan rana zatazo mata kwana kusaba lallai angama mata komi da aka jajirce aka ga andaura mata aure da Abdallah
Abu dayane yatsaye mata arai bawai jin Abdallan baya son taba ko baya dokin Auran a,a jin cewar Tanada kishiya ashe su biyune amaren na Abdallahn.
Tabbas inta tuno kyanta da matsayinta na ita dangin arxikice saitaji bacin rai wai ace itace me kishiya "yar kauye
Abinda take yawan tunani shine shin itanma yar kauyen baya son tane? koko ita yakeso ba ita Ni,iman ba …… ????
*Auntyn Sayyada da Shahidah ce*[9/26, 6:08 PM] Itz B Y ebrerheem:👌🏼
🐄 *"YAR FILLO* 🐄
_Dijen kauye_
🏕🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕🏕
🏕🏕🏕
🏕🏕
🏕
*True life Story*
*Nabilancy Luv*💘
(Auntyn S &S)
PG 25 - 30
Tamfatsetsen gida Dady yabaiwa Abdallah me part biyu
Sannan kowanne yazuba furnitures masu tsada da kayan kicin ack
Kowanne part yahadu iya haduwa babu banbancin kaya da akayi sai daga gidansu Ni,imane suka karayiwa amaryarsu wasu karin decoration din suka kuma kara zuba kayan kicin din amaryarsu akan na dady dayayo musu
Ga parking space daxaici motoci uku xuwa hudu agidan sai dakin me gadi akusa da get
Motoci biyu dady yabada aka tafi dauko amarya dije a kauyen rogo wacce suke ashirye suna jiran motocin domin suna da masaniyar aranar za.a xo daukar amarya
Iyayanta kannan uwa da yan,uwan uba da yan unguwa sunyi kara wajen son xuwa birni don suga kwakwaf
"yan rakiyar amarya sunsha kallo sunsha mamakin kyan gidan dady da kyan tsari tamkar Aljannar duniya dayake can suka fara kai amaryar domin saida aka kawo Ni,ima gidan kana aka hadasu akai musu fada da nasiha don su zauna lfy
Dady yayi musu Nasiha me tsima jiki tamkar yadda uba kanwa "yayansa dai
Dije tasha mamakin jin cewar wai ashe da kishiya zata zauna
Lallai data san da hakan baxata taba yarda tazo zaman aure birniba sbd tasan matsaltsalun zama da kishiya da yanda ake fadin kishiyoyin burni suke illata kishiyoyinsu ita kuwa batada gata saina Allah wazata kaiwa kokenta kenan in wata baraka ta sameta? Wata xuciyar tata tace mahaifinsa mana ai mutumin kirkine kuma yana sonki.
Kowaccensu kanta akasa anlullube kai da mayafi sai zabga kanshi suke amma turaran Ni,ima shine yafi daukar hankalin mutane domin bazaka bambance kanshinba ita kuwa Dije dakaji zaka tabbatar karamine
Abdulhakim yana daga can dakinsu yaji tashin motoci yai xumbur ya mike daga kan gadon dayake kai yabude labulen windon nasu yahango gwanon motoci sunyi biyar ta amare zata futa dg gidan
Saikawai yaji hawaye ya xubo akuncinsa yasa hannu yagoge yana tambayar kansa dalilin kukan sa da damuwar da yayi akan wannan Aure na dije da Abdallah
Me yasa ya damu da yawane yana tausayin dije kuma yanajin wani abu akanta murmushinta yana masa gixo yana hangota akayan sakinta taci ado
Yakwanta ruf da ciki akan gado ya rumgume filo akirjinsa yahau fadin "khadija ki yafemin halin dana sakaki nine silar zamowarki matar wanda kikafi tsana aduniya,nine nazama musabbabin kasancewar ki ckn damuwa Amma nayi alkawarin baxaki wulakanta ba khadija.
Tunda aka daura Auren khadija da Abdallah yaji abin yana damunsa abin ya tsaya masa gashi yana yawan tunaninta
Shiko ango Abdallah adaidai lokacin da aka shigar masa da amarensa cikin gidan nashi toshi adaidai lokacin yana can gidan Abokinsa Anwar su hudu sunata shan shisha da sigari
tabbas
Yaji garau aranar domin sigari kwali guda yasha saida ya tabbatar damuwarsa ta ragu kana yabar falon yakoma ckn d'aki kan doguwar kujera yafara bacci da tunanin babynsa lowerst yakwanta
Yaita mafarkin suna tare da babyn nasa suna gudanarda daddadar soyayyarsu
Wayarsa tayita kara baijiba bacci yayi dadi
Abdulhakim ne keta kiransa alokacin tara da rabi na dare
So yake yazo yai masa rakiya xuwa gidansa
Saida Anwar yashiga dakin yafarga domin su sunacan falone
Ya d'aka masa duka yace "abokina tashi ga kira daga gida.
Yafarka agigice yakarba yaduba dayaga kiran Abdulhakim ne sai yaja tsaki yaso k'in d'agawa amma kuma saiya fasa yadaga yana masa tsawa"ya akaine mallam meye na kirana awannan lokacin ??
Abdulhakim ya murmusa yace "kayi hkr ranka ya dade kana ina?
Abdallah yasha mur " meye damuwarka da inda nake?,
Abdulhakim yace "kayi hkr abokina so nake muhadu yanzun
Tsaki Abdallah yaja yace "to me zakaimin inmum hadun kai bana son duk wata takura ayanzu kabarni da abinda ke damuna
Abdulhakim yace "naji kayi hkr kazo muhadu yanxu ojanty plx
Abdallah yace "waime xakaimin ne? kabari sai gobe mana dan kwana xanyi a inda nake.
" Amma dai kasan kai angone ko!? Kasan dai yanzu haka amarenka suna gidanka kuma inhar bakaje garesuba to ubangiji saiya tuhumeka dan haka aduk inda kk kataho in rakaka muje gidan.
Abdallah yaji wani abu yatsaye aransa wato ma yaune za,akaisu gidan shine ba,a gaya masaba tabbas yanda ake masan nan akansu xai rama yanda aka wulakantashi shima saiya rama wulakancin nan da akai masa
Ahankali yabaiwa Abdulhakim amsa "to kajirani ganin.
Yana dire wayar yakalli Anwar daya daga kwalbar giya yana kurba yace "abokina kajifa wai ankai min amare inje arakani gidan
Anwar yahau tafawa yana jinjina masa "kaga angon mata biyu walh kagodewa Allah inama nine akaimin wannan gatan hakan.
"Kaga dakata ba zolaya nace kayimin ba " cewar Abdallah yafada yana kokarin tashi tsaye
Anwar yace "to muje ayi rakiyar tare dani mana.
Abdallah ya harareshi yace "ahakan kana tsamin giyar zaka rakani? Lallai kanaso asirina yatonu gun Abdulhakim knn domin inhar yagano kasha giya to dole xaiyi zargin nima inashane dan haka kaxauna zan tafi kawai duk yanda ake ciki zakaji gobe
To shikenan " nan suka sallama yafuta yashige .motarsa sai gida
Abdulhakim shine dan rakiya