Showing 21001 words to 21688 words out of 21688 words

Chapter 8 - KULUWA COMPLETE BOOK COMPLETE BY Nuceey luv.txt

07 Feb 2025

4754

sosae. Basuyi qoqarin kiran kowa ba. "Haka suka duqufa addu'ah Allah ya tashi kafadin kuluwa.


Kusan 2hrs wani doctor ya fito yana share zufa. "Abba d goggo sukaje wajensa. "Yace su bishi office.
Doctor yace yarinyar Ku tana tare d damuwa a ziciyar ta. Sanna a daina fada mata abinda zai tayar mata da hankali.
Abba yace toh za'a kiyaye.
Saida ta huta aka sallamesu. A hanya Abba y balbale ta d fada., abinda be taba yi mata ba. Yace aurne dae babu fashi.
Kuluwa kam sai share hawaye take babban tashin hankalin ta shine batasan dawa za'a mata auren ba.


Nuceey luv😘
[10/27, 4:23 PM] ‪+234 803 325 6478‬: KULUWA 🍇


105....


Haka rayuwar kuluwa da ameer sukaci gaba d gudana cikin farinciki d annashuwa., kuluwa tayi kyau ta murmure ta dawo SARAUNIYA sak matar Dan SARKI.
Yau Friday tana zaune a falo dan ameer taje gun memartaba taji ana sallama. "Hijab tasa sannan ta bude kofa. Ganin goggo CE kuluwa ta fasa ihun murna tana fadin oyoyo goggo nah. "Goggo tace keni cika ni kin wani makalkale ni bakya ganin jikin tsufa. Kuluwa tace hoo goggo nah., bayan ta zauna ta kawowa goggo ruwa d abinci. "Goggo taci tayi hamdala tace me gidan naki kuluwa? "Kuluwa tayi murmushi tace yana nn lpy. "Goggo tayi murmushi ganin kuluwa tayi kyau d haske tace 'Yar jakar uba kikace bakyaso ko harkin hakura? "Kuluwa ta ware ido tace kae goggo nidai bance ba. Goggo tayi murmushi. "Sun dade suna hira goggo ta bawa kuluwa kayan mgn d turaren tsugun no., sannan ta ce tafiya zatayi. "Kuluwa ma cika goggo d tsaraba "tace AF goggo yasu Anty fah? "Goggo tace uhum anyiwa ruky aure d tsohon saurayin ta sale ai daman wannan zabbuwar take ko zabbi ko zabba'u kuluwa ta kwashe d dariya tace kai goggo., goggo ta tabe baki tace "tuni bbnku y korata gida kuluwa tace innalil lahi meya faru kuma? "Goggo tace ai abun duniya baya buya Ashe ita ta tura a saceki Wanda tasa y kasheki taje ta zageshi akan be cika aikinsa ba tace kuma saita kashe shi., shine yazo y samu Auwal y sanar dashi komai bayan y roki gafara. "Kuluwa ta jinjina lamarin tace kai duniya ace kashe mutum ba komai bane a yanzu? Goggo tace uhum Allah y mana tsari tace amin.
A bakin kofa suka hadu d ameer. "Har qasa y gaida goggo. "Goggo taji dadi sosae. Nan ma y sake hadata d tsaraba ta tafi.


Bayan wata Tara Kuluwa ta haifi 'yarta mace., "ranar suna akasa wa yarinya suna ALEESHA. Inda dubban mutane suka zo bikin jikin sarki Wanda akeji d shi a fadin duniya.


Aleesha tayi wayo sosai dan yanxu shekarar ta biyar d haihuwa idan k ganta kamar k saceta k gudu.


Ameer d kuluwa suna saga falo d sunan wasa. "Akayi nockn ameer yaje y bude kofar kuluwa kuma ta koma daki ta sako hijab. "Tana dawo falo taga Arif zaune suna hira d ameer. "Da murmushi ta karaso itama ta zauna tace sannu d zuwa manyan gari saukar yaushe. Arif yyi murmushi yace ai kune manya Kuluwa hira suke sosae. Daga bisani Arif y musu sallama har y kai kofa ya juyo yace AF na manta. "Ameer y ce meya faru.? "Arif y kalli kuluwa yace na samo miki handsome guy dinki fah. "Kuluwa t zaro ido tace a ina.? Arif yyi dariya yana kallon daya daure fuska yanason jin wa suke nufi. "Yace gashi nan a gefen ki. Kuluwa ta kalli ameer taga ita yake kallo saita yi murmushi. "Ameer cikin daga murya yace kuyi mgn mana kunsani gaba kuna kallo. "Arif yyi daria yace toh maida wukar.
Anan Arif y zaiyanewa ameer komai akan mafarkin kuluwa. "Ameer yyi al'ajabin wannan lamari., arif y tafi.
Kuluwa ta dora nata tace haryau har gobe sonka ne yake yawo cikin jinin jikina. "Ameer yace lallama shine kika barni nasha wuya koh. "Kuluwa tayi dariya. Ameer yace kin dauki bashi kuma yanxu nan. Zan fanshe., be jira cewar ta ba y shige d ita daki. "Kafin na qarasa ya rufe dakin. Nidai nuceey haka naja qafata nabar gidan.


ALHAMDULILLAH
Godiya me yawa ga Allah madaukakin sarki daya bani ikon gama dan littafin

6
7
8

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login