Showing 9001 words to 12000 words out of 24696 words

Chapter 4 - Auren Kaddara Ko Na Biyayya Complete.txt

18 Feb 2025

3249

abinda dad d'inku zaice ko,,
To shikenan zuwa gobe zan samu dad muyi magana dan nasan yau yagaji danni ko ganinama bazaiyiba, nima d'in zuwa zanyi na kwanta duk nagaji, yinwace ma ta kawoni gidan,
Mom tace to bari na kawoma abincin.
Bayan fitar mom dady ya kalli Munneerah data idar da sallah tun d'azu, amma takasa tashi,
Waike bazaki cire wannan hijja binba, ko zafi bakyaji, tace ai bangamaba, ya tab'e baki, mom tace ya akayine, yace mom naga tun d'azu ta idar da sallane, amma tak'i tashi ta cire hijjab d'in,
Mom tai dariya to ai kasan Munneerah da kunya.
Yace to mom kunyar wa zataji anan ai mu ba bak'inta bane, ya d'auki abincinsa ya hau ci,.........




🌺billy🌺
{🌹Mrs Abdus'salam🌹}
[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


09093044460
Na billkisa ibrahim 📝📝


24 «*****» wai ina su kairat ?
Mom tace suna d'akinsu tare da k'awayen amarya,
"Yace okey"
Kad'an yaci abinci ya ajiye,
"Mom ta kallesa ba dai ka k'oshiba babana??
"Na k'oshi mom yafad'a yana mik'ewa, bari naje nayi sallar isha'i, nawuce gida barci nakeji,
"Mom tace to saida safe"
"Itama Munneerah tace saida safe yaya, ya juyo ya kalleta batare daya amsaba ya fice,
Yay wa bak'in dake falo saida safe ya tafi.


Saida yay sallah sannan ya nufi gida, husnace kawai afalon yasan jiransa takeyi, azuciyarsa yace yarinya duk jarabar ki kya barni, dan yanda na gajinnan ba abinda zan iya tsinana miki.


Amma afili saiya ce lafiya kika zauna ke kad'ai afalo??
"Tace k'alau kai nake jira"
"Yace to muje, d'akinsa suka shiga, ya kalli d'akin sannan ya kalleta, wai yanzu haka kika bar d'akin nan baki gyara ba??
Tace to ai naga baiyi dattiba.


Ya kalleta cikin haushi akwana biyu ba a kwana ad'akinba, sannan kice babu datti, kinga ki gyara kokuma ki tafi d'akinki ki kwanta nina gyara nan.......




🌺billy🌺
{🌹Mrs Abdus'salam🌹}
[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


09093044460
Na billkisa ibrahim📝📝


25 «*****» ganin yanda yake magana cikin jin haushi tasan gatse yay mata, dan haka tace to bari nagyara,ta fara kakka b'e gadon, dady dake kan kujerar madubi zaune, yace ai wannan zanin gadon saidai ki cire shi, dan bazan iya barci akansaba,sai jikina yazo yana kaikayi,
Azuciyarta tace magulmaci ai k'ilama nan gaba uwarkama saikace mata k'azama, dole ta canja zanin gadon suka kwanta,shikam harga ALLAH ya gaji barci yakeji, amma yasan fitinar husna,jiyyayi ana shafashi doleya daure yabata hakkinta sannan sukayi barci.


Da safe bayan sunyi sallah suka koma barci , cikin barci sukaji ana buga k'ofa kamar zata cire, dady ya daure ya tashi husna ma ta mik'e, sanda suka fito ikileema ma ta fito har tana k'ok'arin bud'e k'ofar,
Jabir ne da umma kakarsu da alama ma jabir abuge yake, ikileema tad'anja baya danganin jabir yana k'ok'arin fad'owa kanta.
Cikin muryar maye yace ina Abdul'aziz d'in dan uwarsa bilkisu, yau saika gaya mana ubanda ya d'aura maka aure batare da saninmuba,
Dady yana tsaye jingine da bango hannuwan sa hard'e ak'irjinsa, yace jabir ganinan ince ko kazo ka dake nine??
Umma tace to mara kunya koka manta jabiru yayankane, dady yace ban mantaba umma, amma kinaji ya kira sunan mom d'ina yazaga,saboda tarbiyya tamasa k'aranci, dady ya nuna jabir kasn ALLAH ka k'ara zagin iyayena saina yimaka rashin mutunci.


Umma tace kai Abdul'aziz rashin mutincinka har yakai haka, tsaki dady yaja yay shigewarsa d'aki harda saka key.
Ikileema da husna sunyi mutuwar tsaye danjin furicin yayansu jabir, cikin k'arfin hali ikileema tace umma bafa mugane abinda kuke nufiba, waye yayi aure??
Jabir yay taga taga zai fad'i ALLAH yabashi sa'a yadafe kujera, yace wannan d'an iskan mijin naku mana, shine yaje yole shida wad'ancan muna fikan iyayen nasa suka d'aura masa aure, yanzu haka amaryar tana gidansu,
K'ara suka kwallah atare suna fad'in dady ka cucemu, ikileema tanufi kofarsa tana bugawa da k'arfi tana masifa.


Shikam yana jinsu yay musu banza k'arshe ma dayaji sun damesa da hayaniya sai ya kunna karatu awaya yasaka iya fis ya k'ure k'arar


Bayan kamar minti talatin yaji gidan shiru saiya cire ya kashe yay murmushi sannan ya mik'e ya bud'e kofarsa ya lek'a falon, dariya yayi mai sauti yara darobon tafiyarku ta kasance kun tafi kenan, dan dama hanyar rabuwa daku nake nema wallahi, ya koma cikin d'akinsa yana k'yalk'yala uwar dariya, kamar wanda akaima bishara da gidan aljannah........




🌺billy🌺
{🌹Mrs Abdus'salam🌹}




[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


09093044460
Na billkisa ibrahim📝📝


26 «*****» dady ya shirya ya nufi gidansu dan yau za'a kawo amarya, bayan ya gaida mutane ya haye saman dad mom ma tana can, ya dur kusa ya gaishesu, cikin fara'a suka amsa, cikin dariya dad yace zonan babana, dady yaje kusa dashi ya zauna, dad yashafa kansa babana kana fushi damu ko ??
"Dady yad'ago cikin murmushi yana kallon dad, ya girgiza kai dad danmi zanyi fushi daku mikuka yimini, ya cigaba wallahi dad bana fushi daku,ko kad'an kawai na d'auka wannan yana cikin K'ADDARA ta ne, dan haka dan ALLAH ku daina damun kanku, ni yanzuma nazone akan maganar inda za'akai Munneerah ne??
" dad yay dariya to shikenan babana ALLAH yayi maka albarka ya baka 'ya'yan daxasu yimaka BIYAYYA kamar yanda kayi mana""
"Amin mom ta amsa"
Dad ya d'akko mukullaye da yawa ya mik'awa dady, cikin rashin fahimta dady yake kallon dad, dad yace karb'a babana wannan makullayen gidankane, dake HOTORO, a SAKKOTO ROUND,
angama zuba ko mai sai kaje kasanar da matanka su shirya yau sukoma, zuwa anjima kuma akawo maka sabuwar amarya.


Dady ya mik'e ya rungume dad yana godiya, ya koma ya rungume mom itama su duka dariya sukeyi dan yau sunga farin cikin d'ansu tilo namiji dasuka dad'e basu ganiba.


Dad yace kar kadamu babana zan iya yimaka komai arayuwa matsawar inda shi dan nima kan mini BIYAYYA, dady yace to dad saidai fa su ikileema basanan, d'azu umma tazo itada jabir sun tafi dasu kuma wallahi dad bazanje nadawo dakowaba tunda bani nace su tafiba


Mom da dad suka dubi juna har suna had'a baki wajan fad'in umma kuma??
"Dady yace eh"
Dad yace karka damu anjima zanje gidan umman da kaina, yanzu kaje kagano tsarin gidan idan yayi maka.
"Dady ya mik'e yana godiya yatafi.
Dad yace kinga abinda nake gaya miki ko bilkisu nasan akwai wani kulli azuciyar su yaya amma anjima zanje gidan, mom batace komai ba sai ALLAH ya kyauta kawai ta mike ta fito......


🌺billy🌺
{🌹Mrs Abdus'salam🌹}
[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


09093044460
Na billkisa ibrahim 📝📝




27 «******» daga nan gidan dady sabon gidan da dad yabashi ya nufa, lallai gidan ya had'u🏘, idan natsaya baku labarin gidan sai mu b'ata lokaci, amma gidan b'angare hud'une kowa danasa baruwan wata da wata, yagama zagaye gidan ya koma gida.


Gado ya haye yay barcinsa tunda yau babu karnika agidan.


Su ikileema kuwa suna zuwa kowa gidansu ta wuce, suka zayyane ma iyayensu abinda ya faru k'arya da gaskiya, suka d'aure musu gindi wai su zauna har sai dady yazo.


Da daddare dad ya shirya ya nufi gidan umma, acan yasamu yayyenasa, abban ikileema da abban husna, ya gaishesu kowa ya amsa fuska acinkushe, baibi takansuba yafara basu hak'uri akan yaran da abinda ya faru, yace kuma suyi hakuri abashi yaran ya maidasu yanzu.


Umma ta watsa masa harara to ubanmu Mansur ba dole abaka yara katafi dasuba tunda yaran wasane su, agabana yaron yaci mutincinsu ya had'a dani sannan kawai dan karainamu, kai mai d'a da kud'i kazo kace abaka yaran ka maida masa, in kaga sun koma sai yazo dakansa gidannan ya basu hakuri, yakuma saki wacan farar koman dannasan farintane yake d'ibarsa ba wata tsiyaba.


Dad yace umma kiyi hakuri saboda yarannan duk d'ayane awajanmu bashi da damar sakin wata yabar wata, dan hakan zai iya b'ata mana zuminci gabad'aya, dan haka kuyi hak'uri kawai sukoma.


Abban husna yace kai Mansur kaje kawai inhar kun yarda da sharad'in umma to yasaki wadda kuka auro masa agobe adawo masa da 'yan uwansa d'akinsu.


Dad ya mike.yana fad'in kudaiyi tunanin mai yuwu wa, duk shawarar dakuka yanke muna jira ya fice abinsa batare dayabi takan kiran da abban ikileema yake masaba...




🌺billy🌺
{🌹Mrs Abdus'salam🌹}
[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


09093044460
Na billkisa ibrahim 📝📝


28 «*****» dad yadawo gida ya sanarwa mom yanda sukayi dasu umma,
Mom tace alhaji aida bakace musu hakaba.
To bilkisu ya kike so nace musu lokaci yayi dazan daina barin su yaya suna danne hak'in iyalina, dan bazai yuwwuba ace ni bani da 'yanci iyalinama basuda shi,
"Mom tace to shikenan ALLAH ya zab'a abinda yafi alkairi"
"Dad yace amin"
"Mom tace to masu kai amaryafa sun shirya dannaga abokan angon harsun iso, dad yace nagansu awaje harma mun gaisa, ai kawai abasu amarya sutafi, tunda bakunce can zasu kwana da k'awayentaba??
"Mom tace eh"
"To sai ku had'asu da manya uku suje su kwana can"
To shikenan alhaji mom tafad'a tana nufar hanya.


Ankai amarya d'akin mijinta kowa yaga gidan saiya rud'e da kyansa. To shima dai ango anan ya kwana ab'angarensa, washe gari akayi walima 'yan yola suka wuce gida, suka bar amarya na kwasar kuka, danma su kairat da kausar suna gidan tare da ita har dare, saida suka gyara mata ko ina sannan, mom ta aiko musu direba da abinci mai kyau da dad'i, yatafi da 'yan biyu gida, suka bar Munneerah na ta kuka.


Dady yana gidan har wajan k'arfe tara yana sak'a da warwara akan amaryar tasa, ak'arahe ya mik'e yay wanka yashirya cikin fararen kayan barci gajeren wando da riga mara nauyi, ya bud'e jikinsa da turare mai k'amahi, sannan ya kwashi wayoyinsa da jakkar aikinsa ya nufi d'akin amaryar tasa.


Itako Munneerah tunda su 'yan biyu auka tafi tayi zaman awa d'aya tana kuka, dataga ba mai lallashin ta, tamik'e tai shirin barci takulle d'akin ta kwanta, wai dan kar dady yashigo.


Ya iso ya tab'a kofar arufe yay d'an tsaki wai wannan yarinyar shi take rufema k'ofa dan ta rainasa, da har yayi niyyar komawa b'angaren sa ya kwanta abinsa, sai yatuna nasihar iyayansa, dan haka yazube kayan dake hannunsa saman kujeran dake kusa da k'ofar bedroom d'inta yafita ya koma b 'angaren sa ya d'akko wani key d'in yadawo.......


🌺billy🌺
{🌹Mrs Abdus'salam🌹}




🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


09093044460
Na billkisa ibrahim 📝📝


29 «******» yasa key d'in ya bud'e d'akin, ya kwashi kayansa yay ciki.
Ta mik'e zumbur zaune tana kallonsa cikin mamaki, kallo d'aya yay mata ya kauda kai, kujerar dake d'akin yanufa ya zube kayansa bisa tebir d'in gaban kujeran ya zauna.


Ya kalli Munneerah dake ta faman kallonsa, sai kuma ya mik'e ya nufi wajan gadon, shima yana kallon ta, ya kauda kai, kinci abinci ya fad'a yana bud'e kulolin dake gefenta??
"Tace na k'oshi"
"Ya d'aure fuska mekika ci??
"Ba komai"
Oya sakko kici abinci kafin na b'ata miki rai.
Ganin ya tamke fuska yasata sakkowa da sauri, dan dady yanada kwarjini sosai duk fitsarar ka in ya had'e fuska sai kaji shakkarsa.


Ya kalle ta tana cikin doguwar riga ta barci, amma bata kai k'asa ba,tayi mata kyau sosai, ya zauna bakin gadon, ita kuma ta zauna k'asa tana zuba masa abincin, ta gama ta jawo wani filet d'in zata zuba, yace karki zuba wannan ma ya ishemu.


Ya sakko ya zauna saman kafet d'in, ya fara cin abincin, itako ta kasa ci sai wasa take da zoben hannunta.
Ya d'an buga cokalin ajikin filet d'in, ta d'ago tana kallonsa,bana son yawan magana fa kici abinci,ba yanda zatayi dole ta d'auki cokali tafara ci, bai kuma bi takanta ba ya ci abincinsa da dukkan kayan abincin ya mik'e ya koma saman kujera, ya bud'e jakkar aikinsa, ya d'akko wasu book's yana dubawa.
Ta d'an ci abincin ta tattare kayan takai kichin,
Ta dawo ta haye gado ta kwanta, shikam yanata bin cikensa har wajan kar fe 2:pm sannan ya mik'e yaje kan gadon daga gefenta ya kwanta yay addu'a sai barci.....


🌺billy🌺
{🌹Mrs Abdus'salam🌹}




[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


09093044460
Na billkisa ibrahim 📝📝




30 «*****» da asuba dady ya tashi, sai da ya tada ita sannan yafice yaje b'angaren sa yay alwala yasaka jallabiya ya nufi masallaci, koda ya dawo b'angarensa ya wuce yay kwanciyar sa.


Munneerah ko da ta idar da sallah saita d'akko AL'KUR'ANI ta hau karatu, dan bata iya barcin safe ba,sai da agogo ya nuna 7:am sannan tai addu'a, ta tashi ta gyara d'akinta fes ta had'a masa book's d'insa da wayoyinsa waje d'aya ta adana masa, ta wanke bayinta, ta dawo falo ma ta gyara ta bad'e gidan da k'amshi, mai dad'i.


Kichin ta nufa tana nazarin mizata fara dafawa yau amatsayin ta na amarya,🤔 can tai murmushi da alama ta tuna,dan haka ta hau aikin girki.


Sai wajan karfe 08:30 am, ta kammala, tajere k'ayataccen break d'inta, a inda aka tanada dan cin abinci,
Bayan ta gama ta nufi d'aki dan yin wanka.


Wajan k'arfe 8:30am shima dady ya tashi, yay wanka, ya shirya cikin jar shadda d'inkin zamani yayi kyau sosai sumarnan da sajensa sunsha gyara sai walkiyar mai sukeyi, yasaka turarensa mai dad'in k'amshi,
Ya fito hannunsa rik'e da farara riga da likitoci kesakawa.
Kaitsaye b'angaren Munneerah yanufa......


🌺billy🌺
{🌹Mrs Abdus'salam🌹}
[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


09093044460
Na billkisa ibrahim 📝📝


31 «*****» tunda yadoso b'angaren nata yakejin k'amshi yana bugosa, ya tura kofar falon ya shiga, yashak'i dadda d'an k'amshin ya lumshe idanu, tare da fad'in ya SALAM, yabi palon da kallo yay murmushi yana nufar kofar bedroom d'inta.


Tana tsaye ga ban madubi tana saka lip stick abaki, jin anturo kofa yasata saurin juyowa tana kallon kofar, shima tsaye yake k'yam yadasa mata fararen idanunsa yana mata kallon sama da k'asa, sanye take cikin farin material da d'igon d'igon ja tayi kyau sosai.
" ta zame kasa ta durkusa, yaya ina kwana??
"Cinkin sark'ewar murya yace kin tashi lafiya??
"Tace k'alau"
Ya k'araso cikin d'akin yana tanbayar jakkar aikinsa💼 ??
Taje ta d'akko masa saida ta russina sannan ta bashi.
"Yace to ni bari nawuce aiki ya fad'a yana kallon agogon hannunsa"
Har ya juya zai tafi, tace yaya !!!
"Ya juyo yana kallonta ba tare dayayi maganaba"
Dama.......sai kuma tayi shiru batare data k'arasa fad'a ba
"Yace ina saurarenki"
Cikin rawan murya tace dama cazanyi bakayi break ba zaka fita, gashi kuma har na had'a tun d'azu.
"Cikin mamaki da al ajabi yake kallonta sukaima juna kallon tsakkiyar ido, tai saurin janye nata dan bazata juri kallonsaba"
"Ya b'oye mamakinsa, yace to muje kibani, dan ina saurine, inada tiyata karfe 11: 30am ya kalli agogon hannunsa gashi har 10: 38am tayi.


Yay gaba tana binsa abaya, taji dad'i da zaici, dan ita atunaninta zaice bazaici abincintaba tayi k'arama, kamar yanda yakebfad'a
Suka k'arasa wajan tebirin cin abincin yaja kujera ya zauna, ita kuma tafara zuba masa abincin, k'amshin ya daki hancinsa ya lumshe idanu,tare da had'iyar yawu.


Ta gama ta tura masa kofin shayin☕ da filet d'in🍝 gabansa, ta mike zata bar wajan
Yace, "k" zonan !!!
"Wani haushi ya turnik'e ta ta tsani ace mata "k" amma ta kula shi wannan d'an latsin rainin wayon yana neman maida mata suna haka"
"Wai ko bakijini bane?
"Ta dawo da tace gani"
Ya nuna mata kujera, sannan ya d'auki kofi ya had'a shayi, tana zaune tana kallonsa 🙍.
Yak'are had'awa ya mik'o mata ☕, tasa hannu ta karb'a, ya d'auki cokali yasaka cikin filet d'in data zuba masa abincin, oya bismillah, dole taci dan tana tsoron wannan d'an hayak'in.


Bayan sun kammala ya mik'e, itama ta mik'e ta d'auki jakkar aikinsa.


Har wajan motarsa tara koshi, ya bud'e ya shiga ita kuma tazagaya d'ayan b'arin tasaka masa jakkar, ya tada motar, tad'an lek'a tace ALLAH ya tsare ya bada sa'a"
Yay d'an murmushi batare da yayi maganaba yaja motar ya fice bayan sun gaisa da mai gadi...


🌺billy🌺
{🌹Mrs Abdus'salam🌹}
{MrsMrs Abdus'salam🀠Mrs


[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


Na billkisa ibrahim 📝📝


32 «******»saida ya fice ta koma cikin gida, ta d'auki waya ta kira 'yan biyu wai dan ALLAH suzo su tayata hira,


Shikam gogan naku koda yafita gidansu ya nufa, zuciyar sa fal tunanin wannan 'yar shilar yarinyar da ya raina, dukkanin abinda tai masa yau ya d'aure masa kai da kwanya, idan ya tuna su husna da ayyukansu,a tsawon shekara d'aya d'auka tare dasu amma ko maka mancin abinda yarin yarnan tai masa yau, basu tab'a yimasa ba, dai dai da d'akinsa sai dai shiya gyara, to bare girki, koda yake nasu d'akunan ma bagyarawa sukeyiba saidai masu aiki su gyara musu, yay hon mai gadi ya bud'e masa get, saida suka gaisa ya k'arasa cikin gidan.


Da sallama ya shiga falon, suna zaune a darning table, suna break, ya gaida iyayensa su kairat suka gaisheshi,
"Babana taso kayi break mana !!
Dady yay dariya dad nida abinci kuma ai sai na rana, yanzu kam akoshe nake.
Shima yay dariyar, babana ina kasamu abinci??
yanzufa naji mom d'inku tanacewa su kairat suzo sukai muku break.


A'a wlh mun hutash sheki mom ba sai an rik'a kaiwaba.
"Matata ta iya girki"
Dad a tanbayi mai mata a ina yaci abinci, ya fad'a yana dariya😃
Suma gaba d'aya suka tun tsire da dariya, ya mike shima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login