Showing 12001 words to 15000 words out of 24696 words

Chapter 5 - Auren Kaddara Ko Na Biyayya Complete.txt

18 Feb 2025

3242

yana dariyar kunga sai anjiman ku ni zan makara.


Dad yarage dariyarsa to kayi k'ok'ari idan aiki yayimaka sauk'i ko zuwa yamma ne kasa meni a office.
"Yace to sai nazo"
"Mom sai anjima"
"To babana adawo lafiya"
Su kairat sukace yaya yanzufa zamu gidanka
To sai kunje, kuna can har dare ko??
"Eh har sai kadawo ma"
To shikenan ya fad'a yana fita


Yana isa asibitin ya fara shirin shiga tiyata bayan ya gama zagaya marasa lafiyar yana musu sannu da tanbayar su ya jiki, wanna kyawawan halayen nasa ya sashi yin fice asibitin, koya kake dady baya wulak'antaka ya iya tattalin mara lafiya da kwantar masa da hankali, in har baka da k'arfi, zai taimaka maka da aljihunsa da basirar sa, duk sanda ya iso asibiti sai ya zagaya marasa lafiya, yay musu sannu, mai buk'ar wani abu yay masa sannan ya dawo office yacigaba da duba marasa lafiya
Shidai barahi da shegen miskilanci kuma abun ajininsa yake.


To yauma bayan yagama zaga yensa ya shiga tiyata bakin sa da addu'oin neman nasara.......


🌺billy🌺
{🌹Mrs Abdus'salam🌹}
[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


Na billkisa ibrahim 📝📝


33 «*****» miye labari su husnane ??
Su husna suna gida abinsu umma anata lek'e lek'en gidajan malamai da bokaye, acewar ta sai dady yazo dakansa yana kuka abashi su ikileema.
To suma sunanan sunata fankama akan sai yazo, iyayensu mata ma suna nemomusu agefe kowa tana shirya d'iyarta acewar su, amma gashi yau har tsawon sati uku ba labarin dady bare zuwansa.


Su har ma abin basu tsoro yakeyi dan sunsan halin dady sarai da,miskilancinsa,
Ikileema tana kwance bisa doguwar kujerar dake falonsu, sauran k'annenta sunata hirarsu.


Maman ta ta fito tazauna kusa da ita ikileema lafiya dai ko naganki akwance?
ga kuma sauran 'yan uwanki sunata hirarsu.
"Ta turo baki gaba gaskiya nifa mama nagaji da zamannan hakanan, nifa gidan mijina zan koma, yakama ta ku daina biyema waccan tsohu war hakanan, dan wallahi nasan dady bazaizo bikonmuba, garama tun wuri kubarmu mu koma, dan gaskiya nidai inason mijina, tafad'a tana juyama uwar tata baya.


Mamarta tace ikileema kefa shashaahace duk wannan k'ok'arin da akeyi dansu ubanwa akeyi badan kuba, shine har kike fad'a mini kefa kina son mijinki.


ALLAH mama ba haka bane ba gara ku bari mukoma ba, dukma abinda za'ayi ayishi muna can, agidan amma azo ahanamu komawa gidan mijinmu, ita kuma waccan she giyar tana can tan shan shagalinta awannan had'ad'd'en gidan.


Maman tai ahiru tana kallonta, kai ikileema dafa gaskiyarki wlh, kumafa hakane mumu nanan muna bad'oso goyon jirge, ita tana can tana shan lagwadar dad'i dak'ara mamaye gida, da mai gidan, nasan hajiya salaha sarai da iya kissa, kuma tana koyar da 'ya'yanta.


FAD'AKARWA :- ni aganina dan mace ta koyar da yaranta kissa inhar bata cutar da wani bace, tofa tayi dai dai, dan kissa nad'aya daga cikin halayyar dake jan ra'ayin miji ga matarsa, ba sai ta hanyar boka da malam ake jan ra ayin mijiba, a'a kema malamar kankice, bari nabarku haka ku biyoni kuji yanda Munneerah take damk'e dady ahannunta cikin ruwan sanyi da kissa irin wadda ta halatta.......


🌺billy🌺
{🌹Mrs Abdus'salam🌹}




[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


09093044460
Na billkisa ibrahim 📝📝


34 «*****» to kinjifa mama dama kinsan wannan amma kika barni agida ita waccan sarkin iyayin husna uwarta tace ba yanzuba, to nidai duk ma yanda za'ayi kiyi nakoma d'akina awannan satin,
Gaakiyarki ikileema in ALLAH ya yarda yau da abban ku ya dawo zan masa magana gara ki koma d'akinki.
"Ta tashi cikin murna ta rungume uwar tata tana godiya.




To ab'angaren husnama haka abin yake ita babanta ma tasanar tanason komawa d'akinta, yace karta damu zaije yasamu umma da yaya da maganar yau da daddare.
"Tace to"




Agidan dady kuwa zama akeyi irin na k'anwa mai girmama yayan ta, da yaya mai kula da k'anwarsa amma babu wata shakuwa data wuce gaisuwa da safe, ta had'a masa break, ta rakashi wajan motarsa in zai tafi aiki, tadawo ta gyara masa d'akinsa, ta wanke kayansa daya cire, tayi girki da rana mai dad'i da gamsarwa akai masa asibiti,inya dawo ta taroshi tarakasa har b'angarensa, ta basa ruwa yasha, dama ta had'a masa ruwan wanka, da dadare ta dafa musu abinci mara nauyi suci, koda ba wata hira mai tsawo ke had'asuba sukan zauna apalo d'aya suna kallo, koyana bincikensa akan aikinsa, ita kuma tana kallo, duk abinda yasakata zatayi babu fushi bare canja fuska kota nuna gajiya warta.
Wannan ne yakansa kan dady girma dajinfa shima fa ya isa maigida, shima yana kyautata mata indai yafita yaga wani abida ya birgeshi zai siyo mata,


TUNA TARWA :- 'yan uwana mata bamu cika san yiwa mai gida wankiba, bare idan ALLAH yad'an bashi karfen nasara ahannu (kud'i) masu d'an k'ok'ari a cikinmu sune masu wanke singlet da gajeren wando, kina zaune mai gida zai had'a wanki ya bayar, sai kiji muna fad'in bazamu iyaba gana yara ganashi kai wallahi aiki yay mini yawa, a'a uwar gida tsarama kanki yanda zaki zauna agidan miji kinji, kula dashi da dukiyarsa sutturarsa, tsara wani d'an lokaci kina yima mai gida wanki yanasa farin ciki da kaunarki azuciyarsa, zaki k'ara samun fada a cikin zuciyarsa,....kudai biyoni 'yan uwa........


🌺billy🌺
{🌹Mrs Abdus'salam🌹}
[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


09093044460
Na billkisa ibrahim 📝📝


35 «*****» Munneerah tana zaune apalo tana kallo bayan tagama sallar isha'i, lokaci lokaci takan d'an cije leb'enta da alama akwai wani guri dayake mata ciwo, ta zame ta kwanta saman doguwar kujerar datake zaune.


Dady ya turo k'ofar ya shigo da sallama, ta amsa cikin dauriya, da cije baki,
" Yad'an kalleta lafiya kuwa??
Ta daure tace bako mai, yanemi guri ya zauna kujerar dake gefenta,
Ta tashi zaune tana fad'in yaya abincifa??
"Yad'an tsura mata idanu dan son gano matsalarta, amma saita kauda kai tana laluben wayarta,
Ta kuma maimaita tan bayar sa cin abinci?
"Ya girgiza kai saidai zuwa anjima, bani dai lipton na sha"
"Ta mik'e tana fad'in to"
Bayan kamar minti biyar ta dawo hannunta d'auke da tire k'arami, ta d'oro butar shayi da kofi sai k'aramin cokali, ta ajiye saman tebirin dake gefen kujerar daya ke zaune, ta zuba tasaka shuga ta motsa, sannan ta bashi, ya karb'a yana binta da kallo harta koma saman kujerar ta kwanta,
"Gaskiya yana buk'atar abokiyar jalittarsa, sai dai yana ganin Munneerah tayi k'ank'anta, babu abinda zata iyayimasa, ab'angaren auratayya, kai idanma ya b'ullo mata da wannan maganar saita rainasa, girma mawar data ke masa ta daina, to inma banda abinsa mai zai samu wajan wannan 'yar shilar yarin yar, wadda ahaihuwar kaji ya haifeta, a gabansufa aka haifeta susuka rainet.....
Wayarsa ta katse masa tunani, ya d'auka yana dariya, ango kasha k'amshi, kaima kazama sojan sama ko ka kashe arna dubu??
Daga can b'an garen jafar yay dariya nida kai a tantance sojan sama, d'an rainin hankali, kai mai mata uku ma ba ace dakai sojan samaba har zakace da wani.
"Dady yay dariya kaini nida gwauro babu maraba ai"
"Kai haba inji jafar, kodaya ke ance mini matanka sunyi yaji, to aikai gaba ta kaika malam saika kwashi amarci abinka"
"Kai daina fad'a dan ALLAH ina abin yake bare romonsa ai da sauran lokaci,
Dariya sosai jafar yakeyi haba d'an uwa kardai nanda wata tara ace muzo suna
Kai d'an iska sai anjima kaji, ya yanke wayar yana dariya.


Da sauri ya mik'e ya nufi Munneerah dake kuka rik'e da ciki, yay saurin tarbo ta tafad'o jikinsa, cikin rikicewa yace Munneerah mike damunki??
cikin kuka ta nuna masa k'asan cikin ta,
"Mararki ke ciwo tad'aga masa kai tana murku susu ajikinsa, ya kalli agogo 8:55 pm, ta k'ank'a mesa cikin zafin ciwo yaya zan mutu wayyo yayan ka taimakeni,
Cikin sark'ewar murya yace bazaki mutuba Munneerah......




🌺billy🌺
{🌹Mrs Abdus'salam🌹}
[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


09093044460
Na billkisa ibrahim 📝📝


36. «*****» duk ya rud'e gashi likita amma ya kasa yimata komai, k'arshe dai ya rarumo waya ya kira wani abokinsa Dr Anuwar, bayan sun gaisa yace my friend ! Please in ban takuraka ba dan ALLAH kazo gidana yanzu??
"Cikin sauri Dr Anuwar yace inazuwa"
Cikin minti 15 ya iso gidan kai tsaye ya shigo dan yasan gidan, har sannan Munneerah kuka takeyi tana fad'in yaya ya taimaketa.
Dr Anwar ya shigo, ko gai suwa basuyiba ya fara tanbayarsa mike damunta ??
"Dady yace mararta ke ciwo""
Allura Dr Anuwar yay mata, cikin minti 3 sai komai ya lafa, barci ya d'auketa ajikinsa, yay ajiyar zuciya my friend nagode fa"
"Dr Anuwar yay dariya karka damu my friend, dama haka tana faruwa akanmu likitoci sai kaga wani naka bai da lafiya amma saboda tsabar rikita mukasa bashi kulawa,
Sai mun nemi taimakon wani.
Wallahi kuwa hakane kagama inada allurar amma tsabar rikicewa tasa na rud'e"
Dr Anuwar ya mik'e yana dariya aidama hakane,bara na wuce saimun had'u gobe a asibiti, to my friend na gode, ya fad'a yana kwantar da Munneerah akan carpet, Dr Anuwar yace kaga yi zamanka wallahi na gode ALLAH ya k'ara lafiya, sukai hannu ya tafi.


Dady yadawo yana kallon Munneerah da take barci, karki damu matata in sha ALLAH sai kin rabu da ciwonnan tunda kina tare da gwarzon namiji, ya d'auketa gabad'a ya kai ta d'aki ya kwantar, sannan ya dawo yana nazari akan ciwon nata abincikensa abu ukune ke kawoma mace ciwon mara yayin al'adah, amma zaidai sake bincike akai.......




Washe gari abban ikilima ya isa gidan umma suka had'u da abban husna bayan sun gaida tsohuwarsu suka gaya mata buk'atarsu ta maida yaransu d'akin mijinsu, abban husna ya d'ora da fad'in umma kinsan taurin kai irin na yaronnan Abdul'aziz, ga shegen miskilanci kamar d'an sarauta, to kawai tinda yaran sun buk'aci komawa d'akinsu a maidasu, duk abinda za'ayi saimuyi suna cikin gidan, kina ganin Mansur tundaga ranar dayazo yabada hakuri sukoma muka k'i baisake yin maganar amaida yarannanba, amma umma yakikagani.


Taja nummfashi to shikenan kuma kun kawo shawara sai su shirya gobe na maidasu d'akinsu in ALLAH ya kaimu
"To shikenan umma ALLAH ya kaimu kowa ya mik'e yanufi gidansa dankai albishir.......




🌺billy🌺
{🌹Mrs Abdus'salam🌹}
[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


09093044460
Na billkisa ibrahim 📝📝


37 «******» dady yakai tsawon awa biyu afalon yana sak'a da warwara, ya kalli agogon dake palon, yata shi zaune da sauri danganin lokaci yaja, ya mik'e ya nufi b'anga ren sa.
Wanka yayi yay shirin barci, ya dawo b'angaren Munneerah, ya kashe komai ya rufe ko ina, sannan ya shiga bedroom d'in ya kalleta tanata barcinta, ya kamata ya canza mata kayanta zuwa na barci, bayan ya canza mata, yay musu addu'a yay kwan ciyarsa.


Da Asuba ya tashi yay alwala ya wuce masallaci batare da ya tasheta ba, bai dad'e da tafiyaba tatashi, tabi jikinta da kallo cikin mamaki waye ya canza mata kaya, wakuma ya kawota kan gado, tunda tasan afalo ta kwanta, zuciyarta tace mata mijinki, ta zaro idanu waje 😳 ni Munneerah kice yagama kalleni abanza, taja bargo tarufe jikinta da sauri danjin an turo k'ofa.


Ya tsaya cak yana kallonta danganin tanata faman cikukuye jikinta cikin bargo, ita kam tai k'asa da kai ta kasa kallonsa, yay d'an murmushi ya k'arasa jikin gadon yana fad'in ya jikin naki??


"tad'an kalleshi kad'an taikasa da kai, dasauk'i ta fad'a asaman leb'enta"
"Yanzu dai ba inda yake miki ciwo ko??
Ta kad'a kai batare datayi maganaba.


Shima bai sake cewa komaiba ya juya ya fita abinsa.
"Ta mik'e ta shige bayi"


*************»«
Tunda labari yajema su husna akan zasu koma gidan mijinsu suketa farin ciki, dan suna son dady da gaskiya, iyayensune kawai suka k'ulla auren nasu da wata manufa.
Tun adaren suka had'a kayansu, karfe goma na safe agidan umma tai musu,
Umma ta rik'e baki oh ni yaran yanzu bakuda ta ido, yanzunan danza ku koma gidan mijinku shine kukayo irin wannan sammako haka.
Husna tace to umma bamuyi dai daiba kenan.
Ah bar tsohuwarnan kinji itama idan itace abinda zatayi kenan,ikilima tafad'a k'asa k'asa,
Umma ta cafe to mara kunya mikikace ??
Ikilima tace nifa umma bance komaiba, tafaki idonta tai mata murgud'e 😘.
Husna tai mata gwalo 😛 fiti nanniyar tsohuwa kawai 😲.......


🌺billy🌺
{🌹mrs Abdus'salam🌹}
[1/14, 4:11 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


Na billkisa ibrahim 📝📝


38 «*****» kamar yanda tasaba ta had'a musu break mai dad'i da gamsarwa, tai wankanta ta ashirya cikin doguwar riga ta shadda, ta fito falon, ta zauna tana jiran dady.


Ya turo kofar ya shigo cikin sallama, jikinsa sanye da k'ananun kaya bulu d'in wando da farar riga, kannan nasa ya d'au mai, sai walk'iya yakeyi, ta zamo daga kan kujerar tana gaisheshi,
Ya amsa yana binta da kallo, yaya jikin naki??


Tai k'asa dakai, tana fad'in da sauk'i, ya nufi wajan cin abincin, to ALLAH ya k'ara sauk'i,
Ta mik'e tana binsa abaya har zuwa wajan cin abinci, ta zuba masa komai ta tura gabansa, ya zuba mata fararen idanunsa, tasan miyake nufi dan haka ta jawo kofi tafara had'a shayi.


Bayan sun gama tarakashi har wajan mota kamar yanda tasabatadawo ta gyara wajan takoma falo tana kallo.


Buga k'ofa akeyi kamar za'a b'allata, cikin mamaki Munneerah ta mik'e ta nufi k'ofar, ta bud'e dan ganin mai mata irin wannan bugu.....




🌺billy🌺
{ Mrs Abdus'salam}


[1/14, 4:10 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


09093044460
Na billkisa ibrahim 📝📝


39«*****» tana bud'ewa suka afko harda k'ok'arin tureta, ta bisu da kallo cikin mamaki, umma ta daka mata tsawa to mara kunya kinyi tsaye kina kallon mutane ko baki sammu bane??
Cikin ladabi Munneerah ta durk'usa tace ina kwana??
Banza umma tai mata, takuma maimai tawa,
Umma ta harareta to sarkin iyayi, tunda kinyi na farko, aiya isa zakibi kidamemu,husna tace, inafa zatai shiru ana neman gindin zama, aiko indai ananne bazata samuba har ta mutu, cewar ikileema.


Umma tace to bara kiji bawai narasa mai gaisheni bane, nazo namiki kashedine ga jikokinanan karnaji karna gani, kinsan dai sunyi k'anwa dake tawajan uku, to wallahi nasake naji wani abu ya b'ullo saikin gawa aya zak'inta, nasan hajiya salaha uwarki sarai, to nasan dai halinta babu wanda 'yay'anta suka bari, makirci,kissa, iyayi,dahad'a kiahiyoyi da miji, to wallahi anan kikai mana irin wannan halin acikin kwana kad'an zaki kama hanyar gidan ubanki, idan kunne yaji jiki ya tsira, ta fice.
Ikileema ta dinguri Munneerah, shegiya faratun banza sai munyi maganinki agidannan,
husna tace saita barsa da k'afarta tsinanniya gadon tsiya, suka tafa suka fice.


Munneerah ta durkushe agurin tana kuka, nashiga uku ni Munneerah wannan wane irin bala'ine haka, tadad'e tana kuka daga k'arshe ta share hawayenta, tatashi tashiga kichin domin yin girkin rana.


Bayan tagama ta nufo d'akinta, ta d'auki waya tanason kiran anty Ni'ima dan tasanar da ita damuwarta.


Ta zaro idanu waje 😳, dan ganin dady yakirata har sau 8, na shiga uku tafad'a tana juya wayar, har sau takwas yaya ya kirani ban ganiba, yau naga ta kaina..........


🌺billy🌺
{Mrs Abdus'salam}
[1/14, 4:11 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳.
🌷ko BIYAYYA🌷


09093044460
Na billkisa ibrahim 📝📝




40 «******» tafara k'ok'arin kiransa, saigashi kiransa ya shigo, jiki a mace ta d'aga cikin sanyin murya tai sallama??
Yakai tsawon second, goma bai amsaba, tasake yin sallama akaro na biyu, saida yaja ajiyar zuciya sannan yace wa'alaiki, cikin muryarsa mai dad'i,
Tace dan ALLAH yaya kayi hak'uri, kakirani ban d'aukaba ina kichinne, wayan kuma tana bedroom,
nanma yaja lokaci bai amsaba,
Saican yace ya jikin naki??
"Dasauk'i ta fad'a"
"Maran naki ya daina ciyon??
"Cikin jin kunya kamar tana gabansa, tace ya daina"
To shikenan ALLAH yak'ara sauk'i"
"Amin ta fad'a asanyaye"
"Yaya ka aiko akarb'i abinci nagama tun d'azu"
"Amma banace karkiyi komaiba ki kwanta kihuta keda bakya jin dad'in jikinki??
Kayi hak'uri yaya aina samu sauk'i".
"Yaja nummfashi !!!, to shikenan zan aiko salisu ya karb'a idan mun fito sallah"
To sai yazo, saida tabari ya kashe sannan itama ta kashe.


Dady ya jin gina da kujera ya lumshe idanu, ya bud'e ahankali waishi mike damunsane, akan yarinyar nan??
Yakuma lumshe idanu
Zuciyarsa tace kakamu da sonta ne, yazaro ido kai so kuma, canza dai zuciya ya za'ayi naso wannan 'yar shilar yarinyar, duka yaushe tazo duniyarma, kawaidai ina girmama tane dan hidimar datake yi dani.
Amma batakai nasota ba.
Ya bud'e idanunsa ahankali danjin anamasa magana, Dr Anuwar yace a'a my friend lafiya dai, nazatama kayi alwalah, ashe kanana kana tunani, miye damuwarka??
Dady yaja ajiyar zuciya yana mik'ewa, bakomai, inadai hutawane, ya shige bayin dake office d'in batare daya jira amsar Dr Anuwar ba.
Dr Anuwar ya girgiza kai yana binsa da kallo, bayan ya fito suka wuce masallaci.


Salisu masinjansa yaje ya karb'o masa abinci kamar yanda ya saba.......


🌺billy🌺
{Mrs Abdus'salam}
[1/14, 4:11 PM] mrs bilkisu: 🌳AUREN K'ADDARA🌳
🌷ko BIYAYYA🌷


09093044460
Na billkisa ibrahim 📝📝


41 «*****» bayan sundawo masallaci, Dr Anuwar ya biyoshi office d'insa, dady yazauna a kujerarsa, shikuma Dr Anuwar ya zauna akan d'aya daga kujerar dake gaban tebir d'in, Dr Anuwar ya tsurama dady idanu my friend dama ina son magana dakai??
"Dady yay murmushi ina jinka my friend"
Inason magana ne akan amaryarka?
Karka damu my friend ina saurarenka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login