Showing 1 words to 3000 words out of 146041 words

Chapter 1 - DUNIYA TA AMNA Complete Book By Asma Baffa .pdf

23 Mar 2025

11134

: DUNIYA TA





BISMILLAH

INA MATUKAR GODIYA GA ALLAH DA YA BANI RAI DA LAFIYA DA KUMA IKON RUBUTA
SABON NOVEL DIN NAN DUNIYATA.


MAKARANTA NOVELS DINA DA BIBIYATA INA MUKU GAISUWA DA FATAN
ALKHAIRI,ALLAH YASA WANNAN NOVEL YA FADAKAR YA KUMA NISHADANTAR,KAMAR
YANDA MUKA FARA LAFIYA ALLAH YASA MU GAMA LAFIYA AMEEN.

KAMAR YANDA KUKA SANI NOVELS DINA NISHADI YAFI YAWA CIKI,INA KUMA GODIYA
DA KUKE KARANTAWA HAR MUTUM YA SA KUDI YA SIYA WANNAN YAFI KOMAI DADI,INA
GODIYA ALLAH YA BAR KAUNA.











1-5










FREE PAGE

LITTAFAN DANA RUBUTA

GASKIYA CE
MARAICIN RAHMA
MAAIKACIYAR GOMNATI
CIRANIN AMANA
DUK INDA TA FADI
KAMARSU CE DAYA
KASUWANCI NA
JIN DADI SABO
HADIN KAI
ME MAGANI
TUBABBIYA



NA KUDI DANA RUBUTA

RASHIN SA'A
TA GYARU
YAR KWANGILA
ADDUAR KAWA
GIDAN GWAURO/DAN NAZIA
DANGIN RABI
DUNIYA TA.......





GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DIN DUNIYATA DARI BIYU 200 NE


ACCOUNT NUMBER
0175487861 ASMAU GARBA MUHAMMAD, GTBANK.

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER TA
08033933642

'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39











Official








By
AsmaBaffa










Page din farko naku ne Fans Dina duk wacce ke cikin groups Dina.

Zaune suke a wani katafaren Palo na Alfarma,Palo Wanda yaji furniture Dan gaske,duk
Wanda ya Shiga wannan Palo bazai so Fitowa ba,wani uban kamshi da sanyi ne ke
tashi,Family Guda su Shida rakacal sai ta bakwan Yar karamar yarinya tana Wasa a kasa,Kidan
Bob merly ne ka tashi a wata katuwar plasma tv kamar ka dakko mutum,gaba Daya sunyi Shuru
duk Basu cikin nishadi,Ahmad Dake narke cikin luntsumemeyar kujera shine yake kada Kai
cikin maye da kwaya da gani kasan Kansa ba kalau ba,sai bin wakar yakeyi da bakinsa,gashi
babu Wanda ya Isa yace ya kashe ko ya daina,baya Jin Maganar kowa,Mummy dattijuya itace
ta nisa fuskarta dauke da damuwa Tace Haba Ahmad Kaine fa babban Danmu Amma ka duba
yanda ka maida kanka Completely Useless har mun gaji da Dake Hanya tun daga Lagos muna
zuwa Nan Kaduna wajenka akan magana Daya kaki ji,tunda hakane yau da Yamma zamu
koma,Wani farinciki ne ya bayyana a kyakyawar Fuskarsa,ya Mike tsaye yace wow Mama the
Mama,Allah yau zaku tafi?yawwa Haka nake so sabo da na samu freedom,yau kwananku biyu
Kun dameni dama,Shut up Daddy ya Furta banzan yaro marar tarbiyya,ai Kai dama Daddy
nasan baka so na,Zama ya sake Yi Yana bin wakar Bob merly,sai Chanel din Suka cire wakar
aka Sako tallan Wani body lotion.

Wata Uwar Tsawa Ahmad ya saki tare da nuna Tv da yatsa cikin mayensa na giya da kwaya
ya kalli dalleliyar Budurwar da aka Nuno tana tallan Body lotion a tv yace Kai...dalla ku matsa
can Kar ku kawo Mana Harkar Daudu anan,mu ba Daudu Muka zo gani ba Ana Harkar arziki
zaku zo Mana da Mata Yan Daudu,ke dalla ja can, Dan uwarki a Nan Nigeria muna da man
shafawar mu Habiba yawwa,Muna da Habiba Muna shafawa Muna Kara Baki wuluk abin mu
yafi Mana,Dariya ya Bawa duka Yan palon har Daddy ya kalle shi yace Ahmad Kai da kake fari
Kal jinin Larabawa Kuma a gidan uban wa kake shafa wannan Man,sannan ce maka aka Yi
Habiba karamin company ne? Mummy Tace Allah ya shirya min kai,Baki ya turo tare da gyara
Ass down dinsa da yayi da wani Creazy jean.

Wata Yar kyakyawar jar mota ce Honda tayi parking a bakin wani Restaurant,Yar
kyakyawar Budurwar ta fito Hannunta dauke da Handkerchief tana goge zufa, Hannayenta ta
Shiga tafawa tana Waka Sannu da Zuwa.....Sannu....da zuwa kekashashe na,Oyoyo Dan
Kedararre na.....Oyoyo Karmashashe na,Barka da dawowa Dan tsomalalle na,My Karmash I
miss you,Wani saurayi ne matashi mugun siriri wuyansa kamar murkin laima,Kugunsa Kamar
zai tsinke,Baki ne wuluk Kamar Iska zata dauke shi Haka ya fito daga jar motarsa Yana wani
basarwa a dole babban yaro,Bakinsa ya Bude da Niyyar magana Yan hakoransa manya na
gaba Guda hudu Suka yo waje,Yana kallon Budurwar yace naga Alama Baki da tarbiyya,Kamar
Ni saurayinki Ina sonki kina so na Amma kina ci min Fuska,glass dinsa ya zare a Fuskarsa ya
kalle ta sama da kasa yace Yar talakawa Dake matsiyaciya ki kalle Ni kina wani ce min Oyoyo
Karmashashenki? Baki da Manner? An fada Miki badan so ba Zan iya tsayawa da Yar

matsiyata irinki? Ki kalle Ni nafi karfinki ta ko Ina,Yar budurwar kyakyawar gaske fara Tace Kayi
Hakuri Wasa nake maka wallahi badan naci fuskarka na fada ba,Tsawa ya daka Mata yace
dalla ja can dama iyayenki Basu Miki tarbiyya ba,Baki da hankali dai,Ran Budurwar ya baci tace
kaga Malam na maka tauna na maka hadiya baka gani ba,to naji bani da tarbiyyar sai kace
Iyayenka suzo su Yi min,daga na maka Wasa Kai baka San wasan masoya ba,wannan ne
wasan a gidan uban wa ya Zama Wasa? Nan take Budurwar ta bashi amsa a gidan Ubanka
Kamalu,Baki Bude ya kalle ta yace Aamna a gidan wa kika ce? Wacce aka Kira da Aamna ta
sake cewa a gidan Ubanka nace Kamalu,Kamalu ransa ya dugunzuma yace it's over between
me and you,bani ba ke,Aamna Tace ae naji Nima bani ba Kai tsotsatsen banza,me zanci da Kai
dama idan anyi auren ma Banda kashinka ya dinga suka na me zanyi,Dana kwanta a jikinka
gwara na hau katifar fasasun kwalaba,Kuma da na aureka ka min kiss da bakinka me hakora
Kamar kacar Keke gwara na tsotsi Kusa me tsatsa,Yace irin na Ubanki ne ai hakoran,naji ta
furta tare da koma cikin Restaurant taci gaba da aikinta.

Wajen masu girkin taje ta faki idonsu ta saci yankan nama Uku ta watsa a Jakarta ta fito ta baya
can ta cinye Naman sannan ta dawo ciki ta Iske Fried rice an Gama an kaiwa wani yaci ya bar
Rabi kadan ma ya ci,Aamna da sauri tazo Wajensa Tace Alhaji ka Gama Zan gyara wajen 2pm
yanzu resturant zai cika,kafin yayi magana ta sunkuce abincin ta dauke Masa lemon da ko
budewa baiyi ba ta Sha kwana tayi ciki,Alhaji ya saki Baki Yana cewa ke ke ke ban Gama ba
Amma Ina Aamna tuni Taki ma kula shi,tana zuwa Tace Alhaji ya koshi ta zauna ta lashe abincin
ta Balle lemon ta shanye sannan ta fito fes da ita da mamakinta sai taga Alhajin Bai tafi ba,da
sauri ta koma Wajensa Tace Alhaji wani abincin Za'a kawo maka ne? Alhaji ya kalleta yace ke
Amma wacce iri ce bance na koshi ba kin dauke abinci lemon ma Dan wulakanci ko Bude shi
banyi ba kin dauke Ina ta kiranka bakya ji? Aamna Tace eyya Allah sarki kayi Hakuri matsalar
kunne gareni banji ba Kuma gashi na zuba komai cikin shara bare na dawo maka da shi,Harara
ya balla Mata tare da zube wani kudin yace kawo min wani abincin,da murna ta dauka dama
Bata koshi ba,taje ta hadowa Alhaji duk abinda ya bukata,wata white rice with salat ga kwai da
kaza,ga lemo,Aamna tunda taga Haka take ta faman zaga wajen da mopper a Hannunta Wai a
dole gyara takeyi,tana ta faman goge goge a saitin Alhaji,Alhaji yace ke kin dameni da goge
goge ga customers can sunzo kije Mana Haba wannan wacce irin Maaikaciya aka dauka Haka
idan bakya so sai na daina zuwa cin abinci a wajenku aikin banza,Aamna tayi murmushi tare da
gyara pcap dinta Tace afwan Alhaji ta juya ta tafi Amma sai ta labe a bayan wani lungu daga ciki
tana ta kallon Alhaji tana so yayi ya Gama ta samu rabonta,Siyama ce kawarta taje ta sallami
wasu customers din Aamna tana labe tana zalama wajen Alhaji,Siyama tayi Dariya tare da
kallon Aamna tana labe labe Tace Allah ya shirye ki,Alhaji kadan yaci ya bar komai ya tafi kafin
ya Gama fita tuni Aamna ta kwashe komai tayi ciki,Nan ma ta zauna ta cinye ta koshi sannan
Tace saura na dare kafin na tafi gida,dole na dinga kiba Ina yin kyau,Aiki a restaurant ai Dadi
gare shi ko ba komai Zan cika tumbi na.


Dattijo ne fari me gemu sosai Wanda shi kanshi gemun ka kalla kasan Dattijon ya tsufa
domin yayi fari,da gudu gudu sauri sauri ya shigo gidansa inda yake wani mugun Rubabben
gida,Gida ne na Haya Kuma gidan Talauci,da gani ba sai an fada maka ba Dattijon Talauci ya

Gama da shi,cikin Gida ya Fado Yana masifa tare da furta me zangani Aishatu?me zangani
yau,wacce ya Kira da Aishatu ta kalle shi shekeke tare da balla Masa Harara Tace mene?
Gashi can kina karar min da kudi,kina min asarar Duniya da Almubanzanranta,yanzu ki duba
sabo da Allah tunda na taho Ina kallon kwalabati kumfar Omo tana ta bin ruwa tana ficewa
Ful...ful,Yanzu a zamanin Nan kumfa ka gani a kwata kasan kudinka ake kashewa,kina ta kashe
min kudi kina abinda kika ga dama,Ga jarabar karar da Ashana kiyi ta kyastata sai ta
Kare,Takaici na yanda kike wanki ko wanke wanke sai asarar Omon bala'i,to wallahi da sake
baza ta yuwu ba,kullum Ina fama a hanyar sakateriya wajen Dan aiki na Wanda masinja ne ni
nayi retired Ina nemowa Ana wulakantawa bazai yuwu ba,Daga yau ko mangyada ne za a zuba
a abinci to kowa cokali Daya Daya babu kari aikin banza,Wata buta yasa kafa tare da yin fatali
da ita Yana zare Ido yace Ina Aamna sakarai da Sweety Zuhra?Aishatu banza tayi Masa ta ci
gaba da aikinta,yace Aamna har yau ba labarin Mijin Aure?

Aishatu tayi Shuru,Dattijon yace na gaji da yahudanci wallahi da nasan Haka ne Aamna ko
secondary baza tayi ba,Dan fa Kawai Ina tunawa Amana ce a wajen mu, Nima ban San ya
akayi basirata ta toshe na biya Mata har tayi wani HND sabo da asara,ai karatun mace Bai da
amfani,amfanin mace aure da girki tayi ta zazzago Haihuwa,yarinya ta Zama bayahudiya
abinda taga Dama shi takeyi,Nima jarabata ce tasa Rana tsaka Ina Kauye tare daku cikin sutura
na dawo damu Birni na Kama haya,da Muna Kauye da tuni hankalinmu kwance,da duk wannan
karyar Bamu shige ta ba,Aishatu Tace ai sai Dana fada maka kaki ji Aamna tana secondary a
Kauye Ss3 ka kwaso mu Muka dawo birni gashi yanzu ta waye Taki aure muna ta ciyar da ita a
banza ,wallahi baza ta Sabu ba,gidana ya koma na yahudu bazai yuwu ba,ai Birni na dawo ne
Kawai Dan na samu sana'a me kyau to gashi hakan Bata samu ba,Dan pension Nawa ma baya
Isa Nawa yake Ina abin,kullum sai talauci ne ke karuwa,birni kwai masifa Ni tunda nazo banga
wayewar ba,ban wani waye ba,Aishatu Tace yo shekarar mu Nawa a Birnin kwata kwata
shekara hudu fa rak Ina wani wayewa Aamna da Zuhra ne Kawai Suka Dan waye Dake su Yara
ne,Dattijon yace ke tafi can Aamna Ina ta waye ai gwara Zuhra,Amma Aamna kina gani
magana ma Bata iya ba ta Kauye takeyi duk abinda yazo bakinta dankarawa mutum takeyi Dan
tayi makaranta ne ma take Dan canjawa,ni dai na fada Miki a kiyaye asarar Omo yawwa ya
furta tare da ficewa falau falau da rigarsa doguwa ta wani tsohon yadi dinkin wani falkeke komai
ta Masa yawa

Kuka Aamna ta saki Wiwi tana Hawaye tare da nuna Budurwar da Hannu tana masifa tare
da Furta In Allah yayarda Shedan sai ya sumbace ki,Shedan sai yayi kissing
dinki,muguwa,Azzaluma, maciya Amana,Baza kiga dai dai a rayuwarki ba Saratu,Saratu anyi
asarar Duniya,An Sarai asarar duniya,Shegiya wacce Shedan yayi Mata fitsari a Kai, Wacce
ake Kira da Saratu murmushi ta saki tare da karkada key din motarta Tace nafi karfinki Kina
talaka kucaka me Deeni zaiyi dake duk kudinsu,ke wawiya ce Baki da hankali da har kina me
siyar da Abinci a Restaurant kike tunanin Dangidan Dan Majalisar jaha Deeni zai so ki,ai ko
kansila Aamna bazai tayaki ba,ganinki kyakyawa Fara Wai zai sa samari su soki? Kinyi kuskure
Aamna,ai yanzu samari sai masu kudi suke Nema gidan da Suka gaji arziki,ai yanzu sai kana
da kudi ake rayuwa da kai,ke Dan Dakikiya ce tunaninki kyau Yana sawa a so mutum? Dan kina
da kyau har Shishigi kike Yi to ki sani samari sai dai su yaudare ki Amma yanzu duk munin

masu kudi Haka ake aure su,Talaka ma Bai son Auren talaka bare irin su Deeni masu kudi,Ina
Baki shawara ki fita Harkar Deeni ba ajinki bane.

Aamna tana tsaye sanye da Jean skert Blue da rigarta T-shirt fara tas me Rubutu Red a
Gaban Rigar An saka A&G Food Joint,ta Sanya pcap Red takalminta ma Red,ba karya Aamna
karshe ce a kyau,haskenta me kyau ba fari Kal Kal ba Amma fara Ce dai ba Wanda ya Isa yace
wankan tarwada ce,dole dai farar ce,Gashinta har gadon baya Baki wuluk,Ga Zararan gashin
Ido tare da kwantaccen Gashinta dake goshinta,Girarta wuluk me yawa,Hancinta me kyau bai
cika tsayi ba,Fuskarta ba doguwa ba baza Kuma ace Round face ba,Dan Bakinta gwanin
Sha'awa Karami with pink lips,Gata doguwa Amma ba can ba,ga Uban Hips kamar ita tayi kanta
komai nata me kyau,hakoranta kanana farare tas,Idonta dara dara, Mashaallah,Aamna baza ta
wuce 24years ba,Haka kanwarta ma Zuhra kyakyawa ce Amma ita chocolate ce kamarsu Daya
da Baba.
Murmushin takaici Aamna tayi Tace ai gaki Nan da Muni yayi Miki yawa Deeni zai kwasa ki
cinye Deeni please ta juya tare da komawa Kan bakin aikinta wurin masu siyen abinci,ita kuwa
Saratu Tsaki ta ja tare da Bude dalelleliyar motarta baka ta Shiga sannan ta fisgeta a Tamanin.

Sai 11pm ta tashi a Aiki ta saka After dress dinta me Dan kyau tare da rataya handbag dinta
tayiwa abokan aikinta Sallama ta wuce gida,Napep ta Shiga zuwa gida,can cikin wata Unguwa
ta masu rangwamen gata aka sauke ta a Kofar gidansu na Bulon siminti Amma ka rantse kango
ne baiyi Kalar gida bane,da Sallama ta Shiga da kyar aka samu aka amsa mata,Mama Wato
Aishatu ta Iske tana Daura Net a dakin babansu Tace Mama na dawo,Tsaki dattijuwar ta ja Tace
to sai me,idan da sabo ta Riga da ta Saba,Baba ta kalla Yana daki Tace Sannu Baba,da kyar ya
amsa,Kai Kawai ta girgiza ta wuce kitchen Nan ta Iske abincinta an zuba Mata Amma an barshi
a Bude baza a iya rufe Mata ba,ta Saba Kawai ta dauka tare da Fitowa sai ga Daya matar gidan
tunda dama gidan Haya ne,mutum Uku ne a ciki ko wacce mata da dakinta biyu da kitchen
Amma toilet Guda Daya ce du,Gaisawa Suka Yi Tace Maman Zeenat ya gida,Tace lfy Alhmdllh
da fara'a, dakinsu ta wuce ta Iske kanwarta Zuhra tana kwance a saman katifarsu tana chatting
da saurayinta Wanda zata aura Nan da wata daya.
Murmushi Aamna tayi Tace Zuhra Ana Shan love, Murmushi Zuhra tayi tana juyi Tace Aunty
Aamna an barki a baya wallahi,Soyayya tayi a rayuwa,Adam ne ke kashe Ni da zafafan
kalamansa masu sweet,Dariya Aamna tayi Tace na tayaki murna kanwata ke kin samu Miji Ni
kuwa kin barni nice Kuma yayarki gashi Mama da Baba sun tsaneni akan ban kawo musu
Wanda Zan Aura ba,Hawaye ne ya silalowa Aamna Tace why me naaa?why Me Zuhra? What
have I done wrong? Tausayin Yayarta ya Kama Zuhra Tace kiyi hakuri Aunty Inshaallah kema
Zaki samu miji very soon,Kuma Inshaallah su Mama zasu hakura su daina fushi da ke.

Kai Aamna ta girgiza Tace Zuhra Ni bazan iya auren Wanda bana so ba,da Zan Iya Dana
fitar da ko ma waye Dan na farantawa Iyayena Rai Amma idan nayi bazan iya yiwa Wanda
bana so Biyayya ba,Illar Hausawa kenan Allah Bai kawo maka Miji ba a takura maka karshe har
sai ka auri Wanda baka so,baza ka Dade ba za a sakeka,ko Kuma kullum ku Kare a fada da
sasanci,bana fata inyi aure na fito Zuhra,Nafi so ko wa Zan Aura ace Ina sonsa sosai sabo da
shine kadai Zan iya Masa Biyayya,kin San halina Ina da taurin Kai,Kuma Ni ba a iya tankwara

ni,So shi kadai ne zai sa nayi Biyayya,Kin San idan bana son mutum wallahi zanci ubansa
ne,Amma su Mama sun kasa fahimtata,Zuhra Tace ai ke matsalarki kenan Aunty akwai saurin
fushi ga rashin barin ko ta kwana,aure Kuma sai Hakuri,Hakuri na Kawai na auri Wanda nake
so ko jibga ta zai nayi kullum Zan zauna Kuma bazan ji Haushin kowa ba.
Mama ce ta fado dakin Tace Ina Jin duk abinda kuke cewa,ke Zuhra ki daina saurarar marar
hankali,ai yanzu ba auren kauna akeyi ba dubawa akeyi aikin mutum ake dubawa me yake
samu,zai Iya rike ki, ci da Sha shi ake kallo ayi aure,ke soyayya Zaki aura Zaki ci ubanki kuwa a
hannun maza,kika sake sai Namiji ya sa Miki ciwon zuciya,Aamna tace kinji ko Mama bakwa
duba Iliminsa da Addininsa Kawai kudi kuke dubawa ayi aure,Baba Yana ji ya tsomo Baki daga
dakinsa yace Ni ki tambaya Sanda na auri Uwarku ban taba ganinta ba Haka itama Bata taba
ganina ba Kuma gashi Muna tare har mun haife ku,wallahi Aamna kika sake Watarana sai na
koreki daga gidana,badan ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login