Showing 114001 words to 117000 words out of 146041 words

Chapter 39 - DUNIYA TA AMNA Complete Book By Asma Baffa .pdf

23 Mar 2025

11384

ma kusan gida Daya Mene abin damuwa? Ko kin daina so
na ne? Kai ta girgiza tace Ina sonka Mana yace to ki kwantar da hankalinki Muna tare Baki da
matsala,Humaira ta kwabe Fuska tana ta faman kallon Ahmad hankalinta a tashe da gani a
firgice take,gashi ance ita za a fara kaiwa,Meke faruwa ne Humaira? Humaira tana so ta fadawa
Ahmad me Mubarak dinta yace tana tsoro Kar ya Mata fada,Hannu ta Shiga yarfewa tace Yaya
dan Allah ka yima Brown magana,akan me? Uhmm...uhm....cewa yayi ....Ahmad ya gane
zancen Maganar first Night yayi ya firgita Masa kanwa,Murmushi yayi yace Jeki na gane Zan
masa magana karki damu Wasa yake, Humaira tana Hawaye tace Allah Yaya ba Wasa yake
ba,nifa na fada Miki sis Haba ko Baki yarda ba? Murmushi tayi tace na yarda,to shiga ciki kinji,
okay ta Furta ta tafi wurin Kawayenta da suke ta chashewa da kida a mugun wasu speakers
duk Yan Lagos ne Basu digon kunya ko ta minti Daya.

Ahmad a bedroom din Mummy ya Iske Aamna tana saka takalminta me tsini ta yafa
mayafi,Yana Shiga ganin ba kowa ya rungumeta Yana Jin dadi a ransa shi Kam ya Gama
dacewa,Mazaunanta ya shafa Yana sinsinar kamshinsa itama haka,kinyi kyau My world,ai ka
fini yin kyau My King,you are the love of my life,I give you all of me my king,Kissing dinta zaiyi ta
matsa da sauri sabo da kar shanye Mata jambaki,hand bag dinta ta dauka me tsada tace let's
go,a Haka Zaki tafi kalli fa Dan mayafin Ni gaskiya maza zasu kallar min Mata,Dan Allah King
kazo mu tafi wanne maza kalli fa Yan biki duk ba gyale, amma Ni na yafa ma gashi da girmansa
ya rufe fa har bayana,juya to na gani,mayafin ya gani ya Dan sauka yace to muje,tare Suka fita
Ana ta kallonsu duk inda Suka gifta,Su Tawaga tuni sunje can suna jiransa,gashi kowannensu
ya canja wanka,Angon wani milk yard ya saka Dan gaske ga skin din Tawaga Kamar wani Dan
Latin America Haka yake.

Ahmad Yana zuwa da Kansa ya fito ya zaga ya budewa gimbiyar tasa mota ta fito,Jakarta
tana hannunsa ya rike mata ko kunya Bai ji ya rike Mata Hannu ga Jakarta ya rike,Yar China ce
ta fito Daga cikin gidan da suke ta Sha gayu Aamna tace Yarinyar Nan tasan gayu fa Ina
ganinta wata shashasha,Ahmad murmushi yayi yace Ni dama nasan tasan me takeyi tunda
Tawaga ya sota zai aure ta,Yar China ta fito da Kawayenta can gefe Kuma masu Algaita ne da
ganguna suke faman kida me shegen Dadi,masu busa Kamar zasu cire kumatunsu,Yar China
ta biyasu kudi sosai ga ruwan liki suna Sha,ai Yar China tana hango Aamna da Ahmad tazo
wajen tana murmushi Tace Aunty kina ji Dani kinzo da safe kin dawo da Yamma wannan ko
kanwarki ce ni iyaka abinda Zaki Mata kenan Ina godiya da yawa da nayi Niyyar Yi Miki kyautar
dubu yanzu amma Ango yace na daina,idan an kawo Ni nayi farfesun Amarci Zan kawo
miki,Aamna tayi Dariya ita da Ahmad,Aamna a ranta tace Zaki bayani yarinya sai dai Ni na Miki
farfesun nazo jinya,Masu Algaita Suka taho Gaban Yar China angwaye abokai sunfi su Goma
suka fito da kudi za ayi liki,a tsakiya aka sa Ango Tawaga da Amarya Yar China,Mutane suna ta
kallo Ana nishadi,masu Algaita Tsayawa sukayi da kida Suka fara yiwa Yar China Kirari Ana ta
dariya suna cewa.

Lafiya Yar sarki jikar Sarki,kaga Yar na gada ba Yar na koya ba,gaishe ki Jikar sarki,Yar China
tana wani girman Kai an nutsu Ana Izza,cikin Kirari suka ce kayi dace saurayi samun Jikar sarki
ba Wasa ba,gabanki lafiya bayanki lafiya Jikar sarki,Hajiya Sadiya Yar Fulanin asali ta Ango
Aliyu Haidar sa gabanka inda kake so kayi dace...ka tsallake rijiya da baya...sai Suka ci gaba da
kida tare da busa algaita angwaye suka dinga fyalli da Naira,Aamna tazo tayi liki itama,ta likawa
ango da Amarya Yan dari biyar biyar sababbi sannan ta koma likawa mijinta,Iyalle ce ta fito da
sauran dangi suma Suka zuba nasu,Yar China tana murna ta rike Hannun Iyalle tace Iyalle ta
Dan Allah kiyi rawa,bikin Yar Chinanki guda,Iyalle tace Allah ya sauwake min da rawa,Iyalle da
sauranki fa birgewa zakiyi a Nan wajen,Iyalle tace ja'ira,Wai Ni Yar China Ina kika samo mutane
Haka ne? Yan Mata sunki karewa,Yar China tace duk kwayena ne kowa da yazo wajen Nan
Indai Ni na gayyace shi to ya sanni na shi babu wani gayyar sodi anan da kike gani,Iyalle tana
Dariya tace amma sun Miki Halacci,Kar ma suyi Mana nima idan na hadu da yarinya naci
ubanta,Iyalle ta furta Yar Nema to ayi sauri sunce 6pm Za'a Zo daukan Amarya sai an gama Kai
sauran amaren kece ta karshe,Yar China tace Dan Allah Iyalle a Bari Mana sai gobe a kaini a
nutse,kinyi kadan yarinya biki Daya zamuyi yau za a kaiki nasan halinki bakin Nan ba karewa

zai Yi ba ana Kara Miki kwana daya Zaki ce gobe yini su dawo,Dariya Yar China tayi harda wani
tafawa da Iyalle tace Iyalle kin San jikarki ai da Kun sake Kun Kara min lokacin alakoro to gobe
Dan asharalle ne zaizo,to Baki Isa ba yanzu ma ya kamata ku sallami masu Algaita,Na fa biya
kudi da su za a kaini suna bina da Algaita,Iyalle ta Bude baki tace dama Haka kika ce? Kwarai
Kuwa na biya kudi Ni ku kyaleni Dan Allah yau Daya bafa ba Kara Yi zanyi ba har abada,Iyalle
tace ai shike Nan ku karata ta tafi gida.

Yar China wajen Aamna taje ta ganta ta rike Hannun Ahmad Gam,Tace Kai Yar Mannau Dan
girman Allah ki kyale bawan Allah ya sake wannan azo dake Unguwa ai masifa ce wlh Zaki
jawo ya daina fita dake,Aamna tayi Dariya tace Wai ke Ina ruwanki ne kije ga sababbin
kawayenki can sun zo,Yar China ta duba ta hango su an sauke su a Napep,Hannu ta Shiga
daga musu su taho gata,Ahmad ta kalla Yana can suna magana da su Jibson Yar China Tace
wannan ba gata bane ka saketa wayo take maka zata kashe maka kasuwa,Dariya Ahmad yayi
ba tare da ya juyo ba.

Bash ne yace mu tsaya Kawai mu tafi da wannan Amaryar,Yar China Idonta ya kawo kwalla ta
koma wajen Tawaganta tace baza a Kara min alakoron lokaci ba? Kina gani dai Yan Uwanki
sunce sun fara shiri kina kallo duk kayanki har Wanda kika cire yau an Kai can gidan kice wani
Karin lokaci,Yar China Baki ta rike tace Yau naji mayu yaushe suka kwashe kayan? Tawaga
yace Brown ne fa ya Kai tare da Salamatu ai sunce tsinke naki babu a gidan Nan,sai kayan
jikinki sai Wanda Zaki canja yanzu,Yar China tace shike Nan karyata ta Kare yau kuma,Tawaga
yace na Gama gajiya ni maybe ma yau bazan iya ko motsa yatsa na ba idan na kwanta,Yar
China taji sanyi a ranta tace na godewa Allah ya gaji yau ba abinda zai min,Yan bakin ciki su
Habiba harda cewa wani Zan Sha zafi to suzo su gani ya gaji ma,tana Maganar zuci Batasan
ma a fili ta fada ba Tawaga yaji,Dariyarsa ya kunshe dama wayo ya hada mata sabo da ta
kwantar da hankalinta,su Habiba ne suka janye Yar China tazo ta shirya za a tafi kaita,Wanda
baza su je Kai Amarya ba sun Gama biki duk sun tafi kasancewar magrib ta gabato,Dangin su
Yar China kaf sunje sun ga gidan Yar China sun dawo da Santi suna mamaki.

Haka wasu kawayen duk sunje sun Sha kallo sun dawo dake wasu Yan Mata Yan Uwan Yar
China suna can sune suka Kara gyara gidan,kayan kitchen da kayan kyale kyale da Suka Kara
siyo Mata na dangi masu kyau Suka Kara a gidan, gidan Suka shirya Mata komai yanda zai
bada kala,komai a tsari suka Yi,Brown Kuwa shi ya maida Aamna gida ta wuce part din
Humaira sabo da Humaira aka fara kaiwa Basu da yawa daga ita sai Kawayenta su hudu,Suma
duk sune suka gyara gidan da komai,Humaira an sake saka Mata wasu kyalekyalen masu
tsada sabo da su akwai abin.
Itama Sameera lokacin da aka kawota sun sake zuba abinda babu da Kuma wasu abin na
bukata na Yan gayu tunda an Gama musu me wahalar, Bangaren Nafeesat Kuwa wow itama ba
karya sabo da Naira itama an Kara zuba wasu abin masu tsada musamman a kitchen,Ita
Babanta da babarta su Suka kawota dakin Miji su biyu rak sabo da Yar Malam ce,sai da yayi
Mata Nasiha,dama angwaye tun kafin bikin ya tarasu ya musu Nasiha sosai da sosai,Humaira
da Sameera ma daidai gwargwado sun Sha Nasiha wajen Iyayensu sannan aka kawo su.

Hafsat ce ta hudu da aka kawo da dunbun Yan Mata da Yan uwa,Basu Dade ba Suka tafi aka
bar Hafsat tana ta kuka Ita Daya tal,duk cikinsu Sameera ce Bata Yi kuka ba,Itama Hafsat ita
Daya tal aka bari ba ko mutum Daya dama su tuni duk gyaran gidan da zasuyi sunyi dama
komai a Leda yake ba abinda yayi Kura da kansu Suka bare komai Suka shirya Mata,Suma
abinda ya Dace zasu karawa Hafsat duk anyi komai ko wacce gidanta sai kamshi yake zubawa
Yana walwali,ko wanne gida a kasa 2 bedroom and Palo ne sai kitchen store da dining
area,sama Kuma 2bedroom and Palo shima ko wanne daki da toilet dinsa masu Fadi da kyau
gidan ya kayatu,kowa ya gani sai abin ya birge shi, compound din ko wacce yasha Interlock da
fulawoyi ga parking space,harda Dan wurin hutawa anyi wata rumfa ta haduwa da shuke shuke
ga wasu kujeru da table masu kyan gaske a wajen.

Yar China kawaye sun sata a gaba sai tsokanarta sukeyi yau zata gane kurenta,Dariya Yar
China tayi tace to algungumai ya gaji da yawa Angon yau bacci zaiyi yace ko motsi bazai iya ba
ta Allah ba Taku ba,Dariya Suka dinga kyalkyalawa Yar China Suna cewa wlh wayo ya Miki,Yar
China Tace bama wasan karya da Tawaga na,wanka tayi ta fito Suka kwashe kayan data cire
da komai nata Suka zuba a leda,wata kaza Salamatu ta kawowa Yar China kafin ta shirya aka
takura Mata sai da ta cinye,aka Bata wasu tsumin ta Sha,Salamatu Tace kayan maganin
tsuminki ki ya bedroom dinki an ajiye Miki su Safiyya zasu nuna Miki ki boye Banda hauka karki
Bari ya gani Kuma,Tace to tana shafa lotion bayan ta gama wata atamfa super aka Bata ta saka
dinkin Riga da skert sun kamata cif,Yar China ta tsula kyau,Atamfar Wata brown and red ta
tsaru ka rantse ma ba atamfa bace wani material ne daban,gashin da yasha gyara Yan matan
suka gyara Mata shi aka Mata wani acuci da shi Suka ce baza ta daura dankwali ba ai Amarya
za a Kai Mayafi zata yafa,Mayafi Kato Amma me sharara da kyalli mayafin ya hadu shi aka
bawa Yar China ta yafa sai ta fito kamar wata Yar India,takalminta me tudu Kalar mayafin red
Haka jakar ma,Habiba ce ta rike kayan da Yar China ta cire a Leda har Inner wears baza su
Bari ba sai an Kai gidanta,Kuma Iyalle ce ta sasu,Sallar Nafeela aka sa Yar China tayi tare da
adduoi,tana Idarwa taji ance motoci sun Zama Ready Amarya ake jira,Yar China tana Jin Haka
ta fara kuka Tace karyata ta Kare Ashe da gaske akeyi bikin Nan,Ashe ba karya bane kaini za
ayi wayyo Iyalleta,Yan Mata suka dinga ihu da shewa Ana dariya,Habiba tace masu Algaita ma
sun Zama ready suna mota sun shiga,Yar China Tace sunci Uwarsu Shegu dasu aka hada baki
za a kaini yau,mutane Suka dinga dariya itace fa tace sune zasu rakata da Algaita.

Wajen Iyalle aka shigar da Yar China Iyalle taga Yar China tana kuka sai itama ta fashe da
kuka tace bazan iya nasihar Nan ba naje daga baya nayi Mata a dakin mijinta,Yar China tana
kuka tace Iyalle ki min Nasiha Allah idan Baki min ba sai tafka tsiya gobe bazan Yi girki ba a
gidan,Iyalle kukanta ya tsaya cak ta bude Baki Tace Dan Ubanki karki girkin Mana yunwa ta
Miki Illa,Yar China tace dama Baki Iya Nasiha ba tsoro kike ji Kar a kureki Baki iya ba komai
ba,irin na mutanen da kike Yi,Iyalle maimakon Nasiha sai Suka bige da fada tace bazan Yi
nasihar ba Dan ubanki idan nazo nayi Miki ai zanzo ganin gida salamatu ku tafi da ita ana
jiranki,na fasa yin kukan rabuwar dake Yar banza fitsararriya cewar Iyalle, aka dinga dariya,Yar
China taji ance a tafi sai kuka ta dinga Shure Shure da burburwa ana riketa taki fita daga dakin
an rasa yanda za ayi da Yar China,tana kuka tana cewa Allah...Allah sai na fasa kofin da kika
siya min Iyalle,Iyalle tace kinwa kanki marar kunyar karya,ke Baki ji kunya ba duk bikin da kika

Yi kin koma kuka,ba fitsarar da bakiyi ba Ashe karamar marar kunya ce,Yar China kuka ta dage
Jin koshi ko kunya babu,babu Wanda Bai lallabata ba taki hakura ta tashi a tafi,Iyalle tace ku
jata ta karfi ku tafi,Yar China ta Dan Bude mayafinta ta leko tare da gallawa Iyalle harara ta rufe
fuskarta again,Iyalle Tace Zaki ci Ubanki Kuwa wlh ku Kira min Tawaga Angonta Yana Nan a
waje suna Jiran Amarya,ai Kuwa su Habiba suka tafi da sauri Suka Kira shi tare da fada Masa
Taki yarda ta fito tana ta kuka an rasa yanda za ayi da ita,Tawaga Wanda da shi za a dauki
Amarya yace gani Nan,su Jibson suna ta Masa dariya ya tafi gidan Haka ya kutsa har dakin
Iyalle,yaga Yar China a lullube ta dunkule tana kuka,tana Jin Muryarsa tayi Mukus tsoron
Tawaga take ji,duk haukarta tana nutsuwa idan ta ganshi,Iyalle tace gata Nan anyi anyi ta fita
Taki,Yar China tana shesheka tace Haka nace Miki bazan fita ba? ai dai bance ba ko daga nace
a Bari na huta,Iyalle tace to tashi ki bisu ko wallahi na Hana kowa zuwa rakaki ya dauke ki shi
da Kansa,tun kafin Tawaga yayi magana ma ta Mike ta cikin Mayafi ta gallawa Salamatu Harara
tace ai sai kuje ko.

Tafiya akayi aka sa Amarya a tsakiya,Sadiya tana kusa da Yar China ta Mata rada tace wai
Yar China Ina kika samo wannan guy ne? Kinga yanda har abokansa duk hadaddu,Yar China ta
daina kukan tace daga zagi wallahi,suna magana ai tana tunawa kaita za ayi gidanta sai ta sake
fashewa da kuka tace shike Nan Yar unguwarmu,ga makwaftanmu duk su Maman Yusrah
shiken nan ta sake sakin kuka angwaye suna ji,motar Ahmad da tafi ta kowa kyau Nan aka
shigar da Amarya da Kawayenta su biyu sun sata a tsakiya,Yar China tana Zama tace kudi na
Dana Tara a gidan Maman Yusra a karbo min abina na tafi da shi nasan kafin nazo Unguwar
Nan sai da tsohon ciki na Dan Allah Habiba karbo min Tawaga ba mutunci ya sani ba wallahi
ciki zai min da wuri,su Habiba suka dinga dariya Allah yasa Ahmad Bai shigo motar ba.

Haka suka je Suka karbi Mata dubu ukun ta duk akan dubu Uku take wannan abin,lokacin
Ahmad ya Shiga motar Ana karbowa yaji Amarya duk uban kukan ta daina Tace ku rike kudin
dubu ukun ku raba idan kun koma gida ku Siyo maltina da Madara ku Sha jininku ya tsatsafo
sabo da a bikin Nan Kun Sha wahala,Suka ce mun gode Amarya.
wurin motoci goma Suka Yi harda ta masu Algaita sun sauke gilasai suna ta uban hurawa
suna kida a motarsu an sasu a tsakiya,wannan algaitar ta jawo duk inda motocin suka wuce sai
an kalla babu tambaya mutane ke cewa wata Yar Sarkin ce ake bikinta,wasu suce kaga masu
abin Yar sarki ce wlh,Har aka Shiga Unguwar Wanda Basu je ba Suka dinga Santi,dayar kawar
Yar China Bilkisu tace Yar Chi na Kan uba wlh kin bar mu a baya Kinga Unguwar da zaku
zauna,lokacin kuka Yar China takeyi amma sai ta daina kukan tace ai Baki gama kallo ba sai
anje latinmu da gidana Dan Uwarki harda lilo,Ahmad Yana jinsu Yana ta dariya a hankali,Habiba
tace bayan biki da sati Daya zamu Zo cin abincin Amarya,Yar China harda dukan Cinyar Habiba
Tace rankem Zan Muku ranar shinkafa dafaduka zazzafa,suna ta dariya ta manta ma da wani
kukanta sai ta Bude mayafin sai ta Gama kalle kallenta sai tace uhm bari na rufe Ni
Amaryace,da taji su Habiba suna yabon wani wajen sai ta sake dage mayafin, sai da aka zo
gidan tace Kun gani ko sai kuka Kuma wayyo Iyalleta wayyooo.....duk sun cikawa Ahmad kunne
sun isheshi da surutu shi Aamnansa ma yake tunawa yanda kwalliyar yau ta Gama tafiya da
Imaninsa gashi ba sukuni bare yaje ya bada tukwici,a ransa yace Nima yau wani First Night din

zanyi.

Bayan an fito Amarya tana ta kuka, masu Algaita suna ta Yi duka sauran kawayen da Suka
rage Wanda suka kawo sauran Amaren sai da suka fito kallo Jin Algaita su kansu sunyi zaton
wata hamshakiyar Yar sarki Tawaga ya auro,aka sa tayi Addua kafin ta Shiga gidan da kafar
dama,can Bedroom din Ango aka kaita kowa Yana ta Santi Ana kallo,Aamna ta shigo gidan
itama,Mamakin Kukan Yar China ya kamata dama duk bikin Nan Yar China zata Yi kuka,Masu
Algaita sun Gama aikinsu motarsu Suka hau aka maida su gida cike da murnar irin kudin da
suka samu.
Mintuna kadan aka kwashe kowa aka maida su gida Bilkisu da Habiba Kawai aka barwa Yar
China,su ma Basu Dade ba su Mashkoor Suka tattaro kansu na kowacce Amarya aka maida su
gidajensu,Yar China taci kuka Lamar me,ita da Humaira sunfi kowa kuka,Aamna dai Ahmad
gida ya ja abarsa a matse yake, yace ba Wani Ango da zai raka,Jibson da ledojinsa na kayan
makulashe ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login