Showing 9001 words to 12000 words out of 146041 words

Chapter 4 - DUNIYA TA AMNA Complete Book By Asma Baffa .pdf

23 Mar 2025

11364

zancen Aure akayi Aamna Bata
kauna,Malamin Yana tauna goro yace Ashsha Aljan ne namijin dare ne wallahi take fama da
shi,Mama Tace biri yayi Kama da mutum,Baki Aamna ta Bude tana kallon Iyayen Nata,Malamin
yace yanzu Zan kwana Uku ba bacci Ina wani Aiki Amma dole aikin Nan kullum sai an yanka
zakara Guda Uku har na kwana Uku,Baba duk talaucinsa sai yace dama na samu wasu kudi
Nan take ya biya kudin zakaru tare da bawa malamin dubu goma kudin Aiki,yace Nan da kwana
Uku ku dawo ku karbi wata laya wacce zata soke ta a cikin gashinta,Fuska Aamna ta Bata
kamar zata saka kuka,Ace Allah Bai kawo lokacin Abu ba Amma Iyayen nata basa gani.

Suna Fitowa Kawu Ismail yace saura wajen Malam Kare Aiki,Wannan malamin sanatoci layi
suke Yi a Wajensa,Aamna ta girgiza Kai Tace Baba wallahi ba kyau,Wannan shirka ce baza a
fadawa Allah bukata ba sai Malam,Baba ya kalleta cikin duhun dare yace ai ke Aljanu gareki
sun aureki Bai ma dace a saurare ki ba sabo da ba a cikin hayyacinki kike ba,Yo ka biyewa
sakarai cewar Mama,Kawu Ismail yaci gaba da cewa inshallah Kuna komawa zata samu Miji
itama,Wannan malamin da suka je Wajensa Rubutu yayiwa Aamna a tafin Hannu yace lashe ai
magauta ne Suka mata asiri kuma makwaftan ku ne,Takaici yasa Aamna Tace Allah ya tona

muku asiri masu hada fada tsakanin Musulmai,Rankwashi Mama ta zubawa Aamna tayi
Shuru,Lashe Kawu ya furta Yana zaro Mata Ido,Haka ba a sonta ba Tace Allah na tuba bana
nufin kowa da sharri sannan ta lashe su Baba suna ganin Aljanu ne ke hanata Sha,Haka Suka
je wajen wani malamin shima yayi nasa sannan suka jira Bayan Kwana Uku Suka karbo duk
wasu Magungunan da aka hada Suka dawo ,Duk wani Rubutu da magani da Suka bawa
Aamna Kan tayi amfani da su sai ta samu jikin katanga ta zubar babu Wanda ya sani,Laya
Kuma Haka ta soketa da pin a gashinta sabo da kullum Mama sai ta duba gashin dole ta soke
Laya a gashinta.

Su Baba Basu Sani ba suna ta jira suga saurayi yazo neman Auren Aamna Amma Shuru,ga
Kuma bikin Zuhra yana ta gabatowa,duk sunyi Anko da Dinku Nan su na biki duk wani shiri da
za ayi mun Riga sunyi,Baba ya siyar da manyan shanayensa Guda hudu dake Kauye sabo da
Haka ba Harkar Talauci sunyi komai cikin rufin asiri,Adam Ango ya hada musu Dinner zazzafa
me kyau ranar Saturday,Sunday za a daura Aure a Kai Amarya,daga Aamna sai kawarta
Siyama bata gayyaci kowa ba,Amarya dai taci Uban gayyar kawaye wurin Dinner,Biki saura
kwana daya a fara Aamna tayi lalle da gyaran gashi,amarya kuwa ta Sha gyara sai sheki take
zubawa,dangi na nesa sun zo sai tsiya ake yiwa Aamna kanwa zata Yi aure ta bar
Yayarta,Haka suka Sha bikin Zuhra da Angonta Adam anyi an Gama lfy tare da Kai Amarya da
gararta,gidan Adam madaidaici ne me kyau harda gate yayi kyau gidan,ga Yar motarsa me
kyau Toyota,Itama Zuhra Baba ya Dage ya Mata Kaya masu kyawun gaske.

Ahmad Yana kwance a makeken Gadonsa Yana zuba bacci,wayarsa ta dinga ruru gashi ya
kasa tashi sai da kyar ya farka ba tare da ya Bude idonsa ba ya jawo wayarsa yaga number
Mummynsa dama ta fada Masa zata zo ta ganshi a kaduna ita kadai kasancewar
Daddy,Saddeeq da Humaira suna Saudiya Umrah,Cikin Muryar bacci ya Kara Wayar a
kunnensa tare da Furta Hello Mummy......Muryar Namiji yaji yace da Allah me wannan Wayar
sunyi Mummunan Hatsari Driver ya mutu ita Kuma tana asibiti da Allah ayi sauri azo,Firgigit ya
farka Yace what....?cikin gigita yace please fada min Address din Asibitin,Nan take ya fada
Masa,Da sauri Ahmad ya figi machine dinsa sanye da wando 3qutr da Riga t-shirt fara tas sai
asibiti,a gurguje ya fada ciki Yana tambaya aka kaishi Emergency Nan ya Iske Mummy Rai a
hannun Allah.

Aamna Yau da matsanancin ciwon Mara ta tafi wurin aikinta gudun kar a hanata kudinta cas
sabo da ba aikin Gomnati bane,a Haka take daurewa tun tana aikinta da karfin Hali har abin ya
fara gagararta,Siyama ta kalla tana rumtse Ido Tace Siyama dole Zan hakura da aikin yau
Hospital Zan wuce a duba min marata ya kamata ayi min scanning a gano min mene a wajen
Nan,Siyama da tausayawa Tace Allah ya Baki lafiya kawata a dawo lfy sai munyi waya,Aamna
ta daura After Dress a saman Uniform dinta Riga da wando ta fita tana tafiya a hankali ta Isa
bakin Titi tare da Shiga Napep zuwa Asibitin da suke ganin Likita idan lalura ta taso,asibiti ne na
Gomnati Amma ba laifi akwai kyau.

Tana rike da mara hankalinta baya jikinta tana zuba Uban Sauri tabi wani Corridor,Gaf taji
tayi Karo da mutum,wani kamshi me jarabar Dadi ya daki Hancinta,da sauri taja baya ko kallon

Wanda ta buge Bata Yi ba,shima Bai ko kalleta ba hankalinsa baya jikinsa,Bayan tayi magana
da wani Emergency ta nufa tana matse kwallar wahala gashi Bata fadawa kowa a gidansu
ba,Karo suka sake Yi da juna kamshin mutumin dazu ta sake ji ya cika Mata Hanci Kamar Kar
ta daina Shaka,Tsaki Yaja sosai yayi cikin Emergency Yana ta faman yiwa Doctors masifa,Yana
cewa a bani Mummy na dole ne,Ni Nace bana son wannan Hospital din me Araha,a bani Uwata
wannan so kuke ku kashe min Mummy a Asibitin Gomnati, Wallahi Mummy na ta mutum sai na
daure ku,wani babban Likita ne yace Haba Malam Ahmad kake ko wa? Da masifa yace karka
sake ce min Malam,Ni ba Malam bane,a masallaci ka ganni Ina Kiran Sallah ko Tafsiri kaga Ina
Yi? Idan zaka iya Call me king,Doctor yayi Murmushi sabo da daga ganin Ahmad kasan inda
tarbiyya take ma Bai nufa ba,Cikin tausasawa Doctor yace kayi Hakuri zamuyi Aiki iya yin mu a
samu ta farfado wallahi Matukar ba a Bata agaji ba ka dauke ta to kafin kaje da ita wani Asibitin
zaka iya rasa ta kayi Hakuri idan aka samo kanta sai ka dauke ta idan kaga dama ma ka tafi da
abarka China.

Aamna kwance take tana hawayen wahala Ana ta lallaba Ahmad Anki kulata,Cikin masifa
Tace da Allah ku rabu dashi azo a duba marata Likita mayu sun kamani sun min Ajiya a marata
watakil ma Tukunya ce a wajen ko wani karfen Kun zauna a wajen wannan muma ai ba daga
sama muka Fado ba Kuma Nan gaba Aure zamuyi mu haihu,muma Iyayen wasu ne,Wani
mugun kallo Ahmad ya aikawa Aamna sannan ya koma gefen Mummy ya zauna Yana cike da
tashin hankali,Likita Yana zuwa kanta yace Rannan anyi Miki scanning nace ciwon sanyi ne
dake sai kin dage da magani,Aamna Tace to ai har na gaji da maganin, wannan sanyi da naci
yake jaraba Kawai,kankara nake Sha ko me?Ni ba Yar Madara ba Bamu da ko fridge ace wani
sanyi,Ahmad sai lokacin ya kalli Aamna kadan tana kwance yace Doctor da Allah kazo wajen
Mummy na ka rabu da wannan rubabbiyar Sanyi ya Gama kashe ta mijinta shike nan sai asosa
Mata asosa,Aamna tunda ta kalli Ahmad Bata sake Kallonsa ba sabo da kyawunsa da wani
mugun kwarjini da yake mata,cikin lokaci kadan Doctor ya yiwa Aamna Allurai tare da Bata
magunguna,sai gata ta watsake ta warke yayin da Mummy itama ta farfado bayan likitoci sunyi
aikinsu,Ahmad sai murna yake Yi,Mummy ta sa Hannunta tare da shafa sumarsa Tace karka
fadawa Humaira da Daddy tunda naji sauki yanzu da ace akwai mace wacce zata kula Dani sai
ta zauna har a sallame Ni,idan za a samo min Yar Aiki ma Zan biyata kudin jinya cewar
Ahmad,Aamna ta dauki Handbag dinta ta wuce kenan taji Ana Neman me Aiki Sai gashi ta
dawo baya da sauri tare da tambaya Nawa za a biya Ni?


Mummy ta kalli Aamna sama da kasa Tace daga dubu Hamsim zuwa sama,Aamna ta Bude
Baki Tace yanzu idan yau na fara jinya aka sallameki gobe dubu Hamsim Zaki bani? Ahmad
yace kaji barauniya, Mummy ce ta kalli Aamna ta daga Kai Alamar ae,Aamna Tace Alhmdllh na
karba zanyi Bari naje gida nayo Shirin jinya,Mummy Tace a dawo lfy tana rufe Ido sabo da da
kyar take magana ba laifi Mummy ta Sha wahala.

Agurguje Aamna ta koma gida ko abinci bata ci ba ta sanarwa Mama komai,Baki ta tabe Tace
yo tunda kinki aure ai sai kici gaba da neman kudin tunda ke kudi ne a gabanki,Baba kuwa Baki
ya tabe yace ba abinda kika sani sai neman kudi to a dawo lfy dama bikin Zuhra ya cinye Mana

komai,ita dai Aamna kayanta ta bukata ta hada a karamar Akwati tayi wanka tare da yin Sallar
Isha sannan ta wuce Asibitin abinta,tana tafiya kamar Namiji sabo da Tace ta daina Zama ta
kirki.

Tana Shiga ta Iske Ahmad ya jibgo kayan ci da Sha da duk wani abin bukata,Kallon Aamna
yayi tare da galla Mata Harara cikin kallo na wulakanci,Aamna ta kalle shi itama tare da tabe
Baki ta shiga rera Waka lalatacce....lalatacce ne ko a gidan su,da sauri ya kalle ta ransa a bace
gashi ba damar fada Amma duk da Haka sai da Yaja Tsaki yace Talakar banza
barauniya,Aamna tace ae naji da me kudi da talaka ai duk Allah yaga dama ya bawa kowa,You
are very stupid....nayi magana dake? Ina wakata Zaki sa min ths your Smelling mouth,Mind
your fucking Business ya Furta da karaji Wanda sai da Mummy ta farka tare da dafe kanta,duk
abinda sukeyi tana jinsu, Nishi tayi Tace Son gobe a canja min Hospital wannan akwai sauro
gashi ba Ac,Ahmad Yana maganarsa ta Yan duniya sai kace wani Me wakar Raps yace comfirm
Mum,ki Dade kiyi karko and ki mutu AC Mum,Allah ya ja da nisan kwana,Mummy tayi Dan
murmushi Tace Ameen a hankali,Aamna ta kalla tace dauki katin Nan ki Siyo maganin da ba a
karasa siya ba,Ga kudi Nan a jaka ta,Aamna ta zuge jakar Mummy zata dauki katin da
kudin,Ahmad ya fisge jakar ya dauko katin tare da zaro kudi a aljihunsa ya Watso a jikin Aamna
yace Jeki,Aamna tayi murmushin bacin Rai Tace ba komai ta Eba ta fita,wurin siyen maganin
taje ta Mika katin wani yaro matashi ne a ciki Yace dubu Uku da dari biyu,Me bada maganin da
hantara yace ba canji malama,Dan Rainin hankali baza ki samo canji ba.

Aamna ta Bude Baki tana kallon yanda yake masifa,Kai Malam kayi hankali da Ni Kanwar
uwarka ce Ni da zaka dinga min magana Anyhow,Uban me kika Isa kiyi,Tas kake ji Aamna ta
zuba Masa Mari Tace fito mu Buda wallahi Naga baka da tarbiyya,Wanda suke wajen ne Suka
fito tare da raba fadan sannan Aamna ta wuce abinta ta siyo maganin a wani chemist dake
wajen Hospital din,tana masifa an fada musu Ina tsoron fada da Namiji,In cakwumi Namiji,inci
kwalarsa,muyi dambe ba komai ne a wajena ba,girman Kauye ce Ni,har yanzu da ragowar
Tuwon dawa a jikina cewar Aamna har ta Shiga dakin da Mummy take tana fada cewar in Balla
Namiji ba komai bane a wajena,In samu mutum in farke Masa makoshi Dan uban
mazaje,Ahmad ya bita da kallo sororo Yana mamakin mace da tsaurin Ido Haka,Tsaki Yaja yaci
gaba da latsa wayarsa.

Amma ita Aamna ta manta ma da wata marar lafiya take jinya taci gaba da cewa ko wanne
Namiji Dan iska,to Billahillazi girman Kauye ce Ni sai na soke mutum da kwalaba,Ahmad ya
sake zaro Ido a ransa yace tab Wanda ya auri wannan yayi bye bye da duniya kawai,irinsu ne
masu kashe mazaje,Aamna Ta fake da wayo tana zagin Ahmad Tace Dan Iskan mutum Dan
Kawai Yana da kyau da kudi ai muma Muna da kyan,ae munji mu talakawa ne sai akayi kaka?
Duk kudin mutum Dan ubansa malaikan mutuwa Yana Nan zuwa duk tsayin katanga da katon
gate haka zai haura ya zare ruhin mutum,abi duniya a Sannu,Duk wani shiga katuwar mota
Haka mala'ika zai zaro ran mutum,Wani mugun razana tayi sakamakon tsawar da Ahmad ya
buga Mata,shut up kina min Ihu akan maralafiya Zan fa barar dake,Zan Baki certificate wlh
watch your words,Mukus Aamna tayi a ranta Tace wannan shege ne shima.
Babu yanda Mummy Bata yi ba Akan Ahmad ya tafi gida Amma yaki yarda ya tafi Yana Nan

ya kafa ya tsare.

















AsmaBaffa
10/26/21, 8:51 AM - A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA🌵🌵







11-15









DUNIYATA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

NA KUDI NE

GA MASU BUKATAR SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE

ACCOUNT NUMBER TA
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

'YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39










Official







By
AsmaBaffa.







Page naki ne

FANCY HONEY

















Yana Zaune a gefen Mummy ita Kuma Aamna tana zaune a wata kujera,Mararta ce ta sake
murdawa da sauri ta rike mara tare da kwala Ihu Mummy sai da ta Bude Idonta,Da Sauri
Aamna ta samu gadon da ba kowa ta kwanta tana Nishi tare da Kiran Doctor,Likita ya shigo
yace to yanzu me jinya ce zata Yi Jinyar wata? Aamna tana cije lebe Tace zanyi Haka Kai Likita
ba ruwanka yawwa kayi aikinka Kawai wannan kudi Ina Zan bar shi,Dariya Likita yayi yace
Aamna kike ko? Tace no Amy karka sake ce min wani Aamna Aemy(Amy)Baki Ahmad ya tabe
tare da Bude wata Leda ya fito da manyan kwalaban giya masu tsada Yana korawa Abinsa
Yayin da Mummy take ta bacci,tana kwance ta juyo tana kallonsa bata Gane giya bace tayi
tunanin wani lemo ne me Dadi na masu kudi,tana ta Kallonsa tana faman Hadiyar yawu,Aamna
Tace Wanda yaci shi kadai shi kadai zai mutu,kafin ta rufe Baki yace da Ubanki za a sani a
kabari da? Aamna Tace wakata nayi fa,Nima ai wakar nakeyi ko na kulaki? cewar Ahmad Yana
cin magani kamar zaiyi Naushi.

Aamna ita kanta Tsoronsa take Yi Amma karfin Hali Irin nata yasa take maida Masa
martani,Mummy tana kwance tana numfarfashi tasan me yake Sha sabo da taji warinta,baya
kunyar uban kowa,sai da ya Gama Shan wacce zai Sha ya Mike Yana saka wayarsa a cikin
wani Crazy 3qurt Jean Kan Mummy ya shafa tare da furta Allah ya Baki lfy Bari naje gida nayi
wanka Zan dawo,Mummy Tace baza ka canja ba ko son so kake bakin cikinka ya kashe Ni?
Murmushi yayi Kawai sannan yace Zan dawo Mum yanzu 11pm Zan dawo a Nan Zan kwana,aci
gaba da Mana Addua Ina so na shiryu Amma Ina,A gabanta ya tsuguna,Mummy ta daura
Hannunta a saman sumarsa tare da furta Allah ya shirya min kai Ahmad,Allah ya maka Albarka
Allah ya tsare min Kai,Ameen My sweet Mum ya Furta Yana Jin dadi sannan ya Mike ya fita
Yana takunsa da wani takama da Isa kamar Dan sarki,Machine dinsa ya hau tare da Bude wuta
kamar zai tashi sama,Direct gidansa ya nufa ko da ya Isa gidan Toilet dinsa ya wuce ta Sha
gyara ya sakarwa Kansa Shower tare da wanka da wani liquid soap me tsada da kamshi,Bayan

ya Gama a gurguje yayi Sallar Magriba da Isha sabo da akwai Wasa da Addini,Yana Idarwa ya
daga Hannu sama Yana Adduoi tare da rokar Allah Allah ka Bawa Mummy na lafiya.

Yace cikin adduar Allah duk da ba Adduar Nan nake Yi ba kullum Allah Ni me laifi ne a gareka
ya Rabbissamawati Wal ard Allah ka yafe min laifuka na ka shirye Ni,Ina so na shiryu ya Allah
Amma na kasa ya Allah ka dafa min na shiryu,Allah kasa mu mutu Muna Musulmai masu
Imani,Allah karka Bari muyi maka shirka,Ka rabamu da Wutar Jahannama,Ka Bamu lfy da
tsawon Rai,Allah kasa nayi tsawon Rai Allah bana so na mutu da wuri ka ja kwana na,Ka rabani
da cuttuttukan zamani, ya Allah ka raba mu da talauci ka Bamu dukiya ta halak me amfani,Haka
ma ya yiwa Daddy da Yan Uwa da Musulmai,karshe yace yace Allah duk da ba damuwa nayi da
Mata ba Mummy ta tana so nayi aure Ya Rab ka bani mace ta gari me so na tsakani da
Allah,me Ilmin Addini Dana zamani,wayayya,ba Yar Kauye ba,Ya Rab zukekiya ko ko fara ko
light chocolate wacce idan na kalle ta kawai Zan washe Baki ba tare dana shirya ba,mace Yar
dagwas wacce ta Dan dire ta Dan baje daga kasa.
Har zai tashi sai ya koma ya sake daga Hannu sama yace Ya Hayyu ya Qayyum na kawo
karar Daddy wajen ka Allah kasa ya daina min fada kasa ya dinga so na,Allah kana gani dai
Tsoho Nan nawa ya tsane ni kamar ba a son ransa aka haifo Ni ba,to Allah Kaine ka halicce Ni
ya zaiyi Dani Allah kasa ya daina tsanata Yana gamawa ya Mike tare da zare jallabiyar da ya
saka domin yin Sallah,ya dakko gajeren wando wani me tsada iya gwiwa ya tsaya Masa me
Dan Fadi Yana da Aljihuna kala kala a jiki gashi Kalar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login