Showing 54001 words to 57000 words out of 146041 words
Chapter 19 - DUNIYA TA AMNA Complete Book By Asma Baffa .pdf
daya
ba,Ana ta kallonsu Dariya ta cika mutane Amma an kasa Yi sabo da mutuwa kowa sai ya bar
wajen yake Dariya,Wani Dan Majalisa yazo Ta'aziyya,Baban Jibson ya Kira shi yace ga babban
Dana can,Jibson ya karaso wajen,Dan Majalisa yace Sannu da Hakuri Allah yaji kanta yaro kayi
Rashi,Jibson yace Babban Rashi yau na tabbata Maraya Dan Allah ku bani mukami a Gomnati
na shugaban Marayu na Nigeria da Uwata ta mutu wallahi gwara Ubana ya wuce sau dubu
dubu,Danmajalisa shima abin Dariya ya bashi gashi da yanda suke Maganar abin Dariya ta Yan
maye.
Kudi ya zaro dubu Ashirin ya mikawa Jibson yace gashi ko ruwa a siyawa Mutane Jibson
yace Allah kiyaye na karbi bakin kudi,wannan bakin kudi ne tunda baka bani ba sai da Uwata ta
mutu zaka bani wanne amfani zasu min,Baban Jibson ya daka Masa Tsawa Amma Jibson yace
wallahi bazan karba ba,da karfi ya daga Murya Dan wulakanci sai da aka ga Uwata ta mutu
Za'a taimakeni duk an wani cika Mana Kofar gida Ana cinye Mana Dan abincin Daya rage
Mana,Dame zamu ji da cinye abinci ko da jimamin,kowa Yana ci Yana wani jimami,Mata Yan
Uwa suna kuka suna ta girki Ana Dora tunkunya Ana saukewa wallahi baza mu lamunci
wannan ba,Ahmad ya mike shima yace a barmu da abinda ya dame mu na rashin Ummati mun
gaji tun safe muke bi layi layi na mutane Muna rabon ruwan Sha da Abinci,Tawaga yace aikin
banza Muma Haka Dan kudin Sadakar da aka Tara Mana da abincinmu cikin sati Daya aka
cinye shi tas ga tarin Yara an mutu an bar min,Baba ya dinga aure aure ya Tara Yara Ashe duk
Haihuwar da akeyi Ni ake haifawa ban sani ba, wallahi da nasan hakane da kaina Zan dauki
matan Baba na kaisu asibiti Dan ubansu duk a daure bakin Haifarsu,yanzu ga Yara can sunfi
ashirin Ni kadai ne Babba Kuma ba Wani Abu ya mutu ya Bari ba gona ce Kawai a Kauye Guda
biyu.
Ina Shiga gida Yara suna zare Ido Yan kanana turagutsa ba Wanda zai iya aikin karfi to
wallahi a Nan ma tunda Ummati ta rasu Baba baza ka Kara aure ba wallahi ko wace zata aure
ka sai mun farke Mata ciki,Ahmad yace bazai yuwu Iyaye ku dinga aure aure Kuna mutuwa
Kuna bar Mana masifa ba,ga yanda kasa take ciki yanzu a mutu a bar maka Yara Kai kanka da
kyar kake iya rike cikinka, daga yau mun Zama masu yaki da Aure auren Iyayenmu maza,duk
tsohon Daya matsu zai Kara aure to ya Nemo juya wacce Bata Haihuwa ko Kuma aje a cire
Mata mahaifa.
Jibson yace Iya Ummati Abbi ya aura Amma Haihuwar ta Sha Uku Haba jama'a sai kace
macen Zomo, Guda Daya ne ya rasu Sha biyu suna Nan cas da me zanji gasu duk mata,ko
wacce na shiga Yaya kudin makaranta,Yaya kudin kitso,Ya..ya..ya...masu auren ma yau Fa'iza
mijinta ya hanata abinci ta dawo gida an auno Mata shinkafa ta tafi da ita,gobe Safiya mijinta ya
mareta ta kawo Kara,jibi Zakiyya mijinta ya korota to a gaskiya bazai yuwu ba,daga yau kunci
abincin karshe gobe ko koko ba me Fitowa da shi wallahi.
Mutane suna ji Ana ta kallo wasu suna zanzarewa Baba shima yasan Yaran sunyi gaskiya
tsoro yake ji Kar a cinye Dan abincin nasu su fada wani Hali Amma sun tozarta shi ya zaiyi dole
ya kyalesu tunda su suke siyo komai abokan,Ahmad kadai mota guda ya sauke musu ta kayan
abinci da safe,Haka duk abokan kowa iya karfinsa sun kawo tallafi daban daban,Kuma ko ba
mutuwa sune suke taimakonsu basa kukan rashi.
Ranar da akayi Sadakar Uku suka Kori kowa Suka ce Sunna sak ba zaman makoki ya
Kare,Ranar Bash ya tafi gida ya Iske Mamansa tana Aiki yace Mama Yaran naki Mu bakwai kika
Haifa Dan Allah Mama karki sake Haihuwa Haka,Mama ta kalle shi tayi murmushi Tace baka da
kunya Bashir Ni kake gayawa Haka? Wato ka Sha ta maka yawa zaka zo ka min hauka ko?
Bash yace Mama Naga darasi Yaran Nan Ni fa kuke haifawa kina ganin Yayana ba lafiyayye
bane yanzu nine kamar Babba gashi Mama da kuruciyarki,Dake ita Maman Bash sai ka rantse
ba ita ta haife su ba,Allah ya Bata kyan jiki karamin jiki gareta sai ka rantse Yayarsu ko
kanwarsu,Bash yace Mama gobe Monday ki shirya zamu je asibiti ki duba abokina,Mama Tace
Allah ya kaimu Bashir.
Washe gari da Sassafe Bash ya dauki Mama zuwa Asibiti,wajen Likita Mama taga sun
shiga,Bash yace Likita gata na kawo maka ita akan Maganar da mukayi,yace matarka ce ko
me? Kawai Bashir yace Matata ce, Maman Bash Dake akwai saukin Hali ba ruwanta yaranta
Kamar abokanta tana kallo Bash yace a Mata Allurar Family planning Haihuwar ta Isa
Haka,Likita yayiwa Mama tambayoyin da Suka Dace itama dama ta gaji da Haihuwar,Test aka
Mata Bata da ciki Nan Likita yayiwa Maman Bash Allurar wata biyu,yace idan time ya cika ku
dawo Karku tsallake,Bash yace an gama,ya figi Mamansa a Machine suka dawo gida,Kuma
Mama Bata fadawa mijinta ba sabo da Bash yace karki fada Masa kin San Baba Dan gargajiya
ne sai dai yaga Shuru kin daina Haihuwa,daga yau Haihuwa ta Kare a gidan Nan sun Isa Haka,
Mama tana ta dariyar su Bash.
Bayan Mutuwa ta lafa anyi Sadakar Bakwai Aamna yau kwana bakwai Bata ga Ahmad
ba,duk ta Shiga damuwa ta Kira wayarsa Bata shiga,Bata San mutuwa aka musu ba,Shi kuwa
Ahmad da dare Bayan sun Gama shaye shayensu da safe 7am ya koma gida, Mummy ya Kira
a waya, yace Mummy Ina cikin wani Hali,danki ya fada soyayya jiya jiya na gano cewar
Soyayya na fada,Farin ciki ya Kama Mummy Tace wannan wacce me sa'ar ce? Bata kawo
Aamna bace tunda yace wata ce tasan da Aamna ce zai ce Aamna ce,ta so ace Aamna
ce,Mummy Tace to itama tasan kana sonta ko me? Ahmad yace Mummy kwarjini take min na
kasa fada Mata,zuciyata idan na ganta bugawa takeyi,Mummy Tace karka damu Son ka cire
tsoro Kai fa Namiji ne ko wace kaje Ni na baka dama ka fada Mata duk irin son da kake mata,Ni
Mummy Umarni na baka ka furta Mata karka ji tsoro,ta dinga zuga Ahmad tana dorashi a Kan
hanya,suna Gama Wayar yaji wani kwarin gwiwar da Bai taba ji, yace Mummy ce ta bani
Umarni,wannan Umarnin Mummy ne naje na fada Mata.
Ai zumbur Ahmad ya mike sanye da 3qutr blue da Riga Armless wata white and sky,ba Wani
shiri ko wani wanka da canja Kaya na Kamala,lokacin zuciyarsa ta Gama tunzura, Kansa Kuma
ba Wani saiti tunda jiya an cake da yawa,7am da sassaffe ya tsaya a Kofar gidan su Aamna ya
Shiga dukan gidan Baji ba gani kamar zai balla musu gate,gaba dayansu a tsorace Suka yo
waje Baba,Mama , Aamna tare da Siyama sabo da ranar Siyama a gidan su Aamna ta
kwana,Baba Ne ya bude kofa,ko kulashi Ahmad Baiyi ba ya fada gidan a fusace da Masifa
hankali a tashe Yana Bala'i ya tsaya a Gaban Aamna Dake tsaye sanye da kayan bacci ya
nunata da yatsa da karfi a gigice ba nutsuwa Yana haki yace
Kin hanani sukuni...tun Sanda na ganki Bayan kin bar gidana kina shago...zu..zuciyata...ta
kasa sukuni...Dora Hannu yayi aka ya sake nuna ta da yatsa da sauri da sauri yake magana ba
kakkautawa Yana zaga compound din gidan Yana Wallahi na rantse.....ko idona na rufe bana
bacci fuskarki nake gani kina min gizo....kullum idan na ganki zuciyata bugawa takeyi...Ina Jin
tsoronki......ko yaushe bani da sukuni....burina kullum na ganki....ko naji muryarki.....bana...Bana
Iya motsi sai da tunaninki......komai nakeyi kece a Raina....kece.... kike min gizo....sunanki idan
aka ambata sai zuciyata ta buga.....Haka nake tsallakowa gidanku cikin dare in labe inyi ta
kallonki.....Rannan ma Dan karku kamani nayi muku basaja na sace muku startime da
Radio....Baba ya kurma Ihu tare da nuna Ahmad yace Kaine??......Ahmad Bai kulashi ba yaci
gaba da bayani....yace kusan kullum da dare sai na shigo gidan Nan na ganki baki sani ba....har
dakinki nake buya na Sha kallonki tsirara kin shiga wanka......da Ni kike rufe kofa a room Dinki
duk abinda kike Yi Ina kallo....kunya ta lullube Aamna ta sunkuyar da Kai kasa.
Ci gaba yayi da bayani yace duk abinda nake Miki Dan kiji Dadi nakeyi.... komai Danke
nakeyi....har zuwa shago Dan na ganki naji Dadi ne.....Yan....yanzu ma....zuciyata bugawa
takeyi wallahi Ina sonki....sonki nake Yi...da ban Gane sonki nakeyi ba sai yanzu.....Murya ya
canja Kamar me kuka ya hada zufa Yana haki yace Yan....yanzu....ma tunda nazo gabanki
zuciyata Bugawa takeyi.....idan Baki yarda ba taba kurjina kiji ya cafko Hannun Aamna ya daura
a kirjinsa saitin zuciyarsa yace kinji?...kinji?....Aamna Tace ae naji ta zame
Hannunta.....Siyama,Mama,da Baba suna ta tabe Masa Baki sabo da basa son abin,shi kuwa
Bata su yake ba ci gaba yayi da cewa Wallahi Allah Sonki nakeyi......idan Baki yarda ba Kira
number ta kiga sunan Dana saka Miki a Kan number dinki,Aamna ba musu ta latsa Wayarta ta
Kira wayarsa sai ga Sunan Daya sa Mata ya Bayyana MY WORLD.
Bai tsaya ba yaci gaba da bayani Yana tonawa Kansa asiri Wai duk cikin bayyana
soyayyarsa a gareta ne.
KARSHEN FREE PAGE
ASMABAFFA.
10/26/21, 8:53 AM - A Maryam: Pí ¼í¼µí ¼í¼µ DUNIYA TA AAMNAí ¼í¼µí ¼í¼µ
NA KUDI NE
DAN ALLAH KARKI FITAR DA NOVEL DIN NAN BADAN NI BA DAN GIRMAN ALLAH,
IDAN BAKI BIYA BA KARKI KARANTA DAN DARAJAR ALLAH.
DUNIYA TA AAMNA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.
55-60
Official
By
AsmaBaffa
Page naku ne mutanena Yan Albarka
UMMI DEEJAT
ALHUSNA
Yace nine....Nine.....Ni ....ya rasa me zai ce ma karshe yace Ni...dai Dan Allah Ina sonki
kinji....kinji....ya kafe ta da Ido Kamar zaiyi kuka,Mama ce tace ai taji ka kaje kawai....kallon
Aamna yayi yace na tafi kawai? Ae jeka cewar Baba,yace Kawai? Suka ce ae jeka zata baka
amsa daga baya,shi Kam tuni yaji zuciyarsa wasai tunda ya amayar da abinda ya dame shi sai
Kawai ya juya ya tafi abinsa zuciyarsa Kuma na tsoron amsar Aamna da zata bashi Nan
gaba,Haka ya koma hankalinsa ya kwanta ko Bata ce tana sonsa ba ya fada Mata sakon
zuciyarsa.
Gaba Daya ya samu su Mashkoor a gidan su Bash,yace to yau dai anyi ta Ta Kare yau na
bayyana Mata,Ihu Suka saki na murna tare da tambayar me Tace? Yace Wai zata bani amsa
daga baya,Tagumi Suka Yi Suka ce zaman makoki Bai Kare ba,Yarinyar Nan da raini take
kamarka kace kana sonta Tace wani sai Nan gaba ma zata bada amsa,Gaskiya Aunty Balaraba
Bata Yi ba sam,Nima Ina tsoron lamarin Nan cewar Mashkoor yarinya tsigigiya duk ta gigita
Mana Kai,Ahmad yace wallahi Ni kaina zagin kaina da kaina nakeyi,kullum sai na shiga daki na
tsinewa kaina sannan na fito,wannan abin tsinuwa ne Man cewar Tawaga.
Aamna kuwa Bayan ya tafi Mama Tace masifa wannan wanne irin tsagera ne Haka ba ko
kunya bare Kara,Baba yace Yaran karshen tashin alkiyama ne in Banda tambadewa kai
mtswww Baba Yaja Tsaki,Siyama kuwa ranta yau idan yayi dubu ya baci,kallon Aamna tayi Tace
Kar dai ki Kai kanki hallaka wallahi,Mama Tace Idan taje ya kasheta ai ita ta huta da Duniya
Dan wannan zai iya yiwa mutum yankan rago,Aamna ce ta kalle su Tace ba Wanda zai fada min
abinda ya kamata nayi,Ni matar aure ce Kuma matarsa,sannan Ni na San dai dai sabo da Haka
ba sonsa zanyi ba taimakonsa zanyi na taimaki Iyayensa idan ya shiryu shike Nan sai na
barshi,Zuhra ce tayi Sallama ta shigo ta Iske zancen, Siyama tana tabe Baki tana bada
labari,Zuhra tayi murmushi Tace mashaallah Alhmdllh,Ke Aamna wallahi idan Zaki so abinki ki
so shi tsakanin da Allah,ba'a Wasa da zuciyar mutum musamman Daya zurfafa Haka wallahi
idan kika yarda bayan kin San ba sonsa kike Yi ba wallahi Kinga yanda yake zai iya
komai,mijinki ne ki so abinki ki koma ki zauna lafiya,ke da Allah ya taimakeki ma iya shaye
shaye ya tsaya baya Neman Mata da sauransu,karki Raina Masa hankali baza kiji da Dadi ba
na Nan gaba,kiyi amfani da ilimin.....ke dalla rufe Mana Baki banza Shashasha cewar Baba,so
kike ya kashe ta,ai Ni abinda nake so yanzu ta Amince Masa Kamar gaske sai mu samu mu
dinga zarar kudi a jikinsa inda ya makance a kanki Haka nasan har aikin hajji sai ya
kaimu,Zuhra Tace haba Baba haba Bai kamata ba,zuwa Makkah Dole ne?, Kuna cikin rufin asiri
Iyayensa sun Gama muku komai a rayuwa,Baku da Muhalli Suka Baku Muhalli,Muna cikin
talauci Suka fitar damu daga wannan gashi Kuna cikin rufin asiri,ci,Sha,sutura duk kunfi karfinsu
Amma Baku godewa Allah ba.
Dan Ubanki wanne rufin asiri ko motar Hawa bamu mallaka ba cewar Mama,Siyama Tace ai
Kar ma ta wani koma gidansa,Aamna Tace Ni dai ba Wanda zai koya min komai,Kuma bazan
taba karbar kudinsa ba ku daina sa rai,Nima ba gidansa Zan koma ba,Zan dai Amince Masa
Dan na canja shi na taimaki Iyayensa badan komai ba sabo da Haka kowa ya Adana
kalamansa,Zuhra tace to kuwa wallahi Baki tunani ba Kuma wallahi Ni na fada Miki sai kinyi da
na sani Kuma sai kinyi kuka da idonki,Karki bada kofa aci kudinsa Kuma ki so shi ki kula da
mijinki Aamna meke damunki haka? Allah ya gani na Baki shawara duk Sanda kwabarki tayi
ruwa karki zo inda nake,Baba yace ai ke dabba ce Zuhra,Siyama Takaici yasa ta Mike ta tattara
nata ya nata Tace Idan kin tsaya ya kashe ki ke kika jiyo Nan gaba Zaki ga amfanin shawarata
karki biyewa Su Baba sabo da karki fada sonsa,sannan Kuma karki dauki shawarar Zuhra,Baba
yace kaga Munafuka Dan Ubanki sai munci kudinsa Kuma baza ta bi shawararki ba tamu zata
bi,Kuma karki sake zuwa Mana gida algunguma,Siyama tayi waje cike da kunci,Zuhra ta mike
tace Aamna a buga game lafiya Allah yasan me gaskiya,Baba yace koma dakin mijinki Dan
ubanki,Aamna ta Mike Tace Ni ra'ayina zanyi ba shawarar Wanda Zan dauka,Baba yace Zaki ci
Uwarki Sumayya ta lahira,dama bakin halin Ubanki kika gado Wanda ya gudu ya barki,marar
gata marar cikakken asali tunda Ubanki guduwa yayi ya barki,Tambadaddiya cewar Mama.
Bayan Kwana biyu Ahmad shi kadai a katafaren palonsa Yana Zaune Yana kallon wani
wrestling,tun ranar da ya furtawa Aamna Bata neme shi ba shima Bai nemeta ba har kwana
biyu,Wayarta ta dauka ta fito tsakar Gidan can ta baya ta Kira Ahmad,Yana Zaune yaga Kiranta
ya shigo,zuciyarsa ce ta Shiga lugude Haka dai ya daga,Yana dagawa ko gaisawa basuyi ba
Tace Amsarka Yes na Amince Ina sonka Nima,tana Gama fada ta kashe Wayarta cike da kunya
tana ta wani murmushi ita kadai,Shi kuwa tsalle ya buga tare da Kiran Mashkoor a waya,Yana
dagawa yace Tace ta Amince tana so na,Yeeee....Mun lashe zabe Mashkoor ya furta Yana kuri
yace ta Isa Tace Bata sonka ita din banza,haba Fesh King irinka ai karya ne,Ahmad Yana kashe
waya ya Kira su Jibson Daya bayan Daya yana fada musu Suka ce Dole ayi kamarin party yau
a gidan Mashkoor karfe 10pm na dare za a fara.
Mummy ya Kira tana dagawa yace Mummy ki tayani murna ta Amince tana so na,Dariya
Mummy tayi yanda taji Danta ya zauce Tace na tayaka murna Ahmad,yace thanks Mum,suna
gamawa ya Kira Humaira Nan ma ya fada Mata,ya Kira Mufida matar Kaninsa Sadeeq ta dinga
tsalle da Murna Saddeeq Yana kallonta yace kin haukace kema ai, Saddeeq da Daddy kuwa ko
kulasu baiyi ba Basu San ma me ake ciki ba sai da Mummy ta fada musu,Daddy Baki ya tabe
yace wannan mahaukacin Ina zaiyi wani hankali ai Ni na hakura, Saddeeq yace wlh kuwa
Daddy,Harararsa Mummy tayi sannan yayi Shuru.
10pm su Ahmad aka Sha wanka gaba dayansu ba Wanda Bai kure wanka ba aka tafi party
gidan Mashkoor anan suka taru harda wasu abokan daban an gayyato su tare da Yan Mata
zuka zuka,ranar Giya da kwaya taci kwal ubanta,ansha kida Wanda zasu Iya rawa sunyi har
kusan Asuba Ana Abu daya.
Musa kuwa ya tafi ganin gida Kauye Bai San me ake ba,Bayan komai ya lafa Ahmad baya
Kiran Aamna Sam,sannan Kuma tunda ta Amince Bai je wajenta ba,sannan ya dawo da sa
kana Nan kayansa kamar da,Shaye shaye ne dai dama tunda tunaninta ya sashi a gaba ya Dan
rage kadan.
Aamna kwana biyu taji Shuru sai Kawai Tace Bari na bashi mamaki,5pm ta fito ta Sha uban
wanka cikin wani Fari da bakin material cikin na lefenta me kyau da tsada yasha uban dinki
Kamar Readymade,tayi kyau kamar a sace ta,Takalminta me tsini da jaka bakake,Mama Tace
Ina zuwa Haka? Karya Aamna tayi Tace gidan wani bikin kawar mu zamu je da Siyama,Baki
Mama ta tabe tare da Furta shine harda uban gayu Haka idan wani ya tareki a hanya yace Yana
sonki fa? Shuru Aamna tayi Tace sai na dawo tayi waje,Already me Napep din data Kira Yana
jiranta a kofar gida,Shiga tayi Suka