Showing 48001 words to 51000 words out of 146041 words

Chapter 17 - DUNIYA TA AMNA Complete Book By Asma Baffa .pdf

23 Mar 2025

11423

ba da tsohuwar bazawara kika Yi Kama wacce
mijinta ya Dade da rasuwa,Mama ta bude Baki Tace Wai ni na sace maka ne wannan wacce
masifa ce akan Dan abinda Bai Kai ya kawo ba,Idan kinji haushi yau ki biyani cewar
Baba,Mama Tace Zan biya ka Amma kaje Nima Allah ya isa,Baba yace ae ki biya naji Allah ya
Isan.
A ranar Mama ta aika aka siyo Mata sabuwar Radio da Startime,Baba yace kin taimakawa
kanki.

Aamna cikin wata doguwar rigar lace ta shirya sea green and milk ,takalminta,Mayafi da jaka
duk milk tayiwa Mama sallama Mama Tace Yau ki dawo karfe biyu sabo da Zaki Mana wanki,to
ta furta tare da ficewa zuwa Kantin,tunda taje take jiran Ahmad Amma Bai zo ba har 2pm
lokacin ta rufe shagon ta wuce gida,20mnt da tafiyarta lokacin Ahmad ya Sha wanka cikin wata
sabuwar Jallabiya me tsada ruwan zuma Kamar yanda ya Saba ta tsangale Masa,Takalminsa
ma ruwan zuma yayi kyau tare da daura agogonsa me tsada,Sabuwar kitson calabarsa ya

gyara tare da Kama ta yasa Black band ya daure ta a tsakiyar kansa,wani uban kyau ya sake
tsulawa, Mashkoor Yana ta zugashi yace ai dole ma ta rude,Kaga Handsome,shi Kuma a
Gaban mirror ya tsaya Yana kallon kansa sai da ya Gama yace yau ba sauki bazan kalleta ba
karta ce Wani sonta nakeyi, Mashkoor yace Good ka ja ajinka ba yanzu ba kwaila Kar ta Raina
mu,da Masifa Ahmad ya furta wace Kwailar dan Uwarka? Ya bi Mashkoor zai ci ubansa
Mashkoor ya gudu daga room din Yana dariya.

Kwafa ya ja ya fito tare da hayewa machine dinsa ya fita sai shagon Aamna Amma sai ya
ganshi a rufe,Wanda ke siyar da takalma a kusa ya tambaya yace Ina me shagon Nan? Yace
yanzu ta rufe tafi gida naji tana cewa zata Yi Aiki ne,Okay Kawai Ahmad ya Furta ya hau
machine dinsa zuwa gidan su Aamna,har cikin gidan ya shigo da Machine dinsa,Aamna ya
hango a jikin tap da tarin uban wanki a gabanta na Mama Dana Baba,Sanye take da Vest fara
da Skert din atamfa wata maroon,gashinta har gadon baya Bata daura dankwali ba tana ta
fama,Mama zaune take tana hutawa Kawai abinta tana ganin Ahmad ta Bata Fuska,ya manta
ko Sallama baiyi ba ya karaso da Izzarsa yace Mama Barka da Rana,Baki Mama ta tabe Bata
amsa ba Tace sai ka koyi Sallama sai na amsa maka gaisuwar taka,Baki ya tabe tare da yin
Sallama ciki ciki ya kumbura Baki Kamar me shagwaba,Mama ta amsa tana hararsa sabo da
bakin ciki,Juyowa Aamna tayi tana ta Kallonsa yanda yayi kyau,Murmushi tayi Tace Kawana
Sannu da zuwa,Ahmad yace kawa ya Hanya,Lokacin Baba ya fito yace yau me Zan gani bayan
auren da kuke da shi kun sake komawa sababbin kawaye Kuma? Mama Tace tayani jin sabon
salon bariki, Ahmad Bai kulasu ba tunda wacce yazo wajenta tana Nan Ina ruwansa.

Mikewa tayi tsaye suna facing juna juciyarsa sai bugawa takeyi duk sai ya nemi kwarin
gwiwarsa ya rasa,a hankali yace wanki kike Yi me uban yawa duk ke kadai,Aamna Tace ae ya
na Iya,Kallonta yayi da azababbun Idonsa masu narkar Mata da zuciya yace Bari na
tayaki,Aamna tayi Dariya Tace Kaine ka Iya wani wanki kalle ka fa ko Sabulu ai baka iya
wankewa ba,komai fa Yi maka akeyi,Nifa super Man ne Ina da karfi da kike gani na har noma
Zan iya zuwa gona nayi,Zan Iya nome Miki gonar data fi girman gidana lokaci Daya,karfa ka
Sha wahala,ya nuna Kansa yace Wasa kike Dani,Aamna ta Mika Masa kujera ya kalli kujerar
yace ba Aiki kike so ba sai kace wata mace na zauna a kujera Allah kiyaye a tsaye Zan tayaki
kawo bucket ki gani,Baba da Mama Suka saki Baki suna kallo suna Jin haushi su Kuma gashi
Basu Isa su iya ko Masa Maganar banza ba.

Bucket Aamna ta kawo Masa har biyu ya nannade Hannun jallabiyarsa dake me dogon
Hannu ce,agogonsa ya cire ya ajiye gefe,Yace Ina kayanki a nan? Aamna ta Tace ka gansu a
nan,yace Miko ta kansu Zan fara,ai kuwa ta kwaso ta bashi a gabansa kala hudu sai su Hijab
da Vest yace idan an Gama sai kije ki cire na jikinki suma a wanke su yau baza ki kwana da
Kaya masu dirty a gidan Nan ba,Baba Yana gefe yace Uhmmm.....Sun kasa magana suna tsoro
Dan kwaya ne sai ya birkice musu yanzu.

Ahmad wanki ya fara baya wanki Yana wanke kala Daya Hannunsa ya fara Dan fashewa
Amma ya maze yaci gaba da abinsa,Kugunsa ne ya fara ciwo sabo da sunkuyo amma idan ya
Kalli Aamna sai ya fasa mikewa ya huta sabo Kar ya Gaza,Haka ya wanke kayan Aamna fes ya

kwashe kayan Baba da Mama Yana tayata suna wankewa ya kusa wanke na Baba,Mama ganin
banza ta Fadi sai tace ke Aamna tashi ki barshi ya karasa wankin ki Shiga kitchen ki Mana
girki,Ahmad yace ya Zaki ce ta tafi? Mama Tace Kai kace Super Man ne ai sai ka karasa ita ta
Mana girki, to Aamna ta furta ta tafi ta bar Ahmad,tana tafiya ya Mike tare da dauraye hannunsa
ya kwashe Takalminsa a Hannu da agogonsa da wayarsa,Mama Tace ya zaka daina aikin,dama
yayi masifar gajiya,da masifa yace Ni na gaji bazan iya ba dama na gaji yayi tafiyarsa da
sauri,Mama tana Kai...Kai....Amma ko juyowa baiyi ba ya hau machine dinsa ya bar gidan.

Mama da masifa ta shiga wurin Aamna Tace to ya gudu sai ki Koma ki karasa yace ya gaji
shi,Dariya abin ya ba Aamna dama tasan karfin Hali ne Kawai Haka ta fito ta karasa Mama tana
ta masifa taje taci gaba da aikin girkinta.
Ahmad kuwa a gajiye ya shiga gida Yana dafe Kugunsa ya Iske Mashkoor Yana kallo,Yana
yatsina Fuska ya zare rigarsa daga shi sai Singlet da gajeren wando ya fada saman kujera
Yana bawa Mashkoor labari yace yau wanki na tayata wash...bayana...taimaka ka siyo min pain
killer a chemist kazo kayi min gashi da ruwan zafi wayyooo bayana My waist Yana magana da
kyar yace yatsuna sun fashe ....Ni..Ni...nine nace Super man ne Ni, Mashkoor ya dinga dariya
yaje ya siyo Masa ya dawo tare da hado ruwan zafi ya dinga gasa jikin Ahmad,shi Kama sai
Kara da wayyo,Kwana Uku Ahmad Yana jinyar jikinsa kafin ya warke ya dawo normal lokacin
Aamna Bata ganshi ba.

Yau Juma'a cikin sababbin dinkunansa yasa wata farar Shadda kamar ka sace shi yanda ya
zuba kyau,calabarsa ya daure ya shirya Yana kamshi, Mashkoor ya kalle shi yace ban taba
tunanin zaka ja Ni cikin Harkar Nan taka ba,kwana Uku ko Kofar gida ban leka ba wannan
wacce masifa ce Wai,Gemunsa yake tajewa Yana shafe shi da wani turare Mai kamshi yace Ni
fa na fara gajiya da Harkar wani Kawa da Abokin Nan ya kamata ta San me nakeji a
Raina,Mashkoor yace ka bani dama Ni naje na fada Mata kana sonta,Baka da hankali an ce
maka sonta nakeyi Kuma ko sonta nakeyi wani ne zai fada Mata Ina sonta ba Ni ba,ai Ni abinda
nakeji a Raina game da ita Zan fada Mata ba Wani love ba.

Mashkoor yace to yanzu fada Mata zaka Yi? yace ae direct Zan sameta gaba da gaba na
fada duk irin abinda zuciyata takeyi idan na ganta yau yau din nan,Allah ya bada sa'a cewar
Mashkoor,Fita yayi abinsa Musa me Gadi Yana a dawo lafiya ranka ya Dade,Ameen ya Furta
yiyiwa Machine dinsa key ya fita zuwa Shagon Aamna,tana tsaye tana sallamar wata ta siyi
kayan kamshi ta hango shi yayi parking,Murmushi tayi Tace Sannu da zuwa,Kasa magana yayi
sai kallonta yake Yi har ya karaso inda take ya tsaya a gabanta daf da ita Kamar zai shige
cikinta Kuma ya Bata Rai zuciyarsa ce Kawai take bugawa,kasa fada Mata yayi yace ya gida
fuskar Nan a daure,Lfy Alhamdulillah ta furta tare da cewa shigo ka zauna Rana,shiga yayi
Yana ta Fushi,Tace fushin me kakeyi yau Haka? Kadan ya kalleta Bayan ya zauna a farar kujera
yace da zuciyata nake Fushi ita nake nunawa bacin Raina,Dariya ce ta Kama Aamna Yana ta
kallonta a ransa yace kin cuceni zuciyata bazan yafe Miki ba Kuma yau Bari na koma gida sai
kinci ubanki,Me ta maka zuciyar Aamna ta tambaya yace Ni kadai na San irin wulakancin da
take mini Amma ba komai Yaja kwafa,Aamna ta sake kecewa da dariya Tace kana da abun
Dariya wlh,Kawai sai ran Ahmad ya baci shi ga abinda ya dame shi ya fada ya kasa fada duk

akan Aamna Dan rainin hankali ta sashi a gaba tana ta dariya,a ransa yace na koma ma abin
Dariya na koma Comedian ba komai yayi Shuru.

Har ta Gama dariyar ta dakko Gyada soyayya Tace ga Gyada muci,ganin tasa hannnu a
Ledar ta Eba tana ci sai shima zai Eba Aamna Tace tsaya na bare maka,bare Masa tayi Guda
biyar ta zuba Masa a tafin Hannu Tace to ci,kallonta yayi sannan ya zuba a bakinsa Yana daga
zaune Yaja baya yayi wani tangal tangal Kamar zai Fado Aamna ta rike kafadarsa da sauri tana
tambaya lafiya???yace Dadi ne ya kwashe Ni sabo da hannunki da ya shafi jikin gyadar
nan,Dariya Aamna tayi Tace Kai Ni nayi zaton ma wani Abu ne,wani English novel ta dakko na
love tana karantawa Tace ka San littafin Nan? Na Mene ya tambaya? Love Novel ne Baki ya
tabe yace sai ku wannan ai,Mayafinta ne ya Dan zame kadan gashin Gaban goshinta ya
bayyana wani yala yala,Hannu ya sa tare da jawo mayafin ya gyara Mata Aamna dai mamaki
yake Bata kamar ba shi ba,duk irin kiyayyar Daya nuna Mata tana ina ne? A ranta Tace Anya ba
Yana da manufa a kaina ba kuwa? Gaskiya Zan nemi shawarar Siyama.

Kiran Sallah aka kwala Sallar Juma'a,Aamna ta kalle shi tace yanzu za'a fara khuduba sai
muje Sallah ko? Da sauri ya girgiza Kai yace a gida zanyi anjima,Jam'i Yana da Lada fa? Yace
na fiki sani ai, kin San kuwa Islamiyya Nawa nayi a duniya? Kin San saukata Nawa? Aamna
Tace Dan Allah muje tare,a ransa yace Yarinyar Nan fa zata fara juyani karka sake wannan Yar
tatsitsiyar ta juyaka a banza,ai ba sonta kakeyi ba da har zata juyaka,wata zuciyar tace Amma
idan kaje Sallar zata ji Dadi zata samu farin ciki,Kumatunsa ya Mara a hankali yace Kar ka Bari
ta juyaka ka dawo hankalinka,mikewa yayi yace Zan tafi,Tace Nima tafiya zanyi zanje gidan
Zuhra,yace kin fiye yawo to na fasa tafiyar Zama ya koma yayi Dole ta zauna,Lokacin Sallah
yayi Yana kallo tayi Alwala tayi Sallah a Nan shagon,tana idarwa yace Sannu da kokari,Fuska ta
Bata tace Dan Allah kayi Sallah Kar lokacinta ya wuce,Shuru yayi Kuma yaki tashi sai yaga tayi
Fushi ta zauna,Fuskarta ya leka kadan a ransa yace akan Haka har tayi fushi,Bari to na Yi
Amma badan fushinta ba,Mikewa yayi tana kallo yayi Alwala ya Tada Sallah murna tayi ta saki
ranta ta juya tana kallonsa a nutse yayi sallarsa kasancewar Bai Sha komai ba,Yana idarwa ya
Mike ya fice tare da tafiya ko Sallama bai Mata ba.

Mashkoor kuwa Yana can a gidan Ahmad tare da su Jibson gaba Daya Yana ta Basu labari
yanda Sarkinsu ya lalace,duk sukayi tagumi suna jimami,Jibson yace ai kuwa sai munje har
inda yake tayata siyar da citta mun kure shi,yanzu King ne ya lalace Haka abin haushin Akan
wannan Yar Yarinyar Aunty Balaraba cewar Bash,Mashkoor yace yanzu idan kaga shigarsa
Daya canja kamar Limamin masallaci,Salati suka saki Tawaga yace duk akan Yarinyar nan lallai
sai munci ubanta kuwa tunda ta mayar Mana da King Haka, Mashkoor yace Uhm Baku gani ba
har wani sharemu yake Yi ba Amma muyi Masa Uzuri ai King ne sai abinda yace,Allah sarki
masu shaye shaye da hankalinsu sun San Amana da abokantaka duk abinda dayansu ke so
suna so,sannan basa mantawa da Alkhairi da zaman tare,shi yasa sun Shaku da juna sosai.

Ko da Ahmad ya shigo ya Iske su tafawa sukayi ya haura sama,Yana shiga wayarsa ya
dauka tare da Kiran Sis dinsa Humaira,Humaira Tace Yaya na? Ya kake? Ba lafiya sis Dan
Uwanki ya fada cikin bala'i,Humaira ta tsorata sabo da Bata taba Jin yayanta Haka ba,Kamar

zata Yi kuka Tace Yaya mene ya sameka? Sis wata ce Nan idan na Ganda zuciyata kamar zata
fito ta fado,sai ta dinga Yi min kida me zaki,Humaira Tace Kamar ya? Yace idan fa ban ganta ba
bana iya bacci,sai na ganta nake samun nutsuwa,Haka idan naji muryarta sai naji Kamar wani
kidan goge sabo da Dadi,gashi tsoronta nakeyi sai naji na kasa fada Mata me nake ji,Yanzu ya
zanyi? Humaira tayi zaton zaice Aamna ce Amma yace Mata wata,Amma duk da Haka tayi
murna yayanta ya fada soyayya,Tace Yaya kaje ka sameta karka ji tsoro Kawai ka fada Mata
me kake ji,ka daure Haba Yaya kamarka wace zata ce baka Mata,Sis Nifa ba sonta nake Yi ba
Kawai dai Ni na fada Miki abinda nake ji,Humaira tayi Dariya tare da furta ka fada Mata karka ji
wani shayinta kaji,yace to sis Zan gwada ya kashe wayar,lokacin da yayi wanka su Jibson sun
tafi sai Mashkoor sai shi.

Ahmad dakin Aamna ya Shiga Wanda ta bari,cikin kayanta data Bari ya zabo wani Mayafi
Baki ya fito Palo wajen Mashkoor tare da jefa mayafin a jikin Mashkoor yace Man tashi ka yafa
mayafin Nan za mu gwada practical akan yanda Zan furtawa Aamna me nake ji game da
ita,yanzu ka yafa mayafin Nan Kaine a matsayin Aamna Ni Kuma Zan zo na gwada ya zan bullo
Mata idan naje, Mashkoor ya dinga dariya harda buga kafa,ya Mike yayi Rolling da mayafin
Aamna ya taho Yana yanga tare da wani shanye Hannu,a Gaban Ahmad ya tsaya tare da Yi
Masa fari da Ido ya wani tsotsi lips yace Hey.....harda rike hips da Hannu Daya yanda Mata ke
Yi,Ahmad Dariya ta kamashi shima ya kalli Mashkoor yace to ai Ni gemunka ne idan na kalla
Taya Zan maka magana Ina ganin gemu dalla jiba Muscle dinka damatsa na maza,jiki Kamar
katako, Mashkoor ya sake makale Murya Yana fari da Ido yace Dan Allah kayi mu gwada ai
Kawai Kamar shooting Film ne Oya fara Mana nine Aamna gani.

Ahmad Yana daga zaune ya fara magana Kamar zaiyi kuka,Baby Idan na ganki zuciyata wani
Dancing take min,Idan kika min murmushi kuwa har wani Rawar galala zuciyata take
min,Sannan Ni sai naji Ina shakkar Yi Miki magan....da sauri Mashkoor ya dakatar da shi yace
dalla Haka zaka Yi lallai zata Raina ka Haka maza ke magana wani gadangatsai Taya zaka
burgeta oya canja salo Action.....Ahmad yayi Gyaran Murya tare da gyarawa ya kalli Mashkoor
zai fara magana sai ya sheke da dariya yace wallahi idan na kalli Damatsanka hankalina Bai
kwanciya bana kallonka a Aamna ga gemu da saje haba,Kayi sauri Dan Allah wannan fa Kamar
Film ne gwada Ina jiranka Mashkoor ya furta Yana wani Fari da Ido Yana karairaya Kamar Dan
Daudu,Ahmad mikewa yayi tsaye yace Ni bazan iya ba kallonka nakeyi wani Gardin banza dalla
bani ya fisge mayafin daga jikin Mashkoor tare da ajiyewa a gefensa, Mashkoor yace kaga
matarka ce fa ka daina wannan abin ka fadawa Mummy ta fadawa Aamna ta dawo gidanka
kaga shike Nan.

Ahmad yace baka da hankali Nifa ba Wai wani mu zauna tare ko wani Sex ba,ya za ayi na
birgeta,ya za ayi tasan me nakeji a Raina game da ita shine Kawai dawowarta gidana ba shine
mafita ba,Ni ba wannan nake so ba,Dan dawowarta ai ba matsala bane Kawai Ni ka Gane nufi
na,idan ta San halin da nake ciki Nan gaba Sanda taga tana so sai ta dawo gidana Ni wannan
ba shine damuwa ta, Mashkoor yace Amma sai kayi ta wahalar da kanka kana tsallaka musu
gida,Kai banza ne bana so ajina ya zube ta Gane Ina son na kalleta ko wani Abu,ai abin sai da
dabara cewar Ahmad.

Da dare 9pm Ahmad suka Isa gidan su Aamna Mashkoor Yana jiransa a can bayan
gidan,Wai shi lallai Bai so Aamna ta Gane Yana son ganinta sai dai ya kalle ta a boye.







Sharhi



AsmaBaffa
10/26/21, 8:53 AM - A Maryam: 🌵🌵DUNIYA TA AAMNA🌵🌵






51-55



KARSHEN FREE PAGE









DUNIYATA AAMNA IS DEDICATED TO GARBA BUTALAWA FAMILY.

NA KUDI NE


MASU SHIGA GROUP DARI BIYU 200 NE


ACCOUNT NUMBER
0175487861
ASMAU GARBA MUHAMMAD
GTBANK

MASU TURA KATIN MTN KO VTU GA NUMBER
08033933642

YAN NIGER KU NEMI WANNAN NUMBER
+227 90 79 59 39








Official






By
AsmaBaffa




Kinfi karfin page
NAFEE
Allah ya bar kauna

Page naku ne

MAMU GALADIMA
AYUSHEE
MOM PAPI AND ALAMEEN
OUM ABULKHAIR
HAUWANCY COOL LIFE
S.Y.SAGAGI
RA'AYYS
I HAFSAT
UMMY MANGA
MAMAN ARFAT
MAMAN YASIR
M DEWU
HAUWA A CHINDO
HALIMA


GODIYA TA MUSAMMAN

DIYAR KATIBI
UMMIN HIBBAH
UMMA KHURSUM
ASMAU YUSUF
UMMIN DEEJAT
BESTYNBEELAT











Yau Baba Bai dawo da wuri ba,Aamna Kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login