Showing 144001 words to 146041 words out of 146041 words
Chapter 49 - DUNIYA TA AMNA Complete Book By Asma Baffa .pdf
Sha turare
wallahi Zaki Yi Dana sani,Dan masifa kina jegon ma baza ki huta ba,kin makalewa Miji Haka
kika ga anayi,Idan ya shigo kika bishi sama sai ki shafe kusan awa biyar Baki sakko ba uban
me kukeyi a saman da jego? Yaron Nan kullum Ina jiyo kukansa idan kika tafi dashi tsakar dare
zai ta kuka ba'a lallashinsa,Yar China tace to mutum bazaiyi bacci ba sai mu zauna lallashinsa
idan ya gaji ya daina Ni bazan dauki wannan iskancin na jariri ba ace sai dare zai tsiri kuka
uban me aka Masa ai wlh sai dai in ki dinga kwana da shi amma mu dai cikin dare Indai na
bashi nono baiyi Shuru ba baccinmu zamuyi.
Iyalle ta saki Baki tare da furta Haka kika ga anayi Dan Ubanki? Ke Haka aka Miki? Baki da
Hankali Sadiya amma a Haka kike cewa kina son danki Wai?Yar China dai shuru tayi ta shiga
kitchen ta hadowa Tawaga Abincinsa ta haura sama ta Ajiye sannan ta koma bedroom dinta ta
gasa jikinta sosai yanda Iyalle ta koya Mata sannan tayi wanka da Sabulun me kamshi ta fito ta
ci gayu cikin wata sabuwar atamfa super wacce Tawaga ya dinka Mata cikin kayan suna Blue
and White,sun Mata mugun kyau Riga da skert,gashi ta Sha uban lalle me kyau,gashin Nan yaji
Gyara a dakin Iyalle ta sameta tana shafa turaruka Baki Iyalle ta tabe tana cewa aikin banza
Yaran zamani Baku San ciwon kanku ba ga danki Nan yayi bacci, Karbar Yaron Yar China tayi
yasha kayan baccinsa masi kyau farare dama wanka aka Masa Yana ta zuba kamshi,Iyalle
Tace sai da safe,Yar China Tace Allah tashe mu lafiya Naman suna fa da aka fara soyawa Yana
kitchen idan Zaki ci,Iyalle tace na eba ma a plate kizo ki hada min shayi me kauri da breadi na
naci na koshi,Yar China tasan Iyalle da son shayi, Yaron ta Saba a kafada ba tare data wani
tallafe shi ba Jin ya zauna daram a Haka ta bi steps sai ga Tawaga ya dawo suna magana da
Iyalle tana tsokanarsa dake itama ta Zama kakarsa.
Da sauri ya karasa ya cafke jaririnsa Yana cewa Baby Ganganci ne fa wannan Yana binta da
mayen Kallonsa yace kinyi kyau Yar China ta Mika Masa Hannu Suka rike Hannun juna tace
gani Nan zuwa yanzu Bari na sallami Iyalle,okay ya furta ya haura sama da jaririn nasu,Sai da
Yar China ta Gama sallamar Iyalle sannan ta kashe kayan wuta tare da haurawa sama,tana
shiga lokacin ya fito a wanka Yana goge jikinsa da towel,Yar China ta karba tare da karasa goge
Masa jikin,Lotion ta shafa Masa sama sama sannan Tace kayi Sallar Isha ai? Yace ae da su
Ahmad Mukayi ma,Yanzu sai abinci? Yana murmushi yace kadan Zan iya ci Aamna ta Riga da
ta shirya Mana abinci,Yar China hade Rai tayi tace Amma ai sai ka fada min tun wuri Kar na sa
Hafsat tayi girki,itafa tayi ta kawo sabo da Kai,to tunda Hafsat ce ta Yi ai ba laifi idan banci
ba,Amma idan naki ne kin San ban Isa naki ci ba,Murmushi tayi Tace kazo da magana,yanzu
kayi magana ta kirki My Man Bari na kaiwa masu Aiki yanzu zasu cinye,Abincin ta sauka da shi
ta Basu tana dawowa ya jawota jikinsa Yana sinsinar Kamshinta yace Anya Zan iya Kiran
Arba'in Kuwa? Yau sati Daya banyi komai ba gaskiya Ina Shan wahala,Amma ai Ina gamsar da
Kai ko ba ta wannan hanyar ba,Yeah ya furta Yana zuge Mata zip din riga.
Jibson Kuwa Sameera tana bawa Jaririya Nono kasa hakura yayi jaririya tayi wayo sosai tana
Shan Daya ta rike Daya Jibson ya cire Hannun jaririyar ya sa nasa a Kai Yana cewa duk ke
kadai sabo da sangarta da Rashin tausayin Mahaifi kina Sha ma baza ki hakura da Daya ba
sabo da son kai Anya wannan ba hadamar Baban Brown ta kwaso ba kuwa,Dariya Suka dinga
Yi har Sameera tace Dan anace kenan,Yarinyar ya kwace yace Kar cikinta yayi Kato ya isheta
haka,da Kansa ya shiryata sabo da an Mata wanka,har Pampers shi ya sa Mata tare da
kwantar da ita a bed dinta sannan Sameera tayi Shirin bacci itama Suka kwanta,Jibson Yana
Wasa da gashinta yace Ina tausayawa Tawaga kafin matarsa tayi Arba'in ba karamin wuya ake
Sha ba,Sameera Tace to Kai ai baka jira Arba'in ba 2weeks fa Kawai ka dawo Aiki,To ai 2weeks
a wajena yafi shekara ma,rashinki ai masifa ne a gareni cewar Jibson Yana lalubeta.
Bash da Hafsat dinsa Kuwa kallon wani film sukeyi a Palo daga Nan suka fada lobayya,a
Nan palon Suka rakashe abinsu,yayinda Mashkoor me kwasar bacci a jikin Nafeesat dinsa yau
wacce Rana Ana bacci da wuri sai Asuba zai gwangwaje,Brown Kuwa yau fada sukayi da
gimbiyar tasa shi yasa Suka kwanta kwanciyar Kai da kafa,shi ya juya Kansa can ita ta sa kanta
saitin kafarsa ba mutunci,Cikin dare Bai ma San sun koma sun manne da juna ba,Yana farkawa
Yaja Tsaki tare gyara kwanciyarta ya koma yanda suke a farko Kai da kafa,Itama Humaira Haka
ta sake Matsawa can gefe Amma kafin Asuba sun dawo sun makale juna,Brown Yana farkawa
Karo na biyu yace mayya kin dawo kin manne min ai shike Nan sai kiyi ta kwanciya,Humaira
tace gaka Nan bakin Maye Ni da Kai waye yazo wajen wani kowa ya matsa Wajensa mana,to
daga min kirji na tashi,sai lokacin taga Ashe ma a saman kirjinsa ta kwanta,da sauri ta matsa ya
tashi ya wuce Toilet da Niyyar Alwala ya wuce masallaci.
Oga kwata kwata King ba Bata lokacin yau da wuri aka Yi harkar sun gwangwaje abinsu,sai
Asuba Suka Yi wanka sosai tare da Sallah,Fu'ad Yana ta baccinsa Aamna ta haura saman bed
ta kwanta a jikin mijinta tana shafa Sajensa da gemunsa tana son yin bacci tace yaushe zamu
tafi Lagos din ne kaga fa Mufeeda ta Haihu jibi suna ya kamata mu je,Ahmad yace hmm ni
wanne suna Kuma? Ki Bari zamuje wani meeting sai na tafi dake,Ni da Tawaga zamuje sai mu
tafi daku ku biyu ma Amma sai Nan da 2weeks,Aamna zata Yi magana yace bana son jayayya
fa,ai Allah ya kaimu zance Kawai, Alright ya furta Yana shafa gadon Bayanta suka koma
baccinsu.
Bayan Yar China tayi wata biyu da Haihuwa Tawaga ya sama musu Admission shi da ita
Amma shi dama NCE ne da shi Degree ya tafi Yi,ita Kuwa Yar China fresh level one ta samu
Health education, Part-time sukeyi a private University,Shima Jibson da Bash sun koma schl,sai
Hafsat da Humaira,Nafeesat,Aamna,da Sameera duk suna da Degree Basu da matsala Kuma
ba Aiki zasu Yi ba,Yar China Suna karatunsu sosai ba ruwanta.
Aamna Bata samu ciki ba sai da ta yaye danta da watanni sannan ta samu wani,Ahmad sai
murna yake yi,Sai da cikinta ya tsufa sannan sauran ma Suka samu ciki Banda Yar China
again,Wannan lokacin Aamna mace ta Haifo zukekiya,Yar China Tace Alhmdllh Aalim Dina ya
samu tasa, Siyama Kuwa kafin ma ta yaye ta samu ciki sai gashi ta Haifi Namiji itama,Sai daga
baya duk tazarar ba Nisa su Nafeesat Suka Haihu suma,Sameera Namiji itama,Humaira ma
Haka,Nafeesat mace ce tayiwa Danta kanwa,Hafsat Mace itama ta sake Haifa.
Sai bayan ma yaransu sun shekara sannan Yar China ta samu ciki ita Sai da Danta yayi
Shekara Uku sannan ta samu wani cikin sabo da Allura tayi ta planning,Suma sauran matan
wannan karon duk family planning sukayi,Ahmad da kyar ya Amince sai da Aamna ta dinga
kuka kullum sannan ya hakura.
Gaf da zasu Gama school Yar China ta sake Haifo Namiji kyakyawa,Wannan lokacin Yar
China an sake Zama Babba an Kara nutsuwa sai dai surutu da abin Dariya sai Wanda ya karu
ma,ga shegen Iyayi da wani tashe da take ji,Sunan Yar Aamna Suhailat sai Yar China ta sawa
nata Suhail Wai ko za a samu akasi Suhailat taki son Aalim sai ta so Suhail shi ya kwashi dadin
cewar Yar China,Ahmad da Aamna ta bashi labarin target din Yar China ya dinga dariya yace
wlh bashi Kuwa zanyi Ina bayan Yar China nima.
Sai da Yar China tayi Arba'in sannan Tawaga ya Mata kyautar motarta sabuwa
kantamemiya kasancewar karambanin Yar China yasa ta koyi mota wajen su Aamna,Sai Bayan
sun nutsu suka sauke farali daga Nan Kuma sai yawan zuwa Umrah,suna zamansu lafiya da
yaransu abin sai Wanda ya gani,Iyalle ma an kaita Aikin hajji da kaninta,Yayin da Aamna take
waya da Yan uwanta na wajen Uwa da uba sannan sukan ziyarci juna jefi jefi,Abin gwanin
birgewa sai Wanda ya gani,Daddy sai Hutu Kawai yakeyi bashi da matsala,Mummy ma haka.
Yau Ranar auren Aamna da Ahmad ne ya sake zagayowa,Kamar yanda suka Saba shirya
Dan kwarya kwaryan party a hadadden gidansu Wanda gidan duk kusan shekara sai an canja
Masa fasali da furniture.
Iya su ya su ba Wanda aka gayyata daga mazan sai matansu da Yan Yara su dagwai dagwai
Yara Yan gayu da su,Dukkansu kowa ka gani ya dauki uban wanka na kece raini,shigar Ahmad
da Aamna ta musamman ce wata maroon and white suit ya Sha gwanin sha'awa,Aamna ma
kayanta wata gown white an nada Mata gogoro da maroon takalmi da pose dinta maroon gaba
Daya,Tasha makeup ta kece raini,Ka rantse yau aka Daura Auren,anyi wani decoration a
garden kusa da pool dinsu,gwanin birgewa,Ga kida Yana tashi sosai,Su cake dankareren
gaske,Su Tawaga da matayensu an kashe wanka cikin shaddoji na kece raini,matan wasu da
lace wasu da material,Siyama da mijinta itama sun zo,Yar China tana ta pics Haka ga me
daukan pics daban na musamman,girki ba irin Wanda ba a shirya ba,kowa ka gani cikin nishadi
yake.
Bash ne ya fara magana tare da Bude taro da Addua,Ahmad King ya karba speaker din ya
fara magana kamar Haka
Yau ce ranar data fi kowacce Rana muhimmanci a wajena,ranar da Mummy ta gano min matar
aurena,ranar da aka min auren dole,lokacin da muke tsaka da cin duniya,Muna tunanin cutata
akayi wanda Ashe gata aka min ban sani ba,Munyi fada,munyi dambe da matata Ina ganin tana
takura min,har ta gaji ta sare ta bar min gidana,Ina murna ta tafi amma Kuma na sake haduwa
da ita a hanya naji Ina sonta duk zaman da mukayi ban so ta ba sai Dana ganta a kwararo Allah
me iko Kuma lokacin na fada kogin sonta,Ina tsoronta ga sonta zai kashe Ni,Lokacin Ina King
Dina,Sabo da ita na canja shiga,na koma shiga ta Kamala,na haura katanga sabo da ita,na
siyar da citta sabo da ita,nayi wanki sabo da ita,Ni king nayi kuka dalilinta sannan Kuma karshe
ta Zama silar shiryuwata na koma mutumin kwarai Wanda sanadin hakan ya jawo duk abokaina
Suma Allah yasa Suka shiryu duk da cewa Su Hatsari silarsa tafi karfi,Dariya sukayi gaba daya.
Yace Yan Uwana, abokaina, abokai na Amana,Ina ji da ku Ina kaunarku, sannan Ina addua
Allah ya sake hada kanmu ya Bamu lafiya da tsawon rai,Ina tabbatarwa wata abotar tafi Yan
uwantaka,Suna tafi Suka ce Ana tare Our King,Aamna ta kwace speaker Tace My King
dai,Suka ce no our king Aamna ta dage ita Tace My King dai,Nan Suka zauna aka dinga ciye
ciye da shaye shayen lemuka Wanda suna ta tuna rayuwarsu ta baya suna labarin wani ayi
Dariya wani a tausaya,sosai abin nasu ya kayatar,su Mummy ma ta waya Suka musu murna.
Lemo Suka tsiyaya a glass cup kowa ya daga tare da furta cheers.
ALHMDLLH
NAN NA KAWO KARSHEN DUNIYATA AAMNA.
INA MATUKAR GODIYA GAREKU FANS MUSAMMAN MASU SHARHI BASA GAJIYA
MUSAMMAN
UMMI DEEJAT
NA GODE DA ADDUARKU FANS ALLAH YA BAR ZUMUNCI .
Saura idan Allah ya kaimu Kuma novel kyauta Next.
AsmaBaffa