Showing 3001 words to 6000 words out of 146041 words
Chapter 2 - DUNIYA TA AMNA Complete Book By Asma Baffa .pdf
kece kike rage min nauyin gida ba da tuni nayi Miki auren Sadaka
Kuma wallah Matukar Naga dama auren Sadaka Zan bada ke.
To Baba kuyi Addua Allah ya kawo min na gari,Kuma da kuke cewa Baku ga juna ba aka
muku aure ai ku a zamanin da ne Kuma asiri akeyi Ana kafe matar ta zauna dole,Salati Baba ya
saki yace Ni Zaki hada da shirka Ina Dan Izala? Shuru Aamna tayi,Mama Tace mayaudariyar
banza,kin Yaudari Affan kin Kore shi kince kin Kama shi da cin Amanarki Yana kula
Mata,Hassan Kuma kince Dan karya ne,Deeni ma yaro me kudi yanzu kince ya yaudareki ya
koma wajen Saratu kawarki Yar gidan Alhaji Sani Likita, yanzu ga Kamalu kin ci Masa mutunci
ya gudu shima,Jollof din shinkafata wacce ta rigada tayi sanyi ta bushe ita Aamna ke ci su
Mama suna ta mata fada har ta Gama,ta cire kayan jikinta gaba Daya ta wanke tare da shanya
su a daren,Wanka tayi da ruwan zafi tare da Shirin bacci ta kwanta ta bar Zuhra tana chatting
da masoyinta .
Dalleliyar mota ce ta gaske wacce a kalla ta miliyoyi ce,ta danno cikin wani katafaren gida na
Gagara,Gida ne Wanda ya amsa sunansa,Babu abinda babu a ciki,motoci ne zasu Kai takwas a
gidan Wanda suka gaji da haduwa ga tsada,farare Guda hudu a jere bangare daban Haka ga
wasu kaloli daban,Machine ne Guda Uku kala daban daban masu tsada harda Keke na masu
kudi su biyu,Gidan Ya gaji da tsaruwa ga flowers ko ina,idan ka Shiga gidan baza ka so Fitowa
ba,Kalar gate din ma na daban ne,ba ko Ina ake ganin Irinsa ba a kasar Haka furniture sai dai
ko gidajen Gomnoni, Wani Matashi ne ya Bude motar baka Daya shigo da ita,Fitowa yayi da
kyar Wow wani Fari ne tas kamar Balarabe har wani ja yake kamar ka taba shi jini ya fito,dogo
ne Amma ba can ba,gashi shi ba Mai kiba ba baza ace Kuma siriri ba,Fuskarsa me dauke da
hancinsa zarkadede ba irin me tsayi da yawa ba,Sumar Kansa baka wuluk dauke da wani
mayen Aski irin na Yan duniya,an kwashe gefe da gefe an yanki wani waje siriri an Kona shi
tare da maida shi Fari tas,Sajensa me kyau luf luf me dauke da Dan gemunsa cas,idanunsa
Dara Dara farare tas suna wani lumshewa,kowa ya kalli wannan matashi yasan ya Gama gajiya
da haduwa,Naira da Hutu sun zauna a jikinsa,Jikinsa na maza Wanda suka amsa sunansu
maza,sanye yake cikin wani Crazy Jean me tsada gaba Daya wandon a farfashe yake ruwan
toka,da wata T-shirt me Rabinta Fari Rabi Kuma Blue,Takalminsa da agogonsa masu
tsada,Yatsansa sanye da zoben Azurfa,da kyar yake takawa ga takama ga aji Amma Kuma
Yana tangadi da Alama yayi shaye shaye ya gaji,Yana dafa bango Yana tangadi AHMAD kenan
a Haka har ya Isa katafaren palonsa tare da fadawa saman kujera ko Takalminsa Bai cire ba ya
kwanta Haka Yana sambatun maye shi kadai har bacci ya kwashe shi.
Tunda ya fara bacci gab da Magriba Bai tashi ba sai da gari ya waye sannan Rana da
hasken gari yasa ya Bude lumsassun idanuwansa a hankali,Kara ya saki kadan Jin jikinsa a
gajiye,da kyar ya iya tashi a hankali ya haura samansa Direct toilet ya shige ya Dade Yana
wanka dake akwai tsafta,Bayan ya fito daure da Towel jikin mudubinsa ya nufa turaruka ne da
mayuka na maza masu tsadar gaske,Lotion me kamshi ya shafa tare da fesa Body Spray a
jikinsa sannan ya dakko sabuwar jallabiya me tsadar gaske fara sal Amma ta Dan tsangale
Masa baya sa wacce zata Kai Masa har kafa sabo da Damunsa takeyi,Turaruka ya fesa sannan
ya dauki wayarsa me tsada Yana latsawa,a hankali cikin tafiyarsa ta Isa da takama ya sakko
kasa ya Bude kofa ya fito sanye da wani flat shoe fari sal shima Yana tafiya a hankali ya bi ta
wani corido gaskiya gidan Nan ya Gama haduwa tiles din kasan gidan na tsakar gida fari da
Baki ne ko Ina sheki yake Yi da walwali,Me Gadinsa ya hango Yana karasa gyara gidan Yana
kida da bakinsa Yana rawa Yana aikinsa,Ya Dade a tsaye Yana kallonsa,Abin Dariya ya bashi
mutum shi kadai Yana kida Yana Waka Kuma Yana rawa duk shi Daya, murmushi ya saki kadan
tare da girgiza Kansa ya juya ya koma inda ya fito.
Har yayi nisa sai ya dawo ya Kira me Gadi Musa,da sauri Musa ya dago yace Oga tare da
takowa da gudu yazo gabansa yace Ina Peter banga ya gyara ciki ba Sannan ba Abinci,Oga ai
Peter ya tafi kasuwa yace abincinka Yana kitchen yace sauri yake yi,Ni gaskiya Oga Ina
tunanin yafi a dakko mace yar Aiki wacce zata na maka girki da gyara maka ciki tunda Ni Ina
kula da Campun,Ogan yace ba Campun ake cewa ba Musa Compound,Kuma Ni bana bukatar
mace yar aiki,Ni bana son mace ta rabe ni,duk abinda zai sa na hadu da mace bana
kauna,Musa ya zaro Ido yace Oga Mata sune Jin dadin duniya duk wata nutsuwa da Namiji zai
samu tana jikin mace,Baki Ogan ya tabe yace Allah ko? A wajen wawaye ba,gwara naci abincin
Gardi akan naci na mace,Karka sake furta kalmar Nan mace a gaba na,idan ba Haka ba Kora
ce tukucinka,Musa yace an Gama,Kayi Hakuri Ranka ya Dade Namiji gwara nace Namiji,macen
banza Banda Mum dinka Oga,Baki ya tabe ya juya da Gadara ya wuce,Abincin Peter ya Bude
yaga Bai Masa ba,da Kansa ya shirya Girkinsa da lafiyayyen tea dinsa ya karya sannan ya
dauki key din mota yayi waje,Yau da wata mota Ruwan toka ya fita kirar Benz.
Washe gari Aamna wanka tayi tare da Shiryawa tsaf cikin kayanta Riga da wando sunsha
wanki da guga,After Dress ta Dora a Kai tare da yafa Mayafi,ba Wanda ya kalle ta a cikin
Iyayenta Balle Tace Za'a Bata wani abinci dama yanzu basa kulata,ko ta gaishe su basa
amsawa,Sallama ta musu ta tafi,Mama Tace yarinyar banza ace tasan Burin mu Bai wuce mu
Aurar da su ba Amma Taki fitar da Miji abin kunya kanwa zata Riga Yaya aure duk ta tsufa a
gida Allah wadaran Dan Riko,shekara ashirin da Hudu ai ba Wasa bane,mu duk da a cikin birni
muke muna Nan da akidar mu ta Iyaye da kakanni na auren wuri Amma kash Yaran namu
musamman Aamna ta Gama watsa Mana kasa a Ido,marikinta Bai da Buri sai na Aurar da su,ai
mutuncin ya mace gidan Miji Amma ba komai Aamna wahala da azaba ma Sai ta sa kin fito
Mana da Miji,kin daina Jin dadin gidan Nan kwata kwata,yanzu Zan canja Taku wajen gana Miki
azaba duk da Kamar mahaifiyarki ce Ni dole wahala tasa ki fitar da Miji,Zuhra kuwa Shiryawa
tayi tuni tayi Kari me kyau Ana ta nuna Mata gata da kauna ta tafi makarantar Boko Wato
Secondary school sabo da sun kusa yin candy.
Ahmad Bai tsaya ko Ina ba sai gidan Mashkoor inda Suka Fi Zama suna shaye shaye a
gidan,can ya Iske abokansu su Biyar Mashkoor, Abdul Tawaga,Jibril Jibson,Bashir Bash,
Mubarak Brown sai shi Oga Mai gayya me Aiki Ahmad King,Yana zuwa ya Iske su a zaune a
Garden suna zaune a kujeru ga karamin Table an zube kayan maye na shaye shaye kwayoyi da
giya iri iri ga Sigari taba da Wiwi,Kirari suke Masa Suna The King...Our King,shi Kuma Yana
uban Gadara Abdul Tawaga ya Daga Masa kujerarsa ta tsakiya Kuma kujerarsa ta mulki ya
zauna tare da Balle kwalabar Giya ya Shiga tiltila Kamar ya samu ruwa,Bash ya kunna Wiwi
Yana zuka ga wasu kwayoyi Daya hada a cikin wani ruwan giya Yana korawa Yana tiltilo hayaki
ta Hanci ta Baki cikin kwarewa,Tawaga Yana Aswaki Yana cijewa Yana karkace Baki yace Our
King....Sweet Boy,The Handsome King,Fresh Boy, shi kuwa King ya kalli Kansa yace Na
me....Na me My Guy,Look at my skin color....
Mubaraq Brown yace Handsome King,Mashkoor Yana wani tangadi a zaune yace Our King ka
huta baka hura hayaki sai ruwa Kawai kake bulbula sai kwaya,King ya wani girgiza Kai alamar
ya fara daukan chaji shima yace,Hayaki sai dai na shaki na Titi My Guy, Mashkoor yace Look
King akwai wata yarinya tayi Fuck Up,the Girl done Mess up man, Wai Ni Ina sonta Tace Banda
hankali wani yaro Rabiu Yana Nan malamin makarantar Islamiyya ya kwace min ita,King Yana
lumshe Ido duk ya fita a hayyacinsa ya karkace bakinsa gefe Daya irin na Yan shaye shaye
cikin kakkausar da mayen muryarsa yace She must Collect,Dole ta karbi Certificate na abinda
ta aikata,Na yarje muku kuci mamanta,shi Kuma Yaron za a tare shi dole mu bashi
Sample,Sumarsa me laushi ya yamutsa,yace guys gobe Mommy da Dad zasu shugo garin Nan
Karku zo gida na sai bayan sun tafi,Abdul yace Confirm,No wahala,Jibril Jibson ya Mike Yana
tangal tangal yace ya za ayi ace baza mu zo gidan King ba,The sweet Boy,Cikin zafi da daga
Murya King Ahmad yace hey What's up man Ina magana kana magana kana hauka ne? I'm
sorry cewar Jibson ya Fadi a kasa Yana mayensa,da ganinsu kasan talakawa ne Ahmad shine
me kudin shike musu komai,Haka Mashkoor Yana da kudi shima Amma ba Wani da yawa
ba,Sai Abinda Ahmad yace shine King dinsu,duk wani rashin mutunci da sukeyi a gari shine
yake daure musu gindi sai da sa hannunsa akeyi,Ba Wanda ya Isa ya nuna su da yatsa,Dai Dai
ne Basu San da zamansu ba musamman Ahmad King din Wanda ya fita daban sabo da Naira
da hutu,suturarsa Kawai abin kallo ce,Dukkansu baza su wuce 30years ba zuwa
34years,Ahmad 34yrs yake cif.
Washe gari da Yamma su Mashkoor da abokansa gaba dayansu har King din nasu Ahmad
machine sababbi suka hau kowa da nasa Kuma duk King ne ya Siya musu kowa da nasa King
shine a gaba suna binsa a baya sun kure Masa gudu sun biyo Hanya duk Wanda Bai matsa ba
sai dai su bige shi ba ruwansu,sabo da an sansu Ana ganinsu ake kaucewa,Can layin da
Islamiyayyar take suka tsaya Suka Parker machinansu,King shine kadai ya zauna a saman
nasa suna ta Masa Kirari suna Our King,Fresh Boy,Sweet Boy,shi Kuma Yana ji da Kansa,Suna
Haka sai ga malamin Islamiyya ya taho zai wuce matashi da shi Yana tafiya cikin nutsuwa Baki
da shi,Tare shi Mashkoor yayi tare da cewa Yawwa ga dan Iska ya Furta tare da tallafe Masa
keya,King ya Mike cikin maye yace kana gaba na kana tsaye,Robar Lemo Wanda ciki hadin
kwaya ne a ciki Yana Sha ya daga ya tsiyaya wa malamin Islamiyya a kansa,Nan suka rufe shi
da duka Wai yayiwa Sarkinsu magana a tsaye,Wata Mahaukaciyar mota ce me kyau da tsada
ta taho a hankali,Mommy da Yar Autarta Humaira sai Daddy Mijinta a baya gaba Kuma Kanin
Ahmad ne Saddiq da matarsa Mufida a Gaban mota suna tafiya, Saddeeq shi ke tuka
motar,Daddy yace ai Kinga Ahmad din ma gashi Nan da Yan Iskan abokansa,na gaji da zuwa
Kaduna akan Yaron Nan wallahi,Na rasa wannan masifa data sameni,Kinga Ni yanda suke
dukan wani,Kanwar su Humaira Tace ga Yaya can da kayan maye a hannunsa, Saddiq ya tabe
Baki tare da cewa kalli Askinsa Ana ganinsa anga Dan Iska,Mufida matar yayan Tace kuyi Masa
Addua Kawai.
A wajen Suka Yi parking sai tsawar Daddy dinsa yaji a Kansa Ahmad Mene Haka? Baka da
hankali ne,duk suna mota ba Wanda ya fito sai Mummy da Daddy,Daddy ya tashi malamin
makaranta Wanda ya ci duka da gudu ya arce Yaron,Su Mashkoor suka kame a Gaban Daddy
tare da Sara Masa kamar suna Gaban wani Soja,Zaga Daddy da Mummy suka shiga Yi suna
musu Sannu da zuwa Wai Nan murna ce da girmama Iyayen Ogansu,Bash kuzo mu Basu
kariya Guys ba Wanda ya Isa ya daga Musu yatsa a Birnin Kaduna kaf.
Tsaki Daddy ya ja Yana Jin yanda suke wa Ahmad Kirari,Wandonsa ya kalla wani shegen
crazy an Masa daga daga,Askinsa ya kalla yace kalli yanda ka maida kanka Ahmad, Dariya ya
Shiga Yi ta mahaukatan Yan maye,Mommy Tace Ahmad Dina meke damunka muje gidan da
kake,Daddy yace shiga mota mu tafi,Wani fareti ya shiga Yi a Gaban Daddy Yana dariya cike da
maye Yana karkace Baki yace No...no Ni a bike Dina zanzo kasan Ina Jin dadin bike Dina
Kawai kuje zanzo daga baya,Tsawa Daddy ya daka Masa shiga muje,Amma ko a jikinsa sai ma
Dariya da ya Shiga kyakyatawa irin ta basawa Yana kallon Daddy din da Mommy,Dole Haka
Suka shiga mota Suka tafi shi Kuma shi da Abokansa suka take musu baya a machine suna
tukin ganganci Dan Ahmad harda dage kafa Daya ya daura ta can sama Yana tuki da kafa
Daya,Har katafaren gidansa Suka shiga sannan abokan daga bakin Gate Suka tafi gida abinsu
shi Kuma yayi Horn me Gadi ya Bude Musu Gate,Bayan sun Shiga Suka firfito da
akwatunansu,Wani handkerchief ya daura a wuyansa ya tsaya a Gaban Mommy Dinsa Yana
zagata cike da maye Yana cewa Mummy...Mummy....Momma....You are looking Good ya furta
tare da rungumeta yace Ina sonki Mummy,rokonsa ta fara Tace Dan Allah ka nutsu Ahmad,Da
karaji Daddy yace Mene ne kike rokonsa, why are you Begging him,Dan ubansa tunda bashi da
hankali sai yayi ai,Why...why...Daddy Ni dama fa ba tun yau ba nasan baka kaunata,musamman
idan ka saka wannan farin Glass din naka sai ka dinga kwana idan anyi Nan sai kayi can,Ido
Daddy ya zaro Yana kallon rashin kunyar Ahmad,Kaninsa Sadeeq ne yace ka canja wallahi
Yaya,Cikin karaji ya tasowa Saddeeq Yana ce Masa Kai dalla gafara Ina yayanka zaka min
fada,ko Dan kaga munyi Kai Daya Ina da gemu kana da gemu shine zaka rainani Kai wuyanka
ya Isa yanka ko,Ka dai gyara halinka,Tafiya yayi zai Mari Saddeeq Mummy ta rike shi tana
rokarsa yayi Hakuri, Humaira ya riko tare da Rungume ta yace kanwata kin girma,ya school?
Tana Dariya Tace nayi Candy Yaya,Wow ya Furta tare da dagata sama ya ajiyeta suna
Dariya,Matar Kaninsa ya kalla Mufida nutsatsiya kyakyawa yace matar mu ya gida fatan
wannan shashashan yana kula Dake? Dariya Mufida tayi Tace sosai ma,yace Good muje ciki
matar mu ke kadai ce tawa a gidan Nan,kishi ya Kama Saddeeq ganin Ahmad Yana shaye
shaye tunaninsa har Mata yake bi sai kishi ya kamashi yace kaje kayi aure wannan matata ce
Ni Daya ka daina cewa matarmu yawwa,Stupid Boy Kawai Ahmad ya furta Suka jera da Mufida
suna Hira duk da a maye yake Amma Yama Saba Bai fiye buguwa da yawa ba, Sadeeq da
Sauri yazo ya shiga tsakiyarsu ya rike Hannun matarsa ya janye ta da karfi,Baki Ahmad ya tabe
ya Rungume Humaira Suka Yi ciki.
Bayan sun huta sunci abinci Daddy yace da dare Yana neman kowa za ayi Meeting zasu
fadawa Ahmad dalilin zuwansu yanzu ma again, Har dare yayi Ana jiran Ahmad Amma tuni ya
bar gidan Yana can suna shaye shaye har 1am Bai dawo ba sai kowa ya hakura yayi bacci,Da
safe ma Ana ta jiransa har sun karya Shuru Bai dawo ba,can sai gashi a bige ya Fado palon ya
tafi taga taga zai Fadi sai ya cije ya Dage Yana bude Ido da kyar Yana Rufewa ya fada saman
kujera shirim kusa da Daddy yace An tashi lfy?
Ina....Ji...ji..jinku.....m....me.....yaaaaaa....ya...kawo ku Kuma yanzu Kun wani sake dawo min
gida...na tuna ance jiya za ayi meeting yanzu gani Ina da abin Yi ku Fadi meke tafe daku har
zuwa gidana? Daddy ya zaro Ido yace au gidan ka ne ma? Gidana kace gidanka? Yace gida
nane Mana Kai ai Temporary Owner ne Nan gaba mutuwa zakayi naci gado,Ran Daddy ya baci
yace gidan Nawa? ni da gidan gida ka gaje min gida?aikin uban me kake Yi? Kaki
nutsuwa,Mummy Tace Ahmad Dan Allah ka tsaya ka nutsu kaji abinda ya kawo mu,Ina jinku
Mana ku fada,Kaninsa Sadeeq ya tabe Baki,Humaira Tace Addua zaku Masa please,Ita Mufida
ita tunda auro ta akayi Bata cikin wacce zata Shiga matsalar Family tana bedroom.
Daddy yace kana ji na Ahmad? Yace Yeah,yace so nake ka bar Nan ka dawo Lagos kazo mu
koma inda nake da Zama can Lagos Ina so Zan maka Visa mu tafi London gaba Dayan
mu,akwai Company na Dake can kayi Handling dinsa kayi Aiki a can ka dogara da kanka,kullum
sai dai na cika maka account da kudi kana kashewa a banza,ya kace?Ahmad yayi Dariya yace
kasan amsata Mana Daddy Ni bazan je ba wata kasa da zanje Kuma Ni bana son Lagos a Nan
gidana Zan zauna a Nan Zan mutu,Daddy yace to gidanka ne? Ni da gida na,Mummy Tace Dan
Allah Ahmad ka bimu mu tafi kaga London ko Turkysh ko Kuma a Nan kasar Nigeria sai kayi
Aiki an baka company kyauta ka dogara da kanka Kaine fa babban Danmu Kai ya kamata ace
ka nutsu,kalli kaninka ya rike nasa a Lagos Yana aikinsa gashi da Degree da Masters Kai kuwa
Degree daya ma da kyar muka samu ka karasa a Russia,Ahmad yace kunga fa Ni ba inda
zanje Kawai ku daina Bata bakinku mutanen da basa son bakar fata ku Kun damu da su kuje
kuyi harkarku,kuyi rayuwarku nima nayi tawa,yawwa kunji ba inda zanje ya tashi Yana tangadi
ya haura sama,ya barsu a Nan cike da Alajabi yafi karfinsu.Daddy bakin ciki ya Kama shi ya
juya kalli Mommy tare da galla Mata Harara yace Kinga danki ko kin ga abinda kika haifa ko?
Mummy Tace au da nane ma Ni Daya? Daga Nan suka fara cacar Baki.
Aamna ce ta fito tsakar gida sanye da wani gajeren wando ko gwiwa Bai ba Milk color,da Yar
rigarta t-shirt dark Blue,Hannu biyu ta zuba a cikin aljihunta tana tafiya tana