Showing 27001 words to 30000 words out of 39050 words

Chapter 10 - YAN ZAMAN MAKKAH BOOK COMPLETE BY OUMYASMEEN.pdf

18 May 2025

4129

da kuka.
har suka isa nan ma da kafar dama mommy tace ta shiga batai musu ba ta shiga da ita kai
tsaye gurin mahaifyat sa , suka nufa sallama su kayi kanwar sa hindatu ce ta amsa amma innar
su Mamman ko nunawa ba tayi ba tasan da tsayuwar su.
shigowa su kayi wasu suka tsaya a waje mommy tace '' barka da yamma ya taro..?,
dakyar tace '' barka dai alhamdulilah..,
sosai mommy take mamaki to ya akai bata san da wannan matsalar ba , da baza ta bari ayi
auren nan ba , kar ta takurawa yumna danne abin tayi tace '' masha Allah to ga amana nan mun
kawo miki duk..
ai bata karasa ba tace '' da kata ban amshi wannan amanar ba dan haka ku tattara
ƙafafuwan'ku ku fitar min daga daki kafin ba gurza muku tashin mutunci.
tashi su mayi yumna tamkar zata fadi saboda tashin hankali daman fa'iza ta dade tana faɗa
mata innar su hindatu bata da kirki sai yau ita tashe da , da maganar fa'iza a gaban jama'a ta
tozarta ta lallai jiya ba yau ba , ban da tayi sanyi yasin sai dai ta saka danta ya sake ta daman
haka take bukata. dakin ta suka kaita sosai mommy take cikin ɓacin rai faɗa ta kara yi mata tai mata sallama su
fa'iza ma ba jimawa suka tafi.
zazzabi ne ya kara rufe ta da gudu ta fito tana kwara amai tamkar zata amayar da ya'yan hanjin
ta innar su hindatu fitowa tayi ta kama kugu tace '' wallahi ba zata sabo ba daman da ciki kika
shigo min cikin gidan ɗana..,
ba karamin daga mata hankali wannan maganar tayi ba da sauri ta ɗago lokacin Mamman ya
shugo yana baza babbar riga jin abin da mahaifiyar sa tace da sauri ya ƙara so cikin ɗaga
murya da faɗa tace '' gata nan ta shigo maka da ciki cikin gidan ka dan haka wallahi sai ka
saketa ba zan yarda ba ta zauna min da cikin shege a cikin gidan nan ji yadda ta ɗashe tayi fari
anzo za'a cuci ɗana ayi laulayi a gidan sa dan kirufawa kanki asiri kawayen ki ba ƙananan
karuwai bane dan haka kaji na rantsai maka idan baka saketa ba sai na tsine maka kuma saki
uku nake so kayi mata domin wa'yannan mayu ne tsaf ubanta zai ƙara rubuce ka akan sai ka
sake ta ga yarinyar nan yar mutunci na kawo maka amma kaki ka aura ka ɓuge da aurar
ragowar titi..,
ji yayi kan'sa ya sara mai shi ba mace bane balle ya iya tantance abin da innar sa take faɗi
amma tabbas duk abin da ta faɗi gaskiya ne shima kan'sa kyan da yumna tayi ba ƙaramin
mamaki yake bashi ba sai kawai ya barshi a gyaran jikin da aka yiwa amare ne shi ya mai data
haka baya zargin yumna ya yarda da tarbiyar ta amma ya ya iya mahaifiya ba wasa ba. hawaye ne yake zubowa a idanuwan'ta tace '' be kamata ba dan bakya sona kiyi min wannan
ƙazafin ba , ko da ace Mamman zai sake ni karka sakeni da wannan baƙin tabon da har abada
ba zai taɓa gogewa ba a idanuwana da zuciyar'ta kina da ya'ya mata kin haifa be kamata ki
jefeni da wannan kalmar ba. wata uwar buda ta saki tace '' au Allah maza saketa ina gani kuma ta taso na kaita har gidan su
na shedawa kowa abin da , ta aikata..,
Mamman dakyar ya iya haɗiyar yawu ganin yayi shiru innar sa ta saka kuka tare da kakorin
tsine mai da sauri yumna ta girgiza kan'ta tace '' Mamman bakomai karka bari saboda dani ka
ɓata lahirar ka , komai me wucewa ne wallahi..,

a hankali ya furta na sake ki saki biyu..
share hawayen ta tayi ta tashi ta shiga daki mayafin'ta ta dauko ranar daurin auren ta an sake ta
saki da ashe daman haka yake da ciwo ashe daman jin sa kawai take abaki amma wata
zuciyar'ta ta murna take wata na bakin ciki saboda da bakin tabon da aka sake ta dashi.
a daidai nan mahaifinsa ya zo hindatu ta kira shi saboda abin da yake faruwa.
yana zuwa inna ta kora mai bayani tabbas ga amai nan amma yace '' ke kin tabbatar da wannan
zargi tabawa kiji tsoran Allah Ubangijin fa baya yafe hakkin wani akan wani idan kinyi haka ne
domin ki tozarta su wallahi Ubangiji zai jarabbe ki ta inda ba kiyi zato ba..,
a dai-dai nan yumna ta fito tana saka mayafi mahaifinsa yace '' ya'ta koma ki kwanta gobe sai
mu yi magana...,
na rantse da Allah sai ta tafi ta zauna tayi me a cikin gidan nan..?,
tashi yumna tayi ko gaban ta bata iya gani ta fita Mamman kuwa ya zama tamkar wani mutum
mutumi,
dakyar take iya tafiya ikon Allah ne ya kawo ta gida amma ba dan haka ba , da tuni wani
zancen ake yi malam yana zaune asoro shida mommy suma magana ta shigo da yake akwai
hasken fitila da sauri mommy ya zaro idon'ta tare da dafe kirjin ta da yake dukan uku uku
malam kuwa daskarewa yayi dakyar ya iya cewa yumna me ya dawo dake..?, ɗurƙusawa tayi tana kuka tare da shashsheka ta kasa magana ganin haka mommy tace ''
malam mu shiga daga cikin dakin nan na zaure har yanzu akwai mutane a cikin gidan nan wasu
ma kwana za su yi.
tashi yayi jikin sa duk a sanyaye ya buɗe dakin su hafizu shiga su kayi mommy ta ƙara mai
maita mata tambayar dakyar yumna ta iya cewa sakina ta saka yayi saki biyu na fito ina amai
tace cikine dani
salati mommy ta saki shikkenan magana ta ƙare innalillahi wainna ilaihir raji'un haka suka shiga
maimaitawa mommy tace '' Allah ya isa tsakanin mu da ita yarinyar da take al'ada wanne ciki
insha'Allahu akan ya'yanta zata ga ciki alfarmar annabi Muhammadu Sallallahu alaihi
Wasallama sai dai ta gani akan nata badai akan kiba, ni daman tun da ta iya rufe ido ta ci mana
mutunci nasan bata da imani bata da tsoron Allah yanzu maganar da muke yi da malam kenan
a cikin daran nan a ranar da aka daura muku aure ta saka a yi miki wannan sakin hulakancin
gaskiya matar nan bata da imani ko yan baki ba su soma watsewa ba insha'Allahu yumna sai
kin zama wata makaranta kawai zaki koma da zarar takardun ki sun fito ta mai dake ƙaramar
bazzawara.,
malam kasa cewa komai yayi ko da ya tashi binciken Mamman da man ance mahaifiyar sa tafi
karfin mahaifinsa ashe kuwa haka abin yake da ya sani ƙeya da be haɗa wannan auren ba
dama ya bar yarsa tun farko da ta nuna bata so bakomai haka Allah ya tsara daman auren su
na wani lokaci ne , duk da ba'a shedar ɗan yau amma yasan halin kowa daga cikin ya'yansa ita
dai yumna barta da daukan magana amma wallahi baya zarginta balle gashi nan ance ma
al'ada take yi wannan mata ta cuce su bakomai Allah yana nan ma dakata.
dakyar ya iya cewa yumna kiyi hakuri kiyi hakuri kiyi hakuri Allah yana tare da me gaskiya wata
ran zatai nadamar abin da ta faɗa miki kafin su hafizu su zo ku tashi ku koma cikin gida..
da sauri mommy tace '' a'a duk da dare yayi kawai mu koma gidana ai haka kamar tozarta kai
ne..,
haka ne wallahi Allah ya rufamana asiri amin mommy tace ta tashi ta shiga yusra ta kwaso

muku kayan su suka fito daman tun ɗazu kaka ta tafi buɗe Boot tayi ta zuba kayan sannan ta
rufe.
yusra ta shiga gidan gaba saboda ita zatai tukin daman ta matsu su tafi so take yi ta ganta a
gidansu amma mommy tace ba yau ba sai gobe sub koma gidan yumna zuwa jibi su tafi.
tamkar an warke ta daga Makanta taga mommy ta kamo hannun yumna ta buɗe baki za tayi
magana mommy ta hade rai ta buɗe gidan baya ta shiga ganin haka itama ta tsuke bakin ta
kwantar da kan'ta tayi a cinyar mommy tana kuka zazzaɓin jikin'ta ya ƙara tsanani ba irin abin
da yumna bata saka aranta ba wayar ta da take makale da ita a cikin zaninta ta ciro tace ''
mommy ajiye min..,
cikin tausayawa mommy ta karɓar ta ajiye mata ba karamin tauyasin yumna take ji ba , dan ma
yarinyar tana da karfin zuciya da wata ce faɗuwa za tayi idan ta ji wannan zance.
sai karfe goma suka isa me gadi ya buɗe musu gate lokacin juraij ya dawo daga aiki shima
turus yayi ganin yumna ta fito abinka da babban gida ga wadatar hasken wutar lantarki tamkar
rana jikin sa a sanyaye ya ƙara so yace '' mommy sannun ku da zuwa..?,
Yauwa juraij yanzu ka dawo..
Eh wallahi yanzu na dawo nama biya ta gidan su ahlam jikin nata da sauki ba kamar jiya ba.
Mommy tace '' to Allah ya kara sauki nama kirata ɗazu naji ya jikin ta wayar ta a kashe..,
insha'Allahu zan faɗa mata kallon yumna yayi zai wuce mommy tace '' juraij ina son ganin ka..,
gaban sane ya faɗi amma sai ya dake yace '' to mommy..,
buɗe motar sa yayi ya ajiye kayan da ya dauko ya bi bayan su.
lokacin mommy ta shiga daki yusra ta hau sama domin bacci take ji yumna ce a zaune a parlour
be bi takanta ba ya nufi bedroom din mommy sallama yayi tana zaune ta rafka uban tagumi sai
ya ya kara magana sannan taji shi.
da sauri ta ɗago tace '' juriaj ashe ka shigo,
zama yayi a ƙasa ya tankwashe ƙafafuwan'sa yace '' mommy me yake damin ki naga kin yi
tagumi Allah ya saka lafiya wallahi na shiga tashin hankali sosai dana ganki a cikin wannan
hali..,
ajiyar zuciya ta sauke tace '' juraij wallahi ina cikin matsala kai kaɗai ne zaka iya fiddani a cikin
wannan matsalar taufiq baya nan yana karatu da shi zanwa magana..,
kallon ta yake cikin mamaki domin be san ina zancen ta ya dosa ba temako kuma yau mommy
ce take neman temakon sa to duk yadda aka yi ba ƙaramin abu bane wannan dan haka yace ''
mommy Dan Allah ki faɗa min me ke damu ba ki..?,
ajiyar zuciya ta sauke ta share kwallar da take ƙoƙarin gangarowa a kurmin idon'ta tace '' yau an
daurawa yumna aure a yau uwar mijinta, ta saka aka sake ta daman tun daga tarbar da tayi
mana wallahi nasan ba mutuniyar kirki bace..,
gumi ne ya shiga yanko mai ya shiga uku yasan yanzu haka shi momy zata ce , ya auri yumna
ba zai iya adalci ba , ba zai iya haɗa ahlam da ko wacce mace ba , ba zai iya ba ji yayi ya shiga
cikin wani irin hali wanda ya kasa fassara shi to wacce siga.
tissue ta yago ta share hawayen ta tace '' kai nake da yaƙinin zaka iya riki min amana ko bayan
raina ba zaka taɓa iya tozarta yumna ba , taufiq yana da wata dabi'a da wani hali ba ko wanne
abu ya ke so ba , idan na tursasashi ba lallai yace min ba zai iya ba amma abin zai dinga ci mai
rai ƙarshe ya haifar mai da wata lalurar kai nake da ya ƙinin za ka iya yi min wannan aikin kai
zaka iya riƙe min wannan amanar duk da ba lallai ka amsa ba amma ka riƙe min ita ina so ka

aure yumna tun da be ɗora mata idda ba
habawa ji yayi tamkar an dauko ringimeman dotsai an ɗora mai akan zuciyar'sa ina bazai iya ba
duk ba ba zai iya yiwa mahaifiyar sa musu ba amma ba zai iya yin adalci ba ƙasa magana yayi
tun da ya sunkuyar da kan'sa ƙasa be dago ba har ta gama zancen ta bakin sa na rawa yace ''
mommy auren ta zanyi...?, kai ta gyaɗa mai ,
baya son zubar hawayen mahaifansa baya son abin da zai saka tayi kuka yana da kuma
maganin damuwar ta , ya saka yi mata bakin sa na rawa yace '' mommy ki gafarce ni bazan iya
auren ta ba , saboda Muhsin yana son ta ba zan iya zama da abin da aminina yake so ba ina da
yaƙinin Muhsin zai iya riƙe wannan amanar wallahi tun da ya ganta yake min maganar ta sai da
na gaji na faɗa mai an mata miji duk da haka be hakura yanzu haka yau da nake ce mai yau
ake ɗora mata aure wallahi yana kwance akan gadon asibiti idan aureta ban mai adalci ba
hakika na cika bakin amini wata kila ma hakan ya kawo karshen alakarmu saboda so mugun
abu ne zai iya haɗa mu duk irin amintar da take tsakanin mu dan Allah mommy karki ce ban bi
umarnin ki ba amma me zai hana taci gaba da karatun ta yadda zata iya dogara da kan'ta zata
tallafi rayuwar maraicinta har Allah yayi abin da ya tsara..,
ya faɗa yana riko hannunta tare da goge mata hannunta.
Mommy kasa magana tayi wannan ita ake kira da tsaka me wuya taso ace yumna ta auri Juraij
daman tun farko shi taiwa sha'awar'ta sai kuma ya kawo mata ahlam ba yadda ta iya ta amince
da auren ta tabbas ba za ta ita tauye mai hakkin sa ba duk abin da ya faɗi gaskiya ne zata bar
zancen auren nan Allah ya zaɓa mata abin da ya fi alkairi dakyar tace '' bakomai wallahi Juraij
Allah yayi maka albarka ya shige mana gaba daman nima cewa nayi ko a dakin mijinta ta ci
gaba da karatu amma wannan abin har abada bazai bace mata a rai dan Allah ku jata a jiki ku
hanata zaman kaɗaici duk abin da za tayi karku kyareta sai abu yayi mata yawa ku bita a
hankali komai yana da lokaci komai zai wuce tamkar ba ayi shi ba...,
insha'Allahu ya fada yana tashi ba karamin sanyi yayi ba lokacin da ya samu nutsuwa da
amincewa da tayi da maganar sa..

Copy is not allowed
Domin jin audio din Yan zaman Makkah Ku danna wannan link din sannan kuyi subscribe Dan
Allah.
https://youtu.be/cDE5bjYY2HY
___________________
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6817816be532b4a92550458c
Episode 13
sai da safe yayi mata ya fita har zuwa lokacin yumna tana kwance akan kujera ta , takure guri
ɗaya.
wuce ta yayi ya fita tana ganin fitar sa ta miƙe ba karamin bacci take ji ba dai-dai lokacin
mommy ta fito kama hannunta tayi ta kaita har dakin ta , wanda da aka sauketa a cikinsa
kwanciya tayi akan gado tare da yin addu'a mommy ta ja mata kofa rufe idanuwan'ta tayi
zuciyar ta na mata wani irin suya , bawai bakin ciki take da Mamman ya sake ta ba a'a daman
abin da take nema kenan kuma sai ta samu, babban bakin Cikin da sharrin da mahaifiyar sa
tayi mata , ba zato taji hawaye na bin kuncinta sharewa tayi ta gyara kwanciyar ta ranar yadda

taga rana haka taga dare zazzaɓi ne ya ƙara rufe ta ko iya daga idanuwanta bata yi ga ciwo da
kan'ta keyi tamkar zai fashe gida biyu.
ji tayi anyi knocking kofar ta , ba damar tayi magana tayi shiru ko da aka turo kofar ko iya ɗaga
kai bata yi
ashe mommy ce ,,
zama tayi a kusa da ita Alhaji yace '' yumna ya jikin naki..?,
dakyar ta iya cewa Alhamdulilah da sauki..
sosai ya tausayawa yarinyar saukar sa kenan a ƙasar mommy take bashi labari shine ya shigo
domin ya duba ta ,,
kwalla mommy ta share tace'' Alhaji anya kuwa ba za'a kaita asibiti na , jikin nata yayi
tsanani..?,
Alhaji yace '' tun da ga taufiq nan ya dawo, ya duba ta da ace juraij be tafi wajen aiki ba da shi
ya kamata ya duba ta tun da daman ɓangaren mata ya karanta.
ajiyar zuciya ta sauke tace '' to bara na kirawo shi Allah ya saka be kwanta wannan shegen
baccin nasa ba , yawa na mutuwa..,
zauna ki kula da ita,zan kirawo shi
to tace ta shafa kan yumna da yayi zafi raɗau tamkar garwashin wuta.
cikin tausayawa tace '' yumna sannu me yake damun ki..?,
kasa magana tayi sai bakin ta da yake rawa alamun tana so tayi magana ba halin yi hawaye
mommy ta share mata , tace '' kiyi hakuri akwai Allah, komai yayi zafi maganin sa Allah..,
kai kurum ta gyada da kyar, ta riƙo hannun mommy Assalamu alaikum..
da sauri mommy ta juyo jin muryar taufiq tace '' wa'alaikas'salam..,
ƙarasa shiguwa yayi yana cire medical glasses din'sa yace '' wannan ce mara lafiyar..?,
mommy ta kalle sa tace '' eh..,
dan jim yayi sannan yace '' mommy ban tawo da komai ba ko , kayan sawata ban tawo da su ba
, tun da na san ina dasu anan sai dan abinda zan yi amfani dashi, dashi na tawo , ko za aku
kaita asibiti naga jikin nata yayi tsanani..,
tashi mommy tayi tace '' dauko mota ka kai mu..,
to yace ya fita Alhaji ya ci karo dashi yayi mai bayani yace to ba damuwa ya dauko ya kai su
bayan ya gama dai-dai ta parking din'sa, ya dawo daukan ta yayi domin ba zata iya tafiya ba har
cikin mota ya saka ta mommy ta shiga suka fati kai tsaye asibitin da yaza mo mallakin juraij
wato J.M international hospital suka isa cikin gaggawa suka amshe ta saboda yanayin jikin nata
kai tsaye emergency room suka shiga da ita.
mommy jin gina tayi da bango taufiq yace '' mommy me ya haddasa mata wannan ciwon ne..? ,
zama tayi akan waiting

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login