Showing 36001 words to 39000 words out of 39050 words

Chapter 13 - YAN ZAMAN MAKKAH BOOK COMPLETE BY OUMYASMEEN.pdf

18 May 2025

4125

mamaki tace '' mommy yaushe kika fita har wajen kenan kinje..?,
Eh naje yumna kuma yayi min bayani
gaban tane ya faɗi karfa ya faɗa mata gaskiyar duk abin da ya faru da yadda tsarin su yake
tace '' mommy me yace miki wanne bayani yayi miki..,
gyara zama mommy tayi tace '' yayi min bayani wanda ya gamshe ni saboda yace duk lokacin
da mutum ya so dawowa yana iya dawowa sannan a guri me tsabta suke kai mutum wanda
addinin sa ko imanin sa ba zai taɓu ba sai dai in mutum ne ya kaucewa dokar da suka shinfida
mai amma su aiki suke yi da addini abin yayi min dad'i wallahi har ayoyi da hadisai yake karanto
min mutumin masani ne kuma babban mutum wanda yasan kan'sa duk ya nuna min shedar
kasar nan tasan da zaman su akwai sa hannun hukuma da dama ya nuna min..,
ajiyar zuciya ta sauke tace '' to Allah dai ya dafa mana..,
amin ya Allah mommy tace ,
Bayan sallar isha ta shiga daki ta kwanta bacci me cike da jin dad'i har hango kan'ta take a
makka.
Washegari
da asubar fari ta shirya kayanta ma tas ta haɗa su ta daure su a zanin atamfa wayar ta kuwa
soke ta tayi ta saka a kugu
mommy ce ta shigo turus tayi ganin ikon Allah lamarin na yumna tamkar wacce aka jefe anya
kuwa wannan abin da take yi lafiya qalau take
mutum yana cikin gatan sa yace sai yabar cikin gatan sa ya koma wata uwa duniya ta sani sarai
ba yadda suka iya da ita shi ya saka suka barta kuma malam ma fushi yake da ita amma ko a
jikin ta duk da be buɗa baki ya furta ba fuskarsa ta nuna abin da yake zuciyar sa ajiyar zuciya ta

sauke tace '' yumna badai da safe zaku tashi ba..?,
cikin farin ciki tace '' a'a ba da safe za mu tashi ba nice dai kawai na shirya domin kinsan jirgi
baya jira sai dai a jira shi..,
hmmm Allah ya kyauta ta fadi haka zuciyar ta na mata wani irin suya Hajiyar su ma faɗa tayi
tace a kyale ta duniya tafi bagaruwa iya jima tas zata koya mata hankali idan dai son abin
duniya mutum zai yi to ba shakka zai girbi abin da ya shuka kuma zai halaka tana cikin wannan
tunanin ne yumna tace '' mommy wallahi saboda murna bazan iya cin abinci ba Allah ya sani ba
ƙaramin farin ciki nake ciki ba ‘‘ O,, Mamman yana nan yana figar talaucin sa ba damuwa idan
na dawo zan bashi dan na jari...,
da sauri mommy ta kalle ta sai kuma tayi shiru domin bata da bakin magana juyawa tayi ta fita
zama tayi a parlour zuciyar ta ba dad'i da ace juraij ya aure ta ba yadda za tayi dole ta zauna,
ga maganar abokin sa da yayi mata ma lamarin babu shi domin ya koma gida hutu be kuma
ƙara yi mata magana ba , Allah dai ya tsare rayuwar ta
mommy mommy mommy
da sauri ta ɗago tace '' juhud har kin shirya yau da wuri haka..?,
zama juhud tayi tace '' mommy tunanin me kike yi haka..?,
ba komai juhud
hmmm wallahi nasan ba zai wuce na yarinyar nan ba haka kurum kun dauki son duniya kun
ɗora mata kun kasa hanta abin da tayi niya tun da tace sai tayi sai ku zuba mata ido gata ga
hanya nan karta tsaya a makka ta , tafi bangon duniya wannan matsalar ita , ta shafa ni wallahi
ko san ganinta ba nayi haka kurum ta jefe ki a cikin tunani kina ga ranar da malam ya bar gidan
nan idon sa yayi jajir ko wannan hakkin da ta kwasa wallahi Allah ba zai barta ba

da sauri ta ɗaga mata hannu tace '' juhud ya ishe ki, tafi bana son kara jin komai daga, gare
ki..,
tashi tayi jikin ta a sanyaye tace '' mommy Allah ya baki hakuri amma wallahi yarinyar nan..,
Cikin ƙara ji ta tari numfashin ta, tace '' nace miki bana son jin komai daga, gare ki, ki tafi inda
zaki Allah ya kiyaye hanya..,
juyawa tayi tana cewa amin..
dafa kan'ta mommy tayi ta lula duniyar tunani har lokaci yaja bata sani ba a guje yumna ta fito
tana cewa mommy mommy mommy.
da sauri ta ɗago tace '' yumna me ya faru..?,
cikin murna tace '' yanzun nan aka bugo min waya, wai na zo za'a gama haɗawa mu ayi duk
wani bincike da ake yi sannan sai mu tafi kin san fa muna da yawa..,
mommy tace '' to bara salisu ya kai ki..,
a'a barni abin da gurin ba nisa ni daman na gama haɗa kaya yauwa idan kin yi waya da gida
kice kina gaishe su jirgin mu ya tashi insha'Allahu duk wani kunci na rayuwar su zai zama tarihi
idan na samu dama komai yayi dai-dai zan kira ku mu gaisa amma dan Allah kar wanda ya
kirani ya taku ramin ina aikina kin san fa basa son Kiran waya wallahi idan na kirawo Na'ima
dakyar take dagawa dan haka kar wanda ya kirani haka kurum su koreni su dawo dani niger
ban tari abin arziki ba..,
salati mommy ta saki, amma ko a jikin yumna sai ma ƙara washe baki take dan ita bata ga abin
aibun da tayi ba gaskiya ta fadi haka kurum ayi mata kutungwila ayi mata kafar kwaɗo su dawo

da ita Niger babu shiri.
shiga daki tayi ta fito da kayanta a ɗaure a zani ta ɗora su a kanta cikin washe baki tace '' to
mommy saduwar alkairi duk ki faɗa musu fa karki manta da ace ina Agadez da ko wanne gida
sai nabi nayi musu sallama..,
Mommy ta dago da kyar saboda sarawar da kan'ta yake mata tace '' Allah ya kiyaye hanya ya
bada sa'a..,
cikin farin ciki tace '' amin ya Allah..,
ta faɗa tana tafiya cikin farin ciki yau har wa'yanda bata yiwa magana a cikin gidan ta dinga bin
su tana yi musu sallama so sai ma'aikatan gidan suke mamaki tsayawa tayi akan mati tace '' to
mati Allah ya kirani..,
da sauri ya ɗago ya dena gugar da yusrah ta bashi yace '' ikon Allah mutuwa kenan za kiyi..,
wani kallo tayi mai na anya kuwa kana da hankali sannan tace '' a'a lahira zan tafi ku shikkenan
ba yiwa ɗan adam kyakkyawan zato sai ku zargi mutuwa dan nace Allah ya kira ni to ba
wannan kiran nake nufi ba yau makka zan tafi duk wani bukata da kake da ita sai ka rubuta min
a takarda domin muna sauka cewa zanyi akai ni harami na dafa ka'aba na roki Ubangiji.., dariya ya fara yi har da riƙe ciki sanan yace '' uhmm uhmmm yumna a ɗinga haɗawa da
insha'Allahu..,
banza tai mai ta fara tafiya wayar ta ce taji tana ringing da sauri ta ciro ta , ta ajiye kayan ta a
harabar kofar gidan nasu ɗagawa tayi tare da karawa a kunne tana cewa hello shamsiyya bana
son bakar jaraba tun ba saba har kun fara kirana..,
shamsiyya tace '' ke da hallacan wannan tafiyar da za kiyi bata gaba na wallahi tun da kin zaɓi
bin yawon duniya da ki zauna gidan miji zaman bautar aure...,
kuttumar ubancan kayya sa lallai yau kin taɓo tsuliyar dodo dan ubanki ina ruwan ki da rayuwa
ta kaga shegiya yar bakin ciki tafiya ce ba fashi sai na yi ta , muna sauka zan ce musu su kaini
ka'aba na roki Ubangiji na haɗa da munafukai da yan hana ruwa gudu duk Ubangiji ya hana
daku yayi magananin ku shegiya me mutuwar zuciya ni an faɗa miki irin kice to buɗe
kunnuwanki da kyau ki jini billahilazi wuwarramanu ko mamman be sake ni ba , sai na saka ya
sake ni dan wallahi in har be sake ni ba sai na yanka mai ticket din tashin mutunci kala kala sai
ya gwammace kiɗa da karatu dan uwar babanki
dan haka bara na fito mutu miki a mutum ni wannan sakin gaba takai ni kuma itama innar su
hindatu zata ci jakar uban'ta wallahi na dawo sai na siya gidan su na saka an rushe shi,
Cikin yanayin zafin rai da fusata bakin malam har rawa yake bakin ciki ya tokare mai zuciya tari
ya fara yana cewa yumna ko bayan raina karki sake ki dawo cikin gidan nan na yafewa duniya
ke in har na isa da ke ki dawo ki zauna idan kuwa kika saka kafa kika tafi to wallahi ban yarda
ba ki kara tako kafar ki cikin gida na da suwan kin dawo karya kike ki ɓata min suna, karya kike
ki zubar min da mutunci na..
Inna hadiza tace '' da kyau abin da tun farko ya kamata kayi kenan ka tsaya kai mata sako
sako..,
runtsai ido yumna tayi ashe rashin arziki shamsiyya ta shiyar mata hmm dai-dai take da su tace
'' malam tun farko fa kai kace na tafi kuma yanzu kace ba in da zani..,
Yumna in har na isa da ke to ki dawo ki zauna cikin yan uwanki..
to kawai tace ta kashe wayar ta mai dai ta inda take tana cewa wallahi ba wannan Maganar ko
a kotu maganar farko ake dauka dan haka nayi nan munafukai ne suka zuga ka shegu masu

tafiya da lahira da ƙoƙon dambu sai naci kan uwar su a hannu a hankali zasu gane wace ce ni.
ɗaukan kayanta tayi ta ɗora akai ta ci gaba da tafiya tana zancen zuciya har ta isa lokacin tana
shiga ana ƙoƙarin jera mutane a mota da sauri ta ƙarasa ta turmusa ta shiga zama tayi tana
sauke ajiyar zuciya yumna nura da sauri ta ɗago cikin mamaki tace '' lah Layla ashe kin zo..?,
dariya tayi tace '' eh wallahi amma ki sauka kafin wancan ya gano ki ko baki ga saka mutane
yake ba yana kiran serial number su...,
ke kyale sa wallahi naga guri ba in da zan sauka kina tunanin wannan uban yawon namu motar
nan ba tai mana kaɗan ba ai wallahi kawai barsu salon ace sai gobe tun da har yau nayi
sallama da kowa to bazan koma ko ina ba..,
Ke dan uwarki fito na saka kine taji muryar wanda yake jera mutane ya fadi haka da sauri ta
juyo tace '' me uwata tayi maka, ka zage ta haka kurum ina ma laifin kace min na fito sai ka
zage ni..,
a fusace yace '' zaki fito ko sai na fusgo ki tun kafin ki tafi kin fara mai da mana da magana ina
da mun kai ki ai sai dai ki ce zaki dauki hannu ki dake mu..,
a fusace ta fito tana murguda mai baki sakar baki yayi yace '' oga kallo yarinyar nan anya kuwa
ba hakura za mu yi ba kaga tun yanzu neman fasa min baki take..,
wanda a ka kira da oga yace '' muga visa ki..,
da sauri ta kunce kayan ta, ta ciro ta miƙa mai , amsa yayi ya gama dubawa yace '' wannan ba
a nan motar za a saka ta ba a can take...,
da sauri ta dauki kayan ta tabi wanda ya yi mata alama da ta bishi kara chanje kayanta su kayai
sannan suka nuna mata gurin zaman ta ba dadewa motar su ta tashi a hankali ta fara tafiya har
kuma ta hau titi ta soma gudu tamkar zata tashi sama ware ido sosai yumna tayi tana kallon
garuruwa har suka zo filin tashin jirage nan ma ƙara duba su a kayi tare da yi musu rubutu a
cikin visa su sosai yumna take baza ido domin ta ga layla amma na iya ba labarin'ta wata
zuciyar tace to ko ba jirgi ɗaya za su hau ba ne.
bata da me bata wannan amsar a haka aka yi gama checking din su sannan aka basu set
number su shiga yumna tayi tana kalle kalle zama tayi cikin farin ciki ina ma tana da babbar
waya ta dauki kan'ta photo kallon matar kusa da ita tayi zata haife ta tace '' ina kwana..,
matar da taci uban jambaki ga belching dena taunar chingum din'ta tayi ta fara kallon ta sama
da ƙasa sannan tace '' lafiya qalau ke daga ina kike..?,
murmushi tayi tace '' yumna nura Agadez ni yar garin Agadez ce ..,
kai ta gyaɗa tace '' oh kema kenan neman arziki kika fito da kananun shekarun ki..,
gyara zama tayi tace '' aunty wa zai zauna yaga zama ai nima fitowa nayi a dama dani..,
dariya ta sheke da ita tace '' ai kuwa kin yi kyan kai wallahi yanzu rayuwar nan idan baka tashi
ka nema ba , to kana cikin takaici da bakin ciki dan wallahi wannan numfashin da muke shaƙa
da ace a hannun dan adam yake to yasin wani hanaka shekar sa zai yi dan haka tashi mu
nema ya zame mana dole ni kinga aurena na ballo na tawo haka kurum zan zauna ne ina cin
garau garau mijina ga bakin talauci haka na tsallake ya'yana na ce na tafi nemo arziki..,
hmmmm aini dake kamar dan juma ne da dan jummai sai dai banbancin wasu abubuwan
da sauri ta kalle ta , ta miƙa mata hannu suka tafa tace '' Masha Allah kenan zamu ce ta tarar
tawo mu tafi ya akai aka haihu a ragaya..?,
limshe idon'ta tayi tace '' labarin yana da tsayi amma zan baki shi tas..,
dariya ta sheƙe da ita lokacin kuma aka soma sanarwa jirgi zai tashi kowa ya saka belt tare da

kashe waya ko saka waya a play mode da sauri suka fara sakawa a hankali jirgin su ya fara
tashi yana ƙoƙarin keta hazo dad'i ne ya kamata yumna tace '' aunty na yarda da komai nufin
Allah ne yau gamu a cikin jirgi wanda sai wane da wane suke shigar sa..,
dariya tayi tace '' tabbas Allah ya nufa sai fatan dacewa da samun rahamar Allah...
haka ne wallahi ta faɗa tana kwantar da kanta a jikin kujera tare da kallon saman cikin jirgin.
wata mace ce ta soma zagawa ganin kaya a gaban yumna tace '' ki ɗauke shi ki saka a loka..,
to tace ta tashi ta bude abin saman kan'ta daman taga mutane na sakawa amma tace ita gwara
kayanta a kusa da ita yafi mata sauki haka kurum taje su zurare ta ƙasa ya za tayi da za ta saka
idan taje can..
gama sakawa tayi ta komai ta zauna sosai suka dinga keta hazo har suka sauka gama saita
kan'sa jirgin yayi suka fara fitowa zare ido yumna ta fara yi tana kallon wannan matar tace ''
aunty ya ban ga ka'aba ba , kamar wa'yannan mutanen ba larabawa ba kin gan su ba jallabiya
sun ci ƙananan kaya.., nima abin da na gani kenan amma ai larabawa suna saka kananun kaya suna cikin wannan
maganar wani mutum ya ƙaraso yace '' kune wa'yanda kuka tawo daga niger ko..,
kallon mamaki su kai mai ganin yayi hausa raɗau dukkan su kusan su ashirin suka ce eh mune.
okay ku biyo ni.....
bin bayan sa su kayi, har suka isa wani guri wani mutumin ne sukai magana da matar nan da
suka zauna guri ɗaya da yumna sannan ya tafi be kula ba ya ban gaje yumna da sauri yace '' yi
hakuri..,
yumna tace '' bakomai wallahi,
sosai tayi mamakin jin yayi hausa kenan daman yan kasar makka akwai masu jin harshen
hausa kenan
tana cikin wannan tunani ta dauko mata kayanta ya miko mata amsa tayi ya juya ya fara tafiya.
fara binciken su a kayi zuwa gurin yumna su kayi suna bincike kayan ta suka dauko wodar ibilis
da wasu kayan maye..
nan danan gurin ya dauka jami'an tsaro suka hallara a gurin kuka ta fashe da shi ganin an
rutsa ta da bindiga,
ankwa wata yar sanda ta saka mata kuka ta fara yi domin bata san me tayi ba kallon aunty tayi
da sauri matar ta matsa da ga gurin cikin Muryar kuka tace '' wallahi ba abin da nayi me nayi...,
bindiga wani ya saka mata a maƙoshi
wasu motoci ne suka shigo airport din a guje suka za gaye wa'yanda suka rutsa yumna buɗe
motar wani yayi suka tura ta ciki kanta bugar glass din motar yayi hawaye na bin kuncinta sosai
ta shiga cikin wani irin tashin hankali gashi ba damar yin magana duk sun rutsata da bindiga a
kuje suka fita tamkar zasu tashi sama tare da yin jiniya kuka sosai yumna take yi ta shiga uku
bata da kowa sai Allah Ubangiji ya zama gatan ta..
ba irin dana sanin da ba tayi ba tuni yunwar da , ta fara ji ta neme ta , ta rasa ba ƙaramin
tashin hankali ta shiga ba lokacin da suka iso police tasion irin tsaron da ta gani ba ƙaramin guri
aka kawo ta ba baza ta iya karanta komai ba domin rubutun da aka yi a bakin kofar gurin kamar
larabci kamar ba larabci ba kan'ta ne ya ƙara juyewa ta shiga wani irin hali tusa ƙeyar ta su kayi
da bindiga har suka shiga ciki a wani guri me raga aka ajiye ta zate ido ta fara ganin jami'an
tsaro sai bincike suke yi a cikin wata computer wasu kuma na daga abin da ita tasan bata saka
shi ba a cikin kayan ta ba suna rubutu a ciki da kuma wata takarda wasu ne suka ƙara fita.

duk sanyin gurin wani irin gume ne yake keto mata tun daga tsakiyar kan'ta.
a hankali ta furta ya Ubangiji ka fitar dani daga cikin wannan azzaluman mutanen..
hawaye na bin fuskar'ta zuciyar'ta tamkar zata faso kirjinta ta fito...

END OF BOOK

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login