Showing 9001 words to 12000 words out of 39050 words
Chapter 4 - YAN ZAMAN MAKKAH BOOK COMPLETE BY OUMYASMEEN.pdf
buɗe jakar ta kudi ta dauko masu yawa ta bata noke ka faɗa tayi
tace '' biki zanyi hutu fa muke yi..,
to jeki ki faɗawa malam sannan kuma ki bashi hakuri.
da sauri ta tashi ta fita akan igiya ta dauki mayafin'ta ta fita waye har yanzu yana kan tabarmar
sa sallama tayi tamkar wata mumina malam da ya riga ya karan ce ta tsaf ya dauke kansa zama
tayi tai shiru ta matsai kwallar karya tace '' malam dan Allah kai hakuri ka yafe min na dena
wallahi zan zauna dashi yau ba mamman ba ko wani kace na aura zan aura mommy tai min
wa'azi naji na ɗauka duniyar nan nawa take idan yau mune gobe ba mu bane dole sai muna
sakawa zuciyar mu hakuri muna koyi da halin annabawa zan rungumi kaddarata.
dan shiru malam yayi yana auna kalaman ta anya kuwa ba da wata a ƙasa ba yafi kowa sanin
halin yumna ita din kaska ce sannan da musa ce bata ladabi a banza yace '' yumna anya
kuwa..,
hawaye ta matso dakyar ta share fuskarta tace '' wallahi malam da gaske nake karka kasa
shakku akan komai Ubangiji ke shiryar da bawa a lokacin da ya gadama a kuma lokacin da ya
so dan girman Allah ka yafe min shima zan bawa mamman hakuri komai ya wuce mu dawo
kamar da., shiru yayi yana ƙara nazarin maganar ta anya kuwa ba wasan kwaikwayo za tai mai ba yumna
fa yumna fa karfa ya sakan kance ta zame mai yar kunama yace '' to Allah ya yafe mana baki
ɗaya ..,
amin ya Allah malam dan Allah ina so nabi mommy daman ai na ce maka idan akai hutu zan je
kaga tun bikin da tayi ban ƙara zuwa ba , dan Allah malam karka ce min a'a ina son zuwa.
Please subscribe.
https://youtube.com/@nasreenminallah?si=fWc7Wzd4nPx_TifU
EPISODE 5
Shiru malam yayi yana tunanin maganar ta ajiyar zuciya ya sauke yace '' yumna kunfa kusan
komawa makaranta..,
marairaice murya tayi tace '' dan Allah malam.,
to Allah ya tsare hanya ya faɗa yana dauke kai da ga kallon ta yafi kowa sanin wace yumna shi
ya saka baya barin ta taje ko ina , shi da ta zamewa dole ya riƙe abar'sa ɗayan kan yumna
yawa ne dashi riƙon mahaukaci sai sarki.
ganin yayi shiru ta tashi tana washe baki ta fara tafiya a kofar zaure taci karo da mommy cikin
jin dadi tace '' mommy ya barni..,
momy tace '' kai Masha Allahu haka ake so jeki ki debo kayan ki.,
da gudu ta kara sa shiga cikin gidan ba wanda tayiwa magana baba lami da take raba abinci
tace '' yumna zo ki dauki naki..,
uhmm na koshi
ta faɗa tana shiga daki tare da bude kwabar kayan ta tana sauko da su ƙasa.
da sauri ta ɗago ta kalle ta tace '' kin koshi fa kika ce me kika ci..?,
ɗagowa tayi tace '' ɗazu aka kawo min farfesun kaji..,
zaro ido baba lami tayi ta kalli yaya Hadiza ta jin jina kai lallai lamarin aljanun yumna abin
kullum gaba yake yi.
ganin sun lula kogin tunani tace '' ko na saka a kawo muku, kuna so ne..?,
da sauri inna hadiza tace '' a'a yumna mun gode..,
bata ce ƙala ba ta ci gaba da shirinta zuciyar'ta fes bayan ta gama hada itana ina ta , ta fito
tsakar gida tace '' to saduwar alkairi ni na tafi arlit..,
cikin jin dadin tafiyar ta ya'yan su zasu sake su wahala baba lami tace '' Allah ya kiyaye hanya,
amin yumna tace tana ci gaba da tafiya tana fita waje tararwa tayi har sun shiga mota ita suke
jira da sauri ta kwankwasa musu bude kofar mommy tayi ta shigo tare da jakar kayan ta
ɗora su tayi a kan cinya mommy ta rufe kofar suka fara tafiya kwantar da kanta tayi a kan
kayan ta , tai shiru tana sake sake kala kala a zuciyar ta ,
sun fara daukan hanyar arlit mommy tace '' dan Allah yumna ki nutsu aure da kike gani ibada ne
kinga wannan aikin da kike so ki tafi babban hatsari ne idan har baka hadu da na gari ba.,
shiri tayi tana sauraron zancen tamkar tana busa mata sarewa babban burin ta , sudai isa za
nemo agent din na'ima tunda ai a arlit yake itama yayi mata visa bayan ta fito daga gidan
Mamman ta , tafi makka dole ayi gwagwarmayar rayuwa da ita dan cimma burin ta ba abin da
ake samu ta cikin sauki dan haka ta daura damarar yin komai tun da dai ba wata hanya mara
kyau zata bi ba amma sun bi sun ɗaga hankalin su yawan wanda zata tafi yawan karuwanci
tafiya ce ba fashi kamar tayi ta ta gama ne.
anya kuwa ma sun san me duniya take ciki kai gaskiya basu sani ba da sun sani da sun mara
mata baya.
da wannan tunani bacci ya kwashe ta . Cikin ikon Allah suka isa
*ARLIT* ungumar Cité COMINAK
Horn yayi mai gadi ya bude masa tura hancin motar sa yayi ya shiga cikin hamshakin gida kallo
ɗaya zakai mai kasan cewa gida ne masu hannu da shinu..
a parking space ya ajiye motar ya kashe tasowa yayi ya budewa mommy fito wa tayi tana cewa
dan Allah juraij tasar min ita ka dauko mata kayan ta jikin ta ya saki yanzu ba zata iya daukan
komai ba.
takaici ne ya tukare shi bazai iya yi mata musu ba dan haka yace '' mata to..,
zare kayan yayi ya buga mata ledar kayan ta akai da sauri ta zabura tare da danno wani uban
ashar tace '' wane dan takazar uban ne ya dake ni akai.. Alkur'an ba zan yarda ba sai naci
kaniyar mutum.
bata ƙarasa faɗa ba juraij ya buge mata baki kuka ta saka tana kallon sa cikin tsare gida yace ''
zaki dena kallo na ko sai na fasa miki fuska da wani idon ki me kama dana mujiya..,
share hawaye tayi ta fito daga cikin motar tace '' ai a dangin ku ba maƙeri duk wanda ya raina
tsayuwar wata ya nemo tsani ya hau ya gyara..,
da sauri ya zare Écouteur (earphone) da yake ƙoƙarin sakawa yace '' me kika ce..,
kai ta shiga girgizawa tana ja da baya jin tayi taci karo da mutum kafin ta gama tantance wa
taci karo dashi taji an zabga mata mari da sauri ta dafe kuncinta ta kurawa wacce ta mare ta ido
ko kifta wa ba tayi a cikin fusata ahlam tace '' chérie (honey) a ina ka samo wannan bagidajiyar
wallahi ina upstairs na hango ku ban san ma na sauko ba , bana iya ganin gaba na., ahlam ta fadi haka cikin tsananin zafin kishi tare da tallafo habar juraij.
hannun ta ya sauke ƙasa ya riƙe be yi magana ba ya fara tafiya kin binsa tayi tace '' magana
fa nake maka kayi shiru badai da kaje sabon gari ba suka aura maka ita..,
murmushi yayi yace '' aahhlam wallahi ina tsoran randa kishin ki zai illatar min dake, ko dan abin
da ke tare da ke ya kamata ki rage damuwa zuwa tayi hutu..,
ajiyar zuciya ta sauke tace '' wallahi juraij zan iya kisa akan ka duk randa wata tayi gigin
shigowa rayuwar mu to sunan ta gawa na yarda na ƙarshe rayuwata a prison da ka auri wata..,
bata ƙarasa ba taji saukar sanda a dokin huyan ta durkusa'wa tayi ta saki wani irin wahalallan
ihu..
juraij da ya shiga wani hali a riki ce yace '' sweet me ya faru badai cikin bane na shiga uku ya
Allah, duk tattalin da na ke yiwa wannan abu kar ace zu bewa zai yi..,
da hannu tayi mai nuni domin bata da bakin magana ɗagowa yayi ido hudu sukai da yumna
tana murguda baki tare da cin ɗamara da mayafin'ta tace '' ce miki akai jaka ce tayi yaye ni da
zaki dake ni ku da tattabaru sarkin aure ko to wallahi duk wanda yayi min ba zan raga mai ba ai
ba jaka aka kawo miki ba , Allah ya saka mazalkwaila ce uwar alawa kuma idan baki sani ba ki
sani yau aka ɗaura mana aure sai ki mutu dan kishi..,
sakar baki juraij yayi yarinyar ta soma ba shi tsoro yawa aljana kai anya kuwa kanta ɗaya dole
ya koya mata hankali shu'umancin'ta yayi yawa dole ya tauna tsakuwa domin a'ya taji tsoro a
fusa ce ya taso yayin da ahlam ta zun duba ihu ta danƙi huyan, yumna.
duk karfin yumna kasa kwace wa tayi da ga rikon da ahlam tayi wa wuyan ta zaro ido ta din ga
yi
idon ahlam ya rufe babbar buƙatar taga ta kai yumna kasa , taga ko motsi ba tayi cikin ɗaga
murya tace '' wallahi ina gamawa da ita kanka zan dawo daman ni naji a jiki na wannan yarinyar
zaka auro ka kawo ta Cikin gida na to wallahi Allah ahlam daka kai har ita yau sai na koya muku
*DARASI* wanda ko gaba aka ce ka ƙara gigin kawo min wata cikin gida na ba zaka ƙara ba..., Mommy da yusra suka fito cikin tashin hankali saboda me bawa shukoki ruwa ya je ya faɗa
musu ahlam zatai kisa dakyar mommy ta karbi yumna a hannun ahlam yumna kuwa zubewa
tayi a ƙasa tana farfari da idanuwanta zata tada aljanun karya ganin hankalin kowa yayo kanta
ta maƙe murya tace '' wallahi ba zamu yarda ba , ni turkwa dan gidan Sarkin aljanu zata
shaƙewa wuya to yasin sai na kwashe mata hanjin cikin ta tas...,
ahlam tana jin wannan magana ta ɗora hannu akan ta , ta zunduma ihu gumi duk ya karyo mata
ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba da jin wannan zance shikkenan unborn din su zai dena
rayuwa itama tasan mutuwa za tayi ƙara shiga wani hali jin surutan da yumna ke yi.
Mommy kuwa rasa me yake mata dadi tayi ta kalli juraij tace '' juraij dan Allah temaka ka dauke
ta ka kaita parlour muyi mata addu'a ko a samu ta dawo dai-dai...,
ƙara lankwasar da kai yumna tayi ta mai da hannayen ta baya tace '' yasin kana ɗaga kafar ka
sai na cire maka jijiya ɗaya a wuyan ka ka dena motsi na tsawon shekaru goma sha biyar..,
cikin fusata juraij yace '' ke zanci ubanki idan baki dawo dai-dai ba mu za kiyi wa Prétendre
(pretending ) zan babɓallaki idan baki tashi ba.,
sandarewa tayi ta mimmiƙe tare da miƙe hannayen ta tace '' yau zaka ga me zai faru dole su
aljani tsifur su tafi dakai..,
mommy tace '' juraij bana son wauta karka sake ka ƙara cewa ƙala ka tafi gidan liman ka kirawo
shi..,
bece komai ba ya juya yumna najin haka ta dinga sakin atishawa zunbur ta tashi tace '' mommy
jikina ciwo yake min..,
mommy kamo yumna tayi ta rungume ta tace "sannu Allah ya baki lafiya.."
ɗagowa tayi ta kalli mommy tace ''me ya faru..?ni lafiya ta qalau...,
tausayin ta ne ya ƙara kama ta , mata tace '' bakomai tawo mu je ki ci abinci kiyi wanka...,
washe baki yumna tayi ta juya ta dauki kayan ta , tace muje mommy..
mommy tace '' yusra kuje parlour ke da ita ina zuwa juraij tsaya..,
to yusra tace ta riƙe hannun yumna suka shiga daga ciki kallon ahlam tayi da har yanzu ba ta
dena kuka'ba tana shafa cikin'ta takaicin tane ya kama mommy tace '' ahlam sai kiyi shiru tunda
komai ya lafa me ya faru..,
ba kunya ta rungume juraij tana kuka tace '' wancan sandar ta dauko ta buga min a kafaɗata
haka kurum kuma ashe juraij cin amanata yake wallahi ba zan yarda ba sai ya sake ta ko kuma
na cire mata wuya..,
cikin mamki mommy tace '' kanki ɗaya kuwa kinsan me kike fadi..? wa za ki cirewa kai ..?,
dukan kirjin juraij ta fara tana wani gunjin kuka riƙe mata hannu yayi yace '' ahlam kanki ɗaya
kuwa..? karya take fadi..,
a fusace tace '' kai na dubu ba ɗaya ba daman kana da kunyar da zaka iya kallon idanuwana ka
faɗa min haka...? to yasan ka jawa kowa na gidan nan sai na kona yarinyar nan..,
mommy danne zuciyar ta tayi domin a ƙaramin takaicin halin ahlam take ba , ta mai da kan'ta
yawa ' wata naga akan kishi bata ji bata gani tace '' juraij wai me yake faruwa ne ka tsaya ka
zama gunki..,
cikin takaici yace '' wannan yarinyar ce tace mata wai an daura mana aure Ita kuma batare da
dogon bincike ba ta soma kuka shine fa ta shaƙe mata wuya..,
wacce yarinyar mommy ta tambaya cikin tsare gida ban da rashin kirkin juraij sunan yumna ne
ba sani ba kome.
da sauri ahlam ta kalle ta tare da share hawayen ta tace '' mommy sannu da zuwa..,
kai mommy ta dauke tace '' yauwa..,.
tare da juyawa ta bar gurin.
ahlam kallon sa tayi tace '' baby bazan iya zama ni kaɗai ba dan Allah karka fita kana dai ji abin
da aljanunun nan suka ce ko dan girman Allah karka fita.,
kai ya girgiza yace '' ahlam kardai ki ce min kin manta abin da kikai min yanzu..?,
turo baki tayi tace '' kai hakuri..,
kama hannunta yayi be ce mata komai ba suka soma tafiya kai tsaye shashin su , suka nufa,
zama juraij yayi yace '' ahlam yunwa nake ji me kika dafa..,
zama tayi tana kauda kai tace '' ni ba abin da na dafa bana son jin kamshin abincin dan Allah
idan kaga yusra tayi abinci nima sai ka samamamin na dan samu naci yunwa nake ji tun safe
da kai mana breakfast ban ƙara cin komai ba.,
bece komai ba ya tashi yace '' ki haɗa min ruwan wanka.,
turo baki tayi tace '' beb nagaji wallahi yarinyar nan duk ta wahalar da rayuwa ta Please kai
hakuri karka ce kana ta saka ni aiki ban yi ba nasan ba zaka ji dadi ba...,
juyawa yayi ya shiga bedroom yana shiga ta kwanta ta ɗauki wayar ta , taci gaba da kallon ta a
YouTube.
Wannan kenan
yumna tana shiga main parlour gidan ta nemi guri ta zauna tare da ɗora kafa ɗaya kan ɗaya a
zuciyar ta cewa take ina ma wannan gidan nata ne , Allah dai ka kaita makkan nan ta kwashi
arziki ta barshi a mazaunin sa.
ga abincin naki yusra ta fadi tana ajiye mata tray a kan center table.
da sauri ta sauko ta zauna tare da sauke tray din ƙasa tace '' Nagode..,
ya tsuna fuska yusrah tayi ta dauki remote ta zauna ta chanza channel.
taɓe baki yumna tayi tace '' halin ki ɗaya da wanki..,
da sauri yusrah ta juyo tace '' ke magan kike..,
shinkafa yumna ta watsa a bakin ta tace '' ah waka nake..,
ke dan ubanki ni kike faɗawa haka kaga shegiyar kauye..,
yusrah ta faɗa tana yowa kan yumna.
juya idanuwan'ta yumna tayi tace '' ina matsowa sai na hanaki kashi na tsawon kwana takwas
tare da ciwon ciki me tsanani..,
Chak yusra ta , tsaya gaban ta ya fidi yace rass dafe kirji tayi ta bar gurin tane cewa juhud juhud
juhud.
juhud fitowa tayi tace '' lafiya yusrah kike kirana yawa wacce na ci miki wani abin..?,
wallahi juhud mun shiga uku mommy ta kawo mana annoba cikin gidan nan.
cire glasses din'ta tayi tace '' annoba kuma a ina ..?,
zama tayi akan wasu kujeru da suke jere a gurin farare tas dasu gwanin sha'awa tace '' wallahi
annoba yar gidan aunty halima..,.
tunani juhud ta shiga yi domin ta dade ba'a kasar ba sannan koda can bata shiga sabgar
mutane balle yanzu da ta taka wani matsayi me girma aiki take yi a babban Company wutar
lantarki tace '' wace aunty halima ke ba'a raba ki da kwashe kwashe ke da mommy halin ku
ɗaya wallahi.., sister din mommy fa
dafa goshin ta tayi tace '' wallahi na manta ikon Allah ita tazo ..? da kike cewa annoba aka kawo
mana akan ki zata zauna ne yusra ki deba abin da kike yi wallahi haka kurum ki dinga damun
kanki da damuwar mutane..,
Ya Allah ya juhud baki fa ki tsaya kin ji me zance ba kin hau faɗa.,
sarke hannuwanta tayi a kirji tayi '' oya faɗa min ina sauraren ki..,
bata labari ta soma yi tun daga farko har karshe.
dariya juhud tayi tace '' wallahi kun ban dariya da ilimin ku da komai ku tsaya ana raina muku
hankali dama mom ta bar big bro yaci uban'ta gaba ko ce mata akai tayi wallahi ba za tai ba
karya ne ba wani aljanu yanzu ke saboda ta faɗa miki haka shi ne kika tawo nan kafin ta hanaki
kashi right..?,. cikin matsanancin tsoro yusra ta gyaɗa mata kai
murmushi tayi tace '' jeki ki dauke shegiya da mari zata fahimci nan ba can bane..,
cikin kwarin gwiwa yusra ta tashi juhud tace '' yauwa ta gida na idan da hali ki dauki tray din da
kika kai mata abinci ki kwaɗawa shegiya ni wallahi bana son irin wannan rainin hankalin.,
to kawai yusra tace mata ta sauka ƙasa samin yumna tayi ta zauna sai zuba uwar loma take yi
damarar ma da taci da mayafin'ta ta kunce ta ɗan acewar ta wannan damarar da taci hanata
sakewa za tayi gwara ta sakata ta wala ta fararraje gidan mommy ne taci duniyar ta da tsinke.
kaza ta dauka taci ta limshe idanuwan'ta wani dadi na ratsa mata jijiyoyin jikin ta ga sanyin AC
kai jama'a dole ta nemo arziki dole ta tashi tayi faɗa da talauci