Showing 18001 words to 21000 words out of 39050 words

Chapter 7 - YAN ZAMAN MAKKAH BOOK COMPLETE BY OUMYASMEEN.pdf

18 May 2025

4120

na'ima ta saki ƙara kuma taki daga
wayar ta ,

karon farko a rayuwar ta da , ta mike ta dauro alwala ta gabatar da lafi'la tare da rokon Ubangiji
Allah ya shiga lamarin ta ya cika mata burin ta bayan ta idar ta zauna har akai kiran sallar asuba
yadda taga rana haka ta ga dare ana kira ta tashi ta yi sallah ta dade nan ma tana rokar
Ubangiji ya cika mata burin ta na tafiya makka Allah karya taɓar da ita. ya Ubangiji Allah ya saka tayi tafiyar nan a sa'a ta faɗa hannu me kyau hannun da zata sami
abin duniya bayan ta idar ta zauna a lokacin kuma ta ƙara kiran number na'ima sai dai har
yanzu a kashe take to me yake faruwa ta fara zargin anya kuwa lafiya,
tana cikin wannan tunanin ne akai knocking din kofar dakin ta tashi tayi ta buɗe fuskar nan ba
walwala tace '' ina kwana..,
shima fuskar sa a ɗaure take tamau ba ɗigon annuri a fuskar sa yace '' lafiya kije ki ɗora mana
petit déjeuner (breakfast) da wuri nake fita office so bana son ɓata lokaci..,
shiru tayi tamkar me tunani tana sane tayi haka , tayi hakan ne domin ta bata mai rai ilai kuwa
sai da ya magantu yace '' ke ba magana nake miki ba..,
da sauri ta ɗago tana taɓa kunnen ta tace '' oh ban ji ba me kace..,
wani kallo da yayi mata dole ta hadiya sauran zancen ta batare da ta shirya hakan ba miskilin
murmushi yayi ya juya ya rufo mata kofar ta ahlam ta zaune akan kujera tana cika tana
batsaiwa zama yayi yace '' ni zan shirya na fita na siya restaurant domin bazan iya cin kirkin
yarinyar nan ba , tun da ke zaki iya sai kici ko ba komai ta sauke nauyin da ni ya kamata ace na
sauke tun da ke bakya iya shiga kitchen..,
dauke kai tayi tace '' nifa har yanzu ina kan bakana sai ta bar min gida gwara na girka da kai na
ko da abin da ke ciki na zai zube..,
da sauri yace '' a'uzubillahi da bakin ki kike fadar haka haba ahlam me yake damin ke ne..,
Cutar da ka zaɓa min ita take damuna ban da rainin hankali yarinya ta dinga faɗa min magana
amma ko sau ɗaya baka saɓa mata halitta ba sai dai idan akwai wata a ƙasa.
girgiza kai yayi ahlam tayi nisa bata jin kira yarinyar da an kusan bikin ta amma ta dinga fadar
haka yace '' baki san an kusan bikin ta ba me zan yi da ita sanin kan kine da ina da sha'awar
ƙara aure da tuni nayi amma ki bi ki dinga daga hankalin ki me kika nema wanda bana yi miki
shi komai ina miki domin farin cikin ki amma bakya gani..kullum zancen ki kishiya, Wannan littafin na kudi ne ki biya ni ki karanta halalin ki,
500 kacal idan ya zama document ya koma 1k

Amina alhasan Muhammad opay
8141785374
Ku turo da shedar biya ta wannan number 08141785374
Yan niger kuma 1000fcfah
ku turo ta my nita
Amina Muhammad alhasan 08141785374
sai ku turo min da shedar biya ta wannan number 08141785374
Free ya kusan karewa.
https://youtu.be/_IOc2pOwgKk
Copy is not allowed
Episode 9
Juraij idan fa kana so ni da kai mu zauna lafiya a cikin gidan nan to wallahi ka fitar da yarinyar

nan daga gidan nan abincin ma na hakura zan shiga kitchen da kai na , na dafa ana dole ne ni
wallahi duk wani zance da zaka faɗamin wai an saka mata rana an kusan bikin ta an daura
auren ne naga take taken ta ɗan haka tun kafin dare yayi mata tabar min gida na.
Yumna ce ta fito jin abin da take faɗi ta yi murmushi iya labɓanta domin ta kara tun zura ahlam
ai kuwa tayi faɗa ta shiga yi ta inda take shiga ba tanan take fita ba.
ɗurƙusawa tayi tace '' aunty ina kwana..,
tayi pretending bama ta gane me take nufi ba da faɗan da take yi.
haushin ta ne ya kama ahlam ganin ta mai da ita yar iska cikin zafin rai tace '' ke kwaso kayan ki
, kibar gidan nan.,
da sauri yumna ta kalli juraij ganin ba abin da yace tashi tayi ta shiga daki daman itama ta gani
haka kurum su dinga saka ta bauta sai kace wata jaka da sassafen nan shi gashi me mata yar
gwal ta tashi ta yi musu breakfast itafa wannan abu gaba ya kai ta gobarar titi ajos.
kwaso kayan ta, tayi ta fito bata ko kalli inda suke ba ta fita taci sa'a gate din a buɗe yake fita
tayi kai tsaye part din mommy ta nufa shima nan sun tashi suna breakfast ga mahaifin su juraij
yana zaune shima sallama tayi ta sunkuyar da kai da sauri mommy ta ɗago tace '' yumna ya
kika dawo na ganki kuma da kayan ki Allah i saka lafiya me ya faru...?, Alhaji Mahmud ya goge bakin sa da tissue ya tashi yace '' yusrah idan kin gama ki zo sai salisu
ya ajiye a makarantar taku ya wuce dani motar da ake kai ki ta lalace..,
tsugunawa tayi tace '' ina kwana..,
bata re da ya kalle ta ba yace lafiya qalau alhamdulilah kin zo lafiya ya su malam..
suna lafiya tace mai tare da tashi gaishe da mommy tayi batare da ta bata amsar tambayar da
tayi mata ba Alhaji sallama yayi musu ya fita yusrah ta bi bayan sa zama tayi tace '' mommy ta
koro ni wai karna aure mata miji..,
dariya mommy tayi juhud kuwa daman tasan za'a rina an saci zanin mahauciya ci gaba da
cin chips din'ta mommy tace '' to shikkenan za mu haɗu dashi da yazama saunan namiji matar
ka ta kori yar uwar ka kuma ka zauna kana yaƙe mata baki sosai mommy take faɗa juhud ko tari
ba tai ba da ta gama sai ta rataya jakar ta tace '' mommy sai na dawo..., harara ta zabga mata tace '' Allah ya tsare hanya..,
murmushi tayi tace '' amin ya Allah ta fita.
gyara zama tayi tace '' mommy ni bazan ƙara zuwa gidan sa ba tun da korata suke yi..,
bata dai ce mata komai ba sai daukar wayar ta da tayi ta lalubo number juraij bugu ɗaya ya
dauka cikin bada umrani tace '' kazo ina son ganin ka..,
bata tsaya amsa gaisuwar sa ba ta kashe wayar ta.
ɗaukan plate tayi tace '' yumna kin ci abinci..?,
girgiza kai tayi tace '' a'a banci ba.
zuba mata tayi ta tura mata gaban ta farfesun kaji ne ga buredi ci ta fara yi tana ci da biredi
sosai duniyar yumna tai mata dad'i.
tashi mommy tayi ta hau sama
juraij ne yayi sallama yumna da take tsaka da cin kazar ta , bata amsa ba tsawa ya daka mata
yace '' ke bakya amsa sallama ne..?,
lashe hannun ta tayi ta saki wata uwar gyatsa ta kora da kunun tsamiya takaici ne ya ture
zuciyar juraij ransa a matukar ɓace yace '' ba magana nake miki ba ..,
da sauri ta juyo tace '' uhmm ban jika ba ..,

kwafa yayi yace '' ina mommy take ..,
nima ban san inda take ba da zata tashi bata sanar min ba.
da sauri ya ɗago jin amsar da ta bashi lallai yau idan be karya yarinyar nan ba to be ciki jinin
Mahmud ba.
fisgota yayi ta faɗi ƙasa tare da sakin razananniyar ƙara saboda ball da yayi da ita ya mare ta
sai da taga wasu taurari sun gilma mata a idanuwanta.
ba shiru mommy ta dinga hada matattakala biyu uku tana saukowa tace '' juraij lafiyar ka kuwa
me tayi maka banda ci mata mutunci da kuka yi kai da yar gwal shi ne yanzu ka biyota zaka
karya ta ko to wallahi idan ka jamata wata nakasar wanda zai aure ta yace ya fasa kai zaka
aure ta ko kana so ko baka so.., da sauri ya ɗago jin furucinta na ƙarshe me zai yi da yarinyar nan , to ma ya sakata a wanne
gurbin cikin kwantar da murya yace '' mommy yarinyar nan bata da kunya wallahi dan baki ga
maganar da ta faɗan ba tambayar ta nayi kina ina tace bata san inda kike ba lokacin da zaki
tashi baki sanar da ita ba , ke sa'ar ki ce ko kuma ni sa'an tane take faɗan wannan maganar
wallahi taci sa'a da banyi rugurugu da ƙashin ta ba dalilin kenan da ya saka ahlam tace baza ta
iya zama da ita ba jiya cikin girma da arziki ta dauke ta , takai ta daki tace ga dakin ta to wallahi
yarinyar nan ta daddaƙara mata bakar magana ahlam ta faɗa min ban goyi bayan ta ba ,
to nayi abokai sun zo suma tace ta zo ta dauko musu abinci ta kai musu nan ma sai da ta faɗa
mata magana yau ma da safe sai da su kayi..,
jikin mommy yayi sanyi ta ɗaga yumna tace '' kiyi hakuri jeki daki...,
tashi tayi tana ɗin gisa kafar'ta ,ta shiga dakin mommy zama mommy tayi tace '' wallahi abin da
ahlam tayi raina ya ɓaci wanne irin shashanci ne wannan yarinyar da an ma kusan bakinta
kaima bita zai zai har ka bari yumna ta , tawo yawa wani shanyayye..,
shiru yayi ya zauna a ƙasa yace '' kiyi hakuri mommy insha'Allah zan gyara kuskurena Alhaji ya
fita ne..,
Eh wallahi be jima da fita ba tun da kuka dawo daga masallaci sai aka kira shi a waya bayan
fitar ka za ayi meeting gaggawa shine fa ya fita da wuri shi zai sauke yusrah ma saboda motar
da za'a kai ta , ta lalace...
Juraij yace '' to Allah ya kiyaye hanya nima yanzu zan fita office..,
yauwa kama tuna min maganar auren yarinyar nan biki sai matsowa yake ya kamata kai a
matsayin ka na babban wanta kuma ga ba ran mahaifiyar ta mu za mu zama komai nata
mahaifinta ba karfi ne da shi ba bikin ya'ya har biyu kuma mata ba wasa ba ni ba zan iya
tambayar mahaifinku ba idan ya ga dama yayi to falillahil hamdu amma dai kai , ka kawo abin
da zaka kawo ai mata siyayyar kayan daki nima daga gurina zan mata na daki dana kitchen da
kuma sutura...
Mommy ta fadi haka tana kallon juraij domin jin me zai ce .
Shiru yayi yana nazari Sannan yace '' to zan turo miki kudin abinda ya dace sai kiyi mata Allah
ya bada zaman lafiya bama lallai ayi bikin da mu ba zan tafi Ingila wannan project ɗin tare da
ahlam...,
To Allah ya temaka amma da son samu ne ka zauna a yi komai da kai.
tashi yayi yana cewa ni zan tafi Allah ya tsaɓa mana abin da yafi zama alkairi.
Mommy tace '' Allah ya kiyaye hanya.
to haka ranaku sukai ta zuwa suna wucewa kullum da abin da yumna za tai wa ahlam duk da

bata barin ta shigar mata guri amma sai ta san yadda akai ta takaleta sukai faɗa tun mommy
bata lura har ta gane yumna matsokaniya ce hatta juhud da bata fiye zama a cikin gidan ba
bata kyale ta ba mommy ta dage sai gyara mata jiki take yi tayi kyau gwanin sha'awa ga hutu da
jin dad'i da take ciki. Yau tun da safe take buga number na'ima amma shiru ba'a dauka karshe ma dai a ka kashe
layin babban tashin hankalinta gobe zata tafi gashi batai abin da ta dace ba idan ta bar arlit bata
san yaushe za ta dawo ba , bata kuma da kuɗin dawowa tun da suna komawa jarabawa za su
zane ta gama secondary sai kuma auren su. zaman dirshen tayi a ƙasa ta rasa me yake damun ta ko wayo za tai wa mommy ta , tafita ta
nemo inda ake daukan mutane zuwa Saudiyya tana cikin wannan zance a zuciyar'ta taji
sallamar juraij da abokinsa ahlam na take musu baya wannan abu na bawa yumna haushi dul
inda juraij ya taka sai ta taka tamkar bata yadda dashi ba ta dinga leƙe mai dogon tsaki taja ta
mai da hankalin'ta kan wayar ta tana amsa sallamar'su.
zama Muhsin yayi yace '' my friend...,
da sauri ta juyo gashe dashi tayi ta matsa daga gurin tayi nesa da su juraij yace '' ina mommy
take..?,
tun safe ta fita unguwa ta bashi amsa still hankalinta na kan wayar ta.
ji yayi tamkar yayi ball da ita Muhsin yace '' yumna ba magana daga gaisuwa shikkenan nifa
zuwa nayi muyu hira..,
ɗago da idanuwanta tayi ta kalli juraij da yayi kicin kicin da haɗe rai banda iskancin muhsin ya
da faɗa mai an kusa bikin ta amma shine be jiba da yake kan albasa gare shi.
tashi tayi ta shiga kitchen tray ta dauki ta zuba mai snack da lemo ta kawo mai ta ajiye a kan
center table.
godiya yayi mata ta mai da kan'ta ƙasa tace bakomai.
ahlam kuwa ji tayi tamkar ta har bata juhud ce ta sako farim ciki ne ya cika ta , ganin muhsin
gaishe dashi tayi tana zama amsawa yayi cikin kulawa yace '' ya aiki..?,
Alhamdulilah wallahi sai godiyar Ubangiji.
ta fada na kallon sa
Muhsin yace '' ashe jamcy tayi aure..,
eh wallahi tayi aure ina ga wata biyu kenan da yin auren ta.
Kai ya gyaɗa yace '' ta zubar da makaman boko kenan hakan na da kyau aure sittira ce ga diya
mace ..,
dauke kai juhud tayi a zuciyar'ta tace kaga shege ko ina ruwan sa owo.
a fili kuma sai tace '' haka ne wallahi shawarar da ya kamata ni da kai mu bawa kan mu kenan..,
dariya yayi yace '' aini na samu juraij yana neman hana ni..
da sauri ta kalle sa cikin rashin fahimta tace '' ya juraij ne ya hanaka yin auren..,
Muhsin yace '' kusan haka ne wacce nake so yace an riga da an bada ita..,
kallon juraij tayi tace '' yaya wace ita ...?,
juraij yace '' shi da yake baki labarin ba sai ki bari ya karasa miki ba..,
kallon ahlam tayi da tai kicin kicin ta ɓata fuska tamkar ambata bishira da cewa ita yar wuta ce.
mai da kallon ta tayi gare sa tace '' ya Muhsin fahimtar dani me yake faruwa..? wace ita yar
gidan wace haka..?,
yumna da take zaune tana jin su sai tai kamar bata wajen juhud ƙara mai maita maganar tayi

Muhsin yace '' yumna..,
Da sauri juhud tace '' Qu'est-ce que tu dis...?,
Murmushi Muhsin yayi yace '' juhud laifi na aikata ne..?,
kai ta girgiza juhud tayi tace '' a'a amma ka kusan aikatawa saboda ba kyau nema cikin nema..,
Yumna tashi tayi daga gurin ta shiga daki da harara ahlam ta raka ta da ita.
Muhsin shiru yayi juraij yace '' Muhsin yanzu mene amfanin abin da ka aikata...,
Muhsin yace '' idan rabona ce Allah zai bani ita wallahi ina son yarinyar nutsuwar ta , ita ta ƙara
jan hankalina gurin ta...,
da sauri juhud ta zaro ido sai kuma ta sheƙe da dariya har da riƙe ciki lallai ya Muhsin be san
wace yumna ba wata ran sai ta saka shi hawan jini juhud tace '' aunty ahlam bakya jin abin da
yaya Muhsin yake faɗi.. ,

https://youtu.be/_IOc2pOwgKk
Copy is not allowed
Episode 10
Juhud naji mana bani da amsar bayar wa amma lokaci shi zai bashi amsa da kan'sa zai
bambance tsakanin aya da tsakuwa.
kallon ahlam juraij yayi da sauri ta dauke kan'ta ganin irin kallon da ya jefe ta dashi Muhsin
kallon juraij yayi yace '' tun da ban same ta ba zan tafi idan ta dawo kuce ina gaishe ta.
tashi juraij yayi ya saka hannuwansa a aljihunsa yace '' okay insha'Allah zata ji muje na raka ka
ko..,
dafa kafadar sa yayi yace '' no basai ka raka ni ba Nagode sosai...,
kai kurum juraij ya ɗaga ba tare da yace komai ba ,godiya su ahlam sukai mai ya tafi.tashi
ahlam tayi tace '' juhud sai da safe..,
ɗagowa judud tayi ta kalle ta tace '' oh Allah ya tashe mu lafiya..,
a takaice tace amin ta fita a hanya suka ci karo da mommy suka gaisa mommy ta shigo zama
tayi direba ya shigi da kayayyaki yusrah da ta sauko daga sama tace '' mommy wanna siyayyar
batai yawa ba ..? ke ba ganin inda za a kai ta kikai ba kike lodar wannan kayan..?,
judud tace '' yauwa yusrah faɗa mata gaskiya mutumin da yake almajiri ina yaga inda zai zuba
wannan kayan nan ni dan dai kar na fadi ne ace ni ban yi ba na hana ayi..,
murmushi mommy tayi tace '' juhud kenan amma dai ko ba mu ga wajen ba hakkin mu ne mu
siya mata ko..?,
hakane tace ta tashi tare da , daukan wayar ta , tabar gurin mommy kallon yusrah tayi tace ''
gobe fa dake zamu tafi...,
gyara zama mommy tayi ta miƙe kafar ta , tace '' zama tayi akan kujera tace '' dani kuma
gaskiya ina da zuwa makaranta ki tafi da ya juraij..,
yana da uzuri nasan da zai kai ni, bana son tafiya ni kaɗai ne wallahi.,,
Ni da ace bani da zuwa makaranta dana raka ki wallahi amma gobe ina da test har biyu
Tashi mommy tayi tace '' Allah ya temaka..,
Amin ya Allah tace da sauri yumna ta fito tace '' mommy sannu da dawowa..?,
cikin sakin fuska mommy tace '' yauwa ya kaɗaici..?,
murmushi tayi tace '' alhamdulilah an daman mommy ina so naje gidan su kawata da suna
Agadez suka dawo nan yanzu mukai waya da ita tai min kwatance wallahi tun da nazu nake

neman number sai yau na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login