Showing 33001 words to 36000 words out of 39050 words

Chapter 12 - YAN ZAMAN MAKKAH BOOK COMPLETE BY OUMYASMEEN.pdf

18 May 2025

4124


tashi tayi tana murna tace '' to..,
da saurinta ta fita daki kawai ta shiga ta dauko wayar ta da takalminta sannan ta fita tana fita ta
danyi nisa sannan ta kirawo number wannan mutumin sai dai har ta katsai be ɗauka ba ci gaba
tayi da tafiya tana kiransa sai da ta zo gab gurin sannan ya ɗaga kiran ta lokacin tai mai kira
kusan goma sha , da sauri ta kara a kunne tace '' yallaɓai gani nan ina bakin gate din ku na farko yau nazo a yimin
komai da komai..,
Mutumin yace '' to masha Allah kin kuwa yi sa'a wannan satin zan mu kai wasu kinga sai a saka
har dake a ciki tunda kin dade da yin booking..,
wani dadi ne ya kamata tace '' kai amma naji dad'i Nagode Allah ya ƙara arziki...,
ba damuwa ki shigo muyi maza muyi abin da za muyi lokaci yana kurewa dan gani nake na za'a
ƙara kwana biyar ba za ku tafi...
ba ƙaramin dad'i yumna taji ba da wannan zance jin kanta tayi a sama shiga gate din tayi tana
rarraba ido can ta gani office din nasa,
da sauri ta ƙarasa knocking tayi sai da ya dan jima sannan ya buɗe mata samin wata mace tayi
daga, ganin ta yar duniya ce amma ba zata wuce sa'ar ta ba idan ma ta girmeta kaɗan ne
sallama tayi ta juyo ta ƙarewa yumna kallo sannan ta amsa cikin fara'a.
yumna ma ganin bata ja mata aji ba sai ta saki jikin ta tace '' ina wunin ku ina gajiya..,
amsawa sukai da lafiya qalau wannan matar tace '' sunana bintu mukhtar maradi..,
murmushi yumna tayi tace '' ni kuma yumna nura Agadez..,
kai bintu ta gyaɗa tace '' kin sha hanya..,
murmushi kawai yumna tayi ta mai da hankalin'ta kan mutumin nan tace '' nice wacce mukai
waya yanzu..,
dariya yayi yace '' na gane ki yanzu za ayi komai..,
ba karamin dadi taji ba ai kuwa ba ɓata lokaci yayi mata komai bayan ya gama nasa ya turata
office office ta cike takardu tare da saka hannu visa ma anan akai mata abin ka na kudi komai a
ranar aka gama yi mata duk wani chuku chuku suka bata set number ta ashe itama wannan
tafiya za tayi tare da ita akai musu komai ita da yumna sukai chanzan number sannan sukai
sallama yumna ta kamo hannyar gida tun karfe biyu ta fita bata dawo ba ,
sai biyar tana shiga mommy ta fara yi mata faɗa tace '' haba yumna haka mukai dake wallahi
ban ji dad'i ba , yanzun nan malam ya fita daga gidan nan duk da be nuna min wani abu a
fuskar sa ba amma nasan ba zai ji dadi ba , tas an kwaso kayan ki, wannan shegiyar matar ta
cuce mu wallahi yawo take tana cewa cikin shege kika yi labari duk ya baza gari.., zaman yan bori tayi bawai dan abin ya dame ta ba a'a sai dan kawai sun kyale ta, ta yi tafiyar

ta.
kuka ta rushe dashi mommy komawa tayi tana lallashin ta tare da bata baki amma ƙememe taki
yin shiru ta ci gaba da kukan ta zuciyar'ta fes idan bata nuna ta damuwa ba,
ba zata iya zama a kusa da mutane ba zata ƙeɓe kan'ta zuwa na ɗan wani lokaci tasan ba
zasu barta ba , ta sarara dan haka wage baki tayi tana ta kuka har da shashsheka rarrashin
duniya mommy tayi mata taƙi yin shiru.
tamkar zugata tayi ma,
sai da tayi me isarta sannan tayi shiru tace '' mommy yanzu wanne kallo mutane za su yi min
wallahi mommy bazan iya komawa Agadez ba , mommy Dan Allah ku barni nayi nisa da ku,
zuciya ta ko zata samu sukuni bazan iya cire kaina daga cikin wannan zargi ba har abada
mutane da abin za su dinga kallo na ranar da aka daura min aure ranar aka sake ni, sauka ƙasa
tayi ta haɗa hannuwanta guri ɗaya tace '' mommy Dan girman Allah ku barni nayi nisa da kowa
ko hankali na zai kwana dan da ɗan wani lokaci nasan zan dawo dai-dai Wallahi bana son zama
a kusa da wanda na sani dan girman Allah ku barni na tafi makka ko na rabin shekara ne sai na
dawo lokacin nasan mutane sun riga da sun manta da abin da ya faru nima na manta da shi..,
da sauri mommy ta kalle ta cikin mamakin abin da yumna ta faɗi tace..

Ku hanzarta yin payment sauran pages biyu na gama free book 1

Book 2 500

Ne idan ya zama document ya koma 1000
Karku ce ban faɗa muku ba

Domin biya

8141785374

Amina alhasan Muhammad opay
Ku turo da shedar biya ta wannan number
08141785374
Receipt evidence kawai nake so idan kika turo na saka ki a group
bana son wannan tambayar nawa ne bayan kin karanta na baya kinga abin da na saka



YAN ZAMAN MAKKAH

OUMYASMEEN

BOOK 1

Copy is not allowed
Domin jin audio din Yan zaman Makkah Ku shiga wannan link din sannan ku danna min
subscribe Dan Allah.
https://youtu.be/cDE5bjYY2HY
___________________
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6817816be532b4a92550458c
Episode ¹⁵
YUMNA kinsan kuwa me kike faɗa..? anya kuwa lafiyar ki qalau..? karma ki sake malam yaji
wannan maganar, dan wannan abin ya faru sai tunanin ki ya gushe kim bawa mutane ma damar
su faɗi duk abin da suka ga dama..,
kuka ta ƙara rushewa dashi tace '' mommy ke uwa ce nasan zaki san irin radadin da nake ji
cikin zuciya ta , mommy bansan ina zan saka kaina ba. kaɗai ci nake so wallahi a yanzu bana
kaunar kowa ya raɓe ni mommy ku tausaya min ku fahimce ni nasan abin da kuke gudu, anan
ma banyi ba sai a can da bani da kowa garin da ba nawa ba kowa abin da yake ransa shi yake
aikatawa..,
zama mommy tayi jikin'ta yayi sanyi tausasa muryarta tayi tace '' yumna ki fahimci abin da nake
so ki fahimta, zaman ki anan shine rufin asirin ki wallahi bar ganin wa'yanda suke can suna baki
sha'awa baki san rayuwar da suke ciki ba kiyi fatan Allah ya azurta ki, ta hanya me kyau ki
tsaya kiyi karatu Allah ya fito miki da miji kiyi aure wallahi yumna duk inuwar da kike gani kina
hangen ta , to ƙuna ce ba ko wacce inuwa bace inuwa wata zafin ta , yafi na rana akwai dana
sani a cikin'ta mara amfani ba zaki gane wannan zancen nawa ba sai nan gaba , wani ma idan
kin dawo kallon da zai miki daban har sai kin gwammace kiɗa, da karatu..,
share hawayen ta tace '' mommy a tunani na zaki fahimci inda magana ta , ta dosa mommy
komai yayi min zafi..,
shiru mommy tayi domin abin yumna ya fara bata tsoro ganin haka yumna tashi tayi, ta tafi
dakin ta turo kofar tayi ta murza key, zama tayi a kan gado ta zuba ta gumi tabbas idan ba tai
musu wuta wuta ba to wallahi ba za su yarda da wannan tafiyar tata ba ɗaukan waya tayi, ta
nemi number Na'ima har ta katsai ba'a dauka ba dogon tsaki taja ta ajiye wayar a fili tace '' ke
daman tsiyar ki, kenan ai ta kiranki a banza..,
kwanciya tayi tana , ta wassafe wassafe a zuciyar ta , limshe idanuwan'ta, tayi tasan yanzu ba
za su taɓa fuskanta ta ba , sai lokacin da nasara ta zo mata yanzu kowa kallon bai bai zai mata
idan kuma nasara tazo sai a dinga dama nice, sun manta a baya abin da suka ce tabbas me
hakuri yana tare da nasara zata shanye komai zata dauki komai tasan wannan duk abin taki
ake zuba mata.
bacci ne ya dauke ta kiran sallar magariba ne ya tashe ta, tashi tayi ta dauro alwala ta , tayar da
sallama bayan ta idar ta ƙara jaraba number Na'ima still bata dauka ba message ta rubuta mata
tace '' Assalamu alaiki Na'ima ban yi fushi ba , na kira ki amma ba kiyi picking call din ba na
bugo ne na sanar dake nima ina nan tawowa, ki turo min sunan unguwar da kike zan kawo miki
ziyara sannan ina godiya da yi min hanyar tafiya makka da kika yi Allah ya bar zuminci..,
turawa tayi ta ajiye wayar ji tayi ana knocking din kofar dakin ta banza tayi domin hausawa
sunce da zafi zafi ake bugar ƙarfe..,
ko da yusrah ta gama bugunta bata buɗe ba sai ta juya ta tafi gurin mommy tace '' mommy taki
budewa..,

tana faɗar haka ta zauna ajiye chokalin hannunta tayi tace '' to bara naje naga ko lafiya..,
Juhud da take operating system din'ta ta ɗago tace '' mommy sai kace wata yarinyar karama ki
kyale ta idan ta gaji zata fito ne ita fa bari ba shegiya bace da uban'ta amma zaki damu kanki..,
shiru mommy tayi ta bar gurin ƙara zuwa kofar dakin yumna tayi, ta fara bugawa still tai mata
shiri hakura tayi ta barta.
bayan sallar isha ta kwanta tana addu'ar Allah ya fahimtar da yumna gaskiya.
Wasa wasa ƙaramar magana tana ƙoƙarin zama babba yumna har washegari bata fito ba Alhaji
ma yayi mata magana taƙi buɗa kofar gashi aranar taufiq zai koma Ingila acan yake karatun sa
tafiya su kayi rakiyar sa zuciyoyin su duk ba dad'i.
a bangaren yumna kuwa itama ba ƙaramin buguwa tayi ba kwana ɗaya da rabi da tayi ba
abinci.
bayan tafiyar su fitowa tayi a wahale ta dade a kwance a parlour yawa wata matacciya haka
suka shigo suka ganta da sauri mommy ta ɗagata numfashin'ta sai kaiwa yake yana komowa
cikin sauri tace '' juraij zo ka duba min yarinyar nan sakin jikin ta tayi hakan da tayi ba ƙaramin
daga hankalin su yayi ba , ban da juhud da juraij ko a jikin su mommy taɓa kirjinta tayi
numfashin ta sai kaiwa yake
yana komowa zama Alhaji yayi yace '' to ku kuyar da mana ku bita da addu'a, Allah ya tsare ya
kare ba wayon mu ba ba dabarar mu ba Ubangiji shi yake tsarawa yake kuma ikon sa..,
jikin mommy yayi sanyi tace '' Alhaji mu bar wannan maganar za muyi ta , juraij wai ba magana
nake maka ba ..? ka mai dani yar iska yawa da dutsai nake magana..,
Mommy yarinyar nan ku barta duniya ce ɗaga hankalin da taga kuna yi shi ya saka take wani
abin tana nan ma anyi mata wannan sharrin balle ta tsallaka wata ƙasar.
cewar Juraij ran mommy ne ya ɓaci da jin wannan maganar juraij dan haka tayi shiru bata ce
mai komai ba.
runguma ta , tayi, tana yi mata addu'a
ko Allah zai saka zata dawo dai-dai.
ranar yadda mommy yaga rana haka ta ga dare washegari malam ya zo tun da mommy take
mai bayani yayi ƙasa da kan'sa Alhaji na gurin shi daman Juraij yana gurin aiki .
Mommy ta ƙara da cewa kawai mu barta sai a tayata da addu'a dan yau ne ka haife shi baka
haifi halinsa ba zan yi magana ma da hajiyar mu itama nasan ba zata ki ba , kuma da alama
duniyar ce tai mata zafi take ƙoƙarin barin gurin da aka santa duk ranta hankalin'ta ya dawo
jikin'ta zata dawo gida zata waiwayo mu, idan muka matsa abin da zai faru yafi na yanzu dan
zata iya illata kan'ta idan haka ta faru wa za'a zaga mu ne a ciki..,
Alhaji ma yace '' nasan da ciwo dukkan mu ba haka muka so ba amma tun da , tace ita ga abin
da ta za barwa kanta shikkenan ga hanya nan Allah ya bata sa'a iya gata muna yi mata ko da
ace ba zata zauna a can agadez ba to ga nan, nan ta zauna ta ci gaba da karatunta har Allah
ya fito mata da miji tayi auren ta amma ya kanne idanuwan'ta ta toshe kunnuwan'ta, bata
tunanin wannan ɓacin rai da ta saka mu zai iya zame mata matsala a rayuwar ta sufa iyaye ba
abin wasa bane , ba lallai bane wata ran ta budi ido ta gan mu, a lokacin kuma sai tai ta cizon
yatsa tana dama nayi kaza , dan haka kawai kayi hakuri wannan ita ce jarabawar ka , dan kana
malami ba wai ana nufin cewa ba za'a jarabe ka ba a gwada imanin ka wannan abin nasan ka
sani ƙara tuna maka nake malam...,
ajiyar zuciya ya sauke ya ɗago idanuwan'sa yace '' taje na barta..,

hamdala su kayi duk da sun san bawai dan yana so ba kawai ba yadda ya iya ne
hamdala yumna tayi a ranta duniya zata koma mata sabuwa bayan sallar la'asar sallama yayi
musu ya tafi tare da cewa kawai baya bukatar ta ƙara zuwa Agadez ya yafe daga nan tayi
tafiyar ta ,
ko a jikin'ta haka tace '' to malam Allah ya kiyaye hanya..,
be ce mata komai ba ya fice daga dakin ranar haka ta wuni cikin jin dad'i farin ciki ba'a magana
duniya tayi mata dadi sai shirye shirye take ba ruwanta da haɗa ran da su juhud suke yi mata
juraij kuwa yafi kowa yi mata kallon banza abin da tayi ba ƙaramin ɓata mai rai tayi ba murmushi
take yi ta wuce ta bashi guri Washe garin
da za su tashi tana tsaye a harabar gidan tana shawagi da yake garin yayi limshi alamar ko
wanne lokaci ruwa zai iya tsugewa a guje motar sa ta shigo ko dai-dai ta parking din'sa be yi ba
ya fito cikin sauri kusan dariya ce ta kusan kubbucewa yumna ganin yana sauri kamar zai tashi
sama bin bayan sa tayi da kallo ta taɓe baki tace '' a haka zaka ƙare mijin tace duk ka wani
firgice ɗan kadangaren da na saka mata a tsakar daki shi ne take zunduma wannan ihun
wallahi kaɗan kuka gani tun da ni zaku tsana akan nace zan je na nemo arziki kamar kowa..,
be dade ba ya fito yana kwalawa masu wanki da guga kira cikin badda kama ta karaso kamar
bata san me ya faru ba tace '' yaya lafiya naga hankalin ka a tashe..? ni fa wallahi ban iya
zaman gaba, ba..,
tamkar ya ɗora mata ashar sai kuma su yaga rashin dacewar haka tunda wanda ya kula ka , ai
daraja da dashi sannan kuma tabbas ba kyau zaman gaba yace '' wallahi kadangare ahlam ta
gani a kusa da ita , ta kirani ni, tace kamar ta ga wulgawar mutum to sai dai kallo take bata
gama tantance mene bane sai taga kadangare yana yawo..., zaro manyan idanuwan'ta tayi ta ɗora hannu aka tace '' innanallahi wainna ilaihir raji'un amma
dai ba abin da yayi mata..?,
banza yayi mata ganin masu yi musu wanki da guga sun ƙaraso yace "dan Allah mati Ka iya
fitar da kadangaren..?,"
kallon kallo suka shiga tsakanin mati da Haruna dakyar mati ya iya cewa wallahi oga ko son
ganin shi, bana son yi ai wannan muguwar halitta ce..
innanallahi wainna ilaihir raji'un amma dai mati wallahi kun bada maza kuna maza kuna tsoran
kadangare..
ta faɗa tana kallon juraij domin ta yi haka ne da biyu
aikuwa ya gane sarai ita daman ba'a zaman mutunci da ita sai anyi na tsiya juyowa yayi yace ''
dan ubanki shige muje ki ɗauke shi..,
Zaro manyan idanuwan'ta tayi ta nuna kirjinta tace '' na shiga uku ni, ku, kuna maza baku ɗauke
ba sai ni gaskiya ba zan iya ba..,
Haɗe rai yayi yace '' shige mu tafi ko na kwarfe ki..,
ƙara kallon juraij tayi a karo na biyu tace '' sai kace wata ruwa zaka ce zaka kwarfe ni..,
kallon su mati yayi yace '' ku koma bakin aikin ku..,
To suka ce masa suka juya suka tafi yumna tana cikin tunani , bata ankara ba taji ana janta
tamkar kayan wanki.
Ihu ta shiga zab gawa amma ko a jikin sa sai da ya dangana ta da parlour sa fisge hannun ta
tayi tace '' wallahi abin da kake baya dacewa kai , ka kasa sai kace ni nayi..,

Mari zai zabga mata ƙadan gare yayo kan'su da gudu suka , fita har da ahlam yumna tsayawa
tayi tana dariya har da riƙe ciki ganin kamar ba namiji ba ya biyo su a guje nuna shi take tana
zabga uwar dariya har da riƙe ciki,
biyota yayi ta shiga parlour mommy da gudu.
Bayan mommy ta shiga ta ɓoye tana danne dariyar ta mommy tace '' juraij lafiya me ya faru..,
leko da kan'ta tayi tace '' mommy gudun kadangare yake..,
sai ta ƙara fashewa da dariya har da buga cinya tana cewa namiji da gudun kadangare
hhhhh wallahi mommy wannan abu ya ban dariya tare muka dinga gudu dashi yana ƙoƙarin
rikoni wai kar mu tafi mu barsa.
a fusace Juraij ya zagaya bayan mommy zai fisgota ta dawo gabanta tana cewa wayyo Allah
kinga akan na fadi gaskiya shi ne zai dake ni..
Haba juraij sai kace wani yaro ka dinga beye mata
Mommy ta faɗa tana danne dariyar ta , duk jarumtar juraij baya son ganin kadangare barin irin
babban nan wanda har canza kala yake sabo da girma.
juyawa yayi bece komai ba .
ajiyar zuciya ta sauke ta zauna akan carpet tana sauke numfashi tuno ahlam tayi da ƙaton ciki
tana cewa baby karka gudu ka barni dariya ta ƙara shekewa da ita tace '' su baby manya..,
kallon ta mommy tayi tace '' lafiya me ya faru kike magana ke kaɗai..?,
ba komai mommy
dauke kai tayi tace '' dazu naje gurin mutumin nan da kika bani number sa , nayi bincike na
tabbatar da gaskiya..,
da sauri ta ɗago cikin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login