Showing 24001 words to 27000 words out of 39050 words
Chapter 9 - YAN ZAMAN MAKKAH BOOK COMPLETE BY OUMYASMEEN.pdf
nan tayi miki duk kin bi kin tsane ta
ita ba aikata wani abin take ba na ba dai-dai ba amma lokaci ɗaya kin tsane ta haba asabe abin
da ki ke aikatawa be dai-dai ba yanzu an kusan biki shine kike tada mana da hankali da me
yaron nan zai ji da kunji kunjin biki ko da abin da kike yi..
cewar baffa mahaifin Mamman
Mamman wuce wa yayi bece komai ba zama yayi a daki ya zabga tagumi inna tayi yumna tayi
dame zai ji,
Kwance yayi ya rasa in inda zai saka kan'sa saboda tashin hankali yana son yumna baya son
abin da zai raba shi da ita ,
yana so su gina ingantacciyar rayuwa me tsafta wacce zata ginu har zuwa tsufansu share zufa
yayi lokaci ɗaya zazzaɓi ya rufe shi gyara kwanciyar sa yayi ya kudindine a bargon sa da ya gaji
da cin duniya duk ya farfarke.
daga haka bacci ya dauke shi
Washegari yumna suka fara jarabawa tun da suka fara bata ƙara saka Mamman a idonta ba
duk kiran da zai mata bata ɗaukar wayar ace warta zai takura mata rayuwa har suka gama.
washe garin da suka gama aka kawo kayan lefen su ranar inna Hadiza har rawa tayi domin
saurayin shamsiyya yayi bajinta ya zuma mata kaya, Mamman kuwa ba wani abin arziki ashe abin azuciya yake bawai karfi bane haka. Baba lami tace suna zaune suna cin abinci
yumna ko bi takanasu ba tai ba to ita me ne haɗin ta da wannan kaya ko a zuciyar ta bata ji
rashin dad'i ba, saboda sai kana son mutum kake kishin sa.
Shamsiyya ce ta kallo yumna ta gefen ido ita fa wannan kwantan ɓaunar da tayi bata gane mai
ba anya kuwa ba akwai wata a ƙasa ba duk son duniya irin na yumna ta nuna ko a jikin ta ko dai
wani abin arzikin Mamman yake tsara mata shi ya saka mata sauke mai buhun tujara akan sa
ba. Assalamu alaikum
baba lami tace '' wa'alaikis'salam...,
yaron da aka turo yace '' wai yumna tazo inji Mamman..,
kallon ta baba lami tayi taji me za tace, ita kuwa yumna bama ta nuna ba taga yaron balle a
saka ran za tayi magana wannan yarinya ba dai kafiya da taurin kai ba yawa kafurar farko haka
baba lami ta ce a zuciyar'ta afili kuwa sai tace '' yumna ke fa ake kira..?,
ajiye wayar ta tayi akan cinyar ta , tace '' baba ai ke zaki bashi amsa bani ba , yanzu ina
magana ina saka kafana ina fita hmm labari zai sha bamban zaki kwashe min albarka ne kuce
bani da kunya...,
inna Hadiza tace '' ta Allah ya kyauta kai jeka kace tana zuwa..,
tashi yumna tayi ta saka hijabinta ba wanda ta yiwa magana ta fara tafiya da sauri baba lami
tace '' yumna ba zaki dauki daduma ba kullum baki da tunanin karrama bako ki saka mai abin
da zai zauna sai ki bar shi a tsaye sai kace wani soja..,
Jingina tayi da bango jikin ta duk yayi sanyi zuwa sati me zuwa tasan i yanzu tana gidan
Mamman dan haka jikin'ta yayi wani irin sanyi amma zuciyar nan a tsaye take tana nan akan
kudurinta tace '' nazeefa jeki, ki dauko min..,
tashi nazeefa tayi cikin sauri karta dake ta , ta miko mata amsa tayi ta fita yana zaune akan
wani dutsai shifiɗa dadumar tayi ta zauna tace '' gani...,
da sauri ya ɗago ajiyar zuciya ya sauke yace '' wallahi ban ma san kin iso ba , ina ta tunani na
zata ba zaki fito ba wai masoyiya me ya canza min ke lokaci guda na kasa gane kan ki bakya
daukar waya ta ko zanyi kira ɗari ba zaki dauka ba dan girman Allah yumna ki tausayawa
zuciya'ta dame zanji ke kiyi innar mu tayi wallahi ina cikin matsala..,
kura mai ido tayi ta kasa kiftawa azuciya ta tace kai taga me sauƙi ce ƙasa yayi da kan'sa ya ci
gaba da cewa ki tausaya min, ko yaya ta gurin ki na samu rangwami.
ajiyar zuciya ta sauke ta dauke kan'ta daga kallon sa da take tace '' Mamman auren mu ina
tunanin ba me dorewa bane tun yanzu ka fara korafi jarabawa nake ina son hutu amma kai
baka fahimtar haka ko wanne bawa akwai irin tashi ƙaddarar ka dinfa saukaka kanka Ubangiji
shi ne masanin gaibu.. da sauri ya ɗago yace '' to shikkenan wallahi yumna ko me kika yi daidai ne agurina bakya taba
yin laifi zan jure komai nasan wata ran sai labari..,
anya kuwa Mamman ba jinsin mayu bane kai akwai lauje cikin naɗi irin wannan naci haka
turkashi ta raya wannan a cikin zuciyar ta , afili kuwa sai tace '' dare yana yi..,
da sauri sauri yace '' to dame dame kika tsara ina so naki kudin da zaki yi duk abin da kike so
inhar be fi karfina ba ..,
tashi tsaye tayi ta ninke dadumar ta , tace '' ah barshi wallahi kayi wani abin da bakai ba , bani
da bukatar komai ba abin da na tsara, ba abin da zanyi..,
saboda me ranar fa farin ciki ce..?
limshe idanuwan'ta tayi ta saki sani murmushi wanda ake kira da yafi kuka ciwo tace '' Mamman
kenan ni nace kayi abin da ya dace..,
tashi tsaye yayi yana karkadai rigarsa yace '' karfa ya zamo abin Magana yumna ace ba kiyi
komai ba..,
au kenan dan riya zaka bani kudin, da ba dan haka ba ko karfanfana dattin aljihu ba zan gani ba
ta faɗa tana tsare shi da manyan idanuwanta.
ajiyar zuciya ya sauke yace '' wallahi Allah ko ɗaya kawai dai kinsan halin mutane musamman
ma kawayen ki da suke yan duniya kar su dinga ganin kamar bakiyi sa'ar miji ba , bana so a
dinga yi miki kallon kaskanci yumna idan ina da hali duniyar nan gaba ki ɗaya ace mallakina ce
zan iya mallaka miki.., kallon sa take baki sake tace '' gwara da ka fito fili ka faɗa min abin da ke cikin ranka ka dena
boyewa a zuciyar ka, kaga kawaye na ne ni da su kallon da kake mana kenan to ba komai
bakomai Mamman akwai can za ayi hisabi wato shi ya saka yan gidan ku suke min wani irin
kallo dana kasa fassara shi..., Haba yumna wai me ya saka duk hanyar da na kauce kar na biye miki sai ki ƙara fasa wata ni
da baki na , na faɗa miki haka yumna ki dena abin da kike yi kar hakkina ya kama ki..
banza tayi mai ta shiga cikin gida tana kun kuni.
Baba lami tace '' yumna lafiya kika shigo kamar an jewoki...?,
saita kan'ta tayi domin kar su gane me yake faruwa tace '' tofa na shiga uku gani kika yi an cillo
ni..?,
kallon kallo suka shiga tsakanin inna Hadiza da baba lami ganin haka yumna ta shiga daki tana
dariya tunawa da tayi ta bar wayar ta a tsakar gida da sauri ta fito ɗaukan ta tayi ta shiga dakin
su zama tayi ta zuba ta gumi shamsiyya ce ta shigo zama tayi tace '' yauwa yumna me kika
shirya lokaci fa yana kurewa ga katin can ma da Mamman ya bani jiya baki taɓa , ba ni nawa
har na gama rabarwa kamar wacce bakya son auren nan yumna me yake faruwa..?,
afusa ce tace '' uwar ki ce daman tun ɗazu naga bakin ki yana motsi ashe abin da zaki tambaye
ni to ban sani ba idan ma wani ya turo ki kije ki faɗa mai duk abin kikai niya yau nake jin bakar
jaraba ina cewa ni nakawo Mamman gidan nan ina son sa ....? sai kuma na dawo nace bana
son sa saboda bani da hankali ban san me yake damuna ba to wallahi duk wanda ya ƙara
tarata da wannan maganar nan sai na gurje mai baki, haba daman tun da na dawo kallon da
ake min kenan to yasin zan wasa wuƙa ta wani ya kara tarata da wannan zancen zai ga me zai
faru tun da ku baku san zuru ba..,
sum sum shamsiyya ta tashi ta fita baba lami ta fito tace '' wai ke yumna me ya saka kin iya
neman magana da tujara yanzu da ace tayi abin nan bata neme ki fa Allah ne yasan kadai me
zaki yi mata wallahi ki gyara halayen ki gidan wani zaki duk wani datti ki zubar dashi a kofar
gidan nan idan kika tafi dashi wallahi ba lallai su raga miki ba , kamar yadda mu muke raga miki
ba...,
baba lami muna ganin mutuncin ki tun kafin ranki ya ɓaci ki ɓace mana daga gani ko yanzu mu
tarwatsa miki ƙwaƙwalwa..
da gudu baba lami ta fita har tana tun tuɓe yumna tana ganin ta fira, ta kwanta tana dariya har
da riƙe ciki ta sani sarai idan ba haka tayi mata ba , ba zata rabu da ita ba zatai ta Magana ne
ita bata san zuru ba , har sai malam ya shigo ya iske ta , daman ta lura haka take so ɗaga
ƙafafuwan'ta sama tayi tace ''maganin biri ɗan katan uwa wace miki barno gabas ce wallahi
kafin na bar gidan nan sai na saita muku zaman ku yan durin uwa haka kurum ku takura min da
wani banzan zance aita magana ɗaya aure ne , na yarda zanyi to me kuma kuke bukata bayan
wannan..,
Bayan fitar baba lami dakin inna Hadiza ta tafi ta zauna tana zare ido sai leke take yawa wacce
tayiwa sarki karya ganin haka inna Hadiza tace '' lami lafiya naga kina ta gumi..?,
hmmm yaya yau ni naga tashin hankali daman ni nasan yarinyar nan wallahi ba ita kaɗai bace
shi yasaka take iya shegen da ta ga dama malam be sani ba tsoro na ɗaya na fadawa malam
abu ga ɓaci..
Kama haɓa inna Hadiza tayi tace '' me tace miki an shiga uku..?,
hmmm ce min tayi zata fasa min ƙwaƙwalwa idan ban fita daga sabgar su ba ta faɗa ƙasa ƙasa
domin tana gudu ta jiyo su lamari ya ɓaci..
wani yawu ya haɗiye me ɗaci tace '' mun shiga uku ni wallahi dama yau zata bar gidan nan ,
taje zan ta ƙarata sai barazana take mana da rayuwar mu daga wancan sai wannan kalli fa abin
da tayi mana ƙwanaki Allah ne yayi da sauran kwanan mu a gaba..,
Dari biyar ne ba yawa ki biyani hakkin rubutuna karki bari a sato ki karanta...
8141785374
amina Alhasan Muhammad opay
Yan niger
My nita
1000fcfah
Ku turo sheda ta wannan number
08141785374
Dan Allah idan baki shirya ba kar kiyi min magana.
Copy is not allowed
Domin jin audio din Yan zaman Makkah Ku danna wannan link din sannan kuyi subscribe Dan
Allah.
https://youtu.be/cDE5bjYY2HY
___________________
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6817816be532b4a92550458c
Episode 12
Baba lami tace '' wallahi kuwa gwara tatattara ta bar gidan nan ko masa mu sukuni haba
wannan masifa haka dame tayi kama..,
har karfe tara suna tattaunawa akan wannan matsala ta yumna washegari shamsiyya ta fita
tana rabon katim yumna tun da ta fita yumna take Allah Allah ya dawo ta, taci uban'ta tun da ta
faɗa mata bata ji ba to za tayi maganin ta.
tamkar wacce tayiwa sarki karya haka ta ɗinga za gaye tana kaiwa tana komowa su inna
Hadiza ido ne kawai nasu.
domin lamarin yumna sai addu'a har wajen azahar tana wannan kaiwa tana komowa domin yau
dole ta hukunta shamsiyya dan uwar baban ta.
Assalamu alaikum da sauri ta fito jin sallamar shamsiyya sai dai wani abu da be mata dadi ba
tare suke da malam dole tayi saranda ja da baya tayi malam yace '' yumna ashe baki da lafiya
yanzu yar uwarki ke faɗa min me , me ya saka tun da wuri baki faɗamin ba.?,
ƙasa tayi da kan'ta tace '' naji sauki ma bakamar lokacin da na tashi ba..,
zama yayu cikin kulawa yace '' meke damin ki..?,
yumna tace '' zazzaɓi da ciwon kai ne amma alhamdulilah yanzu naji sauki.,
to Allah ya ƙara sauki,
amin ya Allah tace.
tashi yayi yace '' shamsiyya jeki ki dauko min allo nayi mata rubutu..,
shamsiyya da , daman tana tsaye tun da ta shigo ta kalli yumna tasan yan bala'in sun motsa.
shiga dakin sa tayi ta dauko mai allo yumna ta shinfiɗa mai tabarma zama tayi a kusa da shi
rubutu ya zauna yana yi jefi jefi yana tambayar ta ko tana da , damuwa.
yana tausayin rayuwar ta sosai saboda bata da uwa shiɗin ba mazauni bane balle ya san me
yake faruwa duk da yasan halin yar tasa ba kanwar lasa bace.
yumna bata nuna mai akwai wata matsala ba da ya gama ya wanke ya bata , tasha amsa tayi
tasha suka ɗan yaɓa hira ana kiran sallar magariba ya fita ita kuma, ta tashi tayi sallah,
bayan ta idar ta kwanta a tsakar gida tana jij Radio da wayar ta zama kusa da ita shamsiyya tayi
sarai ta ganta sai tai kamar bata ganta ba ta ci gaba da jin radio ta idon ta a rufe yaran gidan
suka ta wasan jakai kwarai yumna tayi lafiya da , dane tun da ta fito tsakar gidan nan , ba
wanda zai ƙara wani kwakkwaran motsi idan kuma mutum yayi taurin kai tofa jikin'sa zai faɗa
mai.
tana cikin jin radio shazali dan gidan baba lami ya faɗi mata aikuwa yaci ubansa domin duka
tayi mai tas tare da han kaɗa shi, taja tsaki ta koma saki ta kwanta.
baba lami tana jin ta amma batayi ƙoƙarin magana ba domin ba mutunci za tayi mata ba.
washegari shamsiyya ta dinka musu kayan su da yake ta iya ɗinki yumna ce dai bata iya ba
saboda ita bata ga me za tayi da sana'ar basir ba.
bayan ta gama ta kai mata wajen kayanta ta ajiye.
haka rayuwa taci gaba da wakana yau ana sauran kwana ɗaya daurin auren su kowa ya zo na
arlit amma ban da ahlam da juraij hakan be wani bawa yumna mamaki ba tun da tasan shi dai
ba mutunci ya cika ba ,
shi da matar sa biyu ce ta haɗu shi ba mutunci haka ma ita, juhud ma bata zo ba sai yusrah sai
mommy da kakarta tawajen uwa sosai suka nuna mata gata domin ko dinki ɗaya bata saka ba
akayan da Mamman ya kawo mata.
zazzabi ne ya rufe ta fa'iza da nana suna tare da ita fa'iza ce tace '' wallahi yumna banga bin
damuwa ba duk kinbi kin takura kanki ke wallahi ki godewa Allah ma zakije kici yancin kanki..,
murmushin tayi, ta gyara kwanciyar ta zuciyar ta ba dad'i in banda tsabar rashin hankali wanne
cin yan cin kai ce mata aka yi anan gidan, ba tacin yan cin kan'ta.
ita wannan ciwon bawai na damuwa bane tana ganin bakwan watan ta dab yake da zuwa cikin
ta ma ciwo yake , tashu tayi ta dafe kan'ta tace '' dan Allah cewa mommy bani da lafiya kaina
ciwo yake da ciki na..,
tashi fa'iza tayi ta fita ba jimawa gabaki ɗayan su , suka zo har da yusrah.
mommy tace "subbanallahi tun yaushe ne baki ɗa lafiya amma kikai shiru da bakin ki...?,"
amai ne ya taso mata da sauri ta fito tsakar gida ta dinga kwara shi kowa sannu ya dinga yi
mata bayan ta gama mommy ta wanke mata jiki kamata tayi suka shiga daki ta kwantar da
kan'ta a cinyar kakarta tana sauke a jiyar zuciya daman haka period ke mata , bata mata , ta
dad'i baka ramar wahala take sha ba. magani mommy ta bata , tasha bacci ya dauke ta kamu ba , ba ai yi da ita ba saboda ba lafiya
sosai take jin jiki,
washegari
RANA bata karya sai dai uwar ɗiya taji kunya.
sosai mutane suka taru daga gari daban daban domin malam na mutane ne ga kuma mahaifin
Mamman alhaji Dauda me wuƙa sarkin fawa, masallaci ma kasa daukan mutanan yayi wasu
suna waje daurin auren shamsiyya aka fara sannan na yumna lokacin da me shela ya sheɗa an
daura auren ta ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba , tuni ta fara kwara a mai jikin ta ya zugage
tas mommy ce ta gyara ta tare da bata magani bayan an gama MAMMAN da saurayin
shamsiyya suka shigo domin gaisuwar surukai sai a lokacin ma ya ga bata da lafiya sosai ya
tausaya mata .
bayan ya fita ya koma gida mahaifiyar sa sai cika take tana batsaiwa.
ko gaisuwar'sa bata amsa ba.
wannan kenan
da misalin karfe biyun suka tafi sukai mata jere dole sai da aka dawo da kaya da yawa saboda
daki daya ne da ban daki sai kitchen shima ba wani babba ba yusrah tace '' kinga ko abin da
nake faɗa miki yanzu ya za kiyi da wannan kaya..?,
Mommy tace "'siyarwa zanyi na bata kudin sa mata wani amfanin taja jari..,"
shiru yusrah tayi bata ce komai ba Hajiya anni kakar mahaifiyar ta , tace '' aikuwa kin kyauta
Allah yayi albarka...,
amin tace da misalin karfe Biyar Na Yamma mommy ta shirya yumna cikin wani lece pink colour
ba ƙaramin kyau yayi mata ba duk da saboda da cutar da tayi ta zabge ta rame lokaci ɗaya.
nasiha tayi mata kuka kawai take yi share hawaye bayan ta gama yi mata faɗa ta haɗa su, su
da shamsiyya ta kara yi musu sannan malam da su inna bayan sun gama daman masu daukan
amarya suna jiran su yumna da ta fito sai da ta juyo ta kara kallon gidan su hawaye ne suka
ƙara zubo mata , da kafar dama mommy tace ta shiga cikin motar.
shiga tayi ta kifa kanta ta ci gaba