Showing 21001 words to 24000 words out of 39050 words
Chapter 8 - YAN ZAMAN MAKKAH BOOK COMPLETE BY OUMYASMEEN.pdf
samu ita ce wacce nake baki labari ban san ko ba zan ƙara dawowa
ba nan kusa gwara naje mu gaisa..,
dan jim mommy tayi sannan tace '' to ba damuwa bara na saka akai ki amma karki dade kinga
dare na kawo kai abin da ya saka ma zan barki gobe zaki tafi..,
ran yumna be so ba da mommy tace kai ta za ayi to ta tafi ta zaga gari ko Allah zai saka ta ga
masu daukan mutane tafiya makka amma bakomai za ta san yadda za tayi tace '' to mommy ba
damuwa bara na shirya..,
okay kiyi maza ki shirya bara na kirawo Salisu ya kai ki.
da gudu ta fita tana murna zama tayi a bakin gado rasa ina za tayi addu'a ta shiga yi a ranta
tare da kiran layin na'ima cikin ikon Allah ta shiga ta ɗauka cikin zumuɗi tace '' na'ima wannan
wanne irin hulakanci ne ina ta kiran ki karshe ma sai kika kashe wayar wato wasa tare ci
banban ko abin da kika samu shine bakya so na samu ko to wallahi bakomai kinyi da yar
halak..,
hmmm wallahi aikine ya sha kai na amma ba damuwa bara na turo miki yanzu dan Allah idan
na turo miki karki ƙara damuna da kira wallahi kina katsai min aiki na ..
saboda bakin ciki yumna kasa Magana tayi ta saki baki ta ma rasa abin da za tace .
jin alamar kudinta yana dab da ƙarewa sai ta kashe wayar ta ɗan jima a zaune sanan ra ji
shiguwar messages da sauri ta dubu wani tsallam murna tayi kamar gurin ba nesa da inda suke
da sauri ta fito tace '' mommy ta turo min address din gidan ba nisa da nan gurin ashe ni
kwatance da tai min ban gane ba Allah ya saka na kara kiranta na tabbatar basai ma ya kai ni
ba dan gaba da kune kaɗan..,
Oh to Allah ya temake sai kin dawo komawa daki tayi cikin sauri take shiryawa har ta gama ta
saka hijabinta sallama tayiwa mommy ta fito gate me gadi ya buɗe mata ta fita kallon ko ina
take tun da ta zo yau ne ta fita unguwar shiru baka jin motsin komai sai na tsuntsaye da yake
kusan rabin su ma'aikata ne a zaune a unguwar kuma manyan ma'aikatan gwamnati da na
Company tafiya ta dinga yi tana dubu sakon da yake cikin wayar ta da yake har da sunan
Company da yake daukar Mutane aikatau ta saka mata cikin sa'ta ta gano gurin anyi rubutu da
manyan baki cikin harshen French an saka Fais semblant d'être humble (do garo da kai) da
sauri ta tsaya tana tunanin to ta ina ce kofar shiga tana wannan tunani wani ya zo wucewa da
sauri tace '' bawan Allah ina wuni..?,
Tsayawa dattijon yayi yace'' barka dai ya'ta..,
am Dan Allah tambaya nake..
dattijon nan yace '' Allah ya saka na sani..,
yumna kallon gurin tayi ta nuna mai yace '' dan Allah ta ina ake shiga gurin nan naga kamar
katanga ce sai karamar kofa itama a kulle..?,
dan jim yayi yana karantar yanayin ta Sannan yace '' eh ba nan ce kofar da ake shiga ba kofar
tana can baya ina ɗaya daga cikin ma'aikatan gurin office wa kike nema...?,
ajiyar zuciya ta sauke ganin kayan ta ya tsinke a gindin kaba tace '' daman ina so na tafi makka
aikatau ne to ban san yadda ake abin ba wata kawata ce ta kwatanta min nan gurin...,
Oh masha Allahu ki godewa Allah ni ke da alhakin daukan duk wasu ma'aikata na turasu
ƙasashe akwai agent din da zai raba su inda za su yi aiki acan amma muna da sharadi zaki
saka hannu muje nayi miki bayani..
to ba damuwa muje zagayawa baya su kayi ta wata kofa suka shiga sai kalle kalle take ganin
ma'aikata suna ta sabgar gaban su wani office suka shiga ya zauna ya fito da wasu takardu
yace '' kin shirya nayi miki bayani..?,
yumna tace '' eh na shirya..,
yauwa a ka idar tafiya aikin nan bana ɗaukan ƙasa da shekara Shata kwas sannan mun fi son
bazzawara wacce tai aure tana da yara biyu haka amma yan matan ma muna ɗauka amma da
saka hannu iyayen su sannan za mu kai ki muyi miki komai za kiyi shekara ɗaya kina biyan mu
kafin ki fara cin gashin kanki kina. kannata ne ya kulle tace '' saboda me aka fi son bazaurawa...,
Masha Allah kina da kyan kai da kikai min wannan tambayar dalilina da yasa muka fi son
daukan zaurawa saboda su, suna da yancin kan'su sannan duk abin da aka saka su za su yi,
duk wani aiki na gida za su iya yin sa..
shiru tayi tana sauraron sa sannan tace '' a gaskiya ni bani da aure amma sai bayan nayi aure
na fito sannan zan yi wannan tafiyar saboda a gidan mu balallai a barni ba ,
okay ba matsala ko yaushe kika shirya zaki iya zuwa sannan akwai ka'idojin mu bama daukan
mace mu kaita batare da anyi general check up ba sannan albashin ki na watanni goma sha
biyu wato shekara ɗaya zamu riƙe shi saboda mun yi miki dawainiyar kaiki da kuɗaɗen mu ,
sannan wannan company na zata dena iko da ke ba sai bayan shekara ɗaya dole kibi dokokin
mu idan mace taga ba zata iya zama ba tana bukatar canjin waje ko dawowa to fa sai ya biya
mu tas abin da muka kashe har da ribar dubu dari bakwai....
da sauri ta ɗago jin abin da yace na ƙarshe murmushi yayi yace '' naga kin kalle ni maganar tayi
miki nauyi ne akai..?,
yumna tace '' kusan haka ne ,
cure hannuwansa yayi guri ɗaya ya sarke su yace '' wannan company yana kashe makudan
kuɗaɗen gurin tafiyar yan aikatau dole zai mai da kudin sa har da riba..,
ajiyar zuciya ta sauke tace '' hakane amma kawata batai min wannan jawabin ba ...,
wace ya sunan ta a wacce shekara ta tafi..?
ya jero mata wa'yannan tambayoyin
yumna tace '' sunan ta Na'ima hamidu Poussin yar Agadez ce shekarar ta ɗaya bana jin ma ta
cika ɗaya amma kuma ta turo da kudade a gyara musu gida ya akai ta samu kudi bayan kune
da kudin ta bata gama biyan ku ba..,
Murmushi yayi yace '' oh na gane ta sosai ana samin alkairi a cikin tafiyar idan har mutum yayi
amfani da damar sa sai ya tara abin duniya bayan ya gama ko kuma yaga ya gaji da zaman sai
ya dena ya dawo gida ya ci gaba da harkokin sa da facaka da kudin sa son ran sa akwai matan
da suka zama hajjiyoyi ko bayan sun dawo to ƙaramin mutum ma be isa ya kalle su ba suna da
yancin kan'su sun san me ne yancin su, su suke zama matan mayan shuwagabanni da manyan
yan kasuwa kinga kamar ke yadda kike da wannan kyan ina me tabbatar miki idan kika je zaki
samu alkairai masu tarin yawa mayan kuɗaɗe sai dai kiyi kyautar su badai a baki ba...,
kallon agogon wayar ta tayi tace '' hakane Nagode sosai lokaci yana ja gashi saka min number
ka idan na tashi zan kiraka..,
karba yayi ya saka mata , sannan yace '' tsaya a dan kawo miki abin jiƙa maƙoshi muna ta koro
bayani na barki ba wani dan abu..,
murmushi tayi tace '' a'a wallahi Nagode sosai Allah ya saka da alheri..,
amin ya Allah yace tai mai sallama ta fito tafiya ta fara tana ta tunane tunane kala kala har ta
kusan zuwa gida ta rasa gano bakin zaren to ita da take so tayi shekara ɗaya ta dawo mene
amfanin zuwa aikin nan shekara ɗaya fa za tayi tana kwaɗago amma cikar burinta da mafarkin
rayuwar ta fa shikkenan sai tayi shekara biyu lokacin ta tara abin da take iya ganin zai fiddasu
daga cikin talaucin da suke ciki , har ta ƙarasa bata dena wannan tunanin ba tana shiga aka tada sallar magariba juraij ne ya fito
yana sassarfa da alama masallaci zai je matsa mai tayi tana kai da kan'ta shima da yake yana
da uzurin gaban sa be kulata ba ita tun da ya kusan targaɗa'ta ta dena shiga sabgar sa ba
ruwanta dashi tunda mugu ne. bata tarar da kowa ba acikin parlour dakin da aka sauke ta nan ta shiga ta dauro alwala ta tada
salla bayan ta idar ta, tashi ta fito bedroom din mommy ta shiga sallama tayi tana zaune tana
jan carbi durkusawa tayi tace '' mommy na dawo...,
Murmushi tayi ta ajiye carbin hannunta tace '' to ya suke da fatan suna Lafiya qalau..?,
murmushi yumna ta mai da mata tace '' alhamdulilah suna lafiya tama ce a gaishe ki da ba dan
tafiya zan yi ba ta , tazo kun gaisa..,
Allah sarki ba damuwa wata ran ta zuwa idan kin zo garin.
tashi tayi tace '' nima haka nace mata ..,
fita tayi ta zauna akan kujera tana game da wayar ta a yanzu da ta kawo karshen wannan
matsalar tata sai take jin bata da wata sauran damuwa malam da sauri zuciyar ta , ta buga
tasan ba lallai ya amince da tafiyar ta ba , amma zata yi duk yadda za tayi ya amince idan kuwa
yaƙi to za tai mai layar zana sai dai ya shafa yaga babu ita haka kurum su kenan ba wani me jin
dad'i kowa wanda zai aura faƙiri ne haka ma wai gwara ita da zata auri mamman saurayin
shamsiyya keke ne dashi yana yawo yana siyar da su karas da ɗa'ta..
dan haka wallahi ba zata kashe kan'ta ba haka kurum sai kace an yiwa malam kauri da kan kifi
ya kasa fahimtar idan burin ta da mafarkin ta ya tafi..
ke da sauri ta ɗago ganin juraij sai ta kau dakan ta tace '' na'am..,
tashi kije ki share min daki na dana ahlam..,
da sauri ta kalle sa tace '' tafa ce idan ta ƙara gani na a cikin gidan ta sai ta yanka ni..,
ni nace miki, ki tashi kije kiyi aikin da na saka ki.
tashi tayi bata ce komai ba ta fita tana shiga pary din ta , samun ta , tayi tayi ɗare dare tana
kallo Oni jikar mutum goma kowa da irin tashi salon kaddarar ita kuma wannan tata ta kallo ce
kuma lalurar kallon a waya take yin ta ..,
ta faɗi haka tana shiga cikin dakin ahlam juyowa tayi tace '' baki iya sallama bane ko ce miki
akai nan chochi ce..?,
ɗaga kan'ta sama tayi tana karewa dakin kallo tace '' ikon Allah sai nake ganin kamar na shigo
chochi jin wasu maganganu na tashi tamkar na arnan da suka dade ba su san waye Allah ba ,
bisa dukkan alamu ma sallar da aka yi ta magariba ba lallai sun yi ta ba..,
Da sauri ahlam ta tashi tace
"Are you even in your right mind? Do you know what you're saying to me..?,,
murguɗa mata baki tayi tace '' aikin san bana jin turanci da kiyi min da yaran da zan gane na
baki amsa dai-dai da abin da kika faɗa min..,
fasa marin ta tayi taja kwafa ta dauki wayar ta , tabar gurin tsaki taja ta fara gyare gyaren gidan
ranta duk a ɓaci ta rasa ahlam wacce irin mace ce wannan ƙazanta haka kullum sai dai ta
bulluwa jikinta turare taci kwalliya tamkar zata je gasar sarauniyar kyau amma daki ba kyan
gani. gama gyara parlour tayi ta tafi bedroom nan ma kaya ne sunfi set ashirin a ajiye a gefen
gado ga Landry basket amma ba amfani kwashewa tayi ta gyara ko ina tare da sala Room
freshener sai karfe takwas sannan ta gama komai ta fito ko arzikin kallo bata samu ba daga
gurin ahlam balle a kai ga godiya a gaje ta koma tana shiga tayi sallah bayan ta idar ta fito kan
dining table ta nufa ta zuba abinci ta fara ciki bayan ta gama tayi wanka ta kwanta.
tun asuba tayi wanka ta shirya wani irin zumuɗi take tun da ta kashe wannan wutar gwara taje
can itama ta ayi wacce za ayi,
karayawa tayi direba ya kwashi kayayyakin ta ya saka aboot sanan ta shiga Alhaji ya bata kuɗi
godiya tayi mai suka dauke hanyar Agadez lokacin da suka isa karfe goma da rabi fitowa tayi
malam da yake zaune yana biyawa almajirai karatu ta ɗago ya kalli Hajiya mommy yace ''
sannun ku da zuwa.., durkusawa tayi tace '' yauwa malam mun same ku lafiya..?,
Malam yace '' lafiya qalau alhamdulilah ya kuma ya yaran namu da me gidan naki..?,
murmushi tayi tace '' alhamdulilah suna lafiya qalau..,
masha Allahu Allah ya kara shiryar mana da su kan tafarki madaidaici ina juraij yake yau ban
dashi kuka zo
Mommy tace '' amin ya Allah baya nan yana gurin aiki..,
to Allah ya temaka Allah ya bada abin da ake nema..
tashi tayi tana amin ya Allah.
Malam barka da safiya.
Barka dai yumna kin dawo lafiya.
lafiya qalau alhamdulilah.
shiga cikin gidan mommy su kayi su baba lami suka tarar suna zaune suna hira gaisawa suka yi
sannan suka kawo musu abin kari kunun tsamiya ne da ƙotsai, mommy tace '' alhamdulilah
wallahi na koshi..,
Inna hadiza tace '' a'a kodai irin namu ne ba zaki ciba abin da kunyi tafiyar mota duk abincin ya
zazzage..,
a haba yau na sana zuwa gidan nan wallahi na koshi
Cewar mommy.
to ba damuwa yumna ba magana kin ja gefe kinyi shiru,
da sauri yumna ta kalle su tace '' nafa gaisheku...,
Baba lami tace '' haka ne wallahi..,
Kaya aka shiga shigo dashi su baba lami wannan ta kalli wannan wannan ta kalli wannan ganin
kamar za'a buɗe shagon sai da kayan kitchen da na daki..,
shugowa malam yayi, yayi mata godiya haka ma su baba lami inna Hadiza tace '' to yumna ki
dubu irin kokarin da wannan baiwar Allah tayi ki daure ko me zai faru kiyi koyi da halin manzon
Allah Sallallahu alaihi Wasallama kiyi hakuri shi zaman aure ibadane yi nayi bari na bari
shikkenan ko dan martabar mahaifinki da gidan da kika taso karki kalli na waje su baki sha'awa
kowa fata yake ya sami irin ni'imar da kika samu kalli kaya kamar yar gidan wani attajirin me
kudi dan girman Allah kiyi hankali ki nutsu..,
ƙasa tayi da kan'ta ta ta share kwallar karya tace '' insha'Allahu zan yi iya bakin kokarina da
yardar Allah ba za kuji wata matsala daga gurina ba..,
Dad'i ya kama malam ganin yadda suka haɗu sukai mata faɗa kuma taji ta amsa albarka ya
saka mata ya koma zaure domin ci gaba da karantu
Karfe biyu mommy ta tafi tare da bata kudi sosai tayi murna.
karfe takwas na dare mamman ya aiko kiran ta ,
sai da ta gama ɓata lokaci sannan ta fita tana wura hanci tsayawa tayi a kofar gida ta jingina da
kofar gidan su tace '' barka da dare..?,
Barka dai masoyiya kinga kuwa yadda kika koma tamkar wata balarabiya ke daman matar
manyan ce irina...
da sauri ta ɗago jin furu cinsa na ƙarshe tace '' Mamman kai sauri ka faɗi abin da ya kawo ka
saboda bacci nake gobe zamu fara zana jarabawa..,
murmushi yayi yace'' wallahi na ƙagu ku gama jarabawar nan na ganki a cikin gidana kin zama
mallaki na yumna ranar ba ƙaramin dadi zan ji ba wallahi yau ga yumna ta zama mallaki na
muna tare da juna kai Allah ya nuna min ranar nan yasin ranar sai nayi sadakar nama asan
cewa yau dan gidan sarkin fawa zai auri yumna zubin larabawa matar manya..., kallon sa tayi yaci hular kauraye dan tsan hannun sa da guro da yake rigar jikin sa yar shara
ce...
dauke kai tayi ita bata san wacce irin kaddara ce ta kai ta ga soyayya da mamman ba gaba ƙi
ɗaya alamun rashin wadata ta game ko ina na jikin sa rigar duk ta kode dan hala wutsiyar
ragumi tayi nesa da ƙasa dole ta nuna mai banbancin tsakanin ita dashi ta rabe mai tsakanin a
ya da tsakuwa...
Copy is not allowed
Domin jin audio din Yan zaman Makkah Ku danna wannan link din sannan kuyi subscribe Dan
Allah.
https://youtu.be/cDE5bjYY2HY
___________________
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6817816be532b4a92550458c
Episode 11
Masoyiya ya kikai shiru kin barni ina ta zuba yawa ya'yan kaɗan ya..
dafa kan'ta tayi tace mamman ciwon kai nake ina buƙatar hutu kazo ka ci kani da zance kaga
sai an jima.
sakar baki yayi yana kallon ta har ta shiga cikin gidan su shafa kan'sa yayi yace '' bakomai aski
idan ya zo gaban goshi yafi zafi..,
kai tsaye gidan su ya nufa tun daga soro yake jin tashin muryar mahaifiyar sa da sauri ya
ƙarasa tare da yin sallama mahaifinsa ne ya amsa amma ita ko kallon inda yake ba tai ba ta ci
gaba da cewa Wallahi idan har kina son zaman lafiya karku kawo min wannan mara kunyar
yarinyar cikin gidan nan kaf garin nan waye ban san ta ba a fagen rashin kunya yau kusan sati
uku kenan ta ganni a hanya ko nunawa ba tai ba , ta sanni balle ta gaisheni dan haka kuka sake
ta shigi cikin gidan nan sai ta dandani ƙudar ta sai na gasa mata aya a hannu me ake yi da
mara tarbiyya ya kwalla fa rai sai ya aure ta , duk yabi ya rame ya kan jame ni wallahi da ace
yar uwar ta ce nazeefa bazan ce bana so ba daman ko lokacin da kakai kuɗi badan raina ya so
ba , bana son ta bana son wannan auren ba da yahuna za ka yi shi ba..
Yan zu asabe abin da ki kayi in kyau ta kenan me yarinyar