Showing 30001 words to 33000 words out of 39050 words
Chapter 11 - YAN ZAMAN MAKKAH BOOK COMPLETE BY OUMYASMEEN.pdf
chair tace'' taufiq labarin yana da yawa mudai samo kan'ta sai nai maka
bayani..,
jan bakin sa yayi ya tsuke ya zauna kusa da ita.
Wannan kenan
AGADEZ
karfe goma malam ya shirya domin zuwa gidan su Mamman yaji ba'asin abin da ya faru har
kawo i yanzu ba wanda yasan me yake faruwa da yaji nazeefa tana cewa zata gidan yumna
hanata yayi yace shi baya son irin wannan daga yin auren har zata fara sintiri ko gidan
shamsiyya be yarda ta je ba.
yana gama fadar haka ya fice kai tsaye gidan su Mamman ya nufa bayan ya isa ya aika yaro
ace yana sallama da mahaifin Muhammadu..,
shiga yaron yayi ya fara rangaÉ—a wata uwar sallama yace '' wai inji malam NURA me sittin yana
sallama da baban Muhammadu..,
Innar su hindatu da take gaban wuta tana dumamen tuwo tace '' je ka , kace mai baya nan..,
da sauri sarkin fawa ya fito yana cewa haba tabawa me ya saka kike haka ne tun da dai kin
raba auren nan hankalin ki , ya kwanta ai sai ki ci wake ki sha ruwa kaf garin nan ana darajja
malamin nan amma shi ne kika ce a faÉ—a mai haka..?,
tamkar da dutsai yake magana bata dago Kai ta kalle sa ba girgiza kai yayi ya fita yana saɓa
babbar riga a kafaÉ—a.
samun malam yayi yana tsaye a kofar gidan nasa gaisawa sukai sannan yace '' bisimallah shigo
zaure...,
Malam yace '' a'a barshi nan ma ya isa..,
Allah annabi yayi mai sannan ya shiga ba yadda ya iya daduma ya shinfida mai suka ƙara
gaisawa sannan malam yace
'' naji wani abu to domin na tabbatar shi ne na zo naji gaskiyar magana me ya faru yumna tace
min Muhammadu ya sake ta..?,
kunya ce ta rufe Sarkin fawa kan'sa yana ƙasa yace '' to, haka Allah ya nufa daman auren ba
me dadewa bane, mahaifiyar sa , ce tace ya saketa wai saboda ta shigo mai gida da ciki Allah
shi ne masani wallahi dole tai mai ya sake ta , ba yadda ya iya , wallahi nauyin ka ne ya hani
zuwa na same ka mu tattauna amma insha'Allahu zan wa tubkar hanci da yardar Allah zata
dawo dakinta saki biyu yayi mata , abin da nake zargi daman bata son ta shi ya saka tayi mata
wannan sharrin..,
kai kurum malam ya jinjina yace '' Allah ya saka hakane yafi alkairi bakomai Allah zai fitarwa da
kowa hakkin sa alhamdulilah tun da kun gane ba haka bane ba damuwa ,ko za ku iya bani
takardar ta..,
dan Allah kayi hakuri nasan ba akyauta muku ba wallahi ba yadda zanyi cewar sarkin fawa.
murmushi malam yayi har yanzu kamilar fuskar sa bata nuna damuwa ba ko ɓacin rai yace '' ba
damuwa Allah ya yafe mana baki É—aya..,
godiya yayi mai ya ci gaba da cewa bara naje na saka shi ya rubuta takarda.
to malam yace mai yana jiran sa be jima ba ya fito amsa yayi, yayi mai sallama ya ta fito yana
tafiya tana zancen zuciya abin duniya duk ya ishe shi, maganar mutanen gari ma ta ishe shi,
ace aure daga kwana É—aya anyi saki to bakomai yasan Ubangiji jaraba shi yayi ya gwada
imanin sa , Allah ya bashi ikon cinye wannan jarabawar har ya isa gida be dena tunani ba. koda ya isa a waje ya zauna yana karatu almajirai suka zauna yana karbar haddar kowa tare da
ƙara musu wani sosai yaji zuciyar sa tayi sanyi tabbas Alkur'ani waraka ne , maganin
damuwane al'ummar annabi mu dage da ibadar Allah.
ko dan muga haske a cikin rayuwar mu.
#####
Sai karfe 1:40 aka fito da ita an saka mata oxygen sannan an É—aura mata drip a hannunta kai
tsaye daki suka shiga da ita mommy za tabi bayan su taga Juraij ya fito ashe dashi aka shiga
ba ƙaramin mamaki tayi ba da ganin sa da tayi saboda ɗazu bata ga an shiga da shiba tace ''
juraij daman kana ciki..?,
cire glove yayi matsawa yayi kusa da wani automatical dustbin tuni ga buÉ—e ya jefa su yace ''
kirani su kayi akwai wata kofa a baya tanan na shigo..,
nifa ince ya jikin nata..?
juraij yace '' da sauki damuwa ce tayi mata yawa amma insha'Allahu zuwa anjima zata
warware..,
to Allah ya yarda mommy ta faÉ—a tana shiga world din da aka kai yumna tura kofa tayi taufiq ne
zaune yana danna waya zama tayi a kujerar da take facing din sa tace '' bata farka ba ko..?,
É—agowa yayi ya kalli yumna da take kwance yace '' a'a ko motsi ba tayi ba , amma wani likita
yace min sai nan da karfe biyar zata farka sun mata allura ne..,
ajiyar zuciya ta sauke tace '' Allah ya kai mu darai da lafiya..,
amin ya Allah ya faÉ—a yana tashi zura wayar sa a aljihunsa yayi yace '' mommy ni zan tafi zan
turo miki yaran nan sa taya ki zama wallahi wani irin bacci nake ji duk na gaji..,
Wallahi kuwa akwai gajiya yau ka sauka kuma kuma baka huta ba , Allah dai yayi albarka sai
dai in yusrah juhud yanzu haka nasan ta , tafi gurin aiki, itama yusrah ko ta tafi makaranta Allah
masani.
Cikin kaunar mahaifiyar tasa yace '' amin ya Allah to zan dai duba na gani duk abin da ake ciki
za kiga nayi miki waya ya jikin ahlam..?,
mommy tace '' da sauki hice ko ka kirawo ta..?,
shafa sumar kan'sa yayi yace '' eh na kirawo ta maman su ce ta É—auka tace tana bacci amma
zata faÉ—a mata..,
To Allah ya ƙara sauki ciki ne me laulayi ga haɗo da rashin lafiya kullum ba lafiya wallahi tun ina
ganin yarinyar nan lanjarewa take har kuma naga ashe ba lanjarewa take ba cutar ce Allah dai
ya raba lafiya haka wani cikin yake sai ranar da aka sauke shi ake samun sauki
amin ya Allah yace yana fita daga cikin dakin.
AGADEZ
kamar ance mai ya É—aga idanuwan'sa ido hudu yayi da zaliha jikar hajiya rakiyar mahaifiyar
marigayya da flask a kanta da wani a hannunta gaban sane ya faÉ—i bayan shi da Hajiya zainab
ba wanda yasan da mutuwar auren yumna ba mamaki abinci tayiwa yumna za akai mata gidan
ta , share zuba yayi be san ya zai yi ba , baya so mutuwar auren yumna ta fito yanzu duk da yasan
koman daren dadewa dole abin ɓoye ya fito sarari.
shiru yayi yana tunanin mafita duk hanyar da yabi sai yaga ba me bullewa bace baya so hajiya
tasan da zancen nan kodan shekarunta sun ja zata iya shiga ko wanne hali.
yana cikin wannan tunanin zaliha ta ƙaraso ba zato yaji tace '' malam ina wuni..?,
wani irin dam kirjin'sa yayi dakyar ya iya dagowa ya kakalo fara'ar dole yace '' lafiya qalau ya
jikin Hajiya..?,
zaliha tace '' alhamdulilah wallahi da sauki É—azu ma ta sha magani, abinci tace na kawo idan
akwai wanda zai ke gidan aunty yumna sai mu tafi tare da shi..,
Malam yace '' to masha Allah, Allah ya ƙara sauki a'a ba wanda zai je, amma kawo a ajiye idan
akwai me tafiya sai na bashi ya kai mata kice ina godiya, ina yi mata kuma ya gajiya..,
ajiyewa zaliha tayi tace '' to insha'Allahu zan faÉ—a mata..,
kuɗi ya ciro a aljihunsa ya miƙa mata kin amsa tayi sai da yayi mata jan ido sannan ta amsa
tana yi mai godiya ta bar gurin.
#########
Misalin ƙarfe biyar dai-dai yumna ta farka buɗe idanuwan'ta tayi lokacin mommy da su juhud
suna hira a hankali ta saka hannu ta cire oxygen din da aka saka mata da sauri mommy ta tashi
tana cewa a'a yumna karki cire.
tashi tayi dakyar tace '' mommy mu tafi gida naji sauki..,
yumna ya jikin naki..?
cewar taufiq da yake facing din ta da sauri ta ɗago jin wata murya da ba , taɓa jin ta ba kallo
É—aya tai mai tasan dan mommy saboda kamar da taga yana yi da ita a hankali tace '' da sauki..,
TAUFIQ yace '' Allah ya ƙara sauki...,
jingina tayi a bango tace amin..
mommy tace '' taufiq kirawo JURAIJ kace ta, tashi..,
tashi yayi yace '' to..,
fita yayi kai tsaye office din Juraij ya nufa sai da yayi knocking sannan ya bashi izinin shugowa
shiga yayi ya zauna a kujera yace '' yaya yumna ta tashi yanzu tama cire oxygen din da kuka
saka mata..,
kwafa yayi yace '' yarinyar nan bata ji wallahi daman nasan zata iya aikata haka ...,
yaya wai me ya faru da ita ne har ta shiga wannan hali..?
cewar taufiq.
Juraij yace '' nima ban sani ba ka tambayi mommy mana..,
Copy is not allowed í ½íº«
Domin jin audio din Yan zaman Makkah Ku shiha wannan link din sannan ku danna min
subscribe Dan Allah.
https://youtu.be/cDE5bjYY2HY
___________________
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6817816be532b4a92550458c
Episode ¹³
Hmm tace min sai ta gama warware wa zatai min bayani abin da yake faruwa.
tashi juraij yayi yana cewa amma kazo kana tambaya ta , ashe ma tace zata baka labari har
yanzu baka dena halinka ba nason jin zance ni wallahi dama karatun jarida su mommy suka
tura ka ba karatun likitanci ba domin dashi ya dace dakai.
dariya taufiq yayi yace '' wallahi kawai abin ne ya dame ni shiyasa nayi magana yarinyar ta
shiga raina, musamman ma dana ji saboda damuwa ta shiga wannan hali ta ban tausayi da
shekarunta kanana ta faÉ—a irin wannan hali..,
hmm kawai juraij yace domin taufiq be san wace yumna ba amma Allah ya bata lafiya kwana
É—aya za tayi ya fahimci wace ita daukan folder yayi yace '' taufiq zaka zauna ne na je na dawo
ko kuwa fita za muyi tare..?,
tashi yayi yace '' a'a yanzu zan tafi sai kuma gobe insha'Allahu zan dawo naga ya jikin'ta yake..,
okay kawai yace tare suka fita wata nurse ta bi bayan'sa yana shiga mommy na lallabata ta ci
abinci takaici ne ya ishe shi ji yayi kamar ya buge ta sai wani shagwaɓa take yi mommy na biye
mata Allah ne kaÉ—ai yasan me tai wa mijinta ya sake ta shikkenan ta cuci kan'ta, ta zama
ƙaramar bazzawara ƙara tamke fuskar'sa yayi domin baya son raini...
jan kujera yayi ya zauna yace '' mommy barka da yamma..,
cikin kulawa mommy tace '' barka dai ashe ya fada maka..,
m
Eh ya faÉ—a min ya faÉ—a yana buÉ—a folder din yumna batare da ya kalle ta ba yace '' ya jikin naki
dame dame kike ji a jikin ki..?,
dauke kai tayi tace '' na samu sauki ni ka sallame ni..,
ji yayi kamar ya buge ta amma sai ya danne yace '' tambayar ki nayi me kike ji a jikin ki..?,
ɗauke kai tayi ranta duk a ɓace tace '' nace maka na samu sauki fa..,
ajiyar zuciya ya sauke yace '' okay..,
ajiye folder din hannunsa yayi ya soma haÉ—a allura gaban tane ya faÉ—i ba abin da , ta tsana
sama da allura har gwara magani tana iya sha idanuwanta ne suka fara kawo ruwa zuciyar ta ,
ta fara rawa tamkar zata faso kirjinta ta fito tace '' mommy ki yi mai magana nafa ce mai na
samu sauki amma kinga yana haÉ—a allura.., mommy tace'' haba yumna ya zan shiga aikin sa, bakya so ki samu lafiya sosai kinga fa kwana
biyu duk kin rame..,
haÉ—e rai tayi zuciyar ta ba dadi wato itama mommy ta goyi da bayan sa ai kuwa ba allurar da
zai mata kallon sa tayi tace '' ya Jawad cire min ƙarin ruwan nan zan shiga bayi..,
be nuna ma yaji me take cewa ba , balle ta saka ran zai amsa mata ranta ne ya ɓaci tana
wannan tunani sai ji tayi ƙarar shigar siriji a dantsan hannunta za bura za tayi tuni ya riƙe ta ya
hanata ko da motsi sai da ya gama yi mata tas, sannan ya saka audiga a gurin yace '' ungo ki
danne ta kar ta zame miki ciwo.., idan ta tanka shi to bango zai magana ganin haka ya saki murmushin mugunta karfin zuciyar ta
yana bashi mamaki ta rasa da wa za ta dinga faÉ—a sai dashi yau zata gane kuranta,
dannawa É—aya yayi mata sai da kashin ta ya amsa cike da mugunta yake mulmula mata gurin ,
kuka ta saki amma be saurara mata ba har sa da yaga jikin'ta yayi laushi sannan ya barta.
daukan folder yayi, yace '' mommy sai da safe..,
Mommy tace '' yau da wuri haka zaka tashi..?,
Eh wallahi ina so na biya gidan su ahlam na ƙara ganin jikin ta.
to Allah ya ƙara sauki
da sauri yusrah tace '' yaya zan bika daman yanzu nake shirin tafiya gida..,
juraij yace '' to tashi mu tafi...,
Juhud ta gallamata harara tace '' ni kuma ce miki aka yi ba tafiya zan yi ba ,
yusrah tace '' ai na zata da yaya taufiq za ku tafi ne shi ya saka ban yi zaton tare za mu tafi ba,
baki tawo da motar ki bane..?,
Mommy tace '' tuni taufiq ya tafi gida..,
mommy ke kika bata amsa a gaban ta ya TAUFIQ yayi miki sallama yace amma shine take
wannan maganar sai kace wacce ta sha kwaya
juhud ta faÉ—a cikin zafin rai
Dafa ta yusrah tayi tace '' Allah ya baki hakuri...,
ganin zai tafi ba abin da kuma yace da sauri tace '' ya Juraij baka sallame ni ba, nace maka naji
sauki...,
wani kallo ya yi mata tuni ta hadeyi sauran zancen ta wannan kallo da yayi mata ba ƙaramin
nutsar da ita yayi ba , kowa shakkar sa yake amma ita ce take ma iya musayar yawu da shi,
saboda zafin sa bama ya shiga sabgar mutane musamman wanda yasan zai raina shi.
bayan fitar su malam ya kirawo Hajiya da sauri ta É—auka suka gaisa yace '' na karbo takardar ta
saki biyu ne , É—azu Hajiya ta kawo mata abinci to wallahi ban san yadda zan mata bayani ba
kinga har yanzu na rasa nutsuwata bana so mutuwar auren yumna ta baza ko ina bana so a
sani.., ajiyar zuciya ta sauke tace '' wallahi nima yau haka na yini cikin tunani ko wacce hanya nabi sai
naga ba me bullewa bace ba , ga jikin hajiya bana so ta sani kar jikin'ta ya ƙara rikicewa azo a
haifi da mara ido...,
malam yace '' nima abin da nake jimami kenan wallahi..,
mommy tace '' to Allah ya shige mana gaba wallahi matar nan Ubangiji ba zai taɓa barin ta ba
da nayi ƙoƙarin daukan mataki sai kuma na gani idan na dauka tamkar na daɓawa kan mu
wuƙa ne
za a san me yake faruwa bayan so muku wannan sirrin ya rufu ba wanda zai ji shi nan kusa...,
tabbas haka ne amma ba yadda muka iya wata ran dole a sani Allah dai ya shige mana gaba.
amin ya Allah mommy tace
kwanan yumna biyu ya sallame ta saboda jikin'ta yayi kyau taji sauki a lokacin ma ahlam ta
dawo sosai suke takun saƙa da ahlam tambayar duniya ahlam tayiwa juraij wai fasa bikin akai
ko kuma wani abu ne ya faru amma yayi mata banza baya ma tanka mata.
hakan da yayi ba karamin fusata zuciyar ahlam yayi ba ji tayi ba wacce ta tsana a duniya sama
da ita tsoran ta É—aya kar juraij yace yana son ta
tunda ta lura duk abin da ake so a jikin mace ta haÉ—a shi , ita da take da aure ma tafi ta komai to
halin namiji ba tabbas duk irin son da yake mata zai iya sakawa idonsa toka yace labari ya
canza.
da taga suna mutunci da taufiq sai hankalinta ya dan kwanta ko kaÉ—an bata so wato kishiya.
Yau ranar Litinin yusrah ta tafi makaranta juhud wajen aiki taufiq ma ya bi juraij asibiti daga ita
sai mommy sai masu aiki rasa yadda za a yi tai wa mommy karya ta barta ta fita, dan a kwana
kusa take son barin kasar niger ta tafi makka.
tana cikin wannan tunani saliha me aikin su ta ajiye mata lemo tace '' gashi nan..,
É—auka tayi ta buÉ—e ta fara sha ba tare da tace komai ba kwata kwata tunaninta baya kan su
yana wani guri can daban hakan da saliha ta gani ya saka ta zauna kusa da ita tace '' yar nan
tunanin me kike haka ..?,
da sauri ta É—ago saita kan'ta tayi tace '' bakomai bana son magana ne baba saliha kaina ke
ciwo..,
dafa kan'ta tayi tace '' ayya sannu Allah ya baki lafiya kin faÉ—awa hajiya..?,
yumna tayi kallar tausayi tace '' a'a ban fada mata ba , bana so hankalinta ya tashi ..,
Baba saliha tace
''gaskiya kinyi kyan kai tunda na lura kamar kwana biyu hajiya na cikin damuwa
bara na kawo miki magani ki sha za kiji sauki..,,
da sauri ta kalle ta , tace '' a'a barshi nagode nan da anjima insha'Allahu zai saki..,
dariya tayi tace '' bakya son Shan magani Allah ya shirye ki..,
shiru tayi mata tabar gurin da sauri ta ajiye lemom hannunta ta shiga dakin mommy samun ta ,
tayi tana danna waya zama tayi a ƙasa tace '' mommy barka da wannan lokaci..,
mommy tace '' barka dai yumna ya jikin naki...,
ƙasa tayi da kai tace '' na samu sauki..,
to masha Allah
wasa ta fara da mayafin'ta tace '' mommy Dan Allah ina so naje gidan su wannan kawar tawa
yau ba kowa a gidan bana so na fara wani tunanin da zai ƙara kaini da kwanciya asibiti..,
murmushi mommy tayi tace '' to ba damuwa amma karki dade kinji..?,