Showing 27001 words to 30000 words out of 39380 words

Chapter 10 - KARUWA CE COMPLETE BOOK BY HaBieBatie.pdf

25 May 2025

2367

Har karfe shida nasafe yana rungume da ita yana bata baki haka baibar
yin kukaba.
Zumbur yamike kamar wanda yatuna wani Abu yafice daga dakin yana huci. Dakin zubaida
yanufa kamar zaki .
Daura hannunsa yayi jikin kofar yamurda yaji a rufe...kifa kansa yayi jikin kofar yanaji kamar
yasama dakin wuta.
Kasa2 yakejiyo muryan zubaida tana maga alamu waya ake.."baby don Allah kayi hakuri, wllh
ba laifina bane, hanani fita sannan sakaren yayi..amma wllh a'matukar bukace nake dakai,, ba
wanda nakejinsa amatsayin da namijin duk cikin mazan da nnke muamula dasu inbakaiba...wllh
duk nafijin dadin naka.." "To baby kinaga kamar yaushe zaki samu fitowa?."
"Kakwantar da hankalinka ..cikin satinnan zanfito ,,karka damu..
Wani wawan daushi yazid yakaima kofar wanda yasata faduwa kasa warwas..
Tashin hankali ne karara ya bayyana fuskar zubaida tamike dasauri tare da buga wayar a kasa.
Pointing dinta yayi da yatsarsa dake kyarma bakinsa narawa dakyar ya iya tattara kalmar "
*ZUBAIDA*...daman ke *KARUWA CE*..yafada cikin wani irin murya wanda bansan yana da
i'taba....!



_M͎a͎n͎a͎g͎e͎d͎ p͎l͎s͎s͎s͎ ._




*hαвєвαh luv*
[3/23, 7:31 PM] hαвєвαh luv: *K̥ͦḀͦRྂUྂW̆Ă CིEི...... 53/54*




_wrítíng вч_
*hαвíєвαh luv*

_єdítíng вч_
*ѕαdnαf*






*ᑕ* ikin wani irin taku mai diri wanda kamar zai fasa gurin yake nufarta, baya2 take a rude tana
bashi hakuri ."don Allah katsaya kaji, ba'abinda kake tunani bane.. Wani wawan naushi yakaima
bakinta wanda ya haddasa hakwarenta biyu suka fita, damko gashin kanta yayi yahada da
bango tare shake mata wuya da dayan hannun ... Lokaci daya jini yafara zuba daga bakinta
kamannin fuskanta suka fara sauyawa.
Shima yazid fuskansa kaurewa yayi, idonsa yay jaa don matukar bacin rea. "Meyasa kikamin
basaja i'ya zubaida!?, meyasa kika zomin amatsayin kamila bayan ke tamba daddiya ce!
Fasika!, mazina ciya!, maciya amana!... Meyasa kikamin hakaaa!!!!??." Wani jakin mari yakifa
mata har saubiyar saida kumatun ya fashi. Wani azababben ihu tasaki wanda saida duka gidan
yadauka.
Kamar a mafarki zahra kejin ihu, a hankali tabude ido nuwanta dasukayi jaa suna mata nauyi.
Gefe guda take jiyo sautin kuka gakuma kakkausar muryan yazid natashi. Kokarin mikewa
tafara, amma dasauri takoma takwanta sakamakon wani ubun radadi dataji gabanta na mata.
Muryan zubaida taji cikin wahala da galaibaita tana cewa ..."zan mutu...zaka kasheni...don Allah
kiyi..hakuri ....momyna..balaifina bane.. Laifin iyaye nane...suna sana diyyar shigana
karuwanci...!".
Zaro i'do zahra tayi *Karuwanci!?*, zubaida mai hijabi!."
Innalillahiwainnailaihirrajiun." Da kyar tatashi tana shije lips tashiga dakin yazid. Wayarshi taga
kan kado karasawa tayi tana tafiya kamar 'yar kaciya tadauka takira layin mami. Saida tai kusan
tsinkewa sannan Miami ta daga duk a tunaninta yazid ne. Cikin kidimewa zahra tace "mami dan
Allah kizo,,,,kizo yanzu ya yazid zaiyi kisa." A zabire mami tatashi daga kwancen datake "kisa
kuma zarah?." "Eh....Miami,,,don Allah kizo yanzu.." Daga haka takashe wayar. Mami gyalenta
kawai tazara tafice daga dakin.. Driver tashiga kwallama kira yazo aguje suka tafi gidan yazid.
Acikin mota mami takira wayar faruq ,bugu daya yadaga yaraka kunnashi tare da sallama ...ko
amsa sallamar batai ba tace "faruq kasameni gidan mahaukacin abokin naka, don zaikashe 'yar
mutane.." Daga haka tai kit takatse kiran..
Makullin motarsa kawai yadauka yafita yashiga yatafi.

Acan kam yazid sai dukan hauka yakema zuby sumanta biyu tana farfadowa haka kuma yaci
gaba da jibgarta. Zahra kam koda tagama waya da mami dakinta takoma takwanta ..zuwan
Yusuf kawai take jira tabar wannan masi faffen gidan.

A guje motarsu mami shigo gidan dagudu driver nta yashiga fαlσn mami nabiye dashi . dakyar
kake jiyo murya zubaida dake wahalallen ihu duk murчαntα tagama dashewa. Haurawa sama
yayi yabi direction din dakejiyo ihun still mami nabiye dashi.
Dagudu yashige cikin dakin ganin zubaida kwance kamar gawa shima yazid baibar jibganta ba.
Dagyar driver n ya fizgeshi ya hankad'a shi gefe .."bakada hankali ne yazid,,, kisan kai zakayi?."
Gadan2 yazid yakara nufosu yana kokarin fizgo ta, wani uwar tsawa mami tadaka masa wanda
i'ta tayi sanafiyyar farfadowar zubaida. Ba ihu ba ,hawaye, amma daka ganta kaga wanda yashiga bala'i da tashin hankali.

Rarimar wayarta tayi dagudu tashige bathroom tasa key.
Anyi sa'akwa tana kunne bata mutuba, dailing no. Din Momy tayi bugu biyu tadaga .."sai a
sannan wani bala'in kuka yazoma zubaida. Akidime Momy ke tambayarta.."Momy don Allah
kizo...yazid zai kasheni..wllh kasheni zaiyi momy..kizo." Katse wayar Momy tayi tashiga neman
layin daddyn zuby. Kintafiya kiran yayi don haka tazari mayafinta tafita driver yaja suka tafi. Gidan mama tace yafara kaita, ko get din ba'a budeba Momy tafita dagudu tashiga tana
kwalama mama kira.
Duk suna zaune dining suna break suka jiyo ihon momy.. Arman ne yafara isa gunta yana
tambaya lpy. Janshi Momy tafarayi tana magannanu wasuma bazaka ganeba "arman kazo
muje,,kazo muje..zubaida ta...zai kashemin ita...don Allah kazo ka kwaceta..."
"Momy waye zai kasheta!?." "Mijinta..mijinta arman..kazo muje.."
Ficewa sukayi mama ma tadauko maya finta tabisu.

Bayadda ba'ayi da zubaida tabude kofaba amma fir taki harsuka gaji suka dawo falo...
Mami tambayar yazid ta shiga yi amma yakasa magana sai ciwo da zuciyarshi ke masa yanaji
kamar yacireta ya huta.


Ko parking driver bai gamaba Momy tafita dagudu tana ihu tashiga falon.. "Ina yar tawa...tana
ina....mugu laananne zai kashemin ya.."
Jin muryar Momy yasa zubaida tafito da gudu tashige bayan momy ..

"Nashiga uku ." Momy tadaura hanu akai tana zunduma ihu lokacin dataga fuskar zubaida gaba
daya tafita daga kamanninta.
"Wayyo nashiga uku ni suwaiba,,,, meye Tanaka kakeson kasheta...wayyo ni.."
Farin ciki kamar zai kashe mama (wihuhuuu)
Arman ne yay karfin hali yaja Momy gefe ya zaunarta yana bata baki , dakyar tai shiru.
Tsit kakeji a falon sai shashshekar zubaida.
A hankali take daga kafarta tana bin bango tare da cije lips tafito falon. Tashi mami tayi
takaraso da i'ta tazaunar ta tana allonta da mamaki.
Maganar da arman yayine yadawo da momi garesu.
"YAZID!, don Allah munaso kasanar damu laifinda zubaida tai maka dahar hukunsan yay tsauri
haka.."
Dagowa yazid yayi yana bin kowa da kallo idonsa wanda suka rine kamar gaushi yasauka kan
zahra ....juyar da kanta gefe tayi tanajin wani irin haushin sa.
Sallama faruq yayi yashigo gaba daya hankalin kowa yakoma kansa.
Zumbur zubaida tamike tana zare idanu hanunta na rawa take nuna faruq ,,so take tai magana
amma takasa. Haka agun faruq ma bakinsa na rawa da kyar ya i'ya furta *zubaida*!,, meye
yakawoki nan, yazid karma cemin itace amaryar taka!?." ..cikin alajabi da kidima yay maganar..
Cikin mamaki yazid yashiga gyadawa gyad'a Kansa..
"Innalillahiwainnailaihirrajiun." Shine kawai abinda faruq ke fada a fili...
"Yazid meye yakaika auren zubaida!?, fasika!, mazinaciya!, karuwa! Mai lasisi a karuwanci!
Yazid!."

Salati duk 'yan dakin suka kaure dashi banda yazid dakejin kamar zuciyarshi tafashe.
"Wllh k'arya kakeyi munafiki,'yata ba karuwa bace...yarinya kamila ..mai hankali."
Wani uwar harara faruq yazuba ma mama..yace "a i'na tazama kamilar?,, to bari kiji.........tun
daga ranar da faruq yahadu da zuby a hanyar hotel taga iskancinta zata tafi gida......har
haduwar su takarshe kafin yayi tafiya ba abinda bai fadaba..." A hakanne zaki cema 'yarki
kamila as how?." "Wllh karya kake sharri kai mata."
Arman dashima gaba daya zuciyarshi a dagule yake da wannan alamari yace "Momy wannan
maganar gaskiyace, koni ma shaidane ."...labarin sheke ayarsu dasuke shida zuby
yayi...yakara dacewa " kuma Momy bamu kadaiba...akwai maza sunfi goma datake tarayya
dasu. Daura hanu Momy tayi akanta tana ihu "wayyo ni..zubaida ya haka rayuwarki?, na haifi
jaraba da kaina...abinda nashuka shi nake girbewa akan 'yata...wayyo."

Kallon yazid daya dafe kansa daduka hannayensa biyu yana balain sara masa mami tayi...sai a
sannan tai magana "YAZID!."
Dago da jajayen idonsa yayi yakalli mami batare dayace komai ba . "kafadamin dalilin dayaja
harma zubaida wannan dukan."
Da kyar yazid ya i'ya bude bakinshi yake magana...tunlokacin aurensa da zahra da wulakan ci ,
da cin mutuncin dayake mata, har i'zu haduwarsa da zubaida da aurensu...har zuwa wannan
lokacin ba'abinda bai fad'aba...
Tafi sukaji daga bakin kofa duk suka juya suna kallonsa. Yusuf ne tsaye, fuskarshi hade
da'alamu yaji duk zancen da suke...
"Yayi kyai malam yazid.. Ka wulakantamin yar uwa , kaci mutuncin ta..kai mata kazafi..da Allah
yatashi sama mata sai yahada ka da karuwa...nagode Allah dayasa kagani zahra ba karuwa
bace..kallon da ake mata bahaka bane,,,takawo maka mutuncin har cikin gidanka...to Alhmdllh
tunda yanzu kowa yasan cewa zahra ba karuwa bace..kuma takawo budurcinta gidan mijinta."
Karasawa cikin falon Yusuf yayi yakamo hanun zahra.. "Sister tashi mu tafi." Bamusu kuwa
tamike da kyar .
"YUSUF!." Mamin takira sunanshi , juyowa yayi yana kallonta. "Yusuf ina goyon bayanka , katafi
da zahra!."
Gyadawa mami kai Yusuf yayi..yama zarah alama dasu tafi.
Ea kuwa yazid yace i'na baisan hakaba,, tashi yayi yaje zai riko zahra mami tabuga masa wata
gigitacciyar tsawa. Cikin bacin rea take magana "har ka kuskura kataba yazid! Kaje kaci gaba
da zama da matarka 'yar mutuncin!." Girgiza kai yafara yi, sai a sannan hawaye suka fara
zubamai.."kiyi hakuri mami...don Allah har kumin haka..plss zahra na kidawo har
kibishi..kitaimaka wllh *ina sonki.*"
Tsaki Yusuf yayi yajuya suka fara tafiya. Kara yunkura yazid yayi zai rike zahra.
"Yazid wllh wllh wllh ka kuskura katabata saina tsine maka!."
Yana ji yana gani Yusuf yafita da zahra suka tafi.

Mami ma tasowa tayi takama hanun faruq suka fita.
Mama ma tabe baki tayi zuciyarta fal murna Yakama hanun danta suka tafi.

Jikin momy yana rawa hakama zuby takama hanunta tace "mutafi zubaida!."
Wani mugun kallon yazid ke binsu dashi wanda yay balain tsoratasu. "Gidan ubanwa zakije da
it's!?, kisaketa." Yadakama mama tsawa. Sake zubaida tayi takoma gefe. "Fitamin daga gida."
Yazid yay commending momy yana nunamata kofa.
"Ayyato 'yarta wafa.." Wani wawan mari yazid yakaimata , Allah yataimake ta kauce tafita da
gudu.

Juyowa yayi yanufi zuby gadan2 yafara ball da i'ta a falon ..dukunta take yana boll da i'ta haka
harya turata wani daki sake downstair ,, duk wani kayan electronic na dakin tsinkewa yazid yayi
yadaureta jikin gado yasa key a dakin yadawo falo.

Kifa kansa da kujera yayi yasaki wani marayan kuka mai raunata zuciya.



*Asalin labarin.....*






*hαвíєвα luv*
[3/25, 9:59 AM] hαвєвαh luv: *KARUWA CE.....55/56*




_Writing by_
*Habiebah luv*

_Editing by_
*Sadnaf*




_Wannan page din dukansa sadaukarwa ne gareku 'yan *GLAMOROUS, HASNA IDRISS
NOVELS, TASAKR HABIEBA LUV $ ANFA, RAZ NOVELLA, NABEELART LEDY NOVELS,
HABIEBAH LUV NOVELS, MATAN KWARAI, KHADIJA KANDY NOVELS, NEENAH COOL
FANS , SADNAF NOVELS....* kukasafta wannan koda *word* daddaya ne. Duk Wanda bai
samuba yaymin magana don bansan rigima�._

_Luv u my fan, inasonku kamar nayi rawa...._







*Asalin labarin...*

*Alh Sulaiman Goni* mahaifin *zahra* yakasan ce haifaffen garin Maiduguri ne, yayin da
rawuwarshi take kano gurin uncle dinsa..acan yay primary yay secondary har jamiar sa acan
yayi. Yafara aiki a karkashin company nin uncle dinsa, yayinda shine manager a company nin
saboda hazakarsa sa kwazonsa...wata rana yazirci i'ya yensa a borno Allah yasa yay gamda
katar da *Fatima Zahra* yarinya mai hankali da natsuwa..tunda yakalketa soyayyarta ta
kamashi lokaci guda yaji baya iya rayuwa inbada i'taba. Baiyi kasa a gwiwa ba yasanar da
i'yayenshi, ba bata lokaci mahaifin Sulaiman yaje dakanshi gurin abban Fatima da maganar.
Dama aka bashi dayaje in Allah yasa suka fahimci junansu falillahil handih..
Cikin kankanin lokaci kuwa tsarka kekkiyar soyayya mai tsafta ta shiga tsakanin Sulaiman da
Fatima. Bab'ata lokaci kuwa magana ta i'sa gurin manya acikin wata shida aka gama komai
aka yanke biki wata daya. Biki budiri rabar bikin Fatima da Sulaiman anyi shagali an zubda
naira domin kuwa akawta ta dangin amarya da dangin ango kowa yanajin shima wani ne sosea
akayi barin kud'i. Bayan la'asar dangin amarya suka shirya akatafi da i'ta gidanta dake garin
*KANO* bayan nasihu datasha gun 'iyayenta da 'yan uwa. Kwanan su biyu suka dawo akabar
amarya daga i'ta sai angonta. Aurensu nada wata shida yatafi karin karatu, ,,,,cikin shekara uku
dukiyar ta harzuga yakoma business tsakanin kasashen waje zuwa nig. Bayan aurensu da
shekaru biyar..shiru2 bazancen haihuwa,, sunje asibiti andubasu domin suna tunanin ko akwai
wani matsalane amma babu..tun suna damuwa har suka share da lamarin ..haka sukaci gaba
da rayuwa cikin kwanciyar hankali.


*Alh Omar Matawalle* shine mahaifin *Yazid* tare da matarshi *Haj Aisha* dukansu 'yan garin
kano ne. Alh umar yakasanci masha hurin mai kudi haka babban dan siyasane..sunyi aure da
Aisha tun kammala secondary school dinta suna zamansu na lpy. Shekaransu d'aya da aure
Allah yaba ta haihuwa ta haifi d'a namiji mai kama da ubansa sak! Karkuso kuga murna a family
nnan ranar suna yaro yaci suna *Yazid* sunan mahaifin Aisha ...anyi shagali naira tayi kuka
ranar sunan.
Abotar Alh Sulaiman Goni da Alh Omar Matawalle tafarane ranar wata litinin agurin wani
occasion na 'yan siyasa yayinda aka gayyaci manya manyan ma'aikatan gwannata..tundaga
nan aminci yashiga tsakanin su, yayinda yazama hatta matansu sunzama aminan juna kamar
*Dangin juna* haka suka zama.

*Alh Usaman Dala* wato daddy n zuby yakasamce bakano, mutum mai tsanani akan boko!
Yana bata muhinmmacin sosea a rayuwarshi..shi prof. Ne, kuma babban doc. ne..sananne ne
sannan kuma attajiri ne.


*Suwaiba* wato *Momy* tareda kawarta aminyar ta Wato *Hajara (mama)*. sun kasance 'yan
*barya*, karamar hukamar a jahar kano.
.sanannu ne sosea garin bawanda bai sansu ba gurin rashin kamun kai, da biye biyen
maza..bankad'anci...da shige2.
Suwaiba ta kasance i'ta kadaice gurin 'iyayenta , talakawa ne sosea gasu da son abun duniya..
Mahaifiyar suwaiba ta kwarance gurin bin malamai da bokaye..gashi bawai abin Duniya
garesuba amma tana zuwa gun malamai kawai don mallake mijinta.
In kasan Suwaiba to kasan hajara don hanta da jini suke tif da taya. Ranar wata talata, ranar
alh usman dala ya ziyarci wani kauye dake kusa da *barya* motarshi ta b'aci a hanyar dadowa,
kamar daga sama suka hamgo wani hadadden matashi, Suwaiba da hajara ne ke tahowa.. Jiki
na rawa cikin rige2 sukayo gunsa. Gaisheshi sukayi ya amsa ba yabo ba fallasa donshi baison
harka yan qauye. Ruwa yace sukawo mishi suwaiba cikin azama takoma cikin gari ta daibo
masa ruyawa..kudi mai uban yawa yabasu yaja motarsa yatafi.. Tun daganan Suwaiba da
mahaifiyarta suka samai kohon zuk'a, da bokaye da malamai saida suka jawo usman ya
haukace akan son Suwaiba. Cikin karamin lokaci akayi auren aka kaita kano dangin usman
bason auren sukeba amma bayadda suka i'ya gannin dan uwan nasu zai iya rabuwa dasu akan
maganar. Hajara kam kamar ta mutu don bakin ciki tanaji tana gani haka aka aurar da suwai a
birni..domin 'iyayenta bamasu son abun duniya bane, mutanene masu saukin rayuwa masu
godema duk abinda Allah yabasu.. A haka wani daga cikin samarin kauyen lauwali yaro mai
hankali da sanyi yafito yace yana son hajara murna agun iyayenta baa maga domin burinsu
baiwuce itama tatafi dakin mijin taba. Hajara kamar takashe lauwali domin bata sonsa, mahaifin
lawwali abokin mahaifin ta ne don haka cikin kankanin lokaci akayi bikin. Ranar da a'akai
hajara dan madaidaicin gidanta..(domin lawwali yanada sana'arsa) hanashi shiga dakinta tai
tarufe kofa sai
a soro yakwana ... Auren hajara nada wata hudu tasamu ciki , karkaga bala'i gun hajara "ita
bazata haihu da talaka matsiyaciba" ..garaba dai kala2 bawanda bataiba tasha yunkurin zubda
cikin amma Allah baiyiba saida ta haifeshi. Ranar suna yaro yaci sunan "Muhammed sani*
anace dashi *Arman wanda Haj. Suwaiba ta nada nasa don (kasan abinka da 'yan birni
wayayyu) .
Haj. Suwaiba shiru2 har shekara biyar ba ciki ba labarinsa, yayinda ta danne zuciyar mijin da
asiri don haka ko damuwa bayayi saidai danginsa suma hasukayi suka hakura. Ashekara na
shidane Allah yabata ciki karkuga tarairaya da kulawa agun Alh usman dayake bata. Ranar da
Hajiya suwaiba tahaihu Alh.usman kamar zai cinyeta don kauna da i'ta da abinda ta haifa, ranar
suna jaririya taci suna *Zubaida* anyi shagali kuma anyi barin kudi ranar. *Zubaida* nada
shekara hudu aka sata nursery yayinda *fauxiyya* (yarinyar da hajara ta haifa bayan haihuwar
arman da shekaru hudu) keda shekaru shidda a duniya shikuma arman nada shekaru goma.
Lawwali yana cikin tashin hankali da masifa domin kuwa masifar yau daban tagobe daban da

hajara ke masa, ahaka harya kamuda hawan jini da ciwon zuciya kullum yana kwance gida ba
lpy gaya bawata kyakkyawar kulawa .. Ana cikin hakane Allah yamai rasuwa saida muce Allah
yaji kanshi. Hajara kam abun bai dametaba ko a jikinta don daman kamar kaya yazame mata,,
yanzu kwa tayada kwallon mangoro tahuta da kud'a. Bayan tagama takabane tashirya ziyara ta
musamman zata kaima kawarta, aminiyar ta *Haj Suwaiba* a kano. Bakaramin mamaki taiba
ganin irin daular da kawarta ke ciki. "Uuhm!...rayuwa kenan! Yanzu suwaiba kece cikin wannan
daular!?." Farr suwaiba tayi "hmm kedai bari ..duniya kam nasameta." "To sumu kuma haka
zamu kare da zani daya kenan." "Aa, kikwantar da hankalin ki, tunda yanzu bakida aure kwai
abinyu." Zabura hajara tayi tamatso daf ta i'ta "ayya menene fada min." "Akwai wani abokin
Alh., sunanshi *Alh Sulaiman Goni*, yanada mata daya kuma bai taba haihuwaba. Zakije
gidan a matayin naiman taimako su taimaka subaki aiki koda share2 ne, idan anyi sa'a sunbaki
daganan kuma saimusan abinyi." Wani tsallen farinciki hajara tayi tarungume kawarta hards dan
hawayenta "ngde kawata, ngde ngde..Allah yabarman ke."






*hαвíєвαh luv*

[3/26, 1:04 PM] hαвєвαh luv: *KARUWA CE.....57/58*



_Writing by_
*Habieba Luv*

_Editing by_
*Sadnaf*






A gidan haj suwaiba hajara ta kwana, sakamakon mijin bainan yaje

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login