Showing 36001 words to 39000 words out of 39380 words

Chapter 13 - KARUWA CE COMPLETE BOOK BY HaBieBatie.pdf

25 May 2025

2375


ranar." "To amin mama, ni zanje gurin my nabil." "Kigaidashi, kije mamanshi na gaidashi.." To
mama zaiji." Ficewa tayi daga falon tana baza duwawu, mama ta fallawa farida harara.."dalla
tashi kishige ciki kullum kina zaman gida bakida mashinshini..mai bakin jini kawai." Dagudu
farida tashige bedroom dinta tafada gado tareda sakin wani kuka maiban tausayi. Kamar
kullum sai da yagama kissing dinta kafin yad'ago jajayen idonsa yana kallonta .plss baby
aunguwa zaki rakani..." Yafada numfashinsa na sama da kasa .. "Wani unguwa kuma baby.."
"Gidan yayar momyne, kullum saita tambayeki..tace inkawo ki..plss don't say noo.." Wani dadi
fauxy taji tunkan tashiga har family sunfara tambayarta.. "OK ..to muje.." "To baby kije kigawa
mama.." "Noo karka damu , ba'abinda zatace." Wuta yay ma motar suka fita daga gidan. Saida
sukeyi tafiyan kusa 1h kafin suka i'so bakin wani gida. Gidane mai kyau nagani nafada..horn
nabil yayi maigadi yabude mai get. Gidan shiru kamar bakowa ciki. "Bismilla baby,,,mushiga.."
Yafada yana shigewa gaba. Abakin falon suka tsaya ya danna doorbell amma shiru sunkusan
kai minti biyar gurin amma ba'alaman za'a bude "baby mushiga kawai maybe basakusa." Shiga
sukayi fauxy tazauna shikum yay upstair. Baidad'eba ya sauko hannunshi rike da ruwan faro
.."baby kigafa auntyn batanan nakirata tace makofta tashiga yanzu zata dawo.." Yafada yana
ganin reaction dinta.. "OK badamuwa, mujirata." Wasa yafara da i'ta sosea wannan karon abin
yafi na kullum,don saida nabil yasamu nasarar shigarta. Tureta yayi, ya hankad'a ta gefe yana
watsa mata wani mugun kallo.
"Damake 'yar iskace Fauziyya!?, damake ba cikekkiyar budurwa ceba!, Allah yatona maki
asiri..gara da Allah yasa ban aureki ba..dama kinje kingama bada kanki awasu 'yan iskan
shiyasa bakida matsala kona tabaki..karuwa kawai..harki kara nunawa ko a hanyane
kinsanni..kuma bazan aureki ba ...get out!!!." Yadoka mata wata uwar tsawa.. Jikina rawa tana
hawaye tace "don Allah nabil kayi hakuri,, wllh insonka..karkamin haka..plss natuba sharrin
shaidan ne..amma zan gyara.." " before I open m eyes kificemin...inba hakaba saina kasheki!."
Jinkisa yasa tatashi tad'aibi kayanta hanu tafice tana kuka. Sai a balcony tasa kayan ta sannan
tafita . abakin titi tasamu abin hawa, har kofar gida yakaita tabishi kudinshi tashige..bakowa falo
don haka dakinta tawuce tasa key tashiga kuka tana tunanin yanda akayi lokaci daya abubuwa
suka dagule mata.
Borno...yazid cikin farinciki yakasance wannan ranar, kwana yayi yana salla yana godema
Allah.. Kuma yana rokon Allah daya sassauta zuciyan zahra tatausaya masa tadawo. Bayan
sunyi breakfast yazid yadauki makullim mota baikobi takan ajibt ba yafice wani babban mall
mai suna *S MATA SHOPPING MALL* . siyayya yayi sosea na kayan kwadayi, saida yacika
manyan leda biyu sannan yakoma gida. Afalo yatarda ajibt zaune yana danna waya, wani
dariya ne yazoma ajibt daya ganshi da leda.."aa malam yazid mijin zahra daga i'na haka ko
gayyata babu.." B'ata fuska yazid yayi "kaga bansan wulakanci, inzaka rakani katashi kashirya
don nima shiryawa zanyi... " daga nan yashige bedroom. Dariya ajibt yarinka yi saida yayi mai
i'sarsa kafin yatashi yashiga shiryawa. Karfe shabiyu dai2 suka gama shirinsu sukama Umma

sallama suka kama hanyar gidan *Alh Alkhali.*
Wannan karon harcikin falon aunty su yazid suka shiga,
Duk suna zaune aunty na karanta wani newspaper su zahra kuma nazaune sunsa laptop gaba
suna kallon pics.
"Assalamu alykum." Sallamarsu tasa aunty duban bakin kofa, fara'arta ta fadada ta amsa
"sannunku da zuwa,,,kukaraso man." Saida sukayi nailing suka gaida aunty kafin suka zaune.
"Ajibt ya ummanka ?." "Lpy lau aunty, tace agaisheki." "To ina amsawa, salma kawo musu ruwa
man." Tashi tayi ta gaidasu kana tawuce kitchen . zahra kam tunda taji muryar yazid gabanta
ke faduwa sosea2, da gyar ta'iya bude baki tace "ina..yininku..." Murya narawa. takara sa, ajibt
ne kadai ya amsa don yazid garara amsawa yayi sai ido daya kafeta dashi.wani irin kyau dayafi
ko yaushe taimasa, sai shining take gawani uban fari datakara da kibar datayi. Gaba daya
zaman gurin ya i'sheta tatakura sosea gashi bata i'yajin kafarta zata dauketa tabar gurin, itadai
burinta sutashi sutafi.
Salma da katon try tafito daga kitchen, baked chicken meatballs ne ciki da pizza with chorizo,
avocado and goatcheese, sai hot drinks. Tunda tafito ajibt kebinta da i'do hakanan yaji ta
burgeshi, wani dan medium centre table ta janyo ta i'jiye kai. "Sunnuko!." Ajibt yafad'a yana
mata murmushi mai kyau. "Yawwa!." Bawani yunwa sukejiba amma don gulma saida suka kusa
cinyewa (sunji delicious). Sunfi awa biyu gidan daga bisani sukama aunty sallama .."to aunty
mu zamu wuce.." "Har zaku tafi ajibt, to kagaidamin da ummanka.." Har ajibt yakai bakin kafo
yazid yananan idonsa nakan zahra da i'ta kuma duk attention dinta nakan system din gabanta..
"Kaga malam inba yanzu zaka tafiba nizan wuce.." Gaba daya kunya yakamashi yajuyo yana
dan sosa kai yama aunty sallama suka wuce.. Haryaje bakin kofa ajibt kuma yafita yajuyo sai
kuma suka tad'a ido da aunty , kasa yayi dakai yana shafawa..juyawa yakarayi zaifita still ay
kara juyowa. Murmushi aunty tayi tace "is there anything!?." "Um..aunty dama..nace..dan
Allah..inason magana..da i'ta.." Yayi maganar cikin kinkina. Gyada mishi kai kawai tayi, dasauri
yafice yba gurin ajibt. Harara ya galla masa "kaje kayi zamanka dalla kasani jira.." "Kai
bawannan ba
,yanzu kajirani mota zanyi magana da gimbiyata ne tananan fitowa." Tsuka ajibt yaja yay
shigewarsa mota shikuma yadawo gurin wani rumfa yazauna yana jiran fitowan ta.

"ZAHRA.." "Naam aunty.." "Tashi kije zakuyi magana da yazid!." Dasauri tad'ago tana kallon
aunty don ita duk da bataji mesuka ceba.."aunty injefa kikace, kumama ni bawani magana dazai
fad'amin.." "Nace kitashi kije.." "Aunty.... Daga mata hanutayi " shotup, don't say anything.. "
gaba daya ranta baiso hakaba , tashi tayi tayafa wani karamin gyele akan doguwar rigan
atampan dake jikin ta tafice. Bata karasa gurin dayake ba tatsaya can wani guri tajuya mishi
baya, murmushi yayi yatako har inda take yana kallon eyeball dinta. "Princess..!" Da mamaki
tad'ago tana kallon sa saikuma tasauke kanta don kwarjini daya mata. "Plss FATIMA! Say
something.. Plss inji muryanki..abaya nayi kuskure nazalunceki amma kiyi hakuri da duk abinda
yafaru, kitaimaka kidawo muzauna innuna maki irinson danake maki..plss ko dan babyna dake
jikin ki !." A mujun razane tad'ago tana kallon sa, sai a sannan ta'iya furta "BABY!!!?." "Yess
Fatima, akwai jinina dake yawo a cikinki! " yafada yana kaiwa hanu cikin tareda shafawa!. "Hey!
." Yusuf yafada da karfin gaske. Karasowa gurin yay ya wullar da hanun yazid dake kan cikinta "
meye hakan? Hargida zakazo kanama mutane iskanci!?." "Hy malam cooldown , ina duba

lafiyan babyna dake cikinta ne!." Kara tamke fuska yayi yana jefama masa banzan kallo "inma
baka cikin hankalinka to garama kadawo, don bawani ciki ajikin zahra..kuma gidanka ne
dabazata komaba!." " Dolene takoma ta haifamin yarona don bazan barta da cikina jikinta
tacigaba dazama nanba..hop kafahim ceni?." "ZAHRA!." Yusuf yakirata ba'alama wasa, "inaso
kifad'a mishi da bakinki cewa bazaki komaba!." Kirjinta ne yay wani mugun bugawa ruwa yafara
taruwa idonta. Same with him shima kirjin nasa bugawa yake yanajin Yusuf yafara fin karfinsa..
"Say it.." Yadaka mata tsawa, cikin rawar murya tace "ban komawa gidanka yaa yazid..!"
Kamar ansauke masa guduma a kirji haka yaji saukan maganar.. Zayyi magana Yusuf yaja
hanunta sukabar wurin. I'donsane yaciko da kwalla kanshi na balain juya masa kawai maganar
zahra ne yake masa suwwa cikin kunnen sa da kwakwalwarsa.."bankomawa gidanka..."
Hawaye kawai yaji yana sauko mai. Ajibt dake cikin mota yana ganin duk abinda ke faruwa
yafito yakamata hanunsa yasashi mota suka wuce gida.
Zahra kam suna shiga falo ta fizge hanunta daga na Yusuf tashige dakinta tasa key tafada gado
tana kuka!. Mike kafada yayi dai2 zaifita yaji muryan aunty "YUSUF zonan!." Juyawa yayi
yaganta tsaye bakin stairs tahad'e rea sosea saida gaban Yusuf yafad'i .. A hankali yataka zuwa
gurin "gani aunty" yafada a hankali. "Karka kara shiga tsakanin yazid da zahra!, mata da miji
ba'ashiga tsakaninsu watara kai zasu bama kunya...kuma meye amfanin sakinma in anyishi
tunda har Allah yakawo rabo a tsakini, yazid yayi laifi kuma yagane laifinsa easai a barshi
haka..plss kabar shi haka.." Cikin sanyi yad'ago yana kallonta,"aunty nima bawai ina abunnan
don wani manufa bane, inayi don inkwata mata 'yanci ne.." "To shikenan hakan yayi kyau kaje
Allah yaymaka albarka." "Amin aunty na , ngde."

Suna komawa gida yazid yashige bedroom yafada gado yana kuka kamar karamin yaro. "Haba
yazid meye kake yi haka!, saikace ba namiji ba kazo kana kuka akan mace.." Dukda kukan
dayake bai hanashi hararan ajibt ba "nayi kuka akan mace, don bakasan irin son danake
mataba ne saisa kake fadan haka , wllh mutuwa ma zan'iya akanta..plss zahra don't leave me I
can't stay without u......plss come back closer to me.." Kuka yarinka yi kamar yaro, ajibt yayi
rarrashin harya gaji yabarshi.
Yau Thursday ranar da abban ajibt zai dawo, karfe biyu guide dinsa sukaje daukoshi a airport.
Bayan yahuta yayi wanka yaci abinci su yazid sukaje mishi sannu da dawowa, gaisawa sukayi
da yazid da fara arsa "when did u come yazid?." ,"since 5days back abba." "Ina maminka"
"Abba tana nan lpy.. Tace agaida ka.." "To yayi kyau...amma yanaga dukka sanza kazama wani
irin?." Yazid dakaman jira yake yafashe da kuka "suhanAllah..what's happen.. Fadamin meye
yake faruwa?." Yazid bai boyeba ya zayyanewa abba komai tundaga aurensu.. "Kakwantar da
hankalinka, insha Allah komai zaizo karshe soon, dakaina zanje gurin Alh anjuma kajiko?" "To
abba ngde Allah yakara girma.." Fita sukayi ajibt na mishi dariya.





*👄habiebah Luv👄*
[4/2, 12:58 PM] 👄hαвєвαh luv👄: *í ½í²KARUWA CEí ½í²....69/70*

*END....*
I’m waiting,hoping and wishing for the time when we can be together again. I miss you so much
my *FANS*😭.


_Writing by_
*👄habiebah Luv👄*

_Editing by_
*💅Sadnaf💅*



í ½í²í ½í²í ½í²í ½í²í ½í²í ½í²í ½í²í ½í²í ½í²


Misalin karfe 9:30pm abban ajibt yadawo daga gidan Alh Alkhali, fuska ba walwala yafito daga
mota bayan wani guide dinshi yabude mashi kofa. Yazid da ajibt kuwa suna zaune compound
suna jiran dawowan abba, tunda yazid yaga yanayinsa ba dadi gabansa ke dukan uku2 lokaci
daya idonsa yafara tara ruwa. Kallon ajibt yayi wanda shi idonsa na kanshi "frnd Allah yasa
bawani matsala aka samuba, don naga mood dinshi is so bad.." Yazid yafada muryanshi na
cracking. Dan bubbuga kafadanshi ajibt yayi "be strong mana man,, insha Allah everything will
be alright..ka kwantar da hankakinka." Tashi sukayi sukabi bayan abba bayan yashiga part
dinshi. A falo suka sameshi zaune yayi crossing legs yana kadasu. Nan kasa suka zauna suka
gaidashi batare da ya amsa ba yafara magana. "YAZID!." Abba yakira sunanshi da babbar
murya. Nan take jikin yazid yakara sanyi kwalla nataruwa idonsa don yasan babu nasara a
wannan lamarin, cikin sanyin murya ya amsa kansa na kasa. "Kasaurareni da kyau, kabar
ZAHRA! , kakyalesu nan da shekara daya mugani..suda kansu zasu naimeka. Harka kara zuwa
inda take muzuba musu ido.." Tunda abba yafara magana hawaye yafara saukoma yazid yanaji
kamar ruwan wuta ake zuba masa jikinsa.."shikenan nashiga uku.." Abinda kawai yake fada
ransa. "Kanajina ko!?." "Eh..ab...ba.." Gud..u can go..." Dakyar ya i'ya Jan kafarsa yafita daga
dakin , suna fita yafashe dawani irin kuka yafada jikin ajibt. "Shknn na shiga uku frnd ..mutuwa
zanyi wllh...wllh zanmutu..ya Allah help me.." Kamar karamin yaro haka yazage yana kuka.
Dakyar yajashi daki yazaunar shi yana bashi hakuri,,amma ko saurarunshi bayayi. "Nikam
rayuwa ta tazo karshe ajibt... Don Allah ko bayan reana ka naimamin yafiya gurin zahra don
Allah... Bazan iya rayuwa ba'itaba..I can't.." Lokaci daya zazzabi mai zafin gaske yarufe shi ,
bakaramin tausayi yabama ajibt ba..injection yay masa yasamishi ruwa nantake yasamu bacci.
A week later... Yazid yagama fita hayyacinsa yarame yayi baki duk ya lallace duk wanda yasan
shi da yakalleshi yanzu dakyar zai ganeshi, kana kallon shi kasan yana cikin bala'i . yana
zaune falo ya buga uban tagumi yana matsar kwalla, ajibt nazaune gefen yana kallonsa.. "Frnd
nikan yau zanje gurin zahra, in mata koda kallon karshe kafin in mutu...don nasan rayuwa ta

tazo karshe.." Yakare maganar hawaye daya nabin daya fuskanshi. Gagara cewa komai ajibt
yayi don baisan mezeciba. Tashi yayi yay wanka yashirya cikin kananan kaya, dukda raman da
yayi amma kyansa nanan inda yake..makullin mota yadauka yafice daga dakin. Tunda yashiga
layin gabansa ke bala'in faduwa lokaci daya sanyi ya shigesa. A waje yay parking yafito yay knocking mai gadi yabude yashiga..kamar wanda kwai yafashewa
ciki haka yake takawa, a compound yagano Yusuf zaune kan rest bench yayi crossing legs
hanunshi rike da jarida yana karantawa.. Lokaci daya maganar Yusuf yadawo mishi.."yanzu
nike da iko da zahra bakaiba..dole sai yadda nayi.." Hawaye yaji nasauka a face dinshi don
yasan yayi wauta ..dayabi Yusuf a sannu da duk abin baikai hakaba..dakyar yaja kafarsa
yakarasa gurin da Yusuf kezaune yay nilling tareda kama 2legs dinshi yana hawaye.. "Broda!
Kataimaka min dan Allah.. Kabani zahra nasan nayi kuskure amma nobody above a mistake..
Ubangijin muna masa laifi kuma yayafa mana inmun rokesa..don Allah kugafar ceni gaba daya
..nagane laifina plss kubani matata ..." Kuka yazid keyi tsakani da Allah harda majina, tunda
yafara maganar Yusuf ke kallonsa da mamaki..shidai yasan abban ajibt yazo gurin abban su
kuma angama magana akan zata koma ..toko meye yanzu?..oho.." "It's okey..ya'isa, yanzu
katashi kaje gobe zan naimeka.." Kara rike kafanshi yayi yana masa godiya kamar zai ari baki..
"Bakomai katashi takaje.." Harya fara tafiya Yusuf yabishi da i'do yana mamakin yanda duk
yafita kamanninsa, dawowa yazid yayi yace "don Allah broda inason ganinta.." Batare da yace
kamaiba yacire wayarshi yay dailing no din zahra , few minute later saigata tafito sanye da
Arabian gown kana kallonta kaga wanda hankalinsa kwance cikin hutu.. Idonsa kyem akanta ko
kiftawa babu.. "Kitsaya zakuyi magana..." Yusuf yafada tareda mikewa yabar gurin.
Kamo hanunta yayi yarike cikin nasa hawayensa nazuba kai..dagowa tayi tana kallon sa eyeball
to eyeball tausayinsa na ratsata, i'ta kanta tasan yasha wahalan rayuwa akan ta. "FATIMA!." Taji
yakira sunanta, bata i'ya amsa mishi ba sai idonta data sauke kasa.. "Abunda nai makine
yakebina, ya hanani samun sukuni a rayuwa..kiyafemin kidawo gareni ..in nuna maki yanda
dake sonki..zan muna maki gatan daba kowace mace kesamuba..zaki alfahari dani amatsayin
miji.. Plss FATIMA for give me..."yakasa controlling kansa hawaye kawai yakeyi sosea yana
shashshek'a . " it's okey yaa yazid.. Kabar kuka, nayafe maka ..nadade da yafemaka yaa yazid..
" baisan lokacin da ya rungumota jikinsa ba ya furta mata "I LOVE U." Cikin kunnanta, zame
jikinta tayi tai cikin gida da gudu.." Farin cikin da yazid ya tsinci kansa cikin wannan lokacin
bazai misaltuba.

Bayan sati...ansa komawan zahra nanda sati biyu , gyara aunty tana ana mata..cikin lokaci
kankani zahra tazamo tauraruwa..su yazid kai sairawa yake yafadama mami duk abinda ke
faruwa.. Gyara tasa akafarayi agidan yazid na musamman. Ranar asabar yazid yazo tafiya da
matarshi , sosea aka sasu gaba akamusu nasiha har airport su Yusuf suka rakasu saida jirginsu
yatashi kafin suka koma gida.Karfe biyu suka sauka international airport dama already mami
tatura masu driver batareda bata lokaciba suka shiga suka wuce gida. Farin cikin da Mami ke
ciki bazai faduba kamar zata cinye zahra sai nan nan take da i'ta , part din Yazid tasa aka
gyara musu kafin agama masu gyaran gidansu. Har karfe goma suna zaune falon mami sunata
hira...yazid yagama kaguwa sutashi sutafi part dinshi. "Mami bacci nakeji.." Yafada yana
hamman karya.. "To ea saika tashi katafi..kona rikeka?.." Murmushi zahra tayi tadago tana
kallon yazid dashima idonsa yana kanta.. Lakwabar da kai yayi a hankali yace "plss mana

wife!." Juya mishi ido tayi tareda yamishi kwalo tana dariya kasa2 . har karfe shadaya suna
zaune saida mami tafara gyangyadi kafin taimasu sallama tace suma suje sukwanta. Mami tana
shigewa bedroom yazid ya dauki zahra cidak kamar wata baby doll suka tafi .
Washe gari.. Karfe tara suka gama shirinsu suka tafo part din mami..itama sauko wanta kenan
suka wuce dinning yin break.
A bangaren su zubaida kuwa ranarda daddynta yadawo ranar momy tafada masa duk abinda
yafaru, bakaramin kuka suka shaba dukansu kamar lokacin abin yafaru. Daddy n yafi ganin abin
laifinsa ne don saida tafito tasanar dasu cewa tanason aure amma boko tarufe mashi ido
yagagara ganewa..naiman yafiyanta sukayi suna kuka i'tama tanema yafiyansi. Daddy n ta
dakansa yaje gurin yazid ya naimi takardar zubaida bamusu kuwa yabashi dama ko baizoba zai
aika musu. Yanzu zubaida tazama mutuniyar kirki tayi watsi daduk rayuwanta na baya takama
Allah kullum tana cikin istigfari. Bayan tagama iddane faruq yafara biyowa tabayan gida,
bamusu tabasi hadin kai suka fara soyayya cikin tsafta donshima faruq yatuba da duk iskancin
dayake.
A gidan mama kuwa komai ya cabe mata domin kuwa fauxy ciki gareta..farida ta natsu takama
Allah baruwan ta da harkar kowa gidan kullum tana cikin tuba da abinda ta aekata. Ranar wata
talata abba yadawo daga abroad , tashin hankali daya shiga lakacinda yaga fauxy da ciki baa
magana..wuta ya bude masu akan ko tasamo wanda yay mata cikin ya aureta ko yakoresu
daga gidan shi..kuka sukarinka yi ita da mama suna rokanshi da kyar ya kyalesu.Wata rana
farida nazaune compound din gidan su kamar daga sama ta hango hisham yazo ya durkusa
gabanta yana kuka yan naiman yafiyar ta..yafemashi tayi itama kuma yace yanzu zai aureta,
dakanta tafadama abban su akan family hisham zasu kawo kudin aure.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya su zahra sunkoma gidan su ,,, son da yazid yake nuna mata
kuwa ba misali don kullum suna nanike da juna yanajin lafiyar babynshi..
Faruq da zubaida kuwa an daura musu aure yayinda suka tare a katafaren gidan faruq son
dasuke nunama juna kuwa baa magana. Anyi auren farida da hisham yayinda arman shima ya
dawo hanyar Allah yanaimi aure akabashi yanzu ansa auren nanda wata daya.. Mama itama
tagane laifin datayi baya , tana kuka taje gurin abban tana naiman yafiyarsa ,cikin ikon Allah
kuwa yayafe mata yarungumi 'yarsa zahra da duk wani abunasa yanzu da sunanta yake
yinshi..don kuwa soyayyarta sabuwa tadawo agareshi yana tunawa da mahaifiyarta. Fauxy kam
wani dattijon

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login