Showing 1 words to 3000 words out of 43444 words

Chapter 1 - ARNAN DAJI BOOK 2 by Feedyn Bash .pdf

[10/23, 2:18 PM] Ummu Subai'a: *ARNAN DAJI*



*NA*


*FAREEDA ABDULLAHI*




*_KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation





*BISSMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHAMA ME JIN KAI GODIYA
TA TABBATA GA ALLAH (SWT) DAYA BANI IKON CIGABA DA ARNAN DAJI BOOK 2 YADDA
NAGAMA 1 LAFIYA ALLAH YASA SHIMA NAKARE SHI LAFIYA NAGODE FANS*





*ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH INAJIN DADIN YADDA KUKE NUNA KAUNARKU
GA NOVEL DINA FANS ALLAH YASAKA MUKU DA ALHERI INAJIN DADIN ADDU OIN KU
GARENI ALLAH YABAR KAUNA YA BARMU TARE*





*WANNAN LITTAFIN SADAUKARWANE GA MAHAIFIYATA ALLAH YA KARA MATA LAFIYA
DA NISAN KWANA YA RAYA ZURI ARTA*

*ARNAN DAJI BOOK 2*



1-5


A guje lamunde ta debo ruwa ta zuba musu suka mike sunata kuka ba kuka zakuyi ba saurarata
zakuyi suhail ne yace tayaya zan saurari wannan tatsuniyar taki ni musulmine cikakke kuko
daga gani arnan daji ne Wanda gwamanati ta manta daku ana tunanin babu ku a duniya kuma
akwai sauran irinku dayawa


Meye sunanka dannan suna na suhail Dana suhel kai Dana nane tabbas saboda dan garin nan
ne kawai me wannan zanen ko wane gida da irin nasu rama juya bayanki ya gani ba iri daya
bane dana tenkwai Dan dai sunyi kama ne a zanen shiyasa zakaga haka amma ba iri daya
bane tana juyawa radau irin nasa ba wani bambanci ga kamarsu nan tsantsa ganewa ne ba
aiba Ashe




Cike da kuka tenkwai tace ni su waye iyayena kenan lamunde dama bake kika haifeniba kinsan
rama yar kice kika barta a hannun wani daban duk shirin mune tenkwai yanzu zakuji komai naji
nayarda cewar suhail zan dai Ji labarinki amma ni bakece mahaigiyata ba tayaya ina birni kina
daji ko sittira bakwa sawa bama kusanta ba sannan kice wai kece uwata Kuban ruwa zanyi
sallah



Suka fito yaga aduke a bakin daki HQ hangame kudaje sai bi suke ga kudansu narka narka ga
tsutsotsi na fitowa kadan kadan subhahanallah ya salam Allah meye wannan mutum CE
wannan kome kuna kallo zata rube kun barta haka



Munrasa yazami da ita fyade akai mata ta samu wannan lalaurar fyade ya furta Allah ya sawake
idan na koma gida zan aiko a dauketa a tafi da ita ai mata magani nayi alkawarin kawo cigaba a
wannan garin da kudina da jikina duk da ban fita wajeba da kyar ya iya watsa ruwa yai wankan
tsarki Dan be yarda da kansaba

Ba soso ba sabulu kasa yadinga sawa yana rage daudar jikinsa gaba daya kyankyamin Kansa
yake ya gama ya maida kayansa yanzu haka ze dinga fama da kaya daya saboda raunin Kansa
amma dole ze bar garinnan yau ko gobe hankalinsa a tashe yai alwala yai sallah kawai kallonsa
suke meye wannan dungure dunguren dayake oho masa ya Dade yana sallah yana addu oi
sannan ya gama mekake haka cewar rama Ku bari ba lokacin tambaya bane yanzu Idan
nagama Baku Baku labarin keda shi da tenkwai sai ya bamu nashi



Kuna saurarata eh sukace gaba dayansu harda aduke a dakin tafara bada labarin kakanku me
suna rana shine ya haifi mahaifinku me suna tabo nice babarku lamunde rama da kai suhel
kakanku ya kasance adalin sarki a wanchan lokacin yayin da da kakan jae shine waziri bashi da
imani ko kadan tun zamanin iyaye da kakakanni ake bautar gunki badu ake cin naman mutane


A yadda aka bamu labari da badu baya magana kuma duk sanda kaso zakaje kaganshi da
bukatarka ze biyama akwai masu kula dashi kimanin mutum talatin maza da mata suna masa
wanka da kwalliya rana daya aka wayi gari badu ya kashe su dukansu bebar ko gudaba ana
zuwa aka tarar da gawarwakinsu


Daga nan yasa dokar hana zuwa sai karshen shekara ko kuma sarki idan anshiga wani hali zeje
yayi bauta sannan Suyi magana yasa dokar yanka maza biyar duk shekara hakan shiya hana
kowa ratsowa ta dajin dajin ya zamana se mukadai yan garine muke rayuwa a cikinsa saboda
mutannen da ake kamawa aka bawa gunki jininsu kwanci tashi aka rasa na kamawa sai aka
koma kan mazan dasuke zaune a gari ana kamasu ana bawa gunki badu jininsu hakan yasa
muka kara Shiga matsi



Haka akaita tafiya har akazo zamanin kakanku yanemi badu ya janye wannan batu na yanka
mutane maza biyar maza sun fara karanci a garin sai mata kuma lallai sai Wanda ya haura
shekara ashirin badu keshan jini sunyi muhawara inda badu yace yaje yagani tunda yaja dashi
zega meze faru shiko ya tsaya kaida fata sarki rana a wannan lokacin ganin yadagene aka wayi
gari duk wani ahalin sarki ankashesu saura shi lokacin be auri kakarkuba yanada tarin mata a
lokacin



Haka yaita kuka yaje wajen badu yanemi gafarar sa akan ya janye Dan badu yace Somin tabine

sai yaga bayan duka yan garin haka gari kowa hankalinsa ya tashi ganin wannan mutuwar ko
da daya ba abar masaba kuma yace bashi ba kara haihuwa haka aka cigaba da wannan dabi ar
dama akwai dabi ar cin jarirai agarin indai ka haifi da haihuwar fari za a cinyeshi tas ai romonsa
Sam kakanku sai ya denacin naman jariran saboda bakin ciki ga ba damar daukar fansa haka
suka hadu da kakarku ya aureta a lokacin




Jeddah bakin ciki yai mata yawa Allah cikin ikonsa saiga afra nan suka Shiga daki itada afra ta
fashe mata da kuka ta debo mata result din tana kuka mtsww meye abun damuwa ina Ahmad
na layinku kije kidinga nemansa ki saki ranki kibi hakan kya samu kema ya yarda dake iyayensa
kuma ki kamasu a hannu nasanki da San abun duniya kwanciyar mage zaki me daukar rai
shima koyazo kice yayi hakuri sai nan da wata ukun kawai kije kibawa hanan hakuri ki Shiga
jikinta yadda zataje gidan tai ta zuzuta kirkinki kinga kece da riba




Shi kuma Ahmad karki yadda Ku hadu a nan gidan danke ba hankaline dakeba kudinga zuwa
hotel wanda yake da tsaro zamu shirya muje gun bokan Dana gaya miki ni yanzu zan koma
dama wayarki na kawo miki nagode afra tabbas nasan kina kaunata yanzu gobe da wuri zanyi
dabara naje mu hadu da Ahmad ya deben wannan muguwar sha awar suka fito ta rakata ta tafi
gida ita kuma ta dawo hanan tagani a parlour tanata kada kafa tana jiran ta tanka mata



Cike da murmushi ta karasa kusa da ita kiyi hakuri kanwarmu da abunda ya faru jiya tai mata
banza nayi kuskure ki yafemun kinsan ciwon ya mace na ya macene inasan suhail sosai kiyi
hakuri nasan kuna fushi banje nagaida mom ba amma yanzu ki tamabayar mana suhail sai mije
ki kaimu mudawo cike da murna ta kalleta haba anty jeddah har naji dadi kinga zami rayuwa me
dadi dake kafin na koma da nayi niyyar komawa sashen anty sadiga amma nafasa yanzu bara
naje taje ta sameshi yanata lele da uwargida rangida tagaya masa yabasu izini yaji dadi har
ransa




Suka fito hanan tajasu sai da sukaje supermarket me kyau tayi siyayya kamar hauka suka je
gidan baki duk sun ragu saura na nesa suka gaisa hanan tanuna musu ita a matsayin amaryar
suhail hajiya taji dadi kowa yanata yaba mata da sa mata albarka sai sunkuyar dakai take irin
na masu kunya aranta ko kira take zakuci ubanku dukanku dani kuke zancen saina raba
tsakanin uwa da danta

*Anan zan dakata sai naji comments dinku fans nagode da yadda kuke kaunar arnan daji haka*






*Feedyn bash*
[10/23, 2:18 PM] Ummu Subai'a: *ARNAN DAJI*


*NA*


*FAREEDA ABDULLAHI*




*_KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation





*Assalamu alaikum inawa kowa da kowa fatan alkhairi Allah yasakawa kowa da alkahairi ya
biya bukatunku na alkhairi gaskiya bansan haka kuke sona ba haka nake aranku ba sai jiya nayi
murna da farin ciki da addu oin gareni da comments dinku Allah ya bar kauna*

*Bissmillahir rahmanir rahim da sunan Allah me rahama me jin kai godiya ta tabbata ga Allah
ubangijin hallittu tabbata ga annabi Muhammad (saw)Allah yasa mu amfana da darasin fake
cikin wannan book din akuma dinga tunawa maguzawan daji ana kai musu tallafi Dan har yanzu
akwaisu duk dajin dazaka wuce akwai halittu masu rayuwa a cikin sa*



*Arnan daji book sadaukarwane ga mahaifiyata Allah yakara lafiya da Nisan kwana ya raya zuri
a*





5-10



Haka aka dinga nan nan da jeddah zuciyar hajiya tadanyi sanyi sai yamma suka koma
suhail yazo wajenta yana bata hakuri ta wani kwantar dakai ta rungumeshi ka kwantar da
hankalinka ba damuwa duk daya Mike nida ita nan yaso tabashi hadin kai amma ta kiya hanan
na labe naji sai hnkln ta ya kwanta ashe yadda ake zato ba haka takeba sharrin shedanne jiki
ba kwari suhail ya fito



Jeddah faduwa tai tasa kuka ga bikin zuwa ba zanin daurawa tuni jataba ta ciyota tai masa text
ummanta ba lafiya suna asibiti bata jira reply dinsa ba ta fice ta kira Ahmad tagaya masa inda
zasu hadu ta kashe wayar gaba daya danma karya kirata tana ganin text taki budewa kafin ta
karasa ya karasa samir guess palace sukai wa tsinke nan sukaci karensu ba babbaka suka
kwana suka hantse Ahmad dai shine ango Dan shi akaiwa gyara



Ya gigice ya fita hayyacinsa Dan ta kashe kudi wajen dibgar magani da kyar ya kyaleta dama
itama jarababbiya Ahmad dine dai dai ita dan yana masifar gamsar da ita duk da bashi da kudi
ita take bashi amma fa akwai kayan aiki haka suka kwana sai da safe taiwa gidansu tsinke
gabanta na gaduwa cikin ikon Allah sai kaninta kawai ta samu a gidan Wanda rabon data
ganshi har ta manta

Shame shame ta same shi ansassara shi an kawoshi anyasar a gidan yafi shekara baya gidan
wai yana Lagos daga baya ya dawo abuja a yadda suke samun labari amma yanaiwa uwarsa
aike idan yasamu dama yazama tantirin Dan iska haka ta dauke shi ta kira makocinsu ya
temaka mata ta kaishi asibiti ita ko ummansu iwar gantali ko ina tayi Allah masani dakayar suka
karbeshi duk da private ne ya jigata ya zubar da jini ko magana baya iya yi



Haka ta kunna wayarta sai ga text din mijinta yafi guda goma hankalinsa a tashe yanata kiranta
baya samun ta yai mata text ba amsa yaje gidansu a rufe ba kowa kamar jira yake saiga
kiransa ina kika shiga meya samu umman taki amma baki kyauta ba kin yafi ba Neman izinina
kefa amaryace me kwana daya a gidan ta amma ki fice ta fashe da kuka ba umma bace ba
lafiya kaninane gamu a asibiti tagaya masa hatsari yai ni kuma na dauka umma akace



Cike da tausayawa yace gashi nan zuwa yanzu da sauri tadinga Neman layin umman cikin sa a
ta shiga ta zayyane mata komai minti goma sha biyar sai gata a fujajan kamar dama tana kusa
ko wadda tazo a iska kafin suhail ya iso tazo tana shigowa yazo ta fashe da kuka cike da
kulawa yadinga bata hakuri yace za a sanja masa asibiti take ya karbi transfer aka sanja masa
asibiti me zaman Kansa providia kafin kace meye wannan kudine ke aiki har angama komai



Haka suka koma gida suka bar umma na jinyarsa duk da haka ransa ya baci fitar datai amma
be nuna ba ganin Mara lafiya kwanci tashi ya warke sarai nan yake basu labari ai abokan
adawarsune suka far masa sukai masa kacha kacha shine aka dawo dashi amma sun kafa
kungiya yanzu dama yasan dole kungiyarsu zata daukar musu fans a saboda kowace unguwa
akwai gang dinta daban amma shi ya dawo kano gaba daya ya hakura dazaman chan




Haka lokaci yai ta tafiya hanan ta koma garinsu adnan ya tafi Istanbul a lokacin watansu biyu da
aure lokacin haleema ta gyagije tayi kyau abunta lokacin ne jeddah ta fito da ainihin wacece ita
lokacin ne komai ya kwabewa suhail lokacin ne aka fara kuka a wnn gidan saboda masifa da
bala I irin na jeddah



Sun Dade har sun fara manyanta a lokacin sai ciki ya bullo jikin kakarku sarki rana yayi farin ciki

amma sai aka boye wannan ciki ba Wanda yasan dashi haka sukai ta boyeshi har ta sauka
lafiya ta haifi danta namiji akwai wata baiwa me suna timi ita ta karbi jaririn ta gudu da shi ta
hada danata dan zuwa chan garin dake makwaftaka danasu wato beguwa takasance tamkar
bokanya tanada danta shine mahaifin tenkwai baban rama kenan guga tabo da guga sun taso
cikin kulawa a hannun timi kwanci tashi suka fara girma a lokacin waziri yana da dansa ya fara
zama saurayi shima kusan sa an su tabo ne ana kiransa kaho



Rana tsaka badu ya umarci waziri dasu je shida mukarrabansa marasa imani su kashe sarki da
matarsa Dan ya duba akwai dansa da ya Haifa Wanda ba Wanda ya sani sai shi yanzu daya
gani yana tare da wannan baiwa data bace bat wato timi kuma zasu dawo saboda ya gaji
sarautar garin Dan haka su kashe shi waziri ya maye gurbin sarautar Dan kaho yazama sarki
tunda beda imani ko tausayi ya gado halin mahaifinsa waziri



Waziri jin wannan batu na badu yayi alkawarin cigaba da bawa badu jinin mazaje biyar koda
mazajen kuguru zasu kare baze fasa ba jin haka badu ransa yai kal ya basu sa a da kwarin
gwiywa cikin rashin sa a timi tazo kamar yadda ta saba zuwa da daddare idan tanasan kawo
musu dansu dansu saba tana boyewa saboda tanada lakani har su shiga su fita bame ganinsu
sun gama ganawa da dansu kamar bazasu rabu ba sunzo fita sukaji waziri da mukarrabansa na
tattauna yadda za a kashe sarki rana da matarsa saboda sunzo fita sukaji tafiya suka makale a
wani daki suka wuce ciki sukuma suna labe sunajin abunda suke kullawa dakin sarki suka tarar
dasu cike da farin ciki sun gama ganawa da dansu kamar bazasu rabu ba



Jin haka waziri yasa kai shida mukarrabansa yace suna ina ina danka da kake boyewa besanar
masa ba yai tsit yana mamaki shi waziri zewa titsiye suko timi suna shigewa taja hannun tabo
da guga suka fara gudu suna boyewa cikin surkullenta bame ganinsu har suka shiga garin
beguwa bame ganinsu kuka kawai timi take yaranma sunata kuka Dan sunji komai


Banda wani da waziri bayan duk sun mutu wace maganace haka mema ya kawoka turakata a
wannan Daren komeye ka bari sai zuwa gobe kuma wayabaka izinin shigowa turakata ya
kyalkyale da dariya nikake wannan tambayar badu yaban dama ya umarceni Dana dau ranku
ya dakawa yaransa tsawa wasu subimun bayan wayanchan munafikan Ku kuma Ku kwantar
mun dasu nayankasu haka sunaji suna gani aka kwantar dasu bazan yanka kuba ma saina fara
yanka danku da kuka fiso agabanku karka taba mana yaro meyai muku

Natabbata wannan badu din bashine ubangijin gaskiyaba akwai wani a boye Wanda bamusan
dashiba na tabbatar shize tsaremun bayana kuma jinina ne ze cigaba da mulki a garin kuguru
har abada yasa Abu ya doke masa baki ya fashe yanata zubar da jini banda kuka ba abunda
suke wayanda ya aika ne suka dawo sunje ko ina basuga kowa ba cike da bakin ciki waziri ya
kalli sarki



Tabbas a yau nasan nazama sarki koda danka ya dawo ba Wanda yasan shi Dan haka agaban
Dana zan yankaku saboda shine sarkin gobe bayan ni yasa aka dakko kaho agabansa ya
yanka kakanninku ransa kal yana ta murna kuka suka jiyo a waje kuma na namijine lamunde ta
dafe kirjinta mun shiga Tara yau shikenan muma kashemu za ai waye ya labe mana dukansu
waje sukai wazasu gani kowa sai da gabansa ya fadi





*Anan zan dakata fans nagode da addu oin Ku gareni sosai wasu sundena comment kome
yasa nice taku akoda yaushe*





*Feedyn bash*
[10/23, 2:19 PM] Ummu Subai'a: *ARNAN DAJI*


*NA*


*FAREEDA ABDULLAHI*




*_KAINUWA WRITERS✍ ASSOCIATION_*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*TALLA TALLA TALLA*

*AKWAI SABON BOOK DINMU WANDA ZAMU FARA MUKU POSTING ME SUNA (ANNOBAR
SHEKARA) LITTAFIN YA HADU YA NISHADANTAR LITTAFINE ME CIKE DA SOYAYYA DA
TSANTSAR ZALINCIN KAFIRAI AKAN MUSULMAI DA YADDA KAFIRAI SUKA DAU TSAFI
SUKE CUTAR DA MUSLMAI DASHI AMMA MUSULUNCI YAFI

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login