Showing 9001 words to 12000 words out of 43444 words
Chapter 4 - ARNAN DAJI BOOK 2 by Feedyn Bash .pdf
suka ruga gida da gudu
suna zuwa suka tarar sarki da dakarunsa a gidan Yana ta sheka dariya Inata kuka inaji Ina gani
ya rabani da jaririyar fegi saiga su tabo da guga sun shigo a guje suna rirrikeni
Haka aka tafi da wannan jaririyar aka yanka ta akayi farfesunsu da sauran Yan uwanta na
wannan shekarar bazan taba mantawa fa fegi ba ta sadaukar da rayuwar yarta agareni da Dana
haka muka hakura muka saduda Amma hankalina betaba kwanciyaba kullum da tunaninka
nake kwana nake tashi suhel Banda wata walwala a duniya tundaga lokacin bankara haihuwa
ba Nima
Bayan haihuwarka da wata biyu aka Kama wasu fulani lokacin bikin shekara ya kusa aka kashe
mahifin yarinyar uwar itama ta mutu sarki kaho ya aure yarinyar kasan wace wannan yarinyar
mahaifiyar kace Ja'e sarki kaho betaba samun haihuwaba sai akan ta ko wata biyu batai ba ciki
ya billo a jikinta matansa suka tsangwa meta suka hanata sakat danma sarki yasa doka me
tsanani da tuni sun salwantar da cikin ka haka taita rainon cikinta duk da shekarunta shabiyar
haka ta haifeka tun daga lokacin sarki ya dauki San duniya ya dorama
Ya doraka a turba Mara kyau ya koyama zalinci cin Amana ha'inci kamar yadda ya gada shima
a wajen waziri haka ka taso cikin gata alokacin ne matan sarki suka had a Kai sukaiwa babarka
asiri Wanda suka hanata Kara haihuwa har abada kaima Dan sarki yasa anma kafi da tsari da
tuni sun Dade da kasheka kasan gidan sarauta ba'a Zama haka tun daga lokacin har yau
mahaifiyar ka Bata Kara farinciki ba tunsanda tarasa iyayenta ta tsani kaho Amma Dan daukar
fansa take zaune dashi garinmu kowa yasan kowa tunda ba girmane dashi ba Mata sunfi maza
yawa saboda kashe maza da akeyi Kuma mu ko Mata dari zaka aura bame hanaka sharadin
sai shekara shekara Amma a shekara ze iya auran Mata ko darine
Bayan shekara biyar da haihuwarka lokaci daya muka samu ciki nida kanwar mahaifinka matar
guga farinciki ya cikamu Sam mahaifinka be damu da Yar uwarsaba shi kawai Kai yakeso Kai
yasaka a gaba tunda tasamu wannan cikin Bata Kara lafiya ba kullum a cikin ciwo take Haka
muka dinga rainon cikinmu cikin kwanciyar hankali Dan munsan wayannan yayan namune
zamu dinga kallonsu cikin ta yayi girma dayawa ko tashi sai an kamata take mikewa haka
tadinga rainon cikin Nan ba lafiya
Kwatsam labari ya iske sarki cewa anga tabo a wajen wannan kabari na sarki wanchan daya
mutu munga tashin hankalin dabamu taba ganinsa ba a wannan Rana a lokacin sarki yasa aka
kamo Masa tabo mahaifinku suhel aka kaishi fada aka dinga dukansa Ana tuhumarsa meye
hadinsa da wayannan mutane Ana duba bayansa akaga katon zane irin na jikinku Rama da
suhel shine ainihin zanen wannan masarauta akagan shi a bayansa ya wahala dakyar ya sheda
musu shidan sarki ne da suka kashe Kuma ko bayan ransa yayi alkawari jininsa zasu dau
fansar abunda suka aikata shida babansa cikin bacin rai yasa aka yanke Masa wuya saboda
bakowa yasan wannan sirrin ba se shi wayanda sukai aikin tare duk ankashesu ba Wanda
yasan wannan labarin sai shi kadai da Kuma mu dabesan munsani ba
Haka yaje gidan guga ya tsaresu ze kashe su akan sai sungaya Masa alakarsu da tabo Nan
suka dinga kuka kanwarsa tazo ta durkusa ta rirrike kafarsa tana neman alfarmar yabar Mata
miji besan komai akansaba kawai garine ya hadasu wajen timi mahaifiyarsa akaje timi tanuna
batasan komai ba a beguwa suka hadu sukazo warkar da sarki idan baze mantaba Amma
dukansu Bata sansu ba wannace Rana ta farko da kaho yaji tausayin wani a duniya wato
kanwarsa ganin harta fara fita daga hankalinta shine ya kyalesu suka dawo gurina
Wayyo Allah kuguna Jeddah Banda lafiya zazzabi nake da ciwon kugi dariya ta sheke da ita
kwantar da hankalin ka Ni kadai ma zan iya gamsar dakaina base ka hauni ba yaushe zan
zauna dama Kai ta hawa kaina kamar jaka yau zakaga yadda Mata ke cin maza suhail yau
zanma cin kacha kuka yake kawai Dan wallahi besaba da wannan jarabar ba Jeddah sai da taci
suhail cin kacha sannan ta kyaleshi jikinsa duk yai tsami (Allah ka tsaremu da rayuwar bariki Ina
Yar mutunci Ina wannan aikin kome zakaiwa miji Dan Dole kake cikin kunya Amma Banda
auren Yar bariki wadda tagama zaga kwalta)
Da daddare haleema nata juye juye akan yagunanniyar katifar maryama jikinta duk yai Mata
tsami ciwo yake maryama ta taba ta Taji jikin zafi zau da hanzari ta ballo Mata paracetamol anty
Kisha kiyi hakuri komai na rayuwa yanada lokaci karki kokarin Saba umarnin ta nasan halinta
nasan wace ita ba duk wani sirrin ta a duniya nasan shi duk abunda take Bata iya boyewa
inajinta tana waya tana sanarwa da kawayen ta ko Kuma idan sunzo suna hirar tun zuwana
gidan Nan kullum burin ta taga bayanki Amma ki godewa Allah batai Miki asiri sai dai mijinta
takewa
Kuka ta fashe dashi nagode Allah dataimun asiri ta cuceni tasamin wari Kota maidani wata
halittar daban Kota haukatani gwara Tai ta bani aikin wahala inamata nabar Mata mijin Akan ta
kassaramun rayuwata Allah ya tsareni da tsarewarsa ya kareni da karewarsa ameen Dan duk
abunda take nasani ki kwantar da hankalinki anty bazan Bari ta cutar dake ba kiyi hakuri kinji
anty Haka suka kwanta itako Sam haleema bacci yai kaura daga idonta sai wajen hudu bacci
dayake barawane yai gaba da ita
Ruwa me sanyi aka zuba Mata na kankara Dan uwarki waye bawanki angaya Miki hutu kikazo
yi futo Dan uwarki jiki na rawa ta mike to anty Dan Allah kiyi hakuri bansan asuba tayi ba
zazzabi nayi daren jiya ita tunda taji asiri take takejin tsoron ta harga Allah zakuma ta Kara zage
dantse da addu'a zazzabin ubanki to ko farfadiya kike wallahi sai kinmun aiki tashi ki doramun
abinci kala goma Kuma wallahi idanbe Dadi ba wallahi saikin ci ubanki shegiya me zubin mayu
kurwata tafi karfinki sai wani sum sum kike mike jiki na Bari ta fita ko sallah Bata barta tayi ba
Maryama kunshe Baki tayi tana ta kukan tausayin haleema tanzu ace kishiyarki ce wannan Kika
maida haka Amma fani ta burgeni gwara tabi umarnin mijinta itama ko ta tserewa asirin Jeddah
ta tseratar da rayuwarta da lafiyarta Amma wannan tsaf zata dau ran mutum haka ta dukufa aiki
ga zazzabi sai da taga takama aiki ka'in da na'in sannan ta koma bacci tana shiga daki
maryama ta fito ta karbi girkin maza jeki sallah ki huta zanyi girkin kafin ta tashi kibar shi bara
dai nai sallah
A'a anty aikina nekefa kije ki huta to maryama nagode sosai taje Tai sallah Bata koma bacci ba
Tai ta azkar da addu'oi tana haka bacci me karfi ya dauketa tana bacci Taji maryama na tashin
ta tashi anty naji motsin ta tana kwala Miki Kira nagama komai da gudu ta fita anty nagama
komai Dan ubanki chanai ki sharen gida Kona saki ubanme Kika barbada mun a gida ta
shaketa tanata kakari
*Muhadu a next page dan allah nice fans kidinga mun comment banasan wani thanks ko
sticker nice taku a kullum akoda yaushe*
*Feedyn bash*
[10/23, 2:29 PM] í ½í±¯í ¼í¿»Ummu Subai'aí ¼í¾: *í ¼í¾ARNAN DAJIí ¼í¾*
*NA*
*FAREEDA ABDULLAHI*
*_í ¼í¼ˆKAINUWA WRITERSâœí ¼í¿¼ ASSOCIATION_*í ¾í´í ¼í¿»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DA SUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI*
*Wannan page din sadaukarwane ga arnan daji fans group 1 saboda jajircewarku wajen
comment da yadda kuke nunawa book dina kauna Dani kaina Banda bakin godiya agareku sai
dai addu'a kamar yadda bakwa gajiya dayimun addu'oi nagode Allah ya sakamuku da alkahairi
ya Raya zuri'a ya baya muku dukkan bukatunku na alkhairi Kuyi yadda kukeso dashi Amma fa
masu comment dayimun addu'oií ½í¸œí ½í¸œí ½í¸œYan labe bandasu*
*Book 2*
35-40
Saida taga zata mutu ta sume ta kyaleta suhail ya fito yaganta a kwance kamar gawa Amma ko
kallonta beba yasa Kai ya fice bangarensa yaje ya shiryo har sannan tana kwance tafarfado dai
Amma ta kasa tashi Jeddah tafito tayi kyau ta shirya sukai kicibus da suhail ta rike hannunsa
takai shi dinning sannan ta dawo taja haleema kamar kayan wanki ta yasar a waje ta koma
dakin tamurza key da gudu maryama ta taho ta kamata ta kaita daki tana ta kuka harta zabge
tayi sauri ta hada Mata shayi da kyar yake tafiya tana gamawa ta Fara amai a ranar dai Bata
Kara bi takanta ba Tai ficewar ta
Ta Kira kawarta wadda Tai me suna zeenatu ita take Kara fanfama ta tana Kara dorata akan
turba Mara kyau haka tazo bayan tasa suhail ya tafi office suka bude sashen haleema Dan ta
karbo key din suka shiga suka Fara binkice Babu inda basu duba ba Babu gwalagwalanta to
Dan uwarta Ina tasa su suka birkice komai Basu samuba cikin ikon Allah Basu ga komai ba
Jeddah har kukan bakin cikin rasa wannan sarkokin tayi Koda suka shigo akwai zobuna a
hannunta Amma yanzu Bata ga ko dayaba Kuma hannunta ba komai cikin bakin ciki da fusata
ta jawo akwatinan ta kaf dinsu zeenatu ta taemaka Mata suka loda a motar haleema abun duk
wani Abu me tsada dai dai Dana kitchen sai da suka kwashe dankam ta cika motar taba
zeenatu key din taja taje zasuyi waya yai gwanjansu
Wata sabuwa dama a super market suka hadu da zeenatu Kuma ita ba Yar kano bace Yar
kaduna ce zaman kanta take anan gidan haya take dama kudinta sun Kare shirye shiryen
komawa wani garin take tunda taga ba ci karkari a cita abata dubu biyu ko daya wanima
guduwa yake sai Kuma jeddah ta bijiro Mata da wannan shawarar ranta kal tazo sukayi aikin
tare
Ta sheke da dariya banza shasha idan Banda shashanci Baki sanni ban kiban dukiyar miliyoyi
sai a lahira Amma bazaki Kara ganina ba Niko nasan ko banza nayi kudi daga Nan ko kayana
bazan biya daukaba danma karki samen tsautsayi ya gifta Zaria zanyi nai gwanjon kayan Nan
ko million biyar nasamu nase gida na Fara business ta kyal kyale da dariya tsintsu daga sama
gasashshe lallai Jeddah kin cuci kishiyarki saboda bakin kishi da hassada kinsan tafiki komai Ni
Kuma na cuceki
Take ta zare layin ta ta wullar a kwallata dodar tabi hanya sai Zaria jeddah ta fito a shirye tadau
motar ta taje gidan zeenatu taganta garkame da kwado a a to Ina tayi tadinga Kiran wayar ta
switch off chan taga message da wata number _jeedah karki kuskuren nemana Dan bazaki
sameni ba nayi nisa a wata duniyar yadda Kika cuci kishiyarki Nima Haka zan Miki kiji idan da
Dadi sai wata Rana karku wahalar Kiran wannan laying dan bazaki same shi ba bye uwargidan
suhail hhhhhhh shegiya muguwa me bakar zuciya nafiki mugun Hali to_
Sakin wayar tayi tadinga birgima tana ihu ba Wanda ya kulata Dan unguwar dama ta karuwaice
haka ta share hawayenta ta shiga mota tana tsinewa zeenatu idanta idanta saita kasheta
Haka zaman haleema ya kasance a gidan tundaga ranar Bata Kara Lekawa ko harabar
gidanba bare sashenta tazama baiwa kazama wadda bata da wani hutu sai aiki sai dai
maryama ta faki ido ta temaka Mata gashi tayi masa zobo da al'adarta idan abun yadan sake
shi zeje su gaisa da iyayensa idan sun tambaye shi haleema yace suna lafiya Amma shiyama
manta da wata haleema suna ambatar ta gabansa na faduwa iyayensa sun so su fuskanci wani
Abu Dan jeddah na zuwa da garar arziki Amma Sam haleema Bata zuwa kuma so biyu hajiya
na zuwa Bata Nan idan ta tambayi jeddah sai tace ai yawo take Bata Zama Bata Nan abun
Yana damun hajiya Amma batace komai ba ko alhaji Bata gayawa ba
Watan ta biyar a bangaren Jeddah tanai Mata bauta duk tayi Baki ta rame a wannan lokacinne
ta farga cikine da ita Dan Bata taba tunanin cikine da itaba ta dauka dai tadena al'adane Dan
Bata yin komai sai dai tana Jin abinci zataji babu kamar an Mata yasa Dan dai maryama tana
yawon Sato Mata abinci ta boye Mata Dan Jeddah Tai Mata iyaka da abincin ita zata dafa anma
Bata da rabo sai dai ragowa sai kowa yadiba har masu gadi sannan zataci kanzo da marayama
taga haka shine take diba tana boye Mata tunda dakinsu daya
Abunda ke karawa Jeddah kaunar maryama shine yadda take zagin haleema agaban jeddah
danta gayamata komai tazama kamar abokiyar shawararta Bata San cewa tafi kowa tsanarta ba
Dan Bata taba ganin mace me mugun Hali irin jeddah ba haka zatai ta biye Mata suna zagin
haleema idan suna tare da Jeddah haka zatai ta daka mata tsawa hakan yasa hankalinta ya
Kara kwanciya da maryama itako haleema dake tasan komai Bata damuwa Dan tasan Shirin
sune
Hankalin hajiyan suhail yaki kwanciya ta shirya tasa driver ya dakkota waya taiwa alhaji ta tafi
gano iyalan suhail Dan tana yawan mafarkin haleema tana Miko Mata hannu ta temaketa ta
rasa me hakan ke nufi cikin ikon Allah suka shiga gidan Tai parking kamar kullum side din
haleema a rufe Jeddah dama duk Wanda ya shigo akwai security data dakko dakanta Wanda
yake kiranta da gudu ta fito tasa haleema a store ta kulle kuka kawai take Mara sauti tana fatan
Allah ya kawo Mata sauki da karshen Wannan lamarin datake ciki
A lokacin dasu guga sukazo bansan inda babanku yakeba inata nemansa nagaji nadawo sai
ganinsu nayi suna zuwa suka Fara dukana sarki yahanasu ya tambayeni menasani game da
mijina nace bansan komai ba tsintoni yai ina tafiya Ni kadai a daji hanya ta kwacemun shine ya
aureni sarki ya gamsu da kalamaina Dan dama ya kwadaitu Dani tun farko yace su kyaleni
Amma dasukaga cikin jikina sukace indai namijine sai ya yankashi a gabana suka juya suka tafi
Har sun tafi ya dawo da baya ya shedamun sun kashe mijina karna Sha wahalar nemansa
Haka nadinga kuka Ina tumami bame temako na tafi gidan timi Ina shiga Naga mahaifiyarki jiki
ya rikice guga Banda kuka ba abunda yake timi ce me dauriya haka muka dinga kuka chan ta
haifo yarta Amma mummuna kamar babarta ta Kara wani yunkurin ta haifo Yar Amma wannan
Bata da Muni ba lefi ko kallonsu batai ba ta mutu yadda ta haifo ta biyun Bata shura ba
Muka dinga kuka muna ihu gashi Bata da kowa sai kaho Yan uwanta duk sun mutu Dole
mukaiwa sarki yaga diyar Yar uwarsa muka yanke shawarar medan kyan mubarwa timi ta kula
da ita mununa Masa daya ta Haifa ze iya karbe daya mike muka je wajen sarki da wannan
mummunar jaririyar muka sanar masa kanwarsa ta mutu be damuba burinsa a bashi diyar data
Bari ya rainarwa Dan sa Ja'e ita ya aura Yana kallonta yaganta wata mummuna gata baka
tuntana jaririya tsorata yai ya saketa karamin yaro Ja'e ne dake gefensa yai hanzarin tareta ta
fado hannunsa duk da shekarunsa shida a lokacin faduwa sukai tare ya kura Mata ido sai yaji
wani irin Bala'in santa ya rungumeta kaho abarmun ita inasanta
Ba shiri ya taso ya fisgeta yabawa guga gata Nan nabar Maka ita kaje kai raineta kuka Ja'e
yake sai anbashi ita yakaiwa iyarsa da karfi kaho ya rikeshi ya koremu yasa aje adau gawar
kanwarsa a Kai daji a wullar Ja'e yadinga zindima ihu aka kaishi wajen iyarsa Yana kuka yake
Gaya Mata shi yanasan jaririyar ta tambayi Wanda ya kawo shi meya faru Nan ya gaya mata
komai ranta ya baci Yar kanwarsa ya wulakanta Haka daya sani ita ya Bata tanaso zata riketa
na karbeta Ina goge hawaye kabarmun zan raineta cikamun kawai yai ya saki ihun kuka
Sarki yasa asanarwa da guga bayasan Kara saka yarinyar a idonsa haka guga ya karaci bakin
cikinsa abunda sarki kaho yai Masa cikin Daren na Fara nakuda na haifi katuwar diyata
kyakykyawa mekama da Dan uwanta kuka nadinga yi nasan sarki saiya rabani da ita a Daren
naje na Sami timi Ina kuka da jariran a hannuna nagaya Mata abunda ya faru murmushi tayi
baze rabaku ba wannan jaririyar bantaba ganin mekyau a garin Nan kamarta ba sai Dan uwanta
wani Abu ta dakko tayiwa jaririyar ki Kai Masa ita da safe muninta daze gani sai yafi na wannan
na rada musu suna yanzu sunanta Rama Yan biyu Kuma ta wajenki tenkwai ta wajen wajena
aduke
*ANAN ZAN DAKATA FANS SAINAJI RA'AYOYI KU NAGODE DA YADDA KUKE KAUNAR
ARNAN DAJI NICE ME KAUNARKU DA BURIN GANINKU A CIKIN FARINCIKI DA NISHADI A
KODA YAUSHE*
*FEEDYN BASH*
[10/23, 2:29 PM] í ½í±¯í ¼í¿»Ummu Subai'aí ¼í¾: *í ¼í¾ARNAN DAJIí ¼í¾*
*NA*
*FAREEDA ABDULLAHI*
*_í ¼í¼ˆKAINUWA WRITERSâœí ¼í¿¼ ASSOCIATION_*í ¾í´í ¼í¿»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DA SUNAN ALLAH