Showing 18001 words to 21000 words out of 43444 words

Chapter 7 - ARNAN DAJI BOOK 2 by Feedyn Bash .pdf

sai ya
biyata gashi ta koya Masa harijanci baya iya hakuri kullum cikin karbe Masa kudi take Amma
hakan be isheta ba sai da ta koma bin mazan data Saba a waje har gida take kawo su
musamman Ahmad Allah cikin ikonsa suhail be taba kamata ba sai dai maryama Bata da
matsala da ita yarinyar tana da sirri



Baban abunda ke damun suhail yadda Jeddah Bata taba yarda dashi sai ya biyata gashi baya
jurewa manyan kudi take sa Masa Kuma shi be iya neman Mata ba da kudinsa ma sai ta ga
dama take bashi (hattara Mata domin akwai Yan iskan Mata da basa taba yarda da mijinsu sai
ya biyasu ko Kuma ya yarda da wasu bukatunsu ze siya musu wani Abu ko wani abun wata
Bata zuwa da bukatar ta sai ta ta tabbatar mijin ta ya kamu da sha'awarta Wallahi Mata kuji
Tsoron Allah kisani kin aikata Haram kinsa mijinki yayi Miki alkawarin Dole Wanda baya cikin
hayyacinsa Dan Allah Mata mugane muna cikin fushin ubangiji da halaka muji Tsoron Allah)
Allah ne ya tsare suhail da addu'ar iyaye da tuni ya Fara bin Mata saboda tsananin Sha awa da
kudin nasa ma inta ga dama sai ta Hana be da abun Sha sai kanwa



Tunda ta haifi ansar akaje akasa Mata implan daga Nan Bata Kara yarda tayi wani cikin ba
tunda ta haifi namiji tasan itace da gida tunda haleema ko Labarin ta Bata Kara jiba karshen
Tama ta mutu shikenan ta tsunduma barikin ta ta juyawa uwar ma baya Dan abunda take ba ta
rage sai ta ga dama ma take Bata inbaso bama sai tazo gidan ta karaci zamanta Taki fitowa ko
kdaga bayama hanawa Tai intazo sai ace ai tafita Haka ta hakura tadena zuwa sai Rana daya
taci sa'a tafito ta same ta

Dama wata shawara nazo Miki da ita tunda Kinga ke kadaice yanzu yayanki ne kawai meze
Hana kisa akashe suhail ido ta zaro kisa umma gaskiya Inasan mijina to tunda kinasan zauna
har haleema ta bayyana tazo da yayanta maza har uku rigis Dan naji labari ta haihu a gidanma
akai suna Amma ance ta Bata bat ba'a Kara ganinsu ba idan asirin ya sake shi tunda wata
Rana Dole ya karye kema kinsani ki duba nida mahaifinku indai ya sake shi yadda yake mana
Dan Haka shawara ce kiyi tunani eh hakane umma Amma wazemun wannan aikin hehehe ke
dakike Dame Miki aiki a hannunki kaninki ai aikin sa Kenan bikiga malam na katsina yaba shi
maganin sabani ba ai group ne dasu da abokansa manya sukewa aiki yanzu manyan kasar Nan
da Yan siyasa suka sheke da dariya nan ta amince sukai akan zata turo Mata shi suyi maganar



Yazo sun tsara komai ta sanar dashi zeje dangin hajiyarsa dake Jos ze Kai musu ziyara wannan
satin ranar talata sukayi da ita zata biya million 2 tace ba matsala Haka ko akai sun yi nasarar
kashe suhai Nan ta Kira afra kawarta ta gayama Tama hankalinta ya tashi Dan dama ita yanzu
tashiryu dama ita Bata bin bokaye sai dai rakiya ko intaji labari wani takai Jeddah amma yanzu
tasan ta tafka babban kuskure tanta istigfari babanta yaji dadin shiryuwar ta Amma matarsa
bataso ba sotai ta lalace takare rayuwarta a haka tagama karatun ta tsaf ta Zama cikakkiyar
likita yanzu Kuma har yanzu suna tare da saurayin Nan nata yace auren ta zeyi Dan haka take
istibira'i bayadda batai da Jeddah ba tadena aikata wa mijinta asiri Taki inda ta godewa Allah
dabata taba zugata Akan ga abunda zatai ba Haka takiji taki daukan shawarata karshe tasa a
kashe shi ita ko tasamu Al ameen ta Gaya Masa be yadda ba tace ya tambayi maryama tasan
komai tafiyarsu Dubai ma shiyace ta bita saboda yanaso Tai Masa wani aikin a chan basaso ta
lalata dukiyar suhail



Babar matsalar da aka samu sai bayan ankashe suhail ta gayamata Dan Haka yanzu a
tunaninsu suhail ya mutune kawai shiyasa suke so su karbe dukiyarsa Dan su ajiyewa yayansa
Dan matarsa saura wata guda ta dawo
(Andawo labari)
Jeddah taiwa afra waya ta shirya jirgin 8 na dare zasubi Sam ita yanzu afra ta fice Mata arai
Haka suka dunguma suka tafi Dubai a ranar datasan meze faru da Bata tafi tabar gidan ba Dan
komai ya lalace Bata sani ba



Rama ce zaune dare ya tsala tana ta binkice sai gumi take sharewa ganin irin yadda aka daure
suhail da wasu manyan asirai andanne zuciyarsa akasan wani katon dutse Dole sai Tai Masa
aiki me zafi zata karya wanna n asirin tayaya ze yarda da wannan lamari duk wannan abun
daya same shi matarsa ce tariga tagano hakan kuka tasa Dan Bata taba ganin wannan masifa

ba su garinsu ba' a irin wannan sihirin me karfi Haka Haka tadinga kuka tafara aikin warware shi
kwana tayi tana aiki ita kanta ta wahala bare suhail da ake Masa wannan hatsabibin aikin tana
gamawa ta yanke jiki ta Fadi firgigit suhail ya Mike jiyai komai na jikinsa ya warware kamar
ancire Masa Kaya haleema ya ambata kirjinsa nawani mugun bugawa kuka yasa a Daren


Sai da takwana biyu ta wuni sannan ta farfado saboda ta gwabzu a wannan wajen kwance
sihirin manyan aljanu taci Karo dasu muraran shine Tai wannan suman bayan ta farfado taganta
cikin sittira me kyau ko Ina a rufe duk Dana fata ne gasu fadeela an rufe ko Ina gaskiya sunyi
kyau har hijab akai musu Wanda suke sallah da shi duk dama duk cikinsu bame fita bayan ta
nustu ta Fara Basu Labarin irin kullin da akai Masa Amma Bata Gaya Masa kowa yayi ba ta
kyale ta ne kawai Ja'e fadeela tace wallahi Ramatu tunda naganshi ranar farko nasan akwai
wani boyayyen Abu game dashi ba asoma ya rayuba sun dauka ya mutu shine suka wulla shi
ruwa wannan ruwan me hatsari sai mu godewa Allah komai ya Kare Amma Dole sai ka dage da
magunguna



Yanzu zamu je daji mu samo wasu harda na subai'a tunda dama sun Kare zan rakaku Ina
waysaka da wayannan kayen yai dariya ya dakko shima na fatar irin nasu suna tayi Masa
dariya suka fito saiga Ja'e sai Ina sai daji Nan suka dauki hanya gaba dayansu sunata Hira Ja'e
yake Basu labari iya fa Yau zatazo suhail itama zata karbi musulunci nagama boye boyen komai nagaya Mata gaskiya
tayi murna tabbas ta Kuma tuna dama chan ita musulmace mantawa Tai zamanta cikin arna
suka sheke da dariya fadeela tace ARNAN DAJI ba Kuma kaima ai da shine yanzu ne haske
yazo Mana duka ko masoyi dariya sukasa gaba dayansu lallai fadeela wato dama tanasan sa
tabakin suhail halinsa Take ki Kuyi gaba masoyiya gamu nan



Babban Yaya kamaidon da matata tunda ta amince suhail ya sheke da dariya aiba aure kuke ba
hauka kuke kawai za'a daura muku aure irin na musulunci duka matanka ka samu su musulunta
ka nuna musu yadda addinin yake sai ka zabi uku tunda ga fadeela duka bansan su fadeela ta
ta isheni sukai ta dariya sannan da shawarata tunda za'a kawo manyan malamai Kar akashe
kaho idan sukazo karshen ta ze musulunta kaga mun Kara samun wani rabon a a suhail wallahi
zuciyarsa irin ta kakanace ze iya yadda daga baya ya kashe mu munada yawa a garinnan ba
lallai sai da shi to shikenan Amma fa ba gunki ne yake magana ba Dan ba yadda za'ai ace
gunki na magana tabbas aljanu ne suka shiga jikinsa suke Kara dulmiyar daku Dan Haka a
gobe nake San tafiya Dan mu dawo kafin kwana biyar masu zuwa saboda Kar a yanka mutanen
da basu da hakki

Haka sukai ta tattauna wa basu saniba Ana ta binsu a baya ba kowa bane ke binsu face
saurayin aduke hayaki Dan yayi alkawarin sai ya kashe Ja'e ga dama ta samu su biyu kacal
maza sai matan dabesan ko suwaye ba a gaba suko sunata hirar Ja'e ne abunsu Basu waiwaya
ba sunata tafiya Ramatu da zabgegiyar takobinta rataye dama ita gwance itako fadeela kwari
da bakane da wasu mugayen kibiyoyinta masu masifar dafi Haka sukai ta tafiya Yana binsu a
baya sunzo daidai wata hanya ya daga takobinsa ya kaiwa Ja'e Sara wata razananniyar Kara
sukaji suka juyo a razane gani abunda ya faru da gudu Suma suka zare makamansu suna
kabbara sukai wajen



*ANAN ZAN DAKATA FANS KUYI MANAGE DA WANNAN NICE TAKU A KULLUM A KODA
YAUSHE*




*Feedyn bash*
[10/23, 2:31 PM] 👯🏻Ummu Subai'a🎭: *🎭ARNAN DAJI🎭*


*NA*


*FAREEDA ABDULLAHI*




*_🌈KAINUWA WRITERSâœí ¼í¿¼ ASSOCIATION_*í ¾í´í ¼í¿»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation





*Assalamu alaikum fans kuyi hakuri kwana biyu kunji ni shiru banda lafiyane amma kuyi
manage da wannan ba kullum zaku dinga samun typing ba pls ina barar addu arku Allah ya
bani lafiya wallahi bana jin dadi ina rokonah ya tabbatar mun fa alherin abunda make zato

nagode sosai*


*Book 2*


60-65



A guje sukai kanta kububuwace ta sari hayaki tana Kuma kokarin guduwa kamar yadda ta Saba
da gudu sukai kanta ramatu ta tare gaba fadeela ta tare baya Nan ta Kara fasa Kai tayi kan
ramatu yayi ya fasa Kai tuni fadeela ta Fara sakar Mata ruwan kibiyu sai Tai girgiza ta zubar
dasu gashi biyota kawai take yi ga Mohd a kwance Dan ya yanku ta bayansa suhail na rike
dashi ga shi sukuma matan sun tari aradu da ka jeka temakesu suhail kububuwace zata iya
kashesu temakesu ku ga bayanta da temakon ubangijin musulunci na kabarni ciwon ba yawa
kawai jinin ne dayawa katafi karta cutar dasu Dan Allah



Suhail ya Mike da gudu ya karasa gaban ramatu Dan har ta fasa Kai tana Shirin sarar ramatu
tagama fusata ta haukace ganin yadda ramatu ke Kai Mata Sara da takobi fadeela na zuba
Mata kibiyoyi da mugun gudu ya janye ramatu duk da haka dafin ya taba kafarta ya tureta gefe
tana ta Mata gungun gurin yai wani irin kore yayi boro kamar Kuna da ya daga takobin ya
fuskanceta ta fuskance shi yanata addu'oi duk wadda tazo bakinsa kawai kamawa yake meze
faru gadan gadan tayo kan suhail ya daga takobin cike da kabbara yasakar Mata a tsakiyar
kanta sai ta Fadi rigijib gashi takobin ta makale a tsakiyar kanta Kuma Bata karasa mutuwa ba
nema take tafeso Masa dafi gashi sai huci take tana birgima tana tunkarar suhail ganin Haka
fadeela ta saki wata kabbara yadda Taji suhail yayi ta dinga sakar Mata kibiyoyi tana ta harbe
harbe tana wani irin ihu da gurnani Wanda ya cika dajin gaba daya



Tadinga ihu jikinta na darewa Nan suhail yadinga karanta bakara ayatul kursiyyu duk wata sura
datazo bakinsa karantawa yake gaba daya dajin girgiza yake wani irin ihu da rugugi ya cika
dajin wata tsawa akai datasa bishiyoyin dajin kamawa da wuta tuni Mohd ya sume yayinda
dafin yake ta ratsa ramatu fadeela ko ta Fadi tuni ta samu suhail ne kawai ya rage a dajin
yanata addu'oi da karatun alkur'ani gaba daya Banda wuta ba abunda keci tuni mafarautan
dajin suka yo wajen a gigice sai ga sarkin daji a sakwane Wanda ya tabaiwa a duke magani duk
Wanda yazo wajen sai ya Suma sarkin daji ne yai kokari ya janye suhail daga wajen Dan ya
Fara galabaita Amma be fasa wannan karatun ba shiko sarkin daji tsananin jikuwane Da
yazama shima kamar su yasa be komai ba

Su jeddah andaga zuwa dubai suna sauka suka sauka a wani hamshakin hotel suka sauka
Suna shiga jeddah ta hadu da wani hamshakin Alhaji shima dan Nigeria ne yanuna yana Santa
ball wani jan aji ta amince ta bada Kai bori yahau nan ya Kama musu daki me masifar kyau
room and parlour ya gayyaci jeddah tazo ta rakashi wani waje tace afra ta zauna zasu dawo
yanzu mezata Siyo mata tagaya mata duk abunda kika kawon yayi cike da farin ciki tafice tana
fita afra tasawa dakin key ta kulle dama ta lura da pin din data rufe akwatin cikin hanzari ta bude
ta




Ta dauke ATM din ta Dana suhail na bank biyar data taho dasu da detail din account dinsa
komai na bankinsa Dan tanaso ta kwashe komai daga bankunansa tunda tanada komai a
hannu gefe guda ga takaddun company dinsa dake Dubai guda uku cikin hanzari ta debe su
jikinta na rawa ta kira al ameen wallahi aikin nan akwai kasada barinsu a hannuna akwai
matsala ga komai da komai nasamu cike da murna al ameen yace alhmdllh bukata ta biya Dan
haka kinyi kokari afra kema alh ya biya miki bukatunki kince bakya bukatar komai amma ba
komai matar Abdul tunda abokin mijinkine jihadi kikai murmushi tayi karka damu amma fa yayi
fushi sosai Dan Allah kabashi hakuri




Ya sheke da dariya kinganmu tare na warware masa komai dake faruwa yayi Allah wadai da
halin jeddah kuma ya yarda ke macece ta gari kaddara ta hada zamanku da jeddah yanzu
zanturo miki wani abokina zan bashi number din wayarki zezo hotel din da kuke kifito kiba shi
zeturon su zuwa gobe nima insha Allah gobe zamuje nida maryama zamu tone komai data
bunne sannan mu kwashe duk wasu abubuwa nasa muhimmai gaskiya kunyi kokari keda
maryama Allah ya biyaku



Ya kashe wayar ya kira abokinsa ya gaya masa hotel din dasuke ya temaka ya turo masa gobe
muhimmun sako ne tunda shi Dan kasar ne yasan duk wasu cuku cuku dazeyi ya turo su tare
sukai karatu a turkey cikin ikon Allah yana gab da wajen tuni ya karasa ya kira ta da hanzari ta
fito komai tasa shi a envelope ta mika masa ya karba ko hira basi ba ta juya Dan kar Jeddah ta
dawo ilai ko tana shiga dakin tana zama sai ga jeddah ta shigo cike da murna da manyan ledoji
ga wata muguwar waya a hannunta iPhone 11 wayar ko Nigeria bata zoba ta rungume afra ki
tayani murna nayi babban kamu kawata nasamu wani alhaji labaran shima Dan kano ne yace
aurena zeyi Dan haka two weeks zami kawai mu koma kafin mu koma angama komai sai daurin

aure





Kuyi manage da wannan tofa jeddah masifa wakuma ta yayibo oho mata muje zuwa nice taku
akoda yaushe





*Feedyn bash*
[10/23, 2:31 PM] 👯🏻Ummu Subai'a🎭: *🎭ARNAN DAJI🎭*


*NA*


*FAREEDA ABDULLAHI*




*_🌈KAINUWA WRITERSâœí ¼í¿¼ ASSOCIATION_*í ¾í´í ¼í¿»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```


https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*ASSALAMUALAIKUM MASU YIMUN ADDU'OI NAGODE SOSAI DA KILAWARKU GASKIYA
BAN TABA TUNANIN HAKA AKE KAUNAR ARNAN DAJI BA SAI YANZU GASKIYA INA
GODIYA MASOYANA DA YAWAN COMMENT DINKU AGARENI BAZAN GAJI DA GODE
MUKU BA INAJIN DADIN KULAWARKU GARENI AKARA HAKURI DAI DA RASHIN TYPING
DINA AKAN LOKACI NAGODE MASOYANA*



*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DA SUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN KAI GODIYA TA
TABBATA GA ALLAH UBANGIJIN TALIKAI TSIRARA DA AMINCI SU TABBATA GA ANNABI

MUHAMMAD SAW*



*BOOK 2*





65-70





Waye alhaji labaran wani hamshakin me kudine Wanda baya bambaruwa kwata kwata yanada
Mata biyu a yanzu uwar gidansa matar ladan nomar sa sai Kuma mabiyarta wadda suka hadu
bayan yadan Fara samun kudi a hankali sunyi soyayya sannan sukai aure Yana auren Mata
dayawa a karshe su rabu matan Nan guda biyu sune basa rabuwa Suma Kuma Basu da Yaya
dayawa uwar gidansa nada Yaya biyar amaryar nada uku bayan su ba Wanda yake Kara
haihuwa a gidan kansu a hade yake duk wadda ta shiga gidan izayarsu kadai ta isheta Banda
wasu dabi'un na megidan Wanda su kansu matan Basu San dasuba dai su matan dayake aure
Dan wasu sun Sha masu Kuma kwadayi sun jawowa kansu wannan kenan




Hhhhhh alhaji duwai komai yayi Dadai nasamu yarinyar data amince da aurena farat daya
zataci kudi cikin sati biyun da zami a Dubai shawara alhaji malamalai kayi kokari ka shiga jikinta
tunda kace idonta a bude yake ka samu kafara saduwa da ita tun yanzu hakan shize Kara
Bata dama ta saki jiki dakai ka siya Mata motoci masu zafi ka mallaka Mata gwala gwalai duk
wani Jin Dadi ka Bata anan yadda zata kagara tana dawowa a daura auren Dan zatai tunanin a
gidanma zata samu wannan jin dadin kasan dai halin matanka kuma kasan sati uku da kwana
biyar ya rage Mana sa sani alhaji duwai Ina bukatar Kaya fa gashi kamun nisa shegen Kaya
kana San wajen Nan baka gajiya hhhhhh sai na shigo garin




Jeddah ce take birkita kayanta ta zazzage akwatin yafi so bakwai ihu ta zindima afra tashi
wallahi sai kin fitomun da takadduna da ATM Dina wallahi kinyi kadan kimun sata duk yadda
muke dake Zaki mun sata mtsww ta hambareta gefe nizaki kalawa sharrin sata da chan ban

tabayi Miki satar ba sai yanzu ki dai tuna inda Kika saka wallahi a akwatina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login