Showing 1 words to 3000 words out of 51633 words

Chapter 1 - NI DA GIDANA BOOK COMPLETE BY ZAINAB MAZAWAJE.pdf

https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe


*NI DA GIDANA*

*BY*

_Zainab ilyas mazawaje_


_Best brilliant enterlligent writter_....️



_Marubuciyar_

Mubarak ko mujahid?
Adalilin zumunci
Ni da gidana
Cobara daga kogi
Jarabtar ubangiji
Gobara daga kogi
Rashin Dangana
Zarge (mugun kulli)
Budurwar zuciya
'Ya'yan mijina
Nadamar aurena
Umma khulsum
Sabanin Zato
Ina bakin zaren?
Tayi Dace
Abdallah
So halitta
Kayan aro
Bazata



_Baa yarda a juya wannan littafiba ta kowacce irin siga ba tare da izinin marubuciyar ba_


*Page 1*



Labarin rayuwa ta d'auke yake da amsoshin tambayoyin wasu mataye,haka zalika d'auke
yake da warwarar matsalolin wasu mataye. Kuma yana d'auke da mafita ga dubban matayen
aure da suka shiga takun kumin Ina mafita ga damuwar su.

Sumayyya, duk ke wad'an nan furutai ga manyan a minan'ta biyu Laila da Aliya da suka sata
a gaba, suka zuba mata idanu, game da tambayoyin da suke ta yi mata a kan rayuwar'ta. Ta
dubesu tayi murmushi.

”Ni ba 'yar kowa bace, ni 'yar talaka ce lis. Kuma ni ba kyakykyawa bace, amma na auri mijin
da ko a mafarki, ban tab'a zaton zan aureshi ba. Na Shiga daula ta arzik'i nayi ninkaya a ciki da
Sai d'ai, d'ai kun mata a duniya ke rabautar irin sa. Na mallaki kadarori da dukiya da ni kaina
bazan zayyano su cikin sauk'i ba. Kuma shaida ne, da zaku labarta kowa wacece sumayya.
Taja dogon numfashi ta d'ora.

Duk da wannan jin dad'in duniyar da daula da sa'ar miji na kerewa sa'a da na rabauta, Ina
tare da wani tabo na mikin ciwo a zuciya ta da ya kasa warke wa da a ka jarrabeni da shi, da
Sai Jifa Jifa yake motsamin yayi ta d'an zugi idan na tuno jarraba ta, a rayuwa. Babu kuma
Wanda yake fahimtar wannan damuwa tawa, sai Mijina da muka zama han'ta da jini.wannan ita
ce mummunar kaddarata da nafi jin ciwonta fiye da kowacce.

Laila ta dafa kafad'ar sumayya Sannan tace.

"Sumy, yanzu nan har kina da Wata damuwa ko
matsala a rayuwa da bata kau ba?. Zato na ai kin gama shan kwana."

Aliya ta karb'a.

"Wallahi yarda kika zama a bar Sha'awa ga mata a ko'Ina babu wanda zai yarda kina da Wata
damuwa ko yaya a rayuwa sumayya.

"Idan kuka fad'i haka, kun jahilci sanin ita kan'ta rayuwar. Babu yarda za'a yi a ce wai mutum
burin sa a rayuwa ya cika d'ari bisa d'ari, ko bashi da matsala ko d'aya, dole ubangiji yatab'a shi,
ta wani b'angaren ko a hanashi ta wani fannin. Cikakken musulmi, zai ce yayi imani, Sannan a
ce wai ubangijin'sa bazai jarrabi imanin sa ba? impossible."

"Gaskiya ne, dole ne Kam." A cewar Aliya.

Laila ta muskuta, ta k'ara matsawa dab da Sumayya, tayi d'an duba kad'an cikin katafaren
falon da samun irin sa zai wahalar a zamanin nan.

"Sumayya, don Allah ki daure ki bamu labarin rayuwar nan taki domin na tabbatar a Kwai a
bubuwa da yawa da mata zasu amfana da shi, domin ke d'in nasan bata wasa bace, Sai dai a
d'au co's a wurin'ki a komai, tun da ga mai gida ma duk kin mallake, kullum tunanin'sa yana
gareki."
"Tabbas, tun da daga zaman mu a nan, ya kiraki a waya ya kai sau biyar." Inji Aliya.

Sumayya tayi 'yar dariya tace.

"Bazan ce ba haka ba ne a minai na, sai dai nayi k'ok'arin mai da tunanin Ku can baya, domin
Kusan gwagwar mayar da sumayya tasha kafin ta samu wannan matsayin wurin Mijinta da
wurin dangin'sa, har ma da ku da duk wad'an da nake burgesu da basu Sha'awa. Duk Wacce
zata iya kwaikwayo na wurin juriya da Hak'uri da dangin sa da dogaro ga Allah, da iya tafiyar da
miji da juriyar irin d'abi'un sa duk hutsancin'sa, to tabbas zata iya dace da irin rayuwar Sumayya
ko ba duka ba.

Sai dai matsalar dole idan Ina baku labarin za'a zo wurin da zan yi ta kuka, k'arshe ma na sare
na kasa ci gaba. Saboda haka domin komai yazo min da sauk'i zan rubuta muku a rubuce
kawai.

Ta dan ja fasali, kafin tace.

Na yarda Ku yad'a shi ma, ko ya zama littafi, domin na tabbatar 'yan uwa na mata zasu k'a ru
da yawa ma. Ku bani Sati biyu, saboda kunsan Mijina yanzu bai fiye yin nisa ba sosai, kuma
yana d'an jimawa bai yi tafiya ba ynz.,kunga kuwa Sai ya fita zan samu dama ko?.

"Wallahi da gaskiyar'ki . Mu dai godiya muke sosai, muna jira ."

Cike da zumud'i Laila ta fad'a.ita ma Aliya jinjina tayi mata.

"Allah yaja da ran gimbiyar mata, Allah ya k'aro twin's biyu bayan su Abalkhair. "

Murmushi Kawai tayi. Saboda sun jima suna yi mata nacin labarin rayuwar'ta saboda ta
zamewa kowa kamar abar shaawa da kwatance.
Amma fa ga Wanda ya San'ta ko ya gan'ta ko labarin'ta da ya shahara ya riski Mutum.

Bayan Sati biyu kuwa Sumayya ta cika alk'awari ta basu rubutaccen labarin'ta.
_______________________

_jigon al'amarin kaddara_


Had'uwa ta da Fa'iz Bukar, daga nan k'addarar ta soma.


__ Ajin ya kaure da hayaniya saboda rashin malami,dama kuma al'adar 'yan a jin na mune
surutun, koma da malamin, saboda sunci sunan mun gagara.

Ni da nake monita na tashi na duba time table, domin naga wani malamine da mu a
lokacin,naga English teachear ne, wato malamin turanci.

Na nik'e na nufi taff room in da mu kaci karo da malam Abba class teacher d'in mu. Na rusuna
nace.

"Sir, babu malami a ajin, Sai hayaniya kuma suke sunk'i yin shiru."

"Wani malami ne daku bai shigo ba?". Yace.

Nace "English teachear ne sir, kuma anyi masa transfer,sabon malamin da a kace yau zai
soma zuwa kuma bai zo ba."

Da sauri yace.

"Ai kuwa yazo. Malam Fa'iz sunan sa, yana ma staff room suna ganawa da princepal na baro
su.muje na nuna miki shi, ki fad'a masa period d'in sa ta Shiga, bai Sani ba ne."

Ban da shi malamai uku ne a staff room d'in biyu maza, Sai malama wasila dake aikin sa hannu
a test a gefe guda.

Yana gefe d'aya shi kad'ai a zaune yana duba wani text book. Dole da ka Shiga, shi zai fara
d'auke maka idanu, saboda farar fatar'sa irin ta shuwa a rab. Matashin saurayi ne da duk cikin
malaman babu mai k'asa da shekarun sa, sai dai sama.


Ni dai Ina yin tozali da shi, na Shiga mamakin sake had'uwa ta da shi a karo na biyu a
rayuwa ta, kuma zai zomin a matsayin malami. Ko da yake had'uwa ta da shi d'in ma ta farko,
ba wani a bu ya Shiga tsakani na da shi ba, face wayata da na tab'a yarwa ya tsinta ya kawo
min.
Tsawon Wata tara Kenan.

Amma a bin mamaki nunawa yayi kamar bai tab'a gane ni ba, da ya d'ago kai muka had'a
idanu. Sai da ya wani ja a ji, cikin jin kai, Sannan yace da k'yar.

"Kece monita"Yace.
Na gyad'a kai.

"Yes, sir".

Har ya mik'e nayi ni kuma gaba, ya kirani yace.

"O K. Jeki, gani nan zuwa.'" Ya koma yayi Zaman'sa kuma bansan dalili ba.

Ban jima kuma da Shiga ba, Sai gashi ya shigo. Duk da an ga shigowar'sa ba'a saurara da
hayaniya ba, kuma duk kuma da jarabar kallon da a ka bishi da shi, kamar bak'on halitta.

A haka ya soma gabatar da kan'sa cikin harshen turanci. Ya dakataYace

"Keep Quiet. I said keep Quiet. "Amma ba'a rage Surutu ba. Ai sai ya daka Mana Wata irin
tsawa da dank'ara mana zagi, ya zarce da.

"Ku wad'an ne irin jakai ne ku, a na cewa Kuyi shiru baza Ku yi ba?"

Ai kuwa sai tsit ka ke ji , saboda dalilai biyu. Farko tsorata, na biyu babu wani malami da ya
tab'a zagin mu, saboda ji da mu da malamai suke, koma me muka yi.

Amma shi wannan daga zuwa har ya fara yi Mana lugude? Saboda Surutu Kawai ma?.

Tabbas da a lamu zai fita zakka. Domin da jin kai da tsare gida ma ya shigo class d'in. Shiru
yayi kuma yana ta harare harare da nufin yaga wata tayi ko uhum! yaci zarafin'ta, haka na
karance shi. Babu Wacce kuwa ta kuma yin ko tari.

Yayi sanyi kad'an ya soma magana cikin harshen Hausa kuma.

"My name is fa'iz Bukar. Ba wasa ne ya kawo ni nan ba. Kuma bazan d'auki ko wani irin
iskanci na d'aliba ba. Kuyi k'ok'arin Sani na kafin ku fad'a tarko na, shine maslaha a gareku.
Bana son wasa, ko kusa cikin darasina.

Bana kuma shiri da dak'ik'ai da jakai da basu San me ya kawo su makaran ta ba. Dole ne ni a
iya darasina in dai na karantar. Idan yarinya bata fahimta ba, to ta tambaya,bayan wannan bata
da uzuri kuma na cewa bata iya ba.Duk wacce tayi sake ta fad'o tarko na, to ta Shiga uku,
ni bansan kalmar hakuri ba, ballantana tayi ceton ta. Ba wasa ne ya kawoni ba, na sake
jaddadawa."

Ya nuna ni da pen.

"Ke monita lallai ki kula da hak'k'in aikin ki, ko kuma ki kwana a ciki. Duk mai Surutu Ina
writing ki rubutamin sunan'ta. Kuma kiyi copy na time table ki kawo min anjima.

"Sit down" .

Yace, batare da ya kalleni ba, cikin jin isa.

Na zauna.

Note yayi mana muka kwafa. Yayi dogon bayani da turanci, yace duk wacce bata gane ba,
tayi tambaya. Amma shiru kake ji. Iya tsiya da fad'in rai yasa wad'an da basu gane ba ma suka
yi shiru.

Ko a jikin'sa. Yace Kowacce taje tayi bita kafin ya dawo.

Yana fita a ka rud'e da sowa. Yasha zagi, a d'abi'ar cin mutunci da ya soma da shi. Ya kuma
Sha zuga da yabawa a b'angaren halitta. Ba'atab'a Samun malami mai kyau da a ji irin sa ba,
bama iya cikin makaranta ba. Da ganin sa kaga half cast. Wato ruwa biyu.

Yabar a bin fad'a Kam da k'orafi. Saboda baki d'ayan makarantar, babu a jin da malamai
ke tarairaya kuma a ke ji da su irin mu. Bawai ga k'ok'ari ba, Sai dalilai biyu. ''ya'yan masu kud'i
su suka cike fiye da rabin a jin. Sannan babu a jin da ya kai shi tsula tsula kuma kyawawan 'yan
mata gagara gasa, daga kan farare zuwa bak'ake. Idan Mutum ya zagaye a jujuwan d'alibai
ko'ina
Mutum zai rantse tsince kyawawan 'yan mata a kayi na makarantar a ka zube a a jin mu.

Shi yasa yawancin malamai suna da wad'anda suke so cikin class d'in mu, dalilin da yasa
kenan saisuyi ta tsiya ba'a yin komai na hukunci.

Amma duk da haka a Kwai d'alibai tsirari a cikin a jin 'ya'yan talakawa, kuma wad'an da baza'a
ce musu kyawawa ba, kuma baza'a kushe ba. Wato irin mu, har dani.

Ni kad'aice ban tofa komai ba, a kan sabon teachear d'in namu. Wato Fa'izu Bukar.

Takun'sa ni ya burgeni sosai, saboda ta hakan na tabbatar zai yi maganin tsagerun d'alibai
masu kuma nuna isar sunfi k'arfin komai. Kuma dole Zai kawo gyara da zakkarar da shagalallun
d'alibai da dak'ik'ai. Saboda babu Wata alama ma da ya nuna na wata yarinya ta isheshi kallo
ballantana a ce ya k'yasa da har zata samu damar kawo masa lalata.
Fari ne sosai, da ganin Sama kasan cikin iyayen'sa a Kwai sirki.
Bayan farin fatar sa a goge take, irin gogewar da ba'a cika samu ba cikin Hausa Fulani.

A gefunan fuskar sa a Kwai k'asumba da ta d'an feso, dake nunin yana da baiwarta askewa
yake.

Idanuwan'sa madaidaita ne, masu launin shud'i, irin idanun nan da idan haske yayi haske yake
dan ba da launin shudi.

Yana da dogon hanci sosai, da madaidaiciyar hab'a da k'asumbar sa ta zagayo ta kewaye ta,
tayi masa wani irin kyau da ta dace da tsari da ita kanta siffar halittar tasa.

Babu a binda yafi komai yi masa kyau, irin turuwar girar sa bak'a da gashin kan'sa da suka
d'ai sun isa bada shaidar irin jinsin da ya cakud'u da shi, ga Wanda yayi musu farin Sani. Wato
(Shuwa).

Madaidai cine a tsawo. Yana da diri irin Wanda mata suka fiso.mai cikar b'araza da gab'b'ai ,da
fad'in k'irji. Bashi da rama Sam. Kuma bashi da k'iba sosai. Idanuwa bazasu tab'a k'osawa ba
da kallon'sa, musamman mace. Kome take nema ga namiji, na dai surar kyau, to dole ta taka
burki, idan tazo kan Fa'izu Bukar. Sai dai fa idan tana k'yamatar namiji mara sakin fuska, mai jin
kai da wulak'anci, tofa baza ta iya da shi ba Sai dai hak'uri.

Cinnaka ba Sani babu sabo, ko kuma mai kyawun dan maciji.

Kirarin da naji d'alibai ke yi masa kenan, wasu lokatan.

Amma Sai da ya d'an jima a makarantar yaci wadan nan kirarin sunayen.

domin lokacin ne kowace d'aliba tasan wanene Fa'izu Bukar, domin halayen sa sun bayyana a
sarari sosai.






Alkalamin...... ✍️

_Zainab mazawaje_



Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe

*NI DA GIDANA*


*BY*



_Zainab mazawaje_


_Best brilliant interlligent writer_.... ️




Page *2*





__Aharkar jajircewa da karatu, da rashin sakin fuskar jawo wasa a karatu, sosai Fa'iz ya
burgeni, saboda malamai da dama wasa suke shigarwa cikin karatun,su .

Amma daga baya nima sai na rink'a k'yamar wasu halayan Fa'iz Bukar. Bayan rashin sakin
fuska kokad'an, a Kwai kuma iya cin zarafi ainun idan an b'a ta masa, akwai shi kuma da
d'agawa da jin kai, kamar d'an sarki.

Na kan had'u da shi a harabar makaran'ta, nayi niyyar gaishe shi, ko nuna sanayya, amma
Sai ya wani d'auke kai ya kuma tsare gida,wato kar ma na samu kafa. Jinkai dai wurin fa'iz ya
shaddade.

Wasu mata suna dagawa idan sun san sun mallaki wani abu kamar kyau ko kudi ko sarauta,
amma namiji yawanci bai fiye yi ba gaskiya, ballantana malam Faiz da iya abu daya nake jin zai
iya jin kai, shine kyau, don ba dan wani attajiri bane da gani, ko mulki ko wani gawurtaccen ilimi
da ya kai ya kawo, don da bazai zo koyarwa secondry ba, a fahimtata. Shi yasa nake jin
haushin yarda yake wani dagawa, da wulakanci. Wannan dalilai yasa naja baya. Idan na ganshi
a gabas, to sai nayi yamma ni.

Washe gari, period d'in sa tana shiga, sai gashi ya shigo. Ya ninka jiya a kyau kam.

Kayan da yasa, bayan haska ka shi da suka k'ara, sun yi masa kyau sosai. Ba kuma wasu Kaya
bane na musamman ba. Kayan sanyi ne. Rigar sanyi ce mai duhu ruwan k'asa mai kwala, Sai

wani gida gida a gaban rigar mai launin fari fari. Jin's d'in wandon daya sa, Shima ruwan k'asa
ne, amma mai haske. Sai safar hannu, ruwan k'asa, safar k'afa ma haka.

Komai dai to mach. Duk dai sanadin sanyin da a ke yi, yayi wannan shigar. Sanyin ranar yafi na
kullum ma. Kayan da yasa jiya ma sun yi masa kyau, Amma na yau kam ba'a magana. ko daya
ke, dole Kaya suyiwa Fa'izu kyau, ko wani iri. Amma fa ba kowa ne zai yarda ba, Sai Wanda ya
ganshi.
Ya tsaya gaban a ji, ya dafa tebur d'in teacher, yana kallon d'alibai d'ai d'ai cikin jin kai da
isa.

"Ina a ka kwana game da topic d'in da na karantar jiya, Kowacce ta fahimta?"

Shiru babu Wacce tayi magana.

"Wata ta tashi tayi min bayani ko in brief."

Nan ma shiru.

"A kwai tambaya? "

Nan ma babu Wacce ta d'aga hannu.

Ya gyad'a kai.

"Cab'? Lallai yau jiki zai yi tsami. Kuna nufin wahalar banza nayi Kenan?"

Ga rashin sanin Fa'iz, yawanci an gane aikin sa. Kawai shiryawa a kayi a nuna masa bai isa
ba. Saboda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login