Showing 36001 words to 39000 words out of 51633 words
Chapter 13 - NI DA GIDANA BOOK COMPLETE BY ZAINAB MAZAWAJE.pdf
sulaiman
gareki? to duk Soyayyar da yake miki ai bazai iya aurenki ba, Kenan no reason da zaki rink'ayin
wani prouding a kan'sa har da wata tutiya.
Kuma tun da haka ne me yasa baki zauna can ba, yayi ta sangartaki yana shagwab'aki da
soyayya, karki auri kowa, tun da, Soyayyarsa da kulawarsa ita kad'ai ke gamsar dake."
Na yarda Ancle Fa'iz ya iya yanka maganganun ramuwa na cusa haushi, idan aka yi masa kan
kara shi kuma na itace yake yi.
Raina kam ya b'aci da jin furutan'sa. Kenan babu inda zanji San yi a gidan. Da sauri na mik'e na
Shiga d'aki na janyo gyale na da takalmi da jaka. Na fito. bada niyyar fita na fito ba, jarrabawa
zan yi naga zai barnin na tafi, kuma idan ya barnin ficewar zanyi, domin zuciyata wani irin suya
kawai takeyi.
Yana nan zaune in da na barshi. Ya bini da kallo, Yayin da na yafa gyalen, nasa takalmi, nayi
kamar banganshi ba, nazo zan fita. Wata tsawa ya dakamin har Sai da jikina ya d'au rawa.
Bana ko kokwanto su momi sunji, kuma nasan ransu zai yi fari tas.
Ya nunani da yatsa.
"Wallahi, kika tsallake tudun k'ofar nan kika fice Sai kin raina kanki." Nayi tsuru tsuru dani,
kamar wacce ta yiwa sarki k'arya. Sai kuma na dawo turus na zube kan kujera na Shiga rera
kuka na rufe fuskata da gyale Ina ta sheshsheka, a zahiri rantsewa za'ayi na gaskiya ne, amma
a bad'ini na k'arya ne.
Ina k'yallaro shi, dai jijjiga kai yake, yana Jan kwafa da ina Kukan, tabbas naga 'Yar damuwa a
tare da shi, naji yace.
"Haka siddan Ina zaman zamana na jawa kaina d'aukakkiya.
Jin furucinsa, Sai na k'ara sautin Kukan sosai. Ya dubeni yaja tsaki, tsam Sai naga ya mik'e
yace.
"Kyayi ke kad'ai ."
Yasa kai ya fice. Yana fita na tashi na Shiga d'aki nasa kayan bacci. Kyakykyawar riga ce silk
mai k'aramin hannu doguwa, nasa da hular bacci mai kyau. Na kishingid'a bada niyyar bacci
ba tukun. Damuwar da naga Ancle ya d'an Shiga sanadin Kukan da nake yi da yake zaton
gaskene ta farantamin. Da wannan na soma fahimtar wani sirri nasa da zan iya cin nasara a
kan sa wani lokacin. Sam bayason a na yi masa kuka musamman na wata damuwa haka na
fuskanta.
Ban sa rai da zai sake waiwayata ba a daren, Sai jin sallamarsa nayi a falo yana Kiran Sunana.
"Sumayya! Sumayya!!.
Naki amsawa ku ma nak'i fitowa, domin so nake ya shigo d'akin.
Kuka ma naci gaba dayi kamar dama can aikin kukan nake yi.
Babu shiri ya fad'o d'akin. Da alamu shirin baccin yayi Shima. Riga ce ta bacci yasa da dogon
wando pure cotton mai taushi, irin kayan. Sunyi masa kyau ainun. gaskiya Sai da ya tsaya a
kaina na sakanni yana kallona Kawai, Sannan ya tsuguna a gabana, murya k'asa k'asa yace.
"Wai Sumayya menene damuwarki? haka kawai kina neman ki d'agamin hankali. Me kike so
ne?".
Cikin shagwab'abb'iyar murya nace. "Bakaine kace bazan tafi gida ba."
Ya kuwa sake k'uluwa yace.
"Bazakije gidan ba na hana,kuma ko me za'kiyi. Ke ko kunyama ba kyaji k'atuwar budurwa
kamarki ki rink'a acting irin na yara, k'anana, har kina kuka saboda sangarta ko? Ko da yake
goyon kakace dole kiyi. Ga Sulaiman kuma ya sangartaki. To Any way ni bazan d'auki sakarci
ba wallahi, tun wuri ki Shiga taitayinki."
Nayi dib! Ko uhum ban sake cewa ba, face mitsitstsike idanu.
Shiru ya ratsa wurin na mintoci, Sai Iskar sama dake motsi tana wulwulawa tana bada iska
madaidaiciya mai dad'I, sakamakon d'an yanayin zafi da ya shigo a tsukin.
Ko tausayina yaji, Sai kuma ya tausasa murya Maimakon kausasawa da fari.
"Sumayya, ni banga a binda zai sa ki rink'a damun kanki ba. Da a ce tun farko na munafunceki,
to shine za'ki damu kanki, idan kika ga wani sauyi. Amma haka siddan ki rink'ayimin tuhumar da
gangan? Me na yi miki? Kullum fa Sai na tambayi me kike so, menene damuwarki, amma duk
ban fita ba. Kinsan manufar auren mu, kin a mince, to me yasa zaki rink'ayi min bore bayan
anyi?.
Naga shiru ba mafita bace, gwara na fad'amasa burina ko zanyi sa'a ya a min ce daga nan
k'ofar farko ta bud'e.
"Ancle nifa buk'atata ka rink'a yagar min lokaci, muna hira ko yaya, na samu mai debemin kewa.
Su khairat da kake cewa muyi hira basu da lokaci kullum suna kan hanyar makaranta, Boko da
islamiyya. Dare kuma Kowacce d'akinta take Shiga, saurin bacci ne dasu. Momi kuma kunyarta
nake ji, bana iya sakin jiki muyi hira sosai."
Nayi dace yace. "To, zan jarraba yarda kike so, amma fa ni ba ko yaushe nake son hira ba,
karki zamemin BBC, uwar watso kanun labarai".
Dariya furucinsa ya bani, har nayi ta fito fili a hankali, saboda yanayin da ya furta. Shima sai
naga yayi 'yar dariyar.
"Ke dai 'yar tawaye ce rigimammiya, mai fuska biyu kuma. Kin rikita mutane da kuka, kuma kin
dawo kina yimin dariya ko? Warki ne ni dai dai k'ugun kowa."
Yanayin da muke ciki, da yanayin lokacin, ya sanyayamin zuciya sosai. Naso mukasance daren
ranar da faranta ran juna irin na ma'aurata, koda iya hira, amma Ina!.Mikewa Ancle yayi.
Nikuma na tuno da a binda nake son ce masa.
Nace"Am, Ancle"
Ya juyo a hankali. "Ina jinki Sumayya."
Nace. "Gobe
nakeson komawa makaranta. Yace"Sai yanzu za'ki fad'amin?"
Nace"To, na bari, Sai Jibi? ".
Yace. "No, kije goben, tunda kin niyyaci hakan.
Daga nan yayi min Sai da safe ya fita. Inajinsa ya b'amemin k'ofar sosai.
Na kuwa kasa bacci. Da nayi juyi, Sai na hango Ancle Sanda ya tsuguna gabana, ya zubamin
kyawawan Idanuwan nan nasa masu hasken blue masu kashe gab'b'ai, yanamin surutai a
hankali. Gaba d'aya kasa dai daita nutsuwata nayi a lokacin. Komai nasa mai ruruta wutar
k'auna ce,
ga ma'abocin kallonsa. Nasan shi a lokacin babu komai a ransa, burinsa ya shawo kaina Kawai.
_Wasa farin girki_
_Muje zuwa_
_Zainab ilyas mazawaje_
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe
*NI DA GIDANA*
Zainab ilyas mazawaje
_Best brilliant interlligent writer...... ️
*Page 16*
Ranar wata alhamis, Ancle Fa'iz ya shigo da daddare ya sameni ni kad'ai a falo zaune nayi
shiru. Mutan gidan duk suna saman Momi ana ta shan hira, da kallon TV. Ya shigo ya zauna,
bayan nayi masa sannu da zuwa yace.
" Sumayya wai zaman kad'aici menene ribar sa? sai kiyi ta jan jikinki da mutane, kina ware
kan'ki why?".
Na d'aga idanu na dubeshi bansan me zance ba. Shi duk zaton sa nike jan jiki da mutan gidan,
saboda baisan komai da yake faruwa ba. Na yarda a je a hakan, gwara ya zargenin da na zama
nice ta farko da zan soma kai masa k'orafi a kan Maman sa da 'yan uwan sa.
Musamman Momin sa da yake ji da ita matuk'a.
Na daure nace. "Kasan fa ni kunyar Momi nake ji."
Yace da sauri cikin dan fushi. "Kinga don Allah ki dai na irin wannan gida dancin. Kunyar lafiya?
Shike nan sai kice lalllai sai dani za'kiyi sabo, ni da ba mazaunin gida ba? ki gyara wannan hali
naki please, in dai kina so mu shirya".
Nace "To". Laifin da ba nawa ba na amsa. Naci sa'a ranar ya zauna wurina, ya d'an d'ebemin
kewa, nafi zaton tausayi na bashi, na kad'aicin da nake ciki babu kowa.
Amma dai hira ce jifa jifa, me kama da tambaya, kuma yawanci a kan karatu na. Duk da haka
yafi babu, domin ko babu komai, muryar Ancle sanyaya zuciyata take, tamkar kaskon da yasha
wuta, a ka tsoma a ruwa, duk da kunyar kallon sa nake yi, musamman idan ya sani a gaba.
A hankali, a hankali kusanci da jituwa ya soma shiga tsakanina da Ancle Fa'iz. mukan jima
muna 'yar hira, musamman da daddare, Saboda lokacin yafi zama a gida. Ya kan jima a falona,
amma kallo yafi yawa a kan hira.
Ancle Fa'iz baya son kowani film Sama da kallon boll , Sai film d'in china. Dole na koyawa
Zuciyata son,su duk da bana k'aunar ganin su, basu dameni ba. Amma har kud'i nake sawa na
sa a turomin a memory da yawa saboda shi. Duk da Shima d'in yana da wasu da yafi gani a
waya. Duk wani a bu da na san ya naso, tanadar'sa nake yi na tarbeshi da shi, saboda sa'ar da
na samu yana shigowa falona ya zauna.
A bin dai da bayaso nake yi, shine narka da shagwab'a. Narka da shagwab'a nake yi masa
muraran cikin mu'a mala ta da shi, musamman idan ina son yayi a bu yak'i.
To shi kuma wannan ce ba ya so, domin bayan k'orafi har hantarata yake yace yi. Yace.
"Ke tafi can ki bani wuri, bani son tab'ara. Wani lokaci ya cuno baki yace. Duk Sulaiman ne, ya
sangartaki ya shagwab'aki saboda mugunta, domin yasan gidan wani za kije bashi zaki
k'warzaba ba.Rannan na kada baki nace " Ancle kaifa kace na rinka kallon ka a matsayin Kawu
Sulaiman, kuma shine na maisheka hakan wurin muamalar da nake da shi, amma sai kuma
kayi tayi mun fada kuma? ". Na karasa furucin cikin 'yar shagwaba.
Abinda dariya sai yayi shiru mukus bayan da yayi min kallo daya kawai. Mikewa kawai yayi ya
fice, nasan rasa amsar bani yayi.
Wani zubin kuma idan ina zuba masa salon shagwaba a hira ya kan kasa yin shiru ya kance
"Bari dai na baki wuri ba dani ba wannan tab'arar, wanda ya sangarta ki, shi zai iya d'auka. To
nan na kaishi gargara Kenan, domin ficewa yake ya barni.
Wani zubin kamar cikin 'yar tsawa zai ce min. "
Za ki soma shashancin ko? Ki shiga hankalinki Allah, ko ranki ya baci, da girmanki ba yarinya
ba, ki rinka irin wannan sokwanci, ki kiyayeni fa".
Bani yin fushi, sai nayi murmushi kadan na sunkuyar da kai na rabu da shi, sai wani jikon,
saboda idan naci gaba, tabbas nasan ran nawa zai baci.
Kuma yafi daukar zafi idan bashi da walwala na fahimta, shi yasa na karanci yarda zan tafi da
shi a komai, game da yanayin da yake ciki.
Duk da bayaso, ni kuma ban daina ba, domin ni kuma ta haka nake so na Shiga jikinsa da
zuciyarsa mu shak'u. To daga baya ma sam daina k'orafin yayi da ya gaji.
Sai dai yayi banza da ni baya yin magana, idan na kai shi kuma bango ya mik'e kawai ya Fice,
Sai yak'i shigomin kuma Sai yayi min ban iska na wani lokaci, ranar da na kai shi gargara
Kenan.
Ban ja baya da komai ba, saboda damar da na samu daga gareshi, nayi ta shigo masa da
abubuwa iri iri,duk da ina shan kyara, wani zubin, banayin zuciya, domin kuwa ni mai ne mace
kuma wataran bazai yi ba, musamman idan shakuwa ta soma shiga tsakanina da shi.
Wata sa'ra dana d'auka, idan zai yiwa kan'sa a bu, Sai nace Sai yayi min, ko munyi tare.
Yana da wani a bin yanke farce mai kyau, duk ranar juma'a yake yanke farce da shi. Na kance
ya kawo nayi masa Sai yak'i. Ni kuma Sai na takuramasa nace Sai yayi min ban iya ba da
kaina. Farkon randa na soma damun sa da magiya, ya jefomin kallon tara saura kwata yace.
"Wai da can wa yake miki? Ko domin Samun wuri?. Nace"Baba Talatu ce. Yanzu kuma bani da
kowa Sai kai Ancle, ka taimaka." .
A ranar fafur yak'i yi min. Amma daga baya ya soma yi min, saboda bak'in naci. Ni bana zuciya,
Sannan ga binbinin magiya da kwantar da kai, ta haka naci nasara kan Ancle da murd'ad'd'en
halin'sa.
Randa zai soma yanke min farcen ma, sai da yaja tsaki har sau uku, irin na na takura masa,
kafin ma na kara sa mika hannu ya fizgo hannun nawa ya soma da sauri da sauri, ni kuma wani
sanyin dadi naji mai sanyaya zuci har ya gama, idanu na na kansa, banki mu dawwama a haka
ba, fuskar sa a daure duk bai san abinda nake ba.
Yana gamawa yace.
"Tashi ki bani sarari, tun da bukatar ki ta biya".
Na narke murya, ina yi masa wani salon kallo nace ." Ancle baka yi min fa na kafa ba".
Ya zabgamin wani kallo, kawai bai tanka ba, ni nasan amsar, shi yasa nayi gum ban kara tofawa
ba, na kunshe dariya ta a ciki na mike don ficewa daga falon nasa, na fahimci kamar ya fahimci
dariyar da nake dannewa, shi yasa naga ya cira kai ya dan bini da kallo, daga bisani ya girgiza
kai a hankali irin na na buwayeshin nan, ya mai da kai ga karasa yankan farcen sa.
Babbar nasarar da na samu ta ya soma gajiya da naci na ya na dan yi min a bu, yasa na k'ara
k'aimi. wani lokaci ni da shi a falona, na tsiri tsifa saboda ganin arhar damar ga Ancle Fa'iz. Da.
na soma nace "Ancle don Allah tayani tsifar kai."
Ko kallona bai yi ba, a fusace yace.
"Sumayya kina nema fa ki raina ni da yawa. Nine ma zan yi miki tsifa?."
hakuri na bashi a nan, saboda naga ya d'auka da zafi.
Ban daddaraba wani lokaci muna tare muna kallo na sake tsirar tsifa. Ina cikin yi nace.
"Wash!. Ya waiwaye ni.
"Me ya faru?" .
Nace"Wani ciwo ne a yatsana da naji, garin tsifa gashi ya yanki wurin".
Yace"Garin Yaya kika ji ciwo?".
Nace "Jiya ne ina yanka nama".
Yace" Sannu, cikin dan tausayawa, zaton sa gaskiyane, yace "Ya kamata ki rink'a kula."
Na faki idon'sa nayi murmushi. Nace "Ancle don Allah ka tayani, kaga gobe mai kitsona zata zo,
kuma ciwon hannu na bazai barni na
Karasa tsifar ba. Please za'ka tayani my Ancle?".
Ga mamakina mai makon ya fara da fusata yarda ya bayi min, sai naji ya ce.
"Sai dai nayi miki aski, ni shi na iya Kawai."
"Haba dai aski. Yaya zan yi aski ina mace dani."
Naci gaba da marairaicewa.
Yace"Sumayya wai ni bawan kine kome?".
Na fik'e murya irin ta d'a,a nace" Haba! Haba!!. ai ko a shirin wasan kwaikwayo, dole a ce da
mijin iya Baba. Darajojinka sun girmi haka tuni, mijina, ba domin na isa ba, sai don larurar nan,
kuma nasan kai mai tausayine fa".
Ya sassauto, domin naga ma ya d'an Saki fuska.
"To, nawa za'ki bani na Lada?".
Na marairaice. "Haba, my Ancle. Ina Daughter guda sukutum Sai na biya"
Yace "Idan baza'ki biya ba, to kisa hak'uri kuwa."
Na Shiga magiya da naci da shagwab'a duk dai, babu shirI ya fizgi kibiyar dake nake mik'a
masa cikin fusata.
"Wannan Yarinyar wallahi da ace kina da maita, kika kama kurwa ba zaki saki ba, daya zan
miki, daga shi babu k'ari".
Banyi fushi ko kusa face 'yar dariya ma.
"Na yarda wallahi, mai shirin zuwa sama ko takarda ya taka ai ya rage".
" inji wa babu in da yaje, kawai zance ne". Yace cikin bani amsa cikin kosawa, don har da 'yar
harara ma, ya fizgi kibiyar daga hannu na cikin fusata ya soma.
Yana kan kujera ina gabansa a kasa.
Daga d'aya Sai da a ka tafi uku, kuwa, saboda naci na. Amma yanayi yana dunguremin kai. A
raina fad'i nake, aje a hakan, naci nasara, tun da ka samu, kazo hannu, hakan yake kuwa tayani
tsifar ya zame masa k'ara'i, ko ba yawa, ina shan dai sababi, amma Sai na jure.
Wani lokacin littattafan makaranta na na kan kwaso nace ya koyamin wasu a bubuwan. Zai
koyamin na gane, amma Sai nace bangane ba, domin mu ja lokaci. Sai Nasha fad'a kafin ya
sake. Duk Ina yin haka ne domin na Shiga jikinsa, da rayuwar sa, mu k'ara shak'uwa. Kuma
bana yarda na zauna nesa da shi, ko tazara kad'an bana bari, jikin sa dab nake rakab'uwa
kamar 'yar kyanwa kullum in dai ya zauna. Farko randa na soma yi masa hakan, matsawa yayi.
A wayance muna hira na kuma matsowa jikin sa. Ya sake dan matsawa, a na uku Sai yace
min.
"Wai duk wadatar wurin nan Sai kin matsamin Sumayya?" .
Murmushi nayi, nayi masa Farr da ido nace"To, ya kake so nayi? bani da kowa yanzu da yafi
kusanci dani Sama da kai. Idan ban rab'u da kai ba, Ina kake so naje?".
Bai tsinkamin ba, ya maida kallon sa ga
mutuniyar tasa, wato boll. Wannan damar tasa na sake shigar da wata. Sai muna zaunen, Sai
na rink'ayin layin baccin k'arya, Sai nayi luuu! na zubo jikin, sa, har sau uku Ina yi, yana d'an
tureni. Nan ma da fari yayi k'orafi yace.
"Wai menene haka ne Sumayya?" Nayi firgigit Ina mitstsike idanu.
"Me ya faru? Menene Ancle.?" .
Kamar bansan komai ba nayi. Mik'ewa yayi yace "Na lura kora da hali kikemin. Bari na tarkata
na barmiki wurinki