Showing 6001 words to 9000 words out of 51633 words

Chapter 3 - NI DA GIDANA BOOK COMPLETE BY ZAINAB MAZAWAJE.pdf

shi baya gaban'sa. Burin sa a samu sauyi da ci gaba. Saboda
haka kuskure ne d'alibi ya zauna yana aibata malami ko da dalili, tun da kullum cikin cin
amfanin sa yake. Kuma ba'a iya biyan malami kun sani sai ubangiji ne kawai zai iya biyansa".

Jikin kowa yayi sanyi. A ka rasa me iya cewa komai. Ni kuwa dama nasan kuka suka kawo
gidan mutuwa. Malam Abba na hannun Daman malam Fa'izu ne, bazai tab'a yarda a ai bata shi
ba ya k'yale, duk da dai gaskiya ya fad'I.

Alkhairan da malam Fa'izu ya kawo, a makaranta, bai kamata a aibatashi ba, koda yayi laifin.
Kowa ma yaji ba domin kud'i yake koyarwa ba, Sai domin kishin k'asar'sa. Wannan kad'ai ya isa
yasa ya karb'i lambar yabo.

Tunani na kenan da na wasu d'alibai da muka zanta daga baya.

Daga baya ga mamakin mu, malam Fa'iz ya sassauta tsananin nan da tsaurara hukunci
garemu. Kuma na lura canzawar da yaga munyi ne, Shima yayi d'an laushi. Sannan ya fito da
wata hanya ta taimakon mu, don mu haye a
jarrabawar mu ta gama makaranta ta gaba to.

Lesson ya tsara duk yamma cikin makaranta ga duk wacce ke ra'ayi amma. Shi ya d'auki
nauyin komai.hud'u da rabi an Shiga a tashi k'arfe shida na yamma. Duk d'alibai kuwa a ka yi ta
tururuwar zuwa, saboda kowa so take taci jarrabawa.

Ba kuma iya darasin turanci yake koyawa ba, har ma da sauran darussa. Kuma yawancin a
binda yake koya mana wanda yake tunanin zai fito mana ne a jarrabawa.

Baki d'aya muka ga ya canza ma. Ya rage zagi da fad'an nan da tsare gida. Amma duk da haka
fa babu fuskar da za'a kawo masa raini ko wasa. Har hira ma yake damu amma fa a kan karatu,
da bamu shawarwari masu kyau, duk a kan harkar karatu, saboda jarrabawar dake dosomu.

Da jarrabawar tazo kuwa mun taki babbar sa'a. Domin kuwa yawancin a bubuwan da malam
Fa'iz ya koyar damu shi ya fito. Har zargi ma muka rink'ayi anya bai samu tambayoyin
jarrabawar ba a boye, domin komai ya fito da ya koyar damu.

Ai sai yayi kuma farin jini wurin mu. Domin yayi mana k'ok'arin da babu malamin da yayi mana
irin sa. Mun kammala jarrabawar cikin sa'a da kyauta ta zato, domin duk wacce ta sare, sai
dakikiyar da kwakwalwarta ba ta aiki.

Ranar da muka kammala jarrabawa da yamma, aka sha hotuna, har da malamai a kayi hotuna.
Amma fa banda malam Fa'izu. Kuma anfi kwad'ayin ayi hoton da shi, saboda tarihi. Kuma abin
alfaharine ga d'alibai, amma mirsisi yak'i.

Ko da yake tsoron tun karar'sa ma a ke yi, malam Abba a ka tura. Ya dawo yace.

"Kuyi hak'uri fa. Abokina yak'i yace yana da mata, kuma zatayi kishin haka.

Duk d'alibai sun yarda, nice dai kunne na bai karb'a ba. Lambobin waya ma na malamai da ake
karb'a malam Fa'izu hanawa yayi. A ka koma takan malam Abba ya bada lambar wayar malam
fa'iz yace shi bashi da ita. Ta yiyu shi ya hana shi ya bayar, nafi kyautata zaton hakan.

Intisar tafi kowa damuwa da lambar Fa'iz, saboda son da take yi masa ma ya fito fili. Amma ko
giyar wake tasha bazata iya tambayar sa ba. Tun daga Sanda tayi masa rashin kunyar nan
suke takun sak'a da shi. Ta gasu a hannun'sa.

Tsakanin sa da ita hararace. Duk Sanda ya shigo class Sai ya tasheta yayi mata tambayoyin
abinda ya koyar. Ta fad'i wanda ta d'an fahimta, tana yi yana jefa mata kallon wulakanci, da ta
kakare kuwa zai ta gasa mata maganganun tozarci da gwara dukan ma dasu gaban dalili bai, to
ya fuskanci tafi jin ciwon bakaken kalmomi, shi yasa baya dukanta ma sai dai ya tozarta ta
gaban jamaa, ta hanyar cin zarafi da furuci.

Gaskiya Ancle Fa'iz yasan takan iya tsiya, da ka fada tarkon sa, gwara a jefa ka gidan yari iya
na waadin laifin ka. A cewar zuciyata .

Tsawon wata guda, tun da na gama secondry, babu in da nake zuwa bayan islamiyya. Sam
kuma fitar bata dameni ba ma saboda ni dama ba ma'abociyar son yawo bace. Sannan soyayya
da tarairayar da nake sha wurin kawuna sulaiman ta isar min daga damuwa da wani a bu a
rayuwa da zai sa na rinka yin tunane tunane.
Kulawa gata, sangarta so da k'auna duk Kawu sulaiman ya tattare su a kaina. Haka ma kakana
Laminu mai turare. Sai 'yar korar su mai taya su, matar kakana Baba Talatu da ya auro bayan
rasuwar Inna Hajara kakata. Duk da baza'a had'ata da kakata ba inna Hajara, amma tana
kamantawa sosai.
Ni d'in marainiyace ta sosai, tun da ban bud'i idanu da iyaye na ba duk sun rasu Ina yarinya
sosai. Bayan nan kuma nazo na rasa kakata Hajara ita ma data rungumi maraicina da kyau,
take nunamin k'auna muraran. Sai da ta shekara da rasuwa kakana yayi aure, kuma saboda ni.
Saboda babu yarda za'ayi ya zauna dani babu mace.
Naga mutuwa a rayuwa ta Kam. Amma Sai a tara masu iyaye Sama da d'ari ba'a samu mai
Samun kulawa da tattalin k'auna iri naba.

Shi yasa bayan rasuwar kakata Soyayyar ta dawo kaina. Haka ma kawuna Sulaiman
Soyayyar dake tsakanin sa da yayarsa mamana Khadija da bazata fad'uba, kaina ya tattarota
bayan rasuwarta. Su biyu ne tal wurin iyayen su, kuma a Kwai k'auna da fahimta mai zurfi
tsakanin su. Wannan dalili yasa Kawu yake mugun Sona da tausayina. Motsi kad'an yana
bibiyar me nake ciki. Kome ya samu ni zai kawowa. Tun da ya gama digree babu aiki ya Shiga
buge bugen aikin Samun k'ud'i na k'arfi, daga wannan zuwa wannan, duk saboda ni. Ma'abocin
son K'wallon k'afa ne sosai. Suna da Club babba ma na matasa irin sa. Suna buga mach kurfa
kurfa na state state bayan na garin su idan an gayyace su. Yama fi Samun kud'i tanan babu
laifi. Amma lokacin daya ke bawa boll dabam, lokacin buge bugen sana'oin sa ma na kafi zuru
da bam. Yayi rini, yayi Aikin gini, yayi aikin electric, har aikin fenti ya iya, idan an kirashi zai
b'adda bami yasa Kayan aikin yaje yayi ya karb'i kud'in'sa.


Mai k'wazon neman na kaine Kawu Sulaiman, bashi da girman kai Sam. Kuma duk sana'ar da
yaji ana Samun kud'i zai koya, ba tare da raina taba. Shi yasa baya rabo da'yan kud'ad'e. Bamu
da shi sai dai na rufin a sirin rayuwa, kakana ma a zaune yake ba kullum yake fita ba, da
harkar Sai da turare ta karye masa. Da kanti ne da shi guda na saida turarurruka, yanayin
rayuwa komai yaja baya. Kawu sulaiman ne ke k'ok'arin a bubuwa da yawa. kuma rayuwar mu
babu fallasa, komai a Siri a rufe ruf.'Yan kayan k'walam na motsa baki ma Kawu na kan sayo
lokaci lokaci. Ban rasa kuma 'yan Kayan ado irin na 'yammata ba, Kawu sulaiman yana fito dani
kunya, ko ban furta ba zai sayo dai dai ikon sa. Ya kuma ban k'ud'i ko zan buk'aci wani a bu.
Wani lokaci zaice na samo takarda da biro na rubuta duk abinda nake bukata na 'yan mata,
nakan rubuta na bashi, shi kuma duk sanda ya samu iko ya kan sayo su a hankali a hankali.
Kuma da an dauki lokaci zai sake cewa na rubuta abinda nake bukata, sannan ya kan bani 'yan
kudi na kashewa ma jifa jifa, kuma ya danganta da nauyin aljihunsa na daga a binda zai bani.
Ya wanke min duk wani hawayen maraici, saboda ubana talaka ne sosai, bai barmin komai na
gado bama. Ko gidan da suke zaune da mahaifiyata ma na hayane, kuma biya masa ake yi.
Tun mahaifiyata tana raye Kawu na yake nunamin Wata irin kulawa da soyayya, da Ina yarinya
naji daga kakata, bawai sai data rasu ba. Domin da ta rasun ninkawa kuma yayi.

Ya kusa zautuwa ma kawu da mamana ta rasu saboda kusancin sa da ita da k'auna. Kakana
ma da matar sa kulawa da k'auna suna bani iyayin'su, saboda maraici hawan hawa da na samu
kaina a ciki.
Ina da ra'ayin son ci gaba da karatu, shi yasa ma aure baya gabana, ko kula kula da shaannin
samari ba nayi, kuma kawu ya goyamin baya.

Ina da samari, tun kafin na kammala secondry. Duk da haka dai i
na da samari biyu da nake sauraren su sama sama.

A Kwai Alhaji Rabi'u magidanci mai mata da yara. Yana da sukunin sa kuma yanayi min 'yan
hidindimu. Yana da mota da yake zuwa wurina ma. Sai usman shi kuma saurayi ne, tela ne na

aikin surfani.

Hankalina ya d'an fi kwanciya da Usman saboda shi saurayi ne dai dai dani. Ina tsoron fad'awa
tsakiyar ma'aurata. A nawa ra'ayin gwara tazo ta sameni.

Amma shi Alhaji Rabi'u kullum zancen'sa na bashi dama ya fito, amma bana bashi had'in kai.
Shima Usman ya damu da azo a yi wani a bu, Shima d'in ma ni nake bashi matsala. Ina son na
samu ilimi sosai nayi aiki na rink'a tallafawa Kawu da kakannina. Wannan shine burin sumayya
a b'oye.
Kwanci tashi jarrabawar mu ta fito na samu sakamako mai kyau k'warai. Shi yasa direct
jami'a,suka amsheni.

Kawu yayi ta samin albarka. Sosai yayi farin ciki, har kyauta yace zai min. K'awaye nama duk
sunci da kan mu yake a had'e. Saboda halayyar mu guda ce ta son karatu. Amma nafi su
kyawun sakamako dai.

Kawu sulaiman yayi min nasiha sosai da shawarwari, wurin tafiyar da rayuwata ta jami'a. Yaja
kunne na sosai a kan kar nayi mu' a mala da k'awayen banza da samari. K'arshe yace.

"Na baki dama, don Allah kar ki bani kunya Sumayya, kija mutuncin ki, kiyi a binda ya kai ki
Kawai, wato karatu."

Nace" Kar kaji komai, Ancle, zan kiyaye, ka ta yani da addu'a."

To ban bashi kunyar ba kuwa. A shekarata ta biyu a jami'a ya dad'a sakin ransa sosai saboda
yarda yaga komai nawa yana tafiya dai dai, Sai ma k'arin ci gaba. Na k'ara nutsuwa wurin kula
da tattalin kaina. Na k'ara sanin darajar kaina sanadin k'yamatar wasu a bubuwa da nake gani.
Na k'ara kyau na gogewa da wayewa kuma, amma wayewa ta sanin mutuncin kai da darajar
kai, da iya muamala da mutane, da kiyaye abinda zai rusamin rayuwa.

Ba fara bace ni, amma za'a iya sani a layin farare idan sunyi k'aranci. Saboda kulawa da kaina
da nake sosai, fatata Sai ta k'ara gogewa ta haskaka sanadin gyara. Kawu lokacin Samun'sa ya
k'aru, ya kuma Saki Samun'sa sosai a kaina ma a lokacin. Burin sa Kawai Sumayya ta zama a
bar kwatance da alfahari.






Alkalamin...... ️

Zainab mazawaje


[6/20, 8:19 AM] Zainab Mazawaje: Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe


*NI DA GIDANA*

*By*



_Zainab mazawaje_


_Best brilliant interlligent writer_..... ️





*page 4*




A tsukin kuma wanda nake kira da dan fodiyo wato (usman), ya matsa lamba.

Sai ya nuna ala tilas sai na barshi ya turo manyan sa shi ya gaji da jirana. Ga a binda yace da
nak'i yarda.

"Sumayya, don Allah ki rufamin a siri nasan Matsayina. A farga ba nake tsindim na zaki iya
kub'cemin. A komai kin canza kin samu haskakar da za'a k'yalla idanu a kan'ki a kawo miki hari.
Babban a binda nafi kwad'ayi a kan'ki shine kamun kan'ki da nutsuwa da tarbiyya. A ina kike
tunanin zan lalubo irin'ki idan na rasa ki?
Tabbas zan shiga tasku idan na rasa ki. Ina sonki Sumayya fiye da tunaninki, don Allah kar kiyi
min wasa da hankali. Ni dai na fito a San dani nasa rai ma. Aure zan jiraki zuwa lokacin da kika
shirya."

Sam aure baya raina a lokacin, ko fidda ma gwani. Tausayin Usman shi yayi rinjaye a raina,
bawai son'sa ko son auren'sa ba. Saboda nacin sa da magiya na a mince amma nace ya bani

kwana ki biyu nayi magana da Kawu na.

Yayi ta murna kuwa.

Ranar da mukayi zan fad'awa Kawu Sulaiman, Usman zai zo yaji inda a ka kwana, ranar Kawu
na ya tashi da gyare gyaren d'akin'sa, saboda ranar lahadice baya fita Sai yamma, ni kuma bani
da lacture. Na shiga taya shi, saboda gyaran da yawa. Kusan yayi d'ai d'ai da komai na cikin
d'akin. gyare gyare da goge gogen da yawa.
Na kafe Sai ya barmin nayi ni kad'ai. Ya saduda ya tafi ya barmin.

Da yake Ina da saurin aiki, sai gashi na gama, ina mai da komai muhallin'sa naci karo da wata
farar ambulan 'yar babba.

Ko Ancle Sulaiman ya sanni da lafiyar bincIke. kamar nawa na Shiga k'ok'arin bud'ewa, domin
naga menene a ciki. Amma a tsorace nake kar ya shigo ya ganni, yace mai hali kin soma ko?
Domin na saba da wannan kalma tun Ina yarinya.

Tuni na fahimci hotuna ne, da sauri na shiga zaro su, duk zatona hotunan budurwar sace da
ban tab'aji da gani ba.

A bin takaici a gareni, hotunan maza na gani, saye da kayan 'yan boll har dashi. Wani Mutum
uku wani mutum biyu wani shida. A Kwai kuma wanda suka had'u su duka suka sa boll d'in a
tsakiya shida 'yan club d'in nasu.

Amma menene yaja hankalina na kasa a jiye hotunan kamar yarda naso da fari, da naga ba
hoton mace bane?

Mutumin da na yanke zaton zan sake gani a rayuwata, Mutumin da nasan babu wani dalili na
sake had'uwata da shi, shine a cikin hotunan 'yan club d'in su Kawu

Sulaiman.wanene?

Faiz Bukar.

Na sake kai ganina ga hoton, amma bisa ga wanda ya d'au hankalina da ganin'sa wato Fa'iz.

Gaba d'aya ya haske hotunan. Kowanne da ka kalla, shi zai fara janye kallonka. Muryar Kawu
Sulaiman naji a tsakar kaina.

"Me hali baya fasa hali dai. Bincike kike min ko gyara sumayya?" .

Nace. "Yi hak'uri my Ancle. Wani malamin mu na secondry na gani shi yasa na tsaya dubawa

ma, dama kasan shi kawu?".

Na nuna masa shi.
Ya duba yace.

"Au, Yarima kike nufi?".

Na sake nuna masa shi, ga zatona bai kulaba.

"Ka ganshi fa, wannan farin na cikin ku, malam Fa'izu fa."

Yace. "Shi d'in nima nake nufi ai , sunan'sa Fa'izu, amma mu a bokan'sa Yarima muke ce masa.
Mu kance masa kuma Gimba, wato d'an sarki, a hausance kenan. Amma mun fi Kiran'sa, da
Yarima, a yaren barbarci ne, saboda usulin mahaifin'sa babarbare ne, mahaifiyarsa kuma
k'abilar shuwa a rab ce. Na dubi Kawu saroro.

"Me yasa kuke ce masa

Yarima Ancle.?".

Murmushi yayi ya karb'i hoton."Abokai suka sa masa kuma ya bishi. Baki ga takunsa yayi kama
da na masu wannan sunan ba kema?".

Nayi gajeriyar dariya.

"Tabbas na harbo jirgin Kam, sunan ya dace da shi sosai, kun iya sa sunan a muhallin'sa. Ai ya
yiwa dalibai horo sosai a school d'in mu. Bana zaton a kwai d'alibar da zata mance dashi.
Sunayen ma da za'a kirashi da shi suna da yawa. Dama d'an club d'inku ne Ancle?".

"Sosai, a harkar boll kuma muka had'u muka saba. Shekara shida Kenan da ya shigo club d'in
mu na Kaduna united. Ya iya boll fiye da zaton mai zato, da shi muke ji a club. Ko jiya na had"u
da shi da yamma a club, mun Sha hira a kan gasar wata boll da muka je. A Kwai mutunci
tsakani na dashi, duk da babu wata a bota dai sosai tsakanin mu, Sai mutunci sanadin club tare
da buga k'wallo.

Hirar ta datse ne saboda baba Talatu da ta kirani.

Usman dan fodiyo da yazo hak'uri na bashi, nace ya k'ara min kwana biyu dai. Mantawa nayi
ban yi Maganar da kawuna bama.

Kwana biyu tsakani da yamma Lis, ina zaune tsakar gida, Kawu sulaiman ya shigo, nayi masa
sannu da zuwa, haka ma baba Talatu. Yayi mata sannu da gida.

Ya dubeni yace.

"Sumayya yau ina tare da Yarima, yace a gaisheki."

Nace"Ina amsawa."

Ya wuce yana yin wani murmushi da bansan musabbabin'sa ba. Ni dai nasan babu yarda za'ayi
wallahi Fa'izu yace a gaisheni. Mutumin dake bala'in jida kan,sa. Ta ina ma ya tuna da
sumayya, a rayuwa? Shekaru biyu fa Kenan rabona da gama makaranta. Kawai bazan iya
k'aryata kawuna bane. Washe garima da Kawu zai fita sai yace min.
"Sumayya yau ma zamu had'u da Yarima da k'arfe uku na rana a club, me zance wa Yarima?".

Nace"Bani da a binda zance masa Kawu."

Yace. "Kikayi haka baki kyauta ba, amma shi yace a gaisheki? amma zan ari bakinki na cimiki
albasa kawai. Ni dai ban tofa ba. A yar tambaya ce ta soma tsayamin a rai name kawuna yake
nufi da son had'a a lak'ata da malam Fa'izu? anya babu wani b'oyayyan al'amari a zuciyar'sa? .

Ture komai gefe kawai nayi na shiga dakon jiran'sa ma na ya dawo nayi masa zancen d'an
fodiyo, domin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login