Showing 30001 words to 33000 words out of 51633 words

Chapter 11 - NI DA GIDANA BOOK COMPLETE BY ZAINAB MAZAWAJE.pdf

kam. Kin hutashsheni ma, na gode Anti Sumayya. Dama na kusa latti wallahi,
wannan yaya Khalifan zai sake b'atamin lokaci. Na gode."

Nace. "Kai Khairat, ina a bin godiyar, ai an zama d'aya."

Cikin mintina kafin ta shirya, na dafa ruwa, ta mik'awa Khalifa nasa.

Ban bata na Ancle Fa'izu ba, nace na a jiye masa, duk da na fahimci ita ke yi masa wannan
aiki, ba kuma fasa bata zai yi ba na sani saboda baya son na yi masa hidima kowacce.

Ni kuma na Hak'k'ak'e aikin ya dawo hannu na duk runtsi.

Da na gama na zuba komai a mazubin da ya dace. Daga Sama na jiyo muryar Momi, nan
nasan ta tashi Kenan.

Na nufi benen domin na gaishe su har Abban.

Amma gyaran muryar Abban da naji yana saukowa daga benen na dakata.

Saye yake da babbar riga babu ta ciki. Nan nasan iya k'ofar gida zai fita.

Na tsuguna na gaisheshi. Cike da farin ciki sosai ya amsa, ya tambayi lafiyata da yarda na
kwana. Ya sake jero adduoi masu kyau
gareni kamar rannan.

"Allah ya shi albarka, ya baku zaman lafiya 'yata." Ba kad'an ba naji dad'in addu'ar nan tasa. Ko
ba 'ace ba,kana ganin sa kaga mutumin k'warai mai karimci. Fara'a Kam a fuskar sa kamar
gonar auduga.

Nasa kai da nufin d'aga labulen mai kauri da ba'a ganin na ciki, na tsinkayi maganganun, kuma
farko Sunana naji an kira, shine dalilin da gabana ya fad'i na kasa shiga, in da maganganun
suka yi ta tururuwar shiga kunne na.

Muryoyin Khalifa ne da momi.

"Sumayyan ai babu laifi Itama Khalifa.Tana da hankali da nutsuwa ga alamu ga ladabi. Gashi
tana karatu, amma banga alamun wayewar banza a tare da ita ba kamar wasu."

Yace.

"Momi, bafa a saurin yabon d'an kuturu, Sai ya mutu da yatsu."

Ta karb'eshi.

"Haka ne Khalifa sai ya mutu da yatsu."

Ya sake cewa.

Momi, ni fa tun kafin ma na ganta na tsaneta. Da na ganta Sai nafi tsanarta. Kallon k'urillama
nayi tayi mata, domin naga me Yaya Fa'izu ya gani, a jikinta har ya zab"i auren'ta, amma
bangani ba, ba kalar auren sa bace ma ko da a kaddarar aure.
Momi kuma naga mai kafirin wayoce fa yarinyar nan, da iya kissa, daga zuwa har ta zama 'yar
gida?anya bazata d'auke miki hankalin d'aba a gaba?".

Da bata ce komai ba ya zarce.

"Momi amma fa Yaya Fa'iz ya kwafsa, kan a bu kad'an yayi wani auren huce haushi, kodai
k'arawa kai haushi, tun da na tabbatar Salima kad'ai yake so a duniya. Laifin mominta ai
bai kamata ya shafeta bako?".

Nan momin tace.

"Shima ai ba Salimar yayi nufin b'atawa ba, nufin sa na kan mamanta, amma dole ita zata fi
kowa jin ciwon hukuncin da ya zartar na yin aure.Nasan labarin bai same ta ba, tun da kaji
shiru.Amma dai ya aikewa da iyayenta katin d'aurin aure, ta yiyu bata ji ba.Nima banji dad'in a
binda yayi ba na zartar da hukuncin yin aure, a matsayin ramuwa. Nafi son sa da Salimar sau
dubu. Babu yarda banyi ba, na hanashi auren nan, amma ya dameni da magiya da lallami,
kullum har Sai da na
saduda.
Ni kunyar had'a ido nake da Salimar ma wallahi. Yarinyar da take mutuwar son'sa, duk in da
d'an uwan sa yake, Sai da ta nemi Sani. Bata gajiya da yi mana d'awainiya, jikinta bai huta ba,
haka ma kud'inta. Amma a ce sakayyarta kenan? Gaskiya Sai yanzu nake jin ciwon auren ma,
bayan anyi. Ko a waya kunyar mu gaisa nake ji. Kasan kusan kullum tana bugowa ta gaisheni."
Khalifa yaja dogon tsaki.

"Dole ma yarinyar nan tabar gidan nan Momi, dole ya sallameta, ko bai shirya ba."

Momin tace"Wani irin furuci kake yi Khalifa? Kai kake auranta, ko kana da wani k'arfin iko ne a
kan mai auranta? ai babu maganar dole, tun da Shima ba sonta yake yi ba, yarda na fuskanta ,
kama hutar da kanka. Idan d'an koli yaci kasuwa, ai gida yake komawa ko?".

Khalifa yace. "Haka ne Momi. Ni dama babbar damuwata, kar ta ritsa dani. Saboda Salima tace
za'ta samomin babban aiki na acounter a kamfanin babanta. Kinga idan auren ta da Yaya Fa'izu
bai yiyu ba, taji yayi auren nan, yaya kike zaton makomata Momi? ni za'ayiwa buk'ulu fa. Ai

dole na shirya
Munak'isar da zai saki yarinyar nan momi, idan naga bashi da niyyar sallamarta da wuri."

Ban tsaya naji me momin zata ce ba, na juya a hankali na sauko, saboda idan na Shiga za'su
tsargu. Idan kuma na ci gaba da tsayuwa, za'su iya fitowa su ganni.

Nayi zaune a d'aki, damuwa duk ta baibayeni. Maganganun Khalifa su sukafi zafafa
k'wak'walwa ta. Bansan zan fuskanci Wata matsala ba kuma a gidan, bayan ta b'angaren Mijina
da nake tunanin ita kad'aice da zan ji da ita.

To A she bayan matsalar da nake da ita ta Mijina, duk gidan ma Ina da matsala da su, babu
mai yi dani a she duk sun fison Mijina da Salima. Gaskiya naga Muhibbat Sai wani fizga fizga
take min. Momi farin cikin Ancle, Fa'iz tace ta fison Salima sau dubu dani. To ko iya nan
matsala ta ta tsaya, ai da aiki gagarimi a gabana. Ancle baya had'a kaunar momin sa da ta
kowa. To ni kuwa da wanne zan soma? ta Ina zan fara? da yaya zan soma warware matsalolin
da suka yi min k"awanya hagu da dama?.

Duk da wad'annan matsaloli dake gabana, amma domin k'arfin hali wai b'arawo da sallama,
Zuciyata Sai rad'amin take da cewa.

Sumayya karki kaya, ba"a sanin maci tuwo, Sai miya ta k'are, kuma mai zabarin nema, yana
tare da nasara, wataran, musamman mai nagarta.

Ni dai nasan, bawai nacin son Ancle Fa'iz ko ya soni, shine babbar matsalata ba. A ra'ayina, a
tsarina, babu a binda nak'i jini irin a ce nayi aure ya mutu, Sannan a ce ma ban dad'e ba. Sam!
ban shiryawa Zaman zawarci ba, ban kuma shiryawa amsa sunan bazawara ba. Domin Muddin
wa'adin aure na da Ancle Fa'izu ya cika ya sallameni, ban isa na goge tambarin sunan
bazawara a goshina ba.

Nasan samarina ma zasu samu labari, suyi min dariya, musamman Usman, da ya tab'a
yab'amin magana da karin magana, yace wai k'arshen a lewa dai kasa ce, suna nan suna zuba
ido kuma, suga k'arshen'ta.

Shi zaton'sa wani mai iko sosai na samu na barshi.

Bayan wani lokaci, na koma na gaishe da Momi. Sam banga wani sauyi a tare da ita ba, sai ma
bangajiya, da tayi min, da cewa, wai taji nice jigon aikin komai, na karin kumallon ranar.

Khairat dama ita ta kwashe komai, ta kaiwa kowa. Nima har d'aki ta biyo ni dashi.

Tace min.

"Anti Sumayya, na tafi makaranta. Fuska ta cike da fara'a nace

"To, a dawo lafiya, K'anwata.

"Khairat, ita ce na tabbatar tana k'aunata da zuciya guda. Kuma nima ta shiga raina, tashi d'aya.

Har lokacin, banga Ancle Fa'iz ba, ya fito daga d'akin'sa ba. Bacci yake ko menene, ban Sani
ba. Kamar na Shiga na gaisheshi, na kasa.

Na had'a ruwan wanka mai zafi dai dai dai, nasa turarrurukan wanka, na rufe da murfin babban
bokitin wankan,mai kyau.

Sai da na gama shiryawa, na zauna a falo, Ina karyawa, Sannan na jiyo muryar Ancle Fa'iz
shida Khalifa a tsakar gida suna magana. Nan nasan a she Khalifa, ba fita yayi ba. Kafin na
farga naji sallamar Ancle Fa'iz. Amma daga bakin K'ofa ya coge, muka
gaisa.

Nace.

"Ancle ga ruwan wankan ka can na kai maka toilet. Nan naga yayi dan jim, kamar bazai ce
komai ba. Ni kuwa nasan shammatar'sa nayi, shi yasa na sashi a kwanar nazarin yarda zai yi
da katsalandan d'in da nayi, na binda bayaso nayi. Wato yi masa d'awainiya ko Wacce iri.
Nace.

"Ancle, Fa'iz kajini kuwa?".

Yanayin sa kamar amsar rashin bukatar hakan zai nunamin, amma sai ya canza niyya, ta yiyu
nauyin ya wofuntar da kyautatawar yayi, ko kuma wani dalilin ne.

Ya shafi, kyakykywar
bak'ar sumar'sa da take a kwance ta soma fesowa, daga askin da yayi mai suna SKIN, da yay
masa kyau kuwa sosai.

Yace. "Naji ki Sumayya."

Daga haka bai sake cewa komai ba, ya tafi. Nasan da bai a mince ba, zai fad'amin ba ya so, tun
da bashi da rufi, ko alkunya.

Naji dadi kuwa sosai da bai gwasaleni ba.

Ranar nayi bak'i sosai. Baba Talatu da Hajiya mariya suka fara bud'e fage. Da Tsokanar wasa
na tarbesu nace.

"Ku kuma tsofaffun nan Sai yau za ku gamo kai, Ku ringid'o kuzo? Ko ku lek'oni jiya? Kuma
naga duk mazajen nan ku ai naga duk sun tsofe, babu sabon jini, sun zama jagwal, ballantana

kuce tarairayar'su tasa kuka kasa lekoni jiya kuka shantake".

Baba talatu tayi jagale tana kallona na shegantakar da nayi musu, nasan kulla kalmomin daukar
fansa ta tsaya yi.








Taku a kullum_

_Zainab mazawaje_

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe


*NI DA GIDANA*





_Zainab mazawaje_


_Best brilliant interlligent writer...✍️_





*Page 14*




Hajiya Mariya tayi 'yar dariya tace.

"Shak'iyyar wofi. Kwana biyu dai munji kunne, da kika yi gaba, yanzu kyayiwa mijinki kuma."

Baba Talatu, tace"Sa'a ma kika yi muka zo yau. Dama idan dad'i yayi wa Mutum yawa, Sai yace
Allah kasheni na huta. Da Kawunki Sulaiman cewa yayi, kar muzo, a bari an d'ebi lokaci tukun.
Kakan kine, ma yace sai munzo mun duba masa ke lallai, duk da dai bake kad'ai bace ma a
gidan, ko menene ai da wasu, amma shine za kiyi mana godiyar mayu ko?".
Naji nauyi, na saddakai k'as nace kuma.

"Yaya Kawuna yake?".

Baba talatu, tace.
"Dama nasan shine a layin farko. To Lfy Lau yace a gaisheki da kyau."

Na yi murmushi kuma nace.

"Allah sarki tsoho mai ran k'arfe, yaya yake, kina kulamin da shi kuwa? (kakana). Tace

"Tace.Ko ke albarka.Lfy Lau yake, yace na gaisheki."

Hira sosai muka yi, daga bisani, na kaisu
wurin Momi. Momi ta karb'esu da daraja kam, suka yi tama hira, har Hajiya Mariya tace da
Momi. Ina Angon yayi, bamu ganshi ba?".

Momi, tace. "Sun tafi ziyarce ziyarce, shida Khalifa, d'azu. Tace"Ai nayi zaton jin za muzo ne, ya
waske, gudun kar muzo muyi masa d'iban Karan mahaukaciya,saboda ya Samu, Sabuwa, ya
ya damu gefe."

A kasa dariya, a tare.momi tace cikin dariya. "Ina zai ya daku, ai da tsohuwar zuma ake magani,
kuma da sabon gini gwara yabe".

Hirar barkwanci tsoffin nan sun Shashi da Momi. Hakan yay min dad'i kam, sosai. Nuriyya tazo
a ranar, kuma da ita muka yi ta tarben bak'i har girke girke, duk da momi ta aiko da nata daron
tace a bawa bak'i.

A Sati na na d'aya a gidan, Ina zaune gaban mudubi Ina taje kaina, Wanda yasha washing da
retourching, yana ta shining ya kwanta lamb'am. Ba kuma wani tsawo ne da shi ba can, iya
saman kafad'ata yake tsayawa. Ina kuma alfahari da a bina a hakan.

Half vase ce a jikina, da under wear na siket iya gwiwa, domin kwalliya na gama nasa
turarurruka na jiki, zan saka kaya na kenan, naji an banko k'ofa da sauri, an shigo. razana nayi,
bawai ga yanayin under wear kawai
dake jikina ba ma, saboda nasan babu mai iya shigomin d'aki kai tsaye haka ba, domin ko
Ancle Fa'iz mijina iya kacin'sa falo, bai tab'a Shiga cikin d'akina ba.

Wanda na yanke tsammanin zai shigo, shid'in ne ya shigo.

Ancle. Sau d'aya ya dubeni, sai naga ya yi saurin juyar da kai, ta yiyu yanayin da ya ganni ne
bayaso idanunsa su sake sauka a kai. Da ya shigo ya wuceni ya isa kan gado, ya zauna.

Na Samu sauk'in razana, ganin shine. Naja dogon Hijab na sallata nasa da sauri domin bansan
me yake faruwa ba, na sake kai duba gareshi, cike da Mamaki. Da ganin'sa kasan daga wanka
ya fito. Silk d'in sumarsa da bata taru da yawa ba, jik'e take da ruwa. Zulaika ce gajera a jikin'sa,
da towel fari, sol, da ya sak'ala a kafad'a. Nace. "Lafiya kuwa, Ancle?" .

Kafin yace komai, k'ofar d'akin da take a bud'e ya tashi ya jawo ya rufe. Sannan
Yace.

"Mutum, domin ya shigo d'akin matar'sa laifine?".

Na girgiza kai.

"Ko kusa, my Ancle. Gani nayi baka tab'a shigowar bane"

Yace. "To, yau na shigo, then so what?".

Nayi shiru, Ina kallon'sa.

Ya sake zama kan gadona, ya cire towel d'in da ya sagala a kafad'a ya ajiye gefe.

"Sumayya, wani a bune ya faru, nake so, Kije falo ki zauna, ko da Momi ta aiko kirana, kice
bananan".

Toh! wata Sabuwa Inji 'yan caca. Kallon da nayi masa galala, yasan tambayace zan masa na
dalili, ya katseni.

"Karki tambayeni dalili. Just ki aiwatar, kyaji komai daga baya. Yanzu babu lokaci, kiyi sauri Kije"
.

Na ja zani zan d'aura, kasan Hijab yace. "Kisa kayanki mana, tun da kin d'ebo. Kiyi sauri
amma".

Bani da zab'i face bin umarnin'sa da nasan zai iya jefani a matsala babba, idan a kasamu
kuskure a ka gane gaskiya. Amma k'arya kuma ba'halin Ancle Fa'iz bace, ko mai amfani ce. Tun
da yau yayi kuwa, nasan da akwai babban dalili, ba kuma k'arami ba.

Na Shiga kici kicin cire Hijab domin saka Kayan da sauri, duk da nauyin'sa da yake zaune a
d'akin yasa nake komai a sanyaye
kuma.Ko Fahimtar hakan da yayi Sai naga ma juyar da kan'sa gefe ya jawo wani littafi irin na
ma'aurata zalla da Nuriyya ta sayomin yana dubawa, kamar na warce littafin, don bazan so ya
karanta ba, amma bazan iya ba, sai na rabu da shi na mai da kai ga abin da ya kawo min
farmaki yanzu, da ana samun a kasi tawa ta sameni.
Ban gama d'aura d'an kwali bama na fito, na jawo k'ofar d'akin na barshi a ciki.

Na fara da kunna kallo, domin Samun Nutsuwar yin basaja.Amma, zuciya ta cike da tararrabi
take, na me yake faruwa. Fatana dai ko maye, kar ya ritsa da ni, wurin yiwa Ancle Fa!iz Mijina
biyayya. Ko minti biyar kuwa, ban cika da zama ba, Sai ga Muhibbat ta d'aga labulen k'ofata
tana daga tsaye k'erere, da jin isar nan da fad"in rai tace. "Yayan yana nan?".
Nace.

"A'a bai shigo ba ai ."

Ta tsuke fuska.

"To, Ina zai Shiga Kenan?".

Nayi tsai, Ina kallon'ta Sai kuma nace.

"Kin duba, d'akinsa baya nan?".

Bata amsamin ba, illa tsaki da taja, ta saki labulena ta tafi.

Na d'an ji ciwon hakan. A binda na kasa tantancewa, ni take yiwa tsakin, ko kuwa rashin ganin
yayan nata.
Bayan mintuna da fitarta na Shiga d'akin na sameshi, a kwance ma yake a binsa. Ya ajiye
littafina can gefe, da alamu ba karantawa yayi ba, ya dan dudduba ne sama sama kawai.

Nace".Muhibbat tazo nace mata baka nan, wai don Allah me ya faru ne?".

Yace.

"Zan fad'a Miki, Jeki d'akina ki d'auko min Kaya marasa nauyi, shirt da jins, ko T. Shirt da troser
da takalmi, da under's, a Kwai sababbi da ban bud'e ba under's, su za'ki d'ebo."

Nace" Tom."

Da na fito a d'arare, nayi sa'a duk suna saman Momi, Ina jiyo hayaniya kuma. Na Shiga d'akin

Ancle, a karo na farko. Gado ne Kawai da kwabar zuba Kaya,set, da kujerar zama guda daya.
Na bud'e kwabar, duk na d'auko Kayan da ya sa na d'ebo. Wasu Kayan duk a hargitse, bayan
da gogaggu a ciki. Nafi zaton wurin neman wani abu ya hargitsa.

Da na kawo masa, na d'ebo mayuka da turarurruka na jiki da na Kaya, da comb nawa. Domin
ban d'auko nasa ba.

Yace"Sumayya kwashe turaren nan, banasa turare mai k'arfi, Sai mai sent, cool, irin nawa.

Nace. "To" .
na kwashe.

Na fito na barshi yana shiryawa. Da na fuskanci ya gama na kai masa Karin kumallo d'akin. Tea
da soyayyan plantain ne da k'wai da Khairat ta kawomin.

Ya juyo yana mai gyara botton d'in riga yace.

"Ke me zaki ci, da kika kwaso Break fast d'inki kika kawomin?".

Nace. "Ancle, ai yayi min yawa dama, na Mutum biyu Khairat ta kawo."

Yace "Duk da haka, Kije ki karya, idan yayi Miki yawa kikai kichean a ba mabuk'aci. Ni a waje
zan karya ma."

Ba haka na so ba, na maze amma, saboda na soma karantarsa, idan yace Bazai yi a buba, to
fa a rabu da shi kawai. Na kwashe kayan da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login