Showing 48001 words to 51000 words out of 51633 words

Chapter 17 - NI DA GIDANA BOOK COMPLETE BY ZAINAB MAZAWAJE.pdf

da nan
Ya juya kan mota, ya canza hanya Sannan ya k'ara speed, Sai gamu a babban wani fili babba,
har da wata mata ma da mijinta, Itama tana koyo.

Ancle ya nunamin komai a hankali, da yarda zan yi komai. Kamar wasa ya bani kan motar, ko
tsoro bai jiba, yace na jarraba, amma yana kusa dani a gefena. Kafin na soma yace" Sai kin sa
nutsuwa sosai fa, kuma ki cire tsoro, idan ba haka ba, zaki jima baki iya ba."

Tiryan Tiryan da na bi shawarar Ancle na kuma bi yarda ya nunamin komai, Sai gashi ina tuk'in
motar sannu a hankali, saboda nima nutsatstsiyar ce ga saurin daukar karatu.

Sai da ya sani nayi round biyar na tafkeken filin wurin.

K'arshe yace.

"Sumayya, Stop the car."

Da na tsaya cak, yace.Na tsaida mota a hankali.

"Kin burgeni gaskiya. Nasan duk in da muka sake yin fita uku ko biyar zaki iya mota. Abinda ya
rage Kawai zai rage miki, hawa titi da lunguna, kinsan Shima training d'insa, dabam yake da na
filin wuri irin wannan.

Yanzu ki mai damu gida."

Na zaro idanu "Daga koyon farko? baka tsoron na tintsirar da kai a hanya. d'an Murmushi
kawai yayi, bai tanka ba, ya karb'i kan motar.

Tun daga ranar kullum Sai mun fita a mota nida Ancle Fa'iz saboda koyamin mota. Mu kanyi
yawace yawace kuma sosai a mota, bayan mun gama da komai. Bantab'a Samun farin ciki ba,

zuciya ta ta rink'a haske tun da na auri Ancle, ba kamar na lokacin. Domin mun sake da juna da
hira da annashuwa fiye da ko Yaushe. Amma dai har lokacin bansan matsayi na ba wurin Ancle
Fa'iz. Ko da wasa banga alamun wai sona a tare da shi ba, duk da kulawar da yake bani fiye da
baya, da kuma hira ta nishad'in da mukan yi.
A k'arshe dai nike Jan mota na fita damu na dawo da mu. Har takai ma yakan bani mukullin
motar na fita, ni kad'ai a cewar sa, da haka zan k'warance. K'iyayya sosai kuma mai zafi, na
ganta a wannan k'arni, tasu Momi da 'ya'yanta, amma nayi biris.

Da muka koma makaranta, Ancle ni ya bawa mukullin motar nake zuwa makaranta da ita. Shi
ba kullum yake hawa, bai fi a Sati sau biyu ko d'aya ba. Domin idan ba wuri mai nisa bane, ya
gwarace ya hau babur. Shi yasa motar kamar tawa. Idan Zai hau Sai dai ya karb'i mukullin a
hannu na.
Nan ma, Ina wuta a jefani. K"iyayya ta ninka ta baya. To na lura Momi, kamar batason b'acin ran
Ancle Fa'izu ma.Domin ran nan na gaji da fitintunin da suka yawaita Saboda hawa motar Ancle
Fa'iz. Na Shiga d'akinsa nayi sauri na ajiye masa mukullin motar, na fito da niyyar na Shiga
motar haya. Ashe Ancle ya ganni, Sanda na a jiye. Ya d'auko da sauri ya biyo ni, in da ya kira
suna na na tsaya cak a tsakar gida. Yace "Banace kibar mukullin motar ko yaushe a hannunki
ba? Me kike nufi da ajiyewa? Kina nufin motar haya zaki Shiga? Kuma idan zan hau, ai ina yi
miki magana ko? banason fa kike min gaddama".

Karab a kunnen Momi, dake shirin saukowa daga bene dama jin muryoyin mu, ya Sata
saukowar.

A fusace tace "Wai Fa'iz, motar nan kan ka ka sayawa ko Sumayya?"

Nan naga fuskar Ancle ta d'an sauya, zuwa ga yanayin jin zafin furucin Momi, amma a tausashe
yace.

"Momi ko kaina na sayawa, ai kamar iyalina na saiwa. Guntun gatarinka kuma ai yafi sari, ka
bani. Rufin a Siri ce motar gida, domin tafi Shiga motar haya sau dubu ni a wurina."

Nan naga Momi tayi shiru ta kasa mayar masa da martani. Ya Mik'omin mukullin motar na amsa
a tsorace.

Domin kuwa Momi tana da k'arfin iko kan d'anta da zatashi, yayi duk a binda taga dama. Na
lura, a Kwai dai a binda yake taka mata burki a yanzu.

Kwana biyu rak da faruwar wannan, Ina zaune da yamma Lis, Ina karatun littafi, gefe a hannu
na biscuit ne short bread, Ina ci a hankali. Saye nake da Kaya English wear masu kyau, masu a
don fari da bak'i na nad'e kaina da bak'in yanki nayi rooling d'insa, gashin kaina da nayi parking
ya fito tsakiyar rolling d'in da nayi ya bayyana saboda ya kara cika da yawa ma sanadin kulawar

da nake bashi fiye da baya.

Khalifa ne tsidim ya fad'omin falon, babu ko sallama. Bai tab'a shigowa ba Sai ranar

"Ina mukullin mota?"

Yace dani yana shigowa.
Na dubeshi a hassale.

"Wace motafa?"

"'Kuji mu da 'yar rainin hankali, a kwai wata mota, bayan ta yaya Fa'iz?"

NayI masa kallon tara saura kwata, na bawa banza a jiya, na ci gaba da karatun littafina.

Ya kunnu sosai "Wani salon wulak'anci kika fito da shi na share mutane? wai kin samu rana har
da baje shanya? . Na d"aga masa hannu

"Kaga Khalifa, ja tsummar rayuwarka ka b'acemin da gani. Bazan bada mukullin ba, Sai naji
shak'a na suma na farfad'o tukun. Baligi kamarka a ce bakasan hak'k'in Shari'a ba, ka shigo min
d'aki kai tsaye babu ko sallama,Sai kace ba d'an musilmi ba."

A harzuk'e kamar ya kaimin naushi yace.
"Ank'i a yi sallamar, gidan ubanki ne.?" Yana fad'in haka Kawai naga ya fad'amin d'aki . Tuni
nasan aikin gama ya gama, domin mukullin kuwa ya d'auko, saboda a kan teburin mudubi na a
jiye. Ya fito rik'e da shi Yana karkad'awa cikin jin Isa . Ya. jamin tsaki ya Fice.

Na dad'e zuciya ta tana ta tafarfasa saboda d'iban albarkar da Khalifa yayi min. Bayan gasa min
magana, ya shigemin uwar d'aka sirrina yayi bincike saboda mukullin mota. Naci alwashin duk
runtsi zan hak'ura da motar nan na zauna lafiya.

Ancle Fa'iz yana shigo min, ko zama bai yi ba yace "Waye ya fita da mota, banganta ba a
farfajiyar gida?".

A tak'aice banja da tsayi ba, nace "Khalifa ne"

Wani irin kallo Ancle yayi min kafin yace cikin fushi.

"A wani dalilin zaki bashi mukullin motar? to karki sake bashi, na fad'a miki."

Fargaba ta afkuwar rigimar da bansan iyakacin ta ba, da kuma ni zan zama a bar zargi, shi
yasa na marairaice nace "Haba my Ancle, d'an uwanka nefa Khalifa, smma a ce bashi da isar
amfanarta?".

Yace "Domin yana d'an uwana Sai a kace wajibi Sai yayi iko da a bina? Kuma babu izinina? For
what reason?.

Zan ci gaba da lallashin sa, ya d'agamin hannu.

"Sauraramin Sumayya, babu ruwanki. Ya numfasa Sannan can yace "Wannan yaron Khalifa
bashi da mutunci da kike gani. Wai ni zai dubi tsabar idona yace Wai ba girma na bane a ce
matata tana hawa motata. Kenan nine dai dai da shi, da zan hau mota ya hau mota? to Wallahi
bai isa ba, zai zo ya sameni Sai na Sab'amasa."
Duk yarda naso na lallashi Ancle gudun afkuwar rikici, bai ma tsaya ba, ballantana ya saurareni,
domin ya hau taken nasa , Sai yarda hali yayi. (Zuciya). Na dafe kaina cike da fargabar a binda
zai biyo baya kuma.

A daren ranar dai Ancle Fa'iz yazo ya sake dank'amin mukullin motar. Baice komai ba, kuma
naga ransa a b'ace . Gudun kar na k'ara masa damuwa yasa na jinkirta fad'a masa k'udirina na
hak'ura da motar, Sai washe gari.
Amma kafin nan, Momi ce ta katsemin hanzari. Shigowa tayi Itama kai tsaye falona tana huci.

"Munafuka, algunguma, kara da kiyashi. Ungulu da kan zabo. Dama masu iya magana, sunce
idan belbela ta samu dama Sai tace masar ne garin ubanta. To Wallahi ba ki isa kisa 'ya'yana
gababa. Tun da suke ko musayar yawu basu tab'ayi ba, amna sanadinki Fa'iz yaci mutuncin
Khalifa gaya, akan mukullin motar da ba daga gidan ubanki kika zo da ita ba. To bani mukullin
motar,ni na k'wace, ki turoshi nima yaci zarafina ya karb'a. Idan bakiyi haka ba, to baki isa
k'aramar shaid'aniya ba ma kanwa kuma uwar gami."

Momi tak'i tsayawa taji mafarin komai saboda rashin a dalci. Iya cin zarafi tayi min a ranar,
bayan ta karb'e mukullin motar. Bansan iya adadin zagin da a kayiwa ubana ba a gidan nan.
Ubana da yake kwance cikin kabari baisan hawa da sauka ba. Wannan shi yafi komai soya min
zuciya. Na kifa kai na Shiga razgar Kukan da bantab'ayin sa ba, tun da nazo gidan.
Menayiwa Momi? ta Ina na kuskurota?.menene Laifina a kan mota kuma? Tambayoyin da
najerowa kaina Kenan, bayan naci kuka na k'oshi. Kyautatawa da biyayya,ninninkawa nake a
b'angaren Momi fiye da kowa, saboda son da nakewa d'anta. Hakan yasa take da Wata daraja
ma mai tsada a Zuciyata. Amma gashi duk a binda nake, Momi bata k'aunata. Nina lallashi
kaina, saboda bana so Ancle Fa'iz yazo ya tuhumi sanadin damuwa ta, kuma ni bazan iya
duban cikin idanun'sa nace Momin sa ta b'ata min ba. Bazan iya ba.

To takaicin bi da bi, ya rink'a zuwar min, kamar Wacce iyaye suka yiwa baki suka ce Jeki kin
gani. Domin bayan fitar Momi da kamar awa d'aya, Sai ga Ancle Fa'iz ya shigo min Shima,
ransa a b'ace. Na dad'e banganshi cikin b'acin rai ba, irin haka, ko nace ma ban tab'a gani ba.
Kuma wuri ya zauna yayi shiru Kawai. Na lura bai kula da yanayin damuwar da nake ciki ba. Na

daure nace "Ancle Fa'iz lafiya kuwa kake? Wani a bu yana damunka ne?"

Ya d'aga idanu a hankali, ya dubeni.

"Zuciya ta ce take ta kai kawo, tana ta jimamin yarda na rasa matsayi tashi guda a wurinki, da
zan baki umarnin kiyi a bu, amma ki k'iyi.
Ya numfasa tukun ya d'ora da.

Nace kar ki sake bawa Khalifa mukullin mota, amma shine kika bashi. Yanzu na shigo na ganshi
yana gyarawa mota parking, da alamu dawowar sa Kenan daga yawon da ya tafi da ita.
Zamana kike Sumayya, amma kika fifita farin cikin wani da nawa. Kika zab'i biyayya da
kyautatawa ga wanina,da bashi da gurbin da ya can can'ta kiyi masa haka Sama dani. Why?" .
Ya k'arashe furucin cikin kasalalliyar murya.

Na sake Shiga kam, sabon rud'ani. Ta yaya zan wanke kaina ga Ancle ba tare da kawo laifin
Momi da na tabbatar ita ta sake bawa Khalifa mukullin motar da ta k'wace a hannu na ba.
Tabbas, ko zan sanar da Ancle Sai ta hikima da tausasa kalamai, saboda kar na fito da laifin
Momin sa a sarari, da ko bai nuna jin zafi ba, ni bazan ji dad'i ba. Sai dai ina bud'e baki zan
soma magana, ya katseni a harzuk'e.

"Look kar kice dani, komai,domin bazan yarda ma dake ba, adana yawun bakinki karki yi
asarar sa a banza".

Ya tashi ya fice a binsa,bai kuwa sake lek'oni ba a ranar.

Hawayen da na tsayar, su na ci gaba da zubarwa. Da nawa zanji a cikin'su. Momi zargina take,
Khalifa ma, haka, ga Uban gayyar ma, yazo min da tasa tuhumar. Kuma ta Ancle tafi tayar min
ma da hankali. Ji nayi Sam,bazan iya juriyar da nake zato zan yi ba,na jure duk rigimar da zata
tunkaro, saboda Soyayyar da nakewa Ancle Fa'iz da tasa nake nacin son zama da shi, duk da
bai nuna a aikace, ni matar'sa bace, face 'yar tayin zama Kawai.idan so cutane,to hak'uri ance
magani ne. to zan d'au hak'urin kawai,domin na zauna lafiya. Bazan yarda da k'uruciya ta ba, a
gadar min da ciwon zuciya.Tak'i kad'an zan k'ara, idan naga a bin yaci tura, zan bar musu
gidan'su Kawai. A she kuwa gab, yake da yaci turar. Wasa ma farin girki a she, matsala na
gaba.

Dai dai k'arfe uku na dare, Khalifa ya sad'ad'o ya shigo min d'aki, bisa ga tsautsayi na sabon da
nayi na rashin rufe k'ofata da mukulli daga ciki, Sai dai na tura ta Kawai, ga kuma fahimtar da
Khalifa yayi, Ancle Fa'iz baya kwana a wurina. Wannan shi yasa ya samu nasarar yin a binda ya
k'udurta a sauk'ak'e. Fitila ya fara kunnawa da ya shigo, haske ya gauraye d'akin Sannan ya ta
sheni, ta hankar bubbuga filon da na d'ora kaina a kai. A tsorace na tashi. Na sake tsorata sosai
da ganin Khalifa a kaina ya zubomin idanu. Na bazama na jawo softcotton blanket da na a jiye
gefena, saboda irin Kayan baccin dake jikina na shan iska ne, saboda zafin da ake yi, a tsukun.

"Lafiya? Khalifa me ya kawoka d'akina cikin dare? Cikin hankalinka kuwa kake?".

Ya zaro min idanu, irin na tsoratarwa.

"Na fikima wadatar hankali Sumayya. Ramuwa ce Kawai ta kawoni d'akin nan, saboda wai
saboda ke Yaya Fa'iz ya cimin mutunci, cin mutuncin da ba'bu mahaluk'in da yayi min irin'sa.
Nasan kuma ke kika zugoshi, to Wallahi kinyi kuskure babba,domin ni ba a takani a Sha!."

Wani irin tsoro ya kamani sosai, domin zatona Wata illar zai min, ko ya hallakani. Muryata na
rawa nace.
"Khalifa, amma Sai cikin dare za'ka yi ramuwar? idan gari ya waye Kayi min komenene, amma
don Allah banda yanzu."

Yace "Ina! ai Wallahi baki isa ba, yanzu zan rama. Ramuwar gayya tafi ta gayya ciwo. Ciwon da
naji a zuciyata Sai na ninninka miki irin'sa. Ki bani had'in kai, na 'yan mintina ne zan idar da
nufina na tafi, idan kuma ba haka ba, zan k'ulla miki sharrin da babu mahaluk'in da zai iya
wankeki a duniya? sai kowa ya tsaneki, ni da yaya Fa'iz Kawai kika had'ani, ni kuma Sai na
had'aki da kowa kin zama a bar k'ya mata.mintina gomz sun isa na ida nufina na tafi, don ba yi
min kika yi ba, kawai domin na cuceki ne, na kuma sake nisantaki da Yayana".

Tuni na d'au hasken me Khalifa yake nufi,na kuma girgiza da mummunar manufar'sa, da ya rik'a
a matsayin ramuwa. Nace

"Wallahi Khalifa bazan aikata aikin ashsha ba, ban aikata ma a baya ba, Sai yanzu da nake da
nauyin hak'k'in aure a wuyana? ni ba halina bane. Na yarda kayi min kowani hukunci idan
kalmar hak'uri bazata ceceni ba, amma banda wannan manufar taka"

Yace "Ai ban baki zab'i ba. Kuma ramuwa fa nace zanyi, kuma ramuwar mugunta ai a binda
Mutum kasan yafi k'i shi za'ka yi masa ka huce. Kuma nasan mijinki ma, duk da baya sonki, zai
tsaneki ya sakeki take, idan ya sa ni." Yana fad'in haka naga ya nufoni, ya fado gefen gadon
kusa da ni.
Nayi zallo gefe a zabure.

"Wallahi zan fasa K'ara na tara Maka jama'a".

Yace

"Haka na fiso ai ki tara Mana ma mutane." Ya nufoni gadan gadan, ya kai min wata
mahaukaciyar cafka. Na zille cikin zafin nama

Na kuwa daddage na fasa wata irin k'ara cikin kad'aitaccen daren. Na kuma fasa ta biyu da tafi

ta farko sauti. Sai naga Khalifa ya tsaya cak.

Ancle Fa'iz ne kuwa farkon shigowa, saboda d'akin'sa yana dab da nawa, dole yafi kowa ji. Da
Khalifa bakin k'ofa yaje ya tare, domin kar na fita, Amma ganin shigowar Ancle, Sai yaja gefe
guda, ni kuma jin Ancle ya kira Sunana yana shigowa falon da sauri, na antayo daga d'aki,
bayan naja wani mayafina dake jikin hunger na lullub'e k'irjina. Yarda na taho karta na nufo
Ancle Fa'iz Sai a zaci jikin'sa zan fad'a, Amma Ina zuwa Sai na tsugune k'as a gaban'sa Ina
kuka. Ancle naga ya Shiga wani irin rud'u da yaga Khalifa, ya juyo da kan'sa ya dubeni. Ya zuba
Mana idanu Kawai, ya dubeni, Sai ya dubi Khalifa kuma. Can yasa hannu ya d'agoni daga
durk'uson.
"Ihun me kike yi? Me ya faru? Me yasa naga Khalifa a d'akin'ki?

Kafin na iya amsawa Sai ga Muhibbat,da khairat sun shigo, ai Sai na sake Shiga d'imuwar rasa
ta Ina zan fara, saboda kunyar Jama'ar da suka soma taruwa, kuma duk Jinin Khalifa.lokaci
guda naga idanun Ancle sun sauya kala, sun yi jawur, Sai a zaci ba'ainihin kalar su fari fat bane,
masu bada launin shud'i shud'i.Khalifa kuma Kawai yake kallo cikin sauyayyen Jan idanun.
Cikin tsawa yace masa.

"Me ya kawoka d'akin Sumayya? giya kasha, ko wiwi, ko kuma hodar iblis, fad'amin."

A dake ya amsa."Sumul nake. Kuma idan Ina shan d'ayan su, ai kaine shaidar farko, Yaya
Fa'iz."

"Karka fad'amin Maganar banza, idan ka tashi shan, Sani zanyi? Fad'amin a binda ya kawo ka
d'akinta, ko nayi Maka illar da bazaka moruba Wallahi."

Bud'ar bakin Khalifa.

"Gayyatoni tayi da kanta. Kuma batun yau ta soma gayyatata ta ba, saboda tace wai baka
sauraronta, baka bata lokacinta, irin na mace da Miji yau ma bore nayi mata, nace zan fallasa
komai, shine tayi ihu, domin reshe ya juye da mujiya."

Muhibbat ta d'au salati, amma wani sakaran kallo da Ancle ya jefa mata, Sai ta d'inke bakin.
Khairat dai bata ce komai ba, illa tagumi na tsantsar damuwa. Da k'yar na samu wani k'ololon a
bu ya fad'amin da ya tsayamin a k'ahon zuci, saboda Shiga firgicin jin sharrin da Khalifa ya
kallafamin.
"Wallahi Ancle K'arya yakemin. Ina kwance na ganshi a tsaye a kaina....

Khalifa ya katse da sauri.

"Ta d'an a dam za'kiyi min? Saboda kina tsoron hukuncin da zaki fuskanta?"

Na sake fashewa da kuka. "Kaji tsoron Allah Khalifa...."

Ya sake katseni."To, tsoronki zanji idan banji tsoron Allah ba? ai tsoron Allan yasa na zab'i na
Toni a Siri komai yazo k'arshe."

Shigowar Momi dai dai nan yasa na sake firgicewa, domin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login