Showing 21001 words to 24000 words out of 51633 words

Chapter 8 - NI DA GIDANA BOOK COMPLETE BY ZAINAB MAZAWAJE.pdf

ba kan wani namiji ba. Gashi na jawa kaina, muna fuskantar juna bare na kub'uce,
gaskiya macen da za ta iya kubuta daga tarkon shauki ko kaunar Ancle faiz ba ace babu ba,
amma zai wahalar, sai dai wacce ba a halitta da shaawar son da namiji ba.
"She is doing fine. Yace cikin dan sakin fuska.

Na barota lafiya Lau. Amma yaya kikasan Momi?".

Nace.

"Tun da nasan'ka ai dole na San'ta"

Yace"A'a ni kad'ai kika sani. Ita dai kinji sunan'ta wurin Sulaiman. Any way, naji dadi da kulawar
ki a gareta." Sai naga ya dan kara sakin fuska kadan.

Karo na farko kenan da na tab'aji ya nuna jin dad'i a a binda a kayi masa a sanina.

Gudun kar na kuma laifi, nayi saurin cika cup da lemon maltina mai sanyi na mik'a masa.

Kafin ya karb'a yace.

"Lady Kinyi karatun ta nutsu Kenan!. Ban tanka ba.

Ya Mik'a hannu ya karb'a, Amma bai shaba, ya Shiga juya d'aya kwalbar lemon da ban bud'e
ba.

"Yaya a kayi, kika San Ina son lemon malt?.

aikin Sulaiman ne dai na sani".

Idanun'sa na kan lemon yake surutan.

Ya shanye, ya sake cika cup ya shanye. Ya bud'e d'aya kwalbar ya cika cup ya Sha, ya a jiye
ragowar a gefe.


"Da k'ishirwa na iso, Sai kika samu ladana kika yi a binda ya dace. Ina son maltina sosai a
rayuwata. Na kansha kwalba uku ko hudu wurin training ko gasar boll."

Nace.

"Lallai kana son"ta da yawa."

"Ke baki son'ta?" .

Yace.

Nace.

"Kadai d'arsa min son'ta, ga yarda ka damu da ita."

Yace cikin wani lumshe idanu kan kwalbar lemon.

"Look, ki fad'i opinion d'inki Kawai, ba ruwan'ki da zab'ina ok? ".

Naji rashin jin dad'in gwaliyar da yayi min,
amma Sai na danne.

"Domin na tayaka son a binda kake so laifine.?"

Yace.

"Kuskure ne dai, saboda ra a yina da bam naki dabam, banga dalilin da zai sa ki tayani son
wani a bu ba, don ni bazan tayaki ba anan zance na fisabilillah, iya nawa zan tsaya, kinga kuwa
bai kyautu kiyi min kara ba, gaskiya ni kullum ba na boyanta bayyana ta nake, ko da kuwa kowa
zai tsane ni, i don't care".
Kafin na wartsake daga wannan ya jefomin wani.

"Sumayya wai addu'a kika yi min ne?".

Na waro idanu waje.

"Wace addu'a zan yi maka ni kuwa Ancle Fa'iz?".

Yayi harr da idanu ya sake kafeni da irin kallon d'azu, jin furucina

"Wallahi da da na tafi, naci alwashin bazaki sake gani na ba, saboda gidadancin da kika
nunamin. Amma bayan few days, Kawai Sai samun kaina naji Ina son waiwayarki kuma, kuma
zuciyata ta nuna min fin karfin sani sai da nazo ba domin na niyyaci zuwan ba, naga kin canza
yau, kina d'an tab'uka abu. Kenan komai da kika yimin rannan kina sane Kenan.?".
Bani da amsa, idan ma a Kwai bazai jiba. shi yasa na zab'i yin shiru.

"Kin a mince zaki jure irin Zaman aure N'a? ".

Samun kaina nayi da juya idanu na rausayar

"Zan jure man, tun da na iya jure zafafan bulalanka goma, masu ratsa k'ashi da tsoka."

Sai ya d'an d'aga idanun'sa Sama, mai nuna a lamun ya tuno komai. Sai yayi dan murmushi da
banyi zato ba.

"A shefa kin tab'a fad'owa tarko na ko? amma wannan shafar mai ne, idan kika yi saken da kika
sake fad'owa tarko na. Kinsan yanzu matsayi uku zan had'a a wurinki da an shafa fatiha.
Malaminki nake, Sannan Ancle,Sai na gaba mijinki.".

Da hannun'sa yake nuni, ta hanyar lank'wasasu.

"Haka ne?".

'Yar dariya na saka.
Yace.

"Zakiyi ta gasken ne"

Ya tattaro, Nutsuwar'sa.

"Ina so ki fad'amin nawa zaki buk'ata na shirin auren'mu na biki, domin na tanadeki , banason
auren nan ya wuce Wata guda fa. "

Da hanzari, na dubeshi. Duk nasan saboda manufar sa ne,da yake so ya cimma. Wani zafi, naji
a k'irjina.

Eh, ga 'yar tsana ka samu, dole ka gaggauta.

A raina na fadi, saboda nasan ban isa na fadi a fili ba mu kwashe lafiya.

"Barshi, na yafe. Ni babu shagalin da zan'yi."

Ya jefa min kallon hadarin kaji.

"Kija Mani zargi ko? to bazai yiyu ba. Bazaki tozarta min aure ba, ko ba kya Sona , kuma ko
banason'ki za'ayi shagali irin Wanda ya dace. Kije kiyi nazarin adadin kud'in da zakiyi amfani da
shi. Idan na dawo naji. Dole ne , kima saddak'ar."

Shiru nayi, jin zai soma hawa dokin zuciyar'sa da nake tsoro.

Bayan sa'oi kamar mai wani tunani sai kuma ya dago kai gareni da nayi shiru cikin kafeni da
idanun'nan nasa masu narkar da zuciya.

"Kiyi min magana ko?"

Nace.

"Zan fad'awa Kawu Sulaiman, idan na lissafa."

Ya kwaikwayi salon yarda na furta.

"Zan fad'awa Kawu Sulaiman idan na lissafa. To Wai meyasa zaki nuna bam bamci tsakanin ni
dashi? Nima ba kawun bane?".

Da nayi shiru, ya tafa hannun'sa a hankali, ya kuma dunk'ule.

Shikenan 'yar gidan Kawu Sulaiman, Sai naji daga gareki."

Ya ci gaba da lissafomin irin shirin da ya soma na auren. Lefema da Sadaki, da kud'in aure yace
rana guda zai kawo. Kenan Ranar d'aurin aure Kawai za'asa . Yarda yake nuna a fuwa da
komai, Sai a zaci, wani auren soyayya za muyi da shi, na an matsu da juna. Bayan nan bana
gaban'sa na Sani, ko na sakan na a gogo. Manufar'sa ya d'anawa k'ahon zuk'a.
Fargaba d'aya nidai ta ragemin, shine kar a zal ta fad'amin Ancle Fa'iz ya samu damar yi min
cuta ta k'arshe. Shine burin'sa Yana cika ya sakenj, nazo na bud'e faifan Zaman zawarci. A
binda nafi tsana Kenan a rayuwata, zawarci..

Jinake yi, har gabana na yankewa ya fad'i idan na tuno.

Nina shirya had'uwata da Nuriyya domin taji labarin da zai kid'imata. Wato na aure na da Ancle
Fa'izu. Mutumin da ta k'wallafarai a kan'sa kamar ta zautu, wai yau shi yake shirin aure na. Inda
a ke neman'sa yayi b'atan dabo..

Ko da yake batasan waye Ancle Faiz ba dangane da halayya, da ko daura mata a kayi sai ta
kwance, duk son da take masa ba za ta iya da halayen sa ba, saboda ita ba ta da hakuri, ga
tsiwa. Ai a guje za ta raina kanta, ta ce ba da ni ba.






_Taku a kullum_





_Zainab ilyas mawaje_

Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe



*NI DA GIDANA*




_Zainab mazawaje_


_Best brilliant interlligent writer_...... ️





*Page 10*

Nuriyya kuwa ta girgiza da jin komai. Nasan baza taji dad'iba, tun da ta nunamin irin son da take
yi masa a baya. Sai dai bani da zab'i face dole na fad'a mata, tun da babbar a miniyata ce dole
taji. Ban sanar da ita sirrin komai ba, na dai ce Kawu Sulaiman ya had'a auran, amma ni a
fargaba nake.idanunta naga yayi rau rau.
Tace"Sumayya al'amarin ubangiji ya shallake tunanin bayi. Tsakanina dake a wannan lamari
addu'a Kawai, to yaya zanyi? bani da yarda zanyi Sumayya."

To nima d'in dabara ta kubce, bani da yarda zanyin da na barmata, toma idan zan iya barmatan
uban gayyar karba zai yi?

Dani da itan da take azabar son sa
duk rukuni guda muke. Babu Wacce ta rabauta da Soyayyar'sa, Sai ni da k'addarar auran'sa ta
sauka a kaina.

"Ni haushi kike bani da kike Kiran wai kina zullumin auren'sa.

Kamar wannan zuk'ek'en saurayin za'a nok'ewa auran'sa?

Wallahi da motsi a cikin kan'ki, ba kalau kike ba koma ba na gari bane, ke dai ko baki tashi da
ribar komai ba, kika tashi da ribar kyawawan fararen yara, ai kin gama da shi. Kasuwa ta
tashima ai d'an koli yaci riba".

Ni kam haushi furucin'ta ya bani. Ana ga yak'i tana ga k'ura.

"Inaji ganin jarabarki ta son kyau da fari, Sai kin auri maye, nasan ko kinsan mayen nema
auren'sa za ki yi ".

Tayi 'Yar dariya.

"Tabbas!. Ko zai rink'a lasar kurwata kullum Ina suma na farfad'o zan aureshi in dai irin Ancle
Fa'izu ne."

Na jinjina furutanta.

"Al'amarinki Sai dai neman sauk'i Nuriyya, amma ba waraka ba."

"Bani buk'atar warakar Dama".

Tace, ni kuwa binta nayi da kallon mamaki kawai.

Akwatu Shida set da kit d'aya Ancle Fa'iz ya had'o min na lefe. Ya zuba abubuwa kuma gaskiya
masu tsada fiye da zaton kowa.

A tamfofi Holand manya guda goma ne. Bayan masu matsakaitan kud'i goma. Lesuna masu
daraja guda goma ne. Shaddodi da material ma sunyi . Hakanan Takalma da jakunkuna babu
masu rangwamen kud'i. Sai a jakar Kayan sarkoki' za'a sha kallo. Duk da babu gold, Sai da aka
zab'a a ka darje wurin zab'o k'ayatattun sark'oki na cinyewa, launi launi. Tilas a ce isashshiyar
mace da tasan kan sirrin iya ado da kwalliya ta zab'o.

Ni dai Abin yayi matuk'ar d'auremin kai, na yarda ya narkar da kud'i irin haka a auren da yafi
kowa sanin manufar'sa da makomar'sa a gaba.

Hajiya Mariya tafi kowa, murnar zuwan aure na, inda tayi ta kod"a lefen tana labartawa ga
wad'anda basu gani ba, tamkar kaina farau, kuma k'arau. Haka ma 'yan uwan uwa da ubana
kowa Sai Sam barka da Fatan alkhairi.

Sati hud'u a kasa d'aurin auren. An tasheni tsaye an kuma tashi Kawu Sulaiman tsaye da
kakana. Domin duk basu shirya ba suma, saboda basu zaci zuwan aurena a tsukin ba. Amma
Kawu Sulaiman naga ko a jikin'sa. Murna yake sosai da zumud'in zuwan auren . Kuma dama
komai Ancle Fa'izu yace ga yarda yake so a yi a kan aurena da shi, to ta zauna. Shi yayi ta
nacin kar a d'aga bikin ma kamar yarda kakana yaso, saboda yasan Yariman nasa, bazai so ba
Sam!. Ashe kawu Sulaiman yayi tanadin'sa na aure na. Duk da yace min, suna Samun kud'I, shi
da Ancle Fa'izu yanzu sosai a kan da a harkar boll, musamman ma Ancle Fa'izu da ya zama
shine champion d'in su, duk yafi su Samun kud'i Amma na jinjina komai sosai da yayi min.

Hidimar Kayan d'aki da komai shine mai kaso saba'in cikin d'ari a cikin 'yan uwa. Cikin
hukuncin Allah komai anyi min na fita kunya. Ko saboda maraicina ne hagu da dama yasa kowa
ya k'ure kan'sa wurin hidimtamin?.

Bayan d'aurin aure na da Ancle Fa'izu da safe naji komai ya fice a raina.

Jikina yayi sanyi, domin na tabbatar na Shiga hannu, Sai yadda ta kaya dani kuma.

A cikin wannan yanayin, Ina cikin k'awayena uku, da 'yan uwa Ancle Sulaiman ya turo yana
kirana. Na Shiga d'akin'sa da sallama, yana zaune gefen katifa, ya nunamin kusa da shi daga
gefe yace.

"Zauna, Sumayya, magana nake so muyi."

Na zauna, na juyar da kaina gefen k'ofa da mutane suke wucewa 'yan uwa, Jifa Jifa, daga
zuwa cikin gidan, ko daga ciki zuwa waje, saboda k'ofar d'akin bud'e take, ana hangen Mu.

"Yaya naga baki da walwala ne? Kina da Wata damuwa ne, Sumayya.?".

Nace muryata tana rawa.

"Allah Ancle banason nayi nesa da kai. Wallahi auren ya ficemin daga rai. Bazan iya jurar na
wayi garin Allah banganka ba, kawuna. Don Allah ka taimaka a sahalcemin auren nan."

Yayi murmushi, ba tare da ya nuna damuwa da furutaina na sokonci, da kuskure gami da
wawtaba.

"Sumayya, hak'uri zakiyi. Ko ba jima ko ba dad'e dole Mu rabu Sumayya. Babu yarda za'ayi Mu
dawwama tare.Aure shine cikar darajar mace, shi yasa nafi kowa farin ciki da auren'ki. A yau
zan cika alk'awari na fad'a Miki dalilan da yasa na aura Miki Ancle Fa'izu, ko kya rage damun
kan'ki, kafin kiga zahir kema da idanun ki ki tabbatar..
Yarima Mutum ne mai gaskiya kuma kaifi d'aya ne a magana, bashi da fargaba ko
tsoro wurin tsage gaskiya, ko kad'an.
Kinga mai irin wannan hali, za'ki sameshi da rik'on a Mana. Babu mai rik'on a Mana kuma Sai
Mutumin kirki.

Babbar d'abi'arsa da tafi burgeni, shine bashi da ZARA.! Wato kule kulen 'yammata, daga
wannan a koma wannan, yarda yawancin a bokan'sa naga wasu suna da irin wannan hali.

Zan iya rantse Miki, Sai kyawawan mata guda goma su wuce ta gabansa bai kulaba, saboda ba
mai ra'ayin kule kulen 'yammatan bane. Macen da yake so, shi ita kad'aice a gaban'sa.

Duk namiji mai zara, za'ki sameshi da d'auka da a jiyewa. Kome kike Tak'ama da shi, da yaga
Wacce ta fiki, tauraruwarki zata dushe, yayi k'ok'arin barinki ya kai mata hari. Kuma namiji mai
zara, kullum cikin hange hange zai kasance, ko aure yayi matarsa ba za ta tab'a gama gamsar
da shi ba.Kenan daga nan, k'ofar matsaloli sun bud'e. A yi hattara mata.
Namiji mara zara kuwa zaki sameshi da tsayawa ka'in da na'in a kan guda d'ayan nan da ya
keso, Wata ba za ta yi ta d'auke masa hankali ba. Kuma ko k'addarar aure ya ratsa zai yi, to
bazai rink'a auri Saki ba. Yau ayi gobe a Saki. Kuma namiji Mara zara, zaki sameshi da son
matar'sa da kulawa da ita sosai da kishin'ta. Ki Sani suffofin Yarima fa nake wassafamiki, cikin
rukunin namiji mara Zara.

Mutane da yawa fassara d'aya suke yiwa Yarima, shi yasa har Sukan manta da wasu d'abiun'sa
kyawawa masu wuyar samu a zamanin nan. Kuma nafi kowa sanin Yarima da fahimtar'sa cikin
a bokan Mu. Shi yasa muka shak'u tamu tazo d'aya.

Tuni na fahimci cikin halittarsa ne wannan d'agawar da jin kan da za'kiga yanayi. Amma a
zuciyar'sa babu wani nufin yanayin hakan ne da nunin d'agawa na yafi kowa wani a bu haka

nan d'abi'arsa take.

Amma idan kika fahimceshi sosai, kika fuskanceshi, kika samu kan'sa Kuna Mu'amala ta
d'asawa, to za'kisan Yarima a wasu juyin Mutum ne a bin so. Yana da kirki Sumayya, amma fa
Sai Kinsan makamar iya zama da shi za'kisan hakan, har ki yarda.
Nasan ke damuwar ki babba, babu soyayya tsakanin Ku. To ki Sani, anayin aure babu soyayya
kuma a sameta daga baya. Kuma a na yin aure da soyayya daga baya ta gushe. Kinsan in'da
matsalar take?".

Na girgiza kai a hankali.

"A cikin d'abi'a matsalar take Sumayya."

Nace "Ancle Yaya a bin yake ban fahimta ba."

Da sauri yace

"Yauwa 'yar albarka, wato kowan ne da Wanda ya dace dashi ya aura wurin d'abi'a, shi ake kira
da Sab'awar halaye. Kinga kamar a kan'ki keda Yarima. Babban a binda yasa nake ta jaddawa
ma Kenan a raina na cewa KE DA SHI KUN DACE.

Farko Kinga Yarima yana da zuciya sosai. Ke kuma kina da hak'uri. Ba komai ne ma yake b'ata
Miki rai ba ke.

Yarima yana da d'an rik'o da rashin saurin yafiya.

Ke kuma kina da saurin yafiya, da mai da komai ba komai ba. Kafin ma a nemi a fuwa kin yafe,
tun da take kin ma manta an b'ata miki ma.

Yarima yana da d'an zafi, a wasu Mu'amalolin. Ke kuma kina da sanyi sosai. Sau tari Yarima
bashi da son magana, Sai ki bashi sunan miskili ma kai tsaye. Amma a wani tsukin Sai kiga
kamar bashi ba, har hira Sai kusha. Amma dai rashin son hayaniyarsa yafi yawa. Na fuskanci
ke kuma kin iya zama da mai irin wannan halin. Kin iya da halayen mutane wurin zama. Kuma
nasan za'ki iya da wannan halin nasa mai kama da miskilanci Shi yasa nace. KUN DACE.

Wannan shine Sab'awar halayen da ake so tsakanin ma'aurata, domin Muddin Mutum ya had'u
da mai irin d'abiar sa a komai, to alamarin ba zai yi kyau ba, ko kad'an, tamkar BOM a ka dasa,
dake buk'atar lokacin tashin'sa yayi, yayi bindiga.

Kema ki auna a bu d'aya rak!.ace mai zuciya, ya had'u da mai zuciya, Yaya kike zaton
makomar?".

Nace

"Ai Sai a binda aka gani Kawai na rigima my Ancle."

Yace k'arshen furutan'sa.

"Ai Sumayya, wurin Sab'awar d'abi'u a ke sanin an dace, amma ba'a wurin Samun mai mai kudi
irin kaba, komai kyau irinka ba, ko ilimi da sauran a bubuwa da akayi tarayya a cikin'sa.

Wata soyayyar ma a waje iskace wani lokacin, Sai anzo an zauna, 'yar manuniya ta nuna na
halayya da za'ayiwa juna dai dai, Sannan soyayya ta gaskiya zata maye gurbi. Shine an dace
da juna, da kuma Soyayyar. Me yasa kike ganin, anyi shaharar riyar soyayya da anzo zaman
auren Sai yak'i dad'i kuma?"
Kawu Sulaiman yayi gaskiya. Na fahimci komai Kam, daki daki. Ya kamata kuwa ma'aurata
kafin suyi aure, su fahimci irin d'abi'un wanda za'su aura, koda da bin cike ne, domin a San an
dace da juna kar Sai an Shiga a fad'a cikin matsaloli.

Dole naso Kawu Sulaiman, sosai ya hanamin kuka lokacin da zan yi. Ya kuma sharemin
hawaye lokacin zubar'su. Na fad'i hakan ne, saboda dangin babana da su ya dace Sufi
tsayamin a aure, cogewa suka yi, kuma babu a binda suka yi min, Sai k'afafuwa suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login