Showing 27001 words to 30000 words out of 51633 words
Chapter 10 - NI DA GIDANA BOOK COMPLETE BY ZAINAB MAZAWAJE.pdf
na dada dumama kazar, tun
da ta kwana.
Na zauna ina karyawa zuciyata tana ta sake saken yarda al'a mura zasu kasancemin a gidan,
gashi na shiga tsakanin tsofaffun masoya biyu masu masifar son junansu, wato Ancle da
Salima, kaddarar aure ta cillo ni auren gun wanda zuciyar sa ta na ga wata har gobe, tare burin
ya mallaketa, amma kaddara ta riga fata, nice kaddararriyar matarsa ta farko da Allah ya
hukunta tun fil azal.
A gurin Ancle auren wata manufa yayi, amma ni a zuciyata sam ba na halarto hakan yanzu
tunda igiyar aure ta sarkemu.
A haka dai kamar bazan fuskanci wata matsala ba a gidan ga yarda na lura, harshi kanshi
Ancle Faiz banga ya nunamin wata halayya mara dadi ba, sauyi ma na gani a kan kafin muyi
aure. To fatana tafiyar ta ci gaba a haka ko bazai rinka shiga cikin sabgogina ba yarda na ke so,
zan dai samu nutsuwar da zan soma janyo raayinsa a hankali, daga alkiblar da yake fuskanta,
duk da gashi ya soma da cewa ma Momi ce zata ci gaba da yi masa girki duk da yayi aure.
Ire iren wadan nan basu soma damuna ba
saboda nasan manufar auren da mukayi da shi a zuciyarsa . Amma ni a Zuciyata, aure ne nake
ji munyi mai manufa kyakykyawa, irin wanda a keso. Shi yasa ni a binda zan maida hankali a
kai, shine ta yaya zan janyo ra'ayin'sa gareni kawai na kuma fahimtar da shi kuskuren da yake
kokarin aikatawa, wanda nake ganin zai yi wuya ya fahimce ni, ko ya ma saurare ni a yarda
nasan waye Ancle Faiz tun tuni.
Bayan na karya na hau sama na gaishe da Abban su Ancle da naji shigowarsa, mutum mai
halin karimci da kirki da ka ganshi, yayi ta samin albarka, tare da adduoi cikin auren mu, duk a
gaban momi, domin suna tare. Zuciyata naji ta washe da samun nutsuwa da farin ciki da halin
karimci da adduoi da Abban yayi min.
A hanyar saukowa daga bene mukayi kicib'is da Khalifa, in da ya dakatamin yaja baya, domin
na wuce. Shine farkon ganina da shi, Shima haka. Ta yiyu wannan dalili naga yana yimin wani
mayataccen kallo Sama da k'asa nasha mur, saboda duk namiji mai wannan hali na kallon
k'urilla, haushi yake bani.Amma duk da haka, bai sauya da k'uramin idanu ba, sai fara'a da ya
sake sakima yana washe hak'ora, a haka muka gaisa, ya haye saman Momi.
Ni kuma na sauko, na nufi d'akina, in da naga Muhibbat tana wanke wuri da tsintsiya. Nayi mata
sannu da aiki, ta amsa cikin wani salo na i sa. Araina nace, wannan miskilanci ta d'orawa kan'ta,
ko kuwa haka yanayinta yake?.
Bani da mai bani amsa, shi yasa dole sai munyi nisan zama da ita zan canki amsa.
A kan kujerar da Ancle Fa'uzu ya tashi ta falona na kula da wata tsadaddiyar wayar sa a kife.
Mantawa yayi, ko a jiyewa yayi yana sane bansani ba domin dazu ai Salimar ta kirashi a waya a
saman Momi ya sauko, kenan a falona ya zauna. Halin nawa nayi, na d'auka, domin a ganina
yanzu ina da hurumin tab'a abin Ancle Fa'izu, tun da Mijina ne.
Numfashina Sai da ya tsaya cak! na wucin gadi, ganin wacce ke kan fuskar wayar Ancle.
Duk da ban tab'a ganin ta ba, nasan ita ce.
SALIMA.
Kyawunta da a ka kod'a to zarta ma da na ganta, a hoto gaskiya.
Wani irin kishi naji ya ziyarci zuciyata mai rad'ad'i.
Shine shaidar farko da yake nunamin na tsundima tsindim a kogin son Ancle Fa'izu wanda da
nake yaudarar kaina da da cewa bana son'sa.
Duk da nasan Salima yake so, ni auransa kawai na rabauta da shi, babu zuciyarsa kuma
sanadin dai salimar.
Hakan baisa na daina jin ciwon kishin sa ba.
Salima tafi kama da irin larabawan Lebanon d'in nan, da basu cika haske ba da yawa, Sai
tsagwaron kyau. Bata kai hasken fatar Ancle ba ko kusa, illa dai cikar halitta ta koina. English
wear's tasa, wacce ta matsemata jiki, surar halittar ta ta d'iya mace, ta bayyana a sarari, domin
rigar daga sama kamar 'yar shimi bata da hannu a jiki, gata mai nuna surar jiki daga ciki, domin
shef din unders dinta har launin kalar a na hangowa, rigar banzar mai shara shara bata boye
komai nata daga ciki ba, don da ita rigar saman da baasa ba, ni banga bam bamci ba, kanta
kuma babu d'an kwali ta Saki yalolon gashinta ya zubo gadon baya,wani kad'an ta gefe ya
zararo kan k'irjinta.
Ni dai nasan tana sane kawai tayi wannan shigar ta iskanci, bawai rashin wayo ko rashin sanin
kuskuren haka ba, duk wanda yaga hoton dole ya karar kai tsaye akwai manufarta. sai dai
meye manufarta ga hakan, ubangiji masani.
Na sake kallon ta a hoton na zumburi baki, na jin haushi. Sam shigar zub da darajar da tayi ta
bawa namiji har ya zame masa mudubin dubawa a waya kullum ya sik"eni, bawai iya Kishi
bane. Saboda kayan da gani masu tsadar gaskene, sai dai sun tashi a banza, tun da masu
nuna tsiraicine gaskiya.
Shi kuma Ancle soyayyace ta rufe masa idanu ya biye mata ya iya ajiye hoton a fuskar wayar
sama, bansani ba, ko ita ta bashi damar a jiyewar, a fuskar waya ya biyewa soyayya ya ajiye
din, duk zai iya yiyuwa.
Sau tari wasu matan, suna ganin tallata surar jiki ga namiji wayewa ce, da k'arin janyo soyayya.
To wallahi karyane. Na karya ta ni Sumayya.
Bayan janyowa kai zunubi, ragewa kai daraja da k'ima ne matuk'ar babu aure gibi kuma
sukewa kan'su sosai. Ko namiji bai nuna ba, ko bai hango aibi ba a lokacin to a gaba kuwa za'a
karb'i raddi wallahi.
To ni Ancle Fa'izu ya fita laifi a wurina, da ya kasa hango kuskuren ballantana yayi mata gyara,
kuma wai nan aurenta yake so yayi, sai gashi har ya a jiye hoton ya zauna a fuskar wayarsa, ko
yaushe kenan da shi zai fara tozali, idan ya d'auki waya.
Tabbas giyar soyayya ta bugeshi yayi yana sane, bawai a ce bai hango illar hakan ba.
Irin haka ne, idan namiji soyayyar banza yake yiwa mace, to ya samu kofa, tun da kalar tarko ne
a ka da na na kama mutum da shi, ko da ba ma namiji bashi da mummunar manufa kan lace
hadari ne, tunda akwai shaidan zuga zugi a gefe.
To al'amarin soyayyar Ancle da Salima, bazan iya sharhi ba, tun da bansan ciki da wajenta ba,
amma a zato da kallon da nake yiwa Ancle Faiz, ba mutumin banza ba ne, amma sanin mutum
na badini, sai ubangijin dai da ya halicce shi. Sai dai nasan ko meye a keyi a boye na rashin
gaskiya, wataran zai bayyana.
Bansan sanda nayi Jifa da wayar ba jikin bango saboda kishi da haushi.
Jikake tus! na d'auka naga glass d'in ya fashe. Na d'ora jikin TV stand. nasan masifa ce kawai
zan sha. Iya ka kenan.
Duk da Khairat ta kawomin break fast , ban karya ba, Sai da nayi wanka na shirya cikin kwalliya
da ado sosai.
Na zauna na karya. Har lokacin Ancle Fa'iz banjiyo motsinsa ba, ko yana dakinsa ne, domin da
na baro saman momi yanzu bayanan.
A shiryen sa ya shigo min, Shima yayi wanka yasa shadda ruwan goro, hartin d'in gajera ce iya
gwiwa, gaban rigar anyi masa aiki na kwala mai kyau.
Sunfi yi masa fiye da wacce ya cire. Duk da sirrin kyawun ba'a kaya yake ba,a halittar ne, sai
baza wani sassanyan kamshi yake yi mai tashi a hankali, da shiga ruhi.
Yana shigowa na dake, saboda laifin da nayi masa, amma jikina na soma jin ya soma rawa
rawa kadan na tsoro kuma, saboda nasan waye Ancle idan ransa ya baci.
Wayar tasa kuwa ya Shiga nema .
"Ba nan na bar wayata bane?".
Mik'ewa nayi tsam naje na d'auko inda na a jiye. Har na mik'a masa naga yanayi min wani salon
kallo, da alamu na tuhuma ne, kafin daga bisani ya d'ora idanu a kan wayar yayi tozali da
ta'asar da nayi. Ya sake dubana.
"Garin yaya kika fasa min waya?".
Na sunkuyar da kai nace.
Garin tsautsayi ne kayi hak'uri Ancle."
Na koma na zauna a bina.
Ransa b'ace yace.
"Garin ganganci dai kika fasa min waya Sumayya. Me ya kaiki d'aukar wayar da take a jiye?
Lek'en a Siri ko meye?".
Naji shigar furucin'sa amma na dake, saboda nina jawa kaina. Kawu Sulaiman ya Sha yi min
nasiha na daina tab'a a binda banawa ba, musamman na sirri, nace sai na gani, gudun fad'awa
rigima, saboda binciken da nake yi masa a d'aki.
Na k'ara bashi hak'uri.
"Ancle kayi hakuri nayi laifi, amma bazan kuma ba please".
Nayi masa tayi da tea da na Sha saboda ko rabi na kasa sha, bansan dalili ba, ga kuma yunwar
ban cike gurbinta ba, duk da nasan yasha tea saman momi, duk domin kau da zancen ya wuce.
Kuma babu dad'i, daga auren mu a ce mun soma samun Sab'ani.
Ancle ya iso gareni, ya zauna gabana, kamar tea d'in zai sha, amma Sai naji yace a hankali
cikin wata galabaitacciyar murya.
"Sumayya, me yasa kike kishi a kaina?".
K'warai gaskiya ya fad'i, kishin yafi kaini ga hakan, amma bazan so ya yarda ba, duk da ya
d'ago, shi yasa nace.
"Wajibine mace tayi kishin mijinta".
Ya sake jefomin tambayar da ta hargitsani.
"To, Kina so na ne?".
Nayi kokarin sarrafa kaina.
"Ai ko da so ko babu so, mace zatayi kishi a kan mijinta".
Da sauri yace.
"That's not true. Sai da da so ake yin kishi. Nayi mamaki da a d'an tsukin nan da zuciyarki ta iya
So na. ke kinga na can canta kuwa?".
Na kasa iya cewa komai, saboda sani a gaba da yayi, ya tsareni da idanun nan nasa masu
sace zuciya farat d'aya.
"Idan za kiyi shawara dani tabbas zance kiyiwa zuciyarki shamaki da soyayyata, domin bata da
amfani a gareki Sumayya Sam ,Sam, kuma ko a gaba bazata amfane ki ba, kece mace ta farko
da bazan so, ki kamu da soyayyata ba. Kamar yarda nake kallon su Khairat, haka nake kallonki
Sumayya.
Zan iya bugar k'irji nace miki k'anwata, zan iya ce miki kuma my Daughter duk dalilin Sulaiman.
Really, ke matata ce, amma a furuci ne kawai, misalin auren mu kamar shirin wasan
kwaikwayone da mutane su ke gani, su rinka zaton gaskiya ne, idan suna gani, amma a badini
ai duk shiri ne, sabanin tunanin su. To a
wurina, haka ne.
Shi yasa bazan yarda na d'ora miki wani nauyi nawa ba. Kema nasan bazaki so ba, ko zaki so,
ni bazan so ba. Shi yasa tun farko ban b'oye miki komai ba, ballantana ki Shiga duhuwa, idan
kika ga ba yarda kika zataba.
Ko da yake Ancle sulaiman yace WAI NI DA KE MUN DACE. To ni ban kai hangen dacewar da
yake nufi ba. Ko matakin benen soyayya bamu hau ba, yace MUN DACE?
Bazan yi miki k'arya ba, nace Ina sonki, saboda kiji dad'i, kuma bayan k'aryar ma kuma ai da
yaudara. Shawara ta, ki daure ki rink'a kallona a matsayin Kawu Sulaiman ba miji ba, hakan zai
kawar miki da damuwar da zaki iya samun kan ki a ciki, ko takura. Zai sa ki Samun sakewa da
farin ciki a zaman mu, idan kika da sawa zuciyarki hakan. Ki jarraba Sumayya, zaki tarar da a
binda na fad'a miki,zaki gasgatani."
Ni dai har ya fice, kamar gawa, na gaza yin motsi.
Nasan shi ko a jikinsa, game da furucin da ya furta min, saboda babu d'igon kunya ko kawaici a
tare dashi, wurin fad'in a bu, ko yin abun da yasa kan'sa. Tun da gashi bai b'oyemin komai ba,
tun farko. Amma a bu da nafi jinjinawa. Farko yace na rink'a kallon'sa a matsayin kawuna
Sulaiman. Wurina kamar haramta halas ne. Shi Mijina ne, to don me zaice na rink'a kallonsa a
matsayin Kawu na,da aure ya haramta a tsakanina da shi.
Sannan ya dubi cikin idanuna yace yana k'yamatar wai na soshi. Kuma wai aure na dashi iya
furuci ne, ban da a aikace.
Banyi zaton za'ta kai mu da nisa haka ba, domin zatona duk wata d'awainiyar aure zai bani
damar nayi masa, iyakaci ya k'aurace min, tun da baya Sona.
Komai kenan bazan yi ba, hoto zan zama.
Gaskiya da sake. Na dad'e a daren ranar ban iya samun bacci ba, ina tsara salo salon yarda
zan fitowa Yariman kawu na, mai wuyar Sha'ani da tsadadden samuwa.
Idan yasan wata ai baisan wata ba. Nayi wayewar sanin komai, da iya komai. Zan fito masa duk
ta inda bai zata ba. Kuma cewar da yayi na rink'a kallon'sa a matsayin Kawu Sulaiman zan
kuwa fitine shi, duk shagwab'a da tab'arar da nake yiwa Kawu Sulaiman tun ina yarinya, har
girmana zai shata salo salo, bashi da k'orafi ko sababi, idan yayi zance ai shi yace na rinka
kallonsa a matsayin kawu na, zan ce shi yaja, tun da shi ya ban damar hakan, sai duk a binda
zai faru ya faru.
Da ace ban riga na aure shi ba, ya furta min kalaman nan, to tabbas zan yi zuciya na barshi.
Amma tun da yayi saken da igiyar aure ta sark'emu, to wallahi bazan hak'ura da shi ba, Sai inda
k'arfina ya gaza.
Bani ba, ko wacece ma a binda zatayi kenan, in dai ta samu nasarar mallakar miji irin Ancle
Fa'iz. Baza ta yarda ta canza shi da wani ba sai dai tayi k'ok'arin canza shi zuwa ga yarda
takeso, idan zata iya, Ko taci layar hak'uri ta
zauna da shi da halinsa.
A ranar dai nayi ta bak'i amma yawanci k'awayena na jami'a saboda su na gayyata a yinin biki
na, saboda bana son tsofaffin k'awayena na secondry su san na auri malam Fa'izu, terere za'ayi
tayi, ana kwazawa.
Daren ranar Ancle Fa'izu ya shigo falona, amma ba muyi hira ba doguwa. Duk yarda naso ya
saki jiki ya jima yak'i, ya kawomin uzurin wai a gajiye yake, na kuma karb'a. Ko minti biyar bai yi
ba, yayi min sai da safe ya wuce d'akin sa.
Da safe na a jiye bak'unci gefe d'aya, tun da nayi sallar a suba ban koma ba. Ancle Fa'iz nema
ya tasheni sallar a suba bai san nima gwanar tashi bace k'arshen dare nayi nafilfili har zuwa a
suba, to Sai yazo ya tarar dani zaune Ina lazumi, Sai ya juya.
Tare muka Shiga hada hadar girkin safe da su Khairat, duk da Khairat tayi tayi na bar aikin sayi
nak'i.
Ta hak'ure, Sai gashi muna aikin tare cikin armashi, har 'yar hira mu keyi. Ita kuwa Muhibbat
baya ga gaisuwa bata sake cemin komai ba. Bayan miskilanci, ma da
naga tana fama dashi da jin kai ainun, ko irin yanayin yayan tane da ita ban Sani ba. Amma shi
Ancle sanadin aure ya d'an sauya,tun da har yana 'yar hira dani. Ta yiyu ita ma ta sauya idan an
Kwan biyu, amma fa a zatona.
Muhibbat dai tafiyar ta tayi ta barmu da aikin, kuma na lura sanadin zuwa na ne. Khalifa ne ya
lek'o kichean d'in ya soma yiwa Khairat Maganar ta dafa masa ruwan wanka idan ta gama.Sai
kuma yayi Jim, da ya ganni, in da ya sake bina da mayataccen kallo, Sannan ya miko
gaisuwarsa gareni.
Na amsa da sauri na kau da kai na ci gaba da a binda na keyi. Zuciyata bata sak'amin komai
ba, game da Khalifa, Kawai banajin dad'in kallon da yake yi min ne, ko santaran nake babu
aure. Ban Sani ba, ko shi kuma tasa d'abi'ar Kenan, ko kuma wani k'uduri ne a ransa. Amma
yaya zanyi, tun da k'addara ta cilloni gidan'su.
Bayan ya tafi, Khairat tace .
"Yaya Khalifa ya cika matsawa mutane idan yaga a na aiki. Da da wutar nefa ma Sai na jona
masa a Heater ko electric cooker. Amma tunda yaya Fa'izu ma zaice na dafa masa ruwan
wanka, Sai kawai na had'a musu wuri guda." Nan nasan itace ke yi musu hidimar komai shi da
khalifa, nasan zuwana kuma bazai Ancle Faiz ba zai sauya hakan ba.
_This is just the begining_
_Taku_
_Zainab ilyas mazawaje_
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe
*NI DA GIDANA*
_Zainab ilyas mazawaje_
_Best brilliant interlligent writer_... ️
*page 13*
Nace da Khairat, bayan tafiyar khalifa. "Bari na d'ora musu a gas cooker d'ina, idan yaso sai ki
d'ebarwa khalifa nasa, kin san yanzu ruwan sanyi ba zai zububa a jiki, dole sai an d'an dafa, tun
da da ragowar sanyi, tun da kuma safiya ce, kije kiyi shirin makaranta, kar ki makara, naji kina
tambayar lokaci, na k'arasa soya dankalin."
Tace "Gaskiya