Showing 12001 words to 15000 words out of 51633 words
Chapter 5 - NI DA GIDANA BOOK COMPLETE BY ZAINAB MAZAWAJE.pdf
gasu sun kafe babur a kusa da k'ofar gidan mu da
taimakon kwatancen da nayi musu a waya da suka shigo unguwar.
Muna tsaye dama a k'ofar gida ni da Nuriyya. Samarin d'aya fari ne sosai, d'aya bak'i. Bak'in
yafi sakin fuska da fara'a a garemu shima black beauty ne gaskiya.
Bayan musayar gaisuwa, farin saurayin ya zura hannu cikin aljihu ya zaro waya gami da
sabuwar caza ya mik'o mana. Ni na karb"a cike da godiya.
Yace.
"Sai ki kula, karki sake yarwa, domin ba lallaine ta dawo ba."
Nayi mamakin canzawar sa kamar ba shine mai barkwanci a waya ba.
Nuriyya tace da sauri.
"Gaskiyane kam, domin ba domin mun yi dace da mutanen kirki irin ku ba, ai da tarasa kenan.
Kuna da kirki da karimci gaskiya, don Allah yaya Sunayen Ku?" .
Ni Kam naga Zak'ewarta, shi yasa nayi kasak'e ina kallon'ta.
Wannan saurayin bak'in ,shi ya bata amsa.
"Sunana Suhail labaran. Shi kuma sunan sa Fa'izu Bukar".
"Kai Amma Sunayenku suna da dad'i, kamar na larabawa? a wace unguwa kuke ne? ".
Nan naga mai suna Fa'iz d'in ya jefeta da wani irin kallo a sakarce, dake nunin ta isheshi da
Surutu. Ni kuwa dama tuni ta k'ular dani na irin wannan shishshigi. Su ya dace su nememu da
hakan, ba suyi ba, Sai mu mata? domin kawai ta zubar mana da daraja?.
Tuni dama na fuskanci wannan Fa'izun d'an ji da kaine da fad'in rai. Tun daga Maganar farko
bai sake cewa komai ba. Ko kallon mu bai sake yi ba, Sai da Nuriyya ta Shiga k'wak'ulen
tambaya ga a bokin'sa ya waigeta sau d'aya, kallo ma na raini.
"Zo nu tafi Suhail, kasan sauri muke yi, kuma ba jiran mu zasu yi ba".
Inji Fa'izun. Inda ya ce masa "To" .
Amma bai motsaba, saboda Nuriyya da ya soma yiwa kwatancen in da suke dalla, dalla. Bai yi
nisan ma da zata gane sosai ba Fa'izun ya sake cewa.
"Idan ba zaka zo mu tafi ba, ni kaga tafiyata. Bazan jiraka ba wallahi idan ka tsaya, ka taho
daga baya."
Faiz Ya dubeni yace.
"Sai anjima."
Nace. "Na gode, Allah ya saka da khairan."
"Amin.".
Yace bayan ya soma tafiya.
Ganin haka Shima Suhail d'in yayi gaggawar binsa
saboda ya fuskanci tafiya zai yi ya barshi, bayan babur guda suka zo kuma. Bai k'arasa yiwa
Nuriyya kwatance ba dai ya tafi.
"Gayun nan sunyi a rayuwa. Musamman ma farin, Fa"iz.Sai dai naga d'an girman kaine da nuna
isa , d'an hana ruwa kuma gudu, abokin'sa ya fishi kirki. Yanason a k'ulla zumunci ya hana.Ya
bani haushi fa!".
Nace".Naji dad'in a binda yayi Miki, haka Kawai daga had'uwar k'addara Sai ki Zak'alk'ale?
Wannan halin zub da ajine Nuriyya. Nayi mata tatas, tayi lub. Amma fa an d'auki lokaci in dai
mun had'u Sai tatada Zancen wai taji ciwon rabuwar mu da su babu a direshi.
Rannan kuma muna hira tacemin.
"Kinsan me Zuciyata ta ayyanomin yanzu?"
"Ta ina zan Sani,baki fad'iba.".
Nace da ita.
Tace"Zuciyata ke sak'amin, Ina ma ina cikin tafiya, na had'u da miskilin gayen nan, ai ko bai
kulani ba naci riba."
Nace.
"Kin Shiga uku Nuriyya."
Tace"A wani dalilin zaki kiramin musifa".
Nace "Ai kuwa kin shiga cikin ta yanzu, tayaya za ki kwallafa rai da mutumin da ko kallo baki
ishe shiba? dama daya hand some din guy bakin kike so, sai ince dan dama dama, don zai iya
sauraronki ko baya sonki, saboda naga yana da saukin kai shi gaskiya. Ke ruwa ma ba saan
kwando bane gaskiya daga yanayin ganin samarin nan kinsan ma ba saan nin yi ki ba ne, sun
kuma kama dahir, kawai kisa hakuri".
Ta harareni kawai taja tsaki. Nayi zaton za ta kuma tankawa na kare mata tanadi, sai tayi shiru.
Domin gaskiya haushin yarda take zubar da aji nake, gashi sun nuna mata a aikace na ba ma
gabansu, amma ta rufe ido ta kulle tunani, wai bata dau haske ba, saboda son zuciya kawai.
Kunji wannan.
Daga bakin alkalamin....️ Zainab mazawaje muje zuwa
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe
*NI DA GIDANA*
*By*
_Zainab mazawaje_
_Best brilliant interlligent writer_..... ️
*page 6*
Tun daga lokacin na fahimci Nuriyya kamar tayi fushi da furucin da nayi, don naga bata kuma
dauko min zancen ba, a raina nace ya dai fiye miki hakan, kisan ciwon kan ki da mutuncin kan
ki gaskiya.
Daga lokacin, na samu lafiya ta dai na yi min Zancen, amma bansan cikin Zuciyarta ba ko tana
sak'awa.
A daren ranar dai Alhaji Rabi'u yazo ya matsamin lamba na sai na bashi dama ya turo iyayen'sa
Yasan matsayin'sa. Sayayya fal yayi min kuma. Yace ya kuma gaji, ko yin ko bari yana son
sani. Nace ya bari, zanyi magana da kawuna.
Kafin ma na fad'awa Kawu Sulaiman, da Nuriyya k'awata tazo, ta rikirkita min lissafi.
"Wallahi ni nafi miki Sha'awar Alhaji Rabi'u domin yafi Usman kud'i . Alhaji Rabi'u yafi Usman
shekaru da gwagwarmayar sanin wahalar aure da juriya da sanin darajar iyali. Kefa kika ce
zaune yake da matarsa lafiya, gashi kince yana yabon matar Sama. Mai wannan ai Sai namiji
na gari. Shi kuwa Usman baki da misali a kansa da zaki samu tabbas, Sai kin Shiga zaki gani.
Kuma kin tab'a cemin kin tsani kiyi aure ki fito a rayuwarki, ba kyason zawarci ko aure sau biyu.
Tun da haka ne, dole kiyi taka tsantsan wurin aure, kar Kibi son zuciya. Tun da su duka sun
yarda da karatunki da aiki da zakiyi to kar kibar Alhaji Rabi'u, shi ya dace dake. Kinsan maza
irin su manya suka auri budurwa, ba k'aramin tarairayarta suke ba da nuna mata soyayya."
Na Shiga rud"ani, domin cikin maganganun'ta a Kwai a bin dubawa ko ba du ba. Bata gushe da
yi min hud'uba ba, Sai da ta cusamin auren Alhaji Rabi'u, naji shid'in kawai zan aura. Shi yasa
banji fargabar sake tunkarar Kawu Sulaiman da Zancen ba, duk da nafa kai masa zancen
Usman yace na saurare shi. Idona ya rufe. dubana yayi cikin 'yar fusata.
"Wai ke Sumayya me kike nufine? Maza biyu za ki aura, ko menene k'udurin'ki?"
Na duk'ar da kai zan soma magana ya katse.
"Fad'amin wakike so da Gaskiya,Alhaji Rabi'u ko Usmanu?".
"Alhaji Rabi'u." Nace.
Jinayi gaba d'aya ya k'aryatani.
"K'arya kike yi, Shima ba son'sa kike yi ba."
Ni kuwa nace me zanyi, idan ba kallon'sa ba.
"Tun da kika tsaya ruwan idanu tsakanin Alhaji Rabi'u da usman, ya nuna su duka ba wani so
na hak'ika kike musu ba. So guda d'aya ne tak! Kuma ba'a yin ruwan ido a cikin'sa. Da kina son
Usman, ba zaki dawo daga baya kice Alhaji Rabi'u kike so ba. Kuma da Alhaji Rabi'u kike so,
tun farko shi zaki zab'a. Nafi zargin cusa miki ra'ayin'sa a kayi.
Ya sauke numfashi a hankali, ya dubeni.
"Bazaki auri d'aya daga cikin'suba, domin duk basu dace dake ba. Wanda ya dace dake a
dabi'ance zai zo nan kurkusa in Sha'Allah. Zaizo, kuma kafin yazo zaki ga alama ta sanarwa ko
nuni na hannunka mai sanda kam idanu na zuba masa kawai.
Cike da Mamaki na dubi Kawu, amma kaina ya d'aure ban fassaro komai ba, a fuskarsa ko a
kalamun'sa.
"Zan sallami Usman da Alhaji Rabi'u da kaina. Babu ke babu su, ko a hanya, kinji na fad'a Miki.
Na sake jadda da Miki, ko ki yarda ko karki yarda basu dace dake ba. Bayan ba son'su kike ba,
kuma bani da garanti a kan'su. A ido kawai nake ganin'su, tunda babu wata huld'a da take
Shiga tsakanina da su. Ina so ki darje Miji Sumayya ko domin maraicinki kinji."
Sam banji dad'in hukuncin da Kawu ya zartar ba, don dai yafi gaban nayi jayayya da shine,
matsayin sa ya wuci nan nesa. Amma na k'alubalanci tunanin'sa. Usman da Alhaji Rabi'u duk
babu na yadawa wurin yabo. Sun Sha d'awainiya dani da Zaman jirana na shekaru, amma tashi
d'aya a koresu? da wani ido zan kallesu? Wani zargi zasu yi min? ta ina zan maida irin'su? Wani
lokaci kuma zan d'auka Zaman jiran wanda zai dace dani a d'abiance, bayan shi hali ba'a goshi
yake ba da za'a gani a tabbatar. Abin a lullub'e yake. Addu'a ce kawai na tabbatar za tayi jagora
Ta ina zan lalubo wanda ya dace dani, amma ba hasashe, ko zato ba.
Na Shiga damuwa har wayewar gari, amma ban bari kawu ya fahimta ba, saboda ina jin nauyi
da kunyar yasan hakan. Domin bani da kamar sa a duniya. Bana iya had'a kaunar'sa da ta
kowa. Abinda yayi min a rayuwa, cikin family d'ina kaf babu Wanda yayi min rabi rabin'sa. Ya
cancanta da nayi masa biyayya a komai da bai wuce k'a'ida ba, wato haramun. Da wannan dalili
nayi ta jinyar damuwar Zuciyata a b'oye Ina had'awa da addu'a har komai ya sassauta a raina.
Ban sake fita zance wurin Usman ko Alhaji Rabi'u ba. Sun dai daina zuwa, bayan d'ayansu
kowan ne da yazo sau d'aya Kawuna Sulaiman yaje ya gana dashi. Bansan yaya suka k'arke
ba. Ni dai nasan, duk Sanda tsautsayi ya had'oni da su a hanya, zan sha kunya, kamar na
nutse. Bana fatan zuwan wannan rana ni Sumayya.
Bayan watanni har biyar da korar Usman da Alhaji Rabi'u, hak'urina ya soma gazawa saboda
Wata uku da suka wuce a ka soma gwab'amin da Zancen aure. Wai naki aure, duk sa'oina suna
d'aki da yara d'aya ko biyu . Wai na fake da karatu. a Kawu na a ke jefa k'orafin, Wai shi ya
huremin kunne na tsiri karatu domin kar nayi aure nayi nisa da shi. Saboda kowa ya lura da irin
k'aunar da yake nunamin. Kuma a binda ya jawo matsalar, duk cikin dangin iyayena na kusa
babu mai karatun jami'a mace. Kakana ma Sai da ya gwab'amin magana cikin hirar wasa yace,
Wai na kusayin kwantai, saboda na tsaya ruwan ido da buri. Kakata Hajiya Mariya ita kullum
naje k'orafin Kenan na aure. Itama kan Kawu Sulaiman ta d'ora laifin. Wani lokacin Hajiya
Mariya fushi take yi sosai har takance. "To ya jik'aki ya shanye mana, tun da bayason kiyi aure.
Na kan sake kunnata nace" Tsohuwar nan kin fiye rigima. Kinci zamani irin naki, ki barmu muma
muci irin namu Mana, kai fa ya waye yanzu, karatu a ke fara zurfafawa kafin aure. To nan fa Sai
ta balbaleni da fad'a har korata ma take yi tace kar na k'ara zuwa mata gida.
Amma Sai na koma. Baza'a rabu ba Sai mun kuma yin fad'an. Sai dai idan bata matsamin da
zancen aure ba. To ban san me zasu ce ba ko zasu yi kuma, idan suka San ya kori masu
zuwa neman aure na. Duk da hukuncin nasa Sam bai min dad'i ba nima, bazan iya suka ko
tona komai na Kawuna saboda bana so aga laifinsa.
. Ina tsananin k'aunar sa, bazan iya b'ata masa ba Ina sane.
Maganganun sun dameni lokacin da Usman ya aikomin da wasik'a a ciki yace wai naci a manar
sa Ina sane, nasan wani za'a bani amma nayi masa alk'awarin aure. Ban ko bashi amsa ba na
rabu da shi, saboda nasan kome zan fad'a masa bazai yarda ba. Alhaji Rabi'u kuwa, ban sake
jin d'uriyar'sa ba shi.
Rannan Ina zaune a tsakar gida, Baba Talatu ta tafi unguwa. Ranar bani da karatu, a hutu
muke. Komai ni nake yi dama in dai Ina gida, kuma ni nake sa kaina, bawai Baba Talatu ke
cewa nayi ba. In dai ta ita ne wanke wanke Kawai zanyi da sharar tsakar gida. Na gama komai,
Ina zaune, Kawu Sulaiman ya shigo, ya sameni zaune nayi shiru .
Ya jawo kujerar k'arfe da Baban'sa yake zama, ya zauna gabana d'an daura dani.
"Sumayya a Kwai wani a bu da zakiyi yanzu?"
Nace"Babu Ancle. Sai girkin dare, kuma Sai yamma sosai zan d'ora,tun da mai
sauk'ine.Wannan damar nake jira da baki komai, kuma babu kowa Mu tattauna Wata magana
dake. Kisa Nutsuwar nan taki da nasan ki da ita ki saurareni, ki kuma fahimceni 'yata".
Kafin nan zan baki wani d'an labari da zai zama shine sharar fage,na a binda zamu tattauna."
"Kinsan ai Yarima ko? .
Na dubeshi da hanzari, Sai ya zarce da cewa. Ko daya ke, Kinfi ganeshi da Fa'izu. Zan baki
labarin'sa a tak'aice, bazan b'oye Miki komai ba, saboda gaskiya da gaskiya ce za'suyi aiki.
Yarima haifaffen garin nan ne, amma a salin'su 'yan maiduguri ne.
Mahaifiyarsa sunan'ta Suwaida. Kuma k'abilar shuwa Arab ce . Baban'sa kuma babarbare ne,
sunan'sa Alhaji Bukar, amma asalin'sa bafulatani ne na sokoto.
K'annen Fa'izu uku, biyu mata Sai namiji dake bi masa Khalifa. Tsiran'sa da Khalifa,shekaru uku
yace min. Bad'an masu kud'i bane Yarima, ba kuma talakawa bane can. Sai sa Sai sa. Amma
dai yawancin d'awainiyar gidan Yarima keyi, musamman na kannensa mata
Yarima d'an boll ne sosai, domin kuwa makarantar school a cadamic yayi dake cikin k'asar
Ghana kuma cikin birnin Ghana ACCRA.
Suna koyar da boll ne da karatu. Tun tashin Fa'izu da son buga k'wallo ya taso, tun yana
k'arami, har girman'sa. Ya kuma samu sa'a a cikin harkar, ko nace yana kan samu. Iya boll
d'insa yasa wani a gent dake hayowa 'Yan club a turai k'wararrun 'yan boll, yace zai kai shi
spen wurin 'yan club d'in bacelona, ko real Madrid dake k'asar turan ta spen su sayeshi. Saboda
ya iya boll sosai Sumayya. Duk fita Sai yaci mana cup. Lamba sha d'aya yake bugawa, Kinsan
sune 'yan gaba, amfi ji dasu. Da yawa ma club Sukan gayyaceshi ya buga musu boll idan za'su
gasa. To sai yasa kan'sa dai yake zuwa, Kinsan halin Mutumin.
Yayi harkar teaching na wani lokaci da yasa kan'sa. Amma fa ya watsar yanzu, saboda harkar
boll tasha masa kai, kullum Samun ci gaba yake yi a cikin'ta.
Burin Fa'izu tafiya spen kawai, amma har hanzu egent d'in dai bai nemeshi ba."
Ni kuwa na kada baki nace.
Ancle, mai yasa sai yaje wata k'asa?".
Yayi a garin'su mana."
Yayi 'Yar dariya.
"Sumayya ai fitar sa k'asar turai shine ribar wahalar buga boll d'insa. Domin kuwa can ne ake
Samun kud'i na fitar hankali. Kinsan idan ya taki wannan sa'a ya tsallake tudun mun tsira kuwa?
Ko kinsan a kwai d'an boll d'in da yake d'aukar miliyan talatin duk Sati a k'asar turai?"
Nace cikin rik'e baki a rud'e.
"Duk Sati Ancle?".
"Sosai kuwa. A Kwai mai d'aukar Sama da haka Sumayya. Nan ma a na Samun k'ud'in
musamman idan club ya shahara, amma ko kusa baza'a had'a shi da k'asar turai ba Kinsan
yawancin kud'in ma daga wurin 'yan kallo a ke Samun yawan kud'in, to can turai, Mutum d'aya
kika ji kud'in da zai biya ya Shiga kallon gasar k'wallo Sai ki rik'e baki. To Mutum miliyan nawa,
ko Mutum d'ari nawa zasu Shiga kallon gasar boll na wata wata na kasa kasa, na cub club ke
karawa da juna. Bari dai mubar Maganar boll, muyi
wacce a kanta za muyi magana.
Yarima yana da Wata budurwa da suke matuk'ar son juna mai suna Salima. Tana da kyau wai
ainun, a fad'in a bokin Yarima na hannun dama mai suna Hashim. Ni dai ban tab"a ganin'ta ba,
Sai jin labari.
Mak'otan mune, suna zaune a Kaduna, cikin unguwar sarki.
Mahaifiyar Salima attajira ce, domin business take na saro furnitures daga k'asashen waje. Sun
rabu da Mahaifin Salima, ta sake wani auren wani attajiri a unguwar malali. Amma Salima tana
gaban'ta. Ita kad'aice 'yarta a duniya, tana son'ta kamar rai.
Salima tana da tarin masoya da yawa 'ya'yan attajiran gaske, amma Yarima take so kadai,
kuma tasan wanene shi.Sun had'u da fa'izu a heal's and Bally da sallah. Shekarar su biyar
Kenan suna soyayya.Wannan Shekarar Salima ta soma bautar k'asa. Maganar auren'ta ta taso,
tace bata son kowa Sai Yarima. Mahaifiyar'ta ta nemi ganawa da Yarima.
Bayan gaisuwa tace masa me yayi tanadi, game da auren 'yarta tun da yasan 'yarta ba gama
garin 'yammata ba ce. Bai b'oye mata komai ba na matsayin'sa da kuma a binda yake yi, amma
yace yana da wani buri da yake so ya cimma. Kuma in dai ya cimmasa to komai da take so zai
yiyu, amma yanzu haka bashi da wani shiri irin Wanda take nufi. Yace yana da dai dai arzik'insa
Wanda zai iya rik'e mace. Sannan gini yake yi ma yanzu ko rabi bai kaiba.
Nan Sai ce masa tayi.
"Haba Fa'izu! yaushe zamu saka rai da a binda bashi da tabbas? Wayasan San'da wannan buri
naka ma zai cika. K'arshe Salima tayi aure har tayi haife haife burin bai cika ba. Nama tabbatar
Sai ta rigaka aure. Kai da kan'ka kasan Salima ba matar talaka bace, ko a talaucin ta taso,
ballan'ta na ta taso, gidan iko.
K'warya ai 'yar uwarta take bi, domin idan tabi a kushi kunya zata sha."
Yarima baya barin ta kwana, da anyi masa zai mai da raddi.
Yace
"Mama, ai ita k'waryar tasan da 'yar uwarta, amma