Showing 18001 words to 21000 words out of 51633 words
Chapter 7 - NI DA GIDANA BOOK COMPLETE BY ZAINAB MAZAWAJE.pdf
kawu
yayi shi ya tabbatar min shi ya kira.
"Lafiya dai Yarima?".inji kawu na.
Yarima ya ce " Tafiya zan yi Sulaiman, shine na kira muyi sallama".
"Haba dai, daga zuwa, ko minti goma ba kayi ba?".
Yace a dan fusace. "Idan na zauna, ciwon zuciya sai ya karni ai, wannan bagidajiyar 'yar taka
taki cewa da ni komai, sai kauyanci take ta dokamin, ina zan iya, gwara na ware kawai".
Kafin kawu yayi magana, na dan dago kai muka hada idanu bazata, sai kuwa ya jefomin wani
kallo da jefamin wata irin harara, da sauri na sunkuyar da kai.
*lallai abin na yi ne inji mai tsoron wanka*.
_mu dai je zuwa_
Alkalamin*....... ️
_Zainab ilyas mazawaje_
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe
_NI DA GIDANA_
_Zainab Mazawaje_
_Best brilliant interlligent writer_..... ️
*Page 8*
Kawu Sulaiman, banga ya nuna komai ba illa yace.
"Karkayi saurin rik'on'ta Yarima, had'uwar kuce fa ta farko".
Yayi saurin d'aga masa hannu.
"Kaga, kar ka bata wata kariya saboda tana 'yarka. Tana sane. Yanzu da cikin k'awayen'ta ne,
da tuni ka soma jiyo shewarta, wai sunan ita 'yar jami'a ce, kyau a maidota primary, kuma ma a
ji d'aya."
Raina kam, naji ya sosu da furutan Ancle Fa'izu nacin fuska a gareni. Tabbas, halin'sa yana nan
nacin zarafi, bai ragu ba ma, Sai k'aruwa ni a ganina. A gaban fa Kawu Sulaiman, Wanda zai
nemi aure na a wurin'sa yake min irin wannan wulak'ancin. Gaskiya Ancle Fa'iz baisan wata aba
wai ka ra ba, ko kawaici, ballantana kunya.
Kawu Sulaiman ya dubi komai da aka kawo masa bai tab'a ba, yace.
"Yaya baka Sha ko d'an lemon bama. Me yasa?".
Yace.
"Ta banine? a jiyewa fa Kawai tayi. Wai look at her, batasan ma yaya zata tarbi bak'o ba? to Sai
yaushe? Wannan 'yar taka Sulaiman da gyararraki, ba gyara ba. Ya juyoyo gareni ya sake
watso min wani kallo mai kama da harara.
"Kinzo kinyi min wani dimkim dake. Sai a bin ya bashi 'yar dariya ya dara kad'an. Sunan fa wani
ganye wai Shima dinkim. Sai ya sake sakin 'yar dariya da ban tab'a ganin yayi irinta ba.
"Ya kuma fa isheka haka haka, Yarima. Kai wani irin siriki ne wai, gaba na sai aibatamin d'iya
kake.Ko mutuwa ance tana alkunyar idanun iyaye.Wai kai bakasan Kawai ci ba, ko kunya?".
Bud'ar bakin'sa yace.
"San'da a kayi rabon su bana nan, ko zaka sammin taka?".
Ancle Sulaiman ya bishi da kallo kawai, kamar bazai taga ba, sai yace.
"Ank'i a sammakan, kasan darajar su ne."
Murmushi Ancle Fa'iz yayi.
"To, rik'e Kayan'ka, ka kuma mai da wuk'ar. Ka Sani, ko nace Sumayya tayi zuciya ta daina
gidadanci kawai, shine zai sa na sarara mata Wallahi, ba Sai ka tada komad'a bama."
Ni dai daganan, Sulalewa nayi na barsu, suna sa insa basu sani ba. Nace, sun fi kusa. Ga duk
kan alamu suna irin wannan karawar, mai kama da wasa, a zahiri idan ka gansu.
Wannan nasan somin tab'ine a kan matsalolin da zan fuskan'ta idan nayi saken auren Ancle
Fa'izu. Duk yarda zanyi kuwa zanyi, domin yakice auren.Sam! ban shiryawa cin fuska ba, da
tozarci da wulak'ancin Ancle Fa'izu. wato Yariman kawuna.
Bazan yarda burina ya rushe ba. Tuni zuciya ta ta tsaramin, yarda nake son rayuwar aure na ta
kasance. Rayuwa nake so, sosai ta soyayya da nishad'i da walwala, da farin ciki, da fahimta. Na
tabbatar na auri Ancle Fa'izu duk sun rushe. Ballantana ma Wai auren wucin gadi, yake so
nayi,wanda zai k'are kusa ne, nesa ne ban Sani ba, shi ya Sani. Abinda na sani, ni zai cuta
kawai. Domin na tabbatar ko wani abu bai ratsa tsakanina na aure da shi ba, tilas ya sakeni
kallon bazawara za'ayi min. Ban isa na goge tambarin zawarci a goshi na ba a idon mutane. Ga
zato mummuna da za'ayi min a ce bani da hali ne. Dad'i ma samarina na baya suyi min dariya,
da Allah ya k'ara, tun da ga zaton'su ni mayaudariya ce. Mak'iya na su sami hakoran yi mini
dariya.
Bani da abokin fad'a Sam. Amma duk Mutum nasan baya rasa masoya da mak'iya.
Nasan kuma Kawu Sulaiman bashi da masaniyar nufin Yariman'sa. Nasan ko giyar wake yasha,
bazai so nayi irin wannan auren ba. Dad'i ma naji daga baya, da yake bani da hak'k'in Yarima,
gashi ya fad'a min k'udirin'sa kafin aure. Kenan na sake Samun hujjar ya kice auren cikin ruwan
sanyi. Sai dai idan Kawu Sulaiman bai ji ba. Dole kuwa yajin.
A d'akin Kawu Sulaiman, Ina rakab'e bakin k'ofa, shi ya fara magana kafin na fara,kamar yarda
naso.
"Abinda kika yi, dole ya b'ataran Yarima, saboda shifa wayayye ne sosai, mai son harka ta
wayewa. Ballan,tana shi da ya sabayin hira da wayayya gogaggiya mai babban a ji irin Salima,
dole ki sik'eshi.Bai kamata ki rikid'e masa ga siffar da nima nasan ba taki bace Sumayya .wani
daliline a ranki, kika yi masa haka ko? Sannan domin k'arin kwab'a kika yi tafiyar'ki baku ko yi
sallama ba. Menene damuwarki Sumayya?".
Wannan damar nake jira.
Kawu, ni wallahi halin'sa bazan iya da shi ba. Ko a makaran'ta tsoron karo da shi nake. Abu
k'arami, Sai ya tozarta Mutum. Ka gani ma da idanun ka Kawu, gaban'ka ya rink'a yab'amin
maganganu, ko nauyin'ka bai jiba."
Ya katseni da hannu.
"Da Kinsan Yarima sosai, da fahimtar'sa baza ki yi wannan k'orafi ba."
Na fahimci kamar kariya kawuna Sulaiman yake bashi ma, shi yasa na fito masa da da Zancen
da idan yaji, Sai ya zargeshi.
"Ancle Fa'izu fa cewa yayi aure na zai yi na wani lokaci ya sakeni Kawu, saboda cikar burin'sa.
Wallahi ya fad"a kaji na rantse."
Ga mamakina wai Kawu nan ma bai damu da furucin Yariman'sa ba, da manufar'sa.
"Karki damu da abinda ya fad'a. Ikon komai da tabbatar komai yana hannun ubangiji. Zukatan
bayi, suna hannun ubangiji, shi yake sarrafasu yarda yaso. Saboda haka karki damu da komai.
Ke ki nufi auren ku, da kyakykyawan zato,da niyya mai kyau, da kuma kyakykywar addu'a zaki
dace.za kuma ki amintu
daga a binda kike fargaba Sumayya. Ba kya gani, ko Mutum ne, ya nufeka da mugun nufi, kai
kuma ka nufeshi da zuciyar alkhairi, sharrin'sa bayayin tasiri a gareka? Karki turje, kan wasu a
bubuwa marasa tabbas d'in d'orewa, ki yasar da a binda yafi alkhairi a gareki, baki Sani ba. Ki
dubama yarda k'addara take ta had'aki da Yarima, Ku had'u ku rabu, Ku sake had'uwa.Sannan
ni da nafi kowa son'ki a yanzu, ubangiji ya jarrabi Zuciyata da son ki auri Yarima. Kuma Sam,
bana k'aunar a binda zai kawo cikas a auren. Gani nake, Yarima shine kad'ai ni ya dace da
rayuwarki a duniya kaf Sumayya. Shine kuma Wanda nake jin zai rik'emin a manarki ko bayan
raina.
Jikina ke fad'amin haka Sumayya. Sai auren ya gabato, zan fad'amiki dalilan da yasa na nace
da aurenki da Yarima.
Ban kuma damu da yana son'ki ko baya son'ki ba. Ke da kan'ki baki Sha Mamaki da ya amince
da auren'ki ba? Aikin k'addara Kenan.Hakan na nufin fa, ke k'addarar cikin rayuwarsa ce ko
yana so ko baya so. Wannan bai i sheki ishara ba? In da na barki, kema auren rashin soyayya
zaki yi da d'aya daga cikin masu son aurenki, domin na tabbatar su suke sonki ke ba kyason su
tun da kika tsaya ruwan ido.
Tun da haka ne, ki jefi tsuntsu biyu da dutse d'aya mana. Ki auri Yarima domin dalilai da zan
fad'a miki su a gaba. Kuma ki yarda shi k'addarar rayuwarki ne, da bakisan me Allah ya shirya
muku ba, ki aure shi saboda wannan. Ni dai ya fiyemin tarkacen samarin ki sau d'ari.
Domin nasan komai a kan'sa, usuli da halayan'sa. Na gani, kuma naji a majiya ta
gaskiya.Amma nasan ba lallai ki yarda da shi ba har zuci yanzu, saboda kallon wasu halaye na
zahiri da kike yi masa. Amma a Kwai na bad'ini da bakisan da su ba. Shi yasa kike gani baza ki
iya da shi ba. Tabbas zaki iya zama da Yarima, matuk'ar kika fahimceshi, kuma kika kiyaye a
binda ya keso da wan"da baya so.
Nasan ko baki gwanance ba, zaki iya koyawa zuciyarki, ki jure kiyi, Saboda kina da hak'uri da
biyayya.
Kuma ki sani, idan ma kink'i auren'sa ba damuwa zai yi ba, ba kuma hak'ura zai yi ba da auren
cimma wata manufa ba. Wata zai samu ya aura. To ita Watan kina zaton irinki ce mai kyawun
zuciya da zata ceto shi daga yin kuskuren da yake son aikatawa, nayin auren wucin gadi? Ke
kuwa nasan ko baki taimakeshi da komai ba, zaki taimakeshi, da nasiha da addu'a. Sanin
kan'kine yin aure da niyyar Saki daga baya saboda wata manufa, haramun ne. Kika yi
kandagarkin hana afkuwar hakan bakiyi babban aikin Lada ba Sumayya? .
Naji jikina yayi sanyi Lis, da furutan Kawu.
Tabbas Gaskiya ya fad'i , a binda nake shakkar
yiyuwar, na yarda Ancle Fa'izu zai karb'i nasiha daga gareni, ko shawara. A yarda yake ji da
kan'sa, ni kuma yake ganina a raine.
Kawu yace.
"Kuma ki rink'a nuna kulawarki wurin mahaifiyar'sa, domin yana tsananin son'ta. Zan iya ce miki
nan ne sirrin farin cikin'sa. Ki soma d'ana tarkon'ki tanan. Ki kula.
_Nan farin cikin sa yake_
ni na sake jaddada wannan a raina, har sau uku ma.
Da wad'an nan kalamai Kawu Sulaiman ya sake farauto Zuciyata ta a minta da auren Ancle
Fa'izu. Amma fa ban daina farga ba ba, da zullumin auren. Tabbas ba domin na yarda da irin
K'aunar da kawuna kemin ba, cewa zanyi farin cikin rayuwata ne baya so, shi yasa yace na auri
Ancle Fa'izu.
Amma duk da haka ni fatana ke dai kar ya dawo, fushin da tafi da shi na nayi masa kaiyanci ya
hanashi dawowa. Amma idan kaddara ta sa ya dawo bazan bujire ba, ba dai haka na so ba.
Babbar fargaba ta kar na kamu da son sa ma, nafi shan wahalarsa, saboda siradi ne mai wuyar
gaske mace mai sunan mace ta dora idanu a kansa ta dauke ba tare da ya zabaro zuciyarta ta
kamu da soyayyarsa ba. Shi yasa ban fiye son na hada idanu da shi ba, domin a kwai sakonnin
da kallon ke aikewa zuciya ta da ni kadai na sani, in da shi kuma yake jin haushin hakan, ya
kuma daukeshi a matsayin kauyanci na ko kallonsa ba na iyawa.
Allah gani gareka, baiwarka marainiya, ka kawo mata dauki.
Na fadi a hakan a zuciya ta ni kadai ina zaune cikin tagumi.
_Taku har kullum_
_Zainab mazawaje_
Alkalami yafi takobi... ️
Follow this link to join my WhatsApp group:
https://chat.whatsapp.com/JhPLFkgTb4U0Y3wVj6YRQe
*NI DA GIDANA*
*NA*
_Zainab mazawaje_
_Best brilliant interlligent writer...... ️
*Page* *9*
Nayi sauri na fito daga d'aki, na karb'e tsintsiyar da Baba talatu, ta soma Shara da ita. Bata
Musa ba, ta sakar min. Sai da na share ko Ina na cikin gidan tas!. Na had'o Kayan wanke
wanke zan'yi Sannan tace.
"Ke dai Sumayya bakison kiga nayi komai, in dai kina gidan nan."
Nace.
"To, Baba Talatu, kina da kamata kiyi aiki? aiko tsari babu. Kiyi kwanciyarki, nayi aiki nayi kuma
girki, Sai dai Kawai na kawo miki kici. In dai ina gidan nan baza kiyi aiki ba."
Tace
"Koda a Kwai d'iya irin'ki mai kyawun hali, gaskiya k'alline. Kina da kyawun d'abi,a Sumayya, ga
biyayya, ga tausayi. Ta Yaya kuwa bakina zai gajiya da sa miki albarka? da Fata na gari. In
Sha'Allah Sai kin haifi masu binki, kuma Sai kin gwangwaje Miji na alfahari. Saboda kowa ya
bud'i baki a kan'ki fata na gari ne. Addu'ar iyaye da 'yan uwa kullum bibiyarki za tayi tayi."
Tuni na saba da lafazan Baba Talatu da d'ad'a, kullum ne bata gajiya.
Tsawon kwana tara, ban sake ganin ko inuwar Ancle Fa'izu ba, ga wawtata farin ciki na Shiga
sosai, a zatona ai ba zai iya dani d'in ba ne, kamar yarda yace, shi yasa ya janye.
A tsukin aka sake gayyatar k'ungiyar su Kawu sulaiman Kaduna united zuwa ga buga boll, cikin
k'asar Enugu, za'su kara da club din
Ranger's.
Nan ma su Kawu na ne suka cinye. Ya bugo min waya, cike da farin ciki yana mai shaidamin,
dama sau biyu muna waya da shi, bayan tafiyar'su. Nasan da Ancle Fa'izu suka tafi, amma ko
zancen'sa bai yi ba, nima banyi ba.
Na fiddaran hakan, Sai ji nayi Ancle d'ina yace.o
"Ga Ancle Fa'izu zan kai masa ku gaisa, kuma kiyi masa murna, domin shi yaci mana k'wallon
nasarar guda biyu. Yana dakin hutu amma na barshi yana shan mutuniyar tasa multina, bari na
kai masa.
Da sauri nace.
"Don Allah Kawu ka rabu da shi, basai munyi magana ba, kace Ina yi masa murna Kawai".
Yace.
"Zai fi kyau ki kira wayar'sa ki fad'i masa. Idan baki da ita zan turo miki. Nayi d'an Jim, daga
bisani nace.
"Ina jin nauyin hakan, Ancle. Naga shi ya kamata a ce yama nemi sanin lambata, ya kirani,
amma bai yi ba. Shi yasa nake ganin kamar zan karyar da kaina idan na fara. Amma idan kace
na kirashi, zan kirashin".
Yace.
"A'a. Rabu da shi kawai, na fad'a masa. Kinsan dai komai a kan'sa. Kinga kuwa komai ba zai
shige miki duhun menene dalili ba. Kinsan dole zaki rink'a had'uwa da irin haka, amma kiyi
hak'uri wataran Sai labari kinji shalelen. Ni da shi mukayi 'yar dariya.
"Gaskiya Ina son Kawu Sulaiman, har bansan adadi ba, ko misali.
Kwanan'su d'aya tal da dawowa kawuna yace min.
"Sumayya, yau Yarima zai zo. Don Allah, ki kula a komai, kar ki bani kunya kuma. Ki canza".
Nace.
"To, Kawu zan yi bakin iyawa ta"
yaji dadi.
Na samu kaina da tsala kwalliya da ado fiye da farkon zuwan'sa sosai. Less nasa kalar marun
mai adon duwatsu da filawoyi ,mai kyau, da nasan sunai mini kyau, saboda kawaye na ma ko
dani suke idan nayi ado dashi. Mayafi da takalmi to mach, daurin nan ya kafu a kaina kamar
nike koyar da dauri ga 'yammata, bansa sarka ba tun da ba gani zai yi ba, sai fasion da
bangles. Sai turare mai sanyin kamshi da humra da nasa. Nasan dai duk a banza wai talaka ya
girmi sarki a wurinsa, nayi ne kawai domin jin hakan ya dace, kamar yarda na cewa kawuna zan
yi a binda ya dace da duk zan iya.
Har bakin k'ofar waje da yake tsaye na isa na tarboshi, saboda Kawu Sulaiman Baba ya aikeshi
ya tafi, kafin fitowata wurin Yarima.
Saboda haka kujeru na roba na Kawu na fito dasu harabar cikin wajen gidan kusa da dakin
Kawu dake kusa da k'ofar fita waje, da yake a katange yake ba'a hangen na ciki.
Kamar had'in baki, Yarima Shima Man less yasa na maza, kalar pink mai cizawa. Sun yi masa
wani irin kyau Kam.
Duk da naje har bakin k'ofa na tarboshi cikin sakin fuska sosai, da sakin jiki da girmamawa,
Sam banga ya sakarmin fuska ba. Ya dai dubeni, a dak'ile ya kau da kai.
Abin a hali ne. Nace a hankali cikin dan tabe baki, duk da nasan ba sona yake ba, amma na
dan ji ciwon kallon saurin da yayi min yayi saurin dauke kai kamar yaga abin kazanta.
Tare muka jeru zuwa mazaunin Zaman, hannun'sa cikin aljihu, yana tafiyar nan tasa ta isa da
jin kai. Naga Sai wani shan k'amshi ma yake, kamar wanda aka tilasta Sai yazo wurina.
Kujerun da zamu zauna, suna fuskantar juna, kuma ni na a jiyesu ina sane a hakan. Zuciyata ce
naji ta soma k'ek'ashewa, daga fargabar da nake ciki ma na auran Ancle Fa'izu, saboda na
hanga gabas da kudu da arewa, ban hango matsera ba, na tserewa auran. Shi yasa Kawai na
mik'a wuya, tare da nemo hanyoyin da zanbi, na k'ubuta daga tozarcin'sa da ya zama lazim.
Nasan idan na ci gaba da nuna d'ari d'ari da shi, da Jan jiki, da alkunyar nan, to kullum
gumamin takaici zai ci gaba da yi, shi ko a jikin'sa, ni zai bari da ciwon zuciya.
Tare ma muka zauna. Bayan na gaishe shi nace.
"Yaya momi, da fatan tana lafiya "
Sai da ya fara da yi min wani irin salon kallo da Idanuwan nan nasa masu farauce zuciya.
Amma na tabbata, babu manufar komai cikin'su.
Baki d'aya Sai naji yanayin komai nawa ya canza tashi guda. Wani irin feeling naji, da
bantab'aji