Showing 6001 words to 9000 words out of 26460 words
Chapter 3 - ZURFIN CIKI book 1 Complete by halima Abdullahi K Mashi .pdf
dai tana ta bacci./ ZURFIN CIKI book 1 part 3 ZURFIN CIKI book 1 part
3 Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:42 Ya kalla kan gadonta, ummi taya dai dai
tana ta bacci. Yace, ummi ke! ummi!! tashi. tsohuwa tana yi masa alama da hannu gami da
gyaran murya, wai ya bar ummi maimakon haka ma sai ya dauki wani kofi nan gefansa da
guntun ruwa a ciki ya watsa mata a fuska. ta farka firgigit, yace taso, da sauri ta tashi yace
dauko hija binki maxa. ta dauka suna fita tsohuwa tana sallamewa. tace kai mai sunan mlm ka
lafama yarinyan nan haka, wai axumi wajaba akanta yayi da xaka tasheta da tsohon darannan
xuwa masallaci? yace kema in xaki, xo muje. ya tasata suna tafiya tana hada hanya suka tafi
tahajjud. sai qarfe hudu na asuba aka tashi. ummi har kuka tayi saboda tsananinjin bacci,
amma tana tsoran kar ta kama bacci yaxo ya same ta. tun tana layin bacci har ta gyagije.
sakamakon tashinta da matan kusa da ita keyi. kafin kwana uku ta saba da sallan dare, lkc nayi
xata farka. abba yana xaune ga dinki gabanshi amma yana can tunanin bushira, yarinyan da
yake matuqan so ce. amma yana shakkan fada mata,dan iyayanta sunada kudu matuqa. kuma
shine yakema duk yan gidansu dinki. Ahmad abokinshi da ke gefe kuma sai yayi murmushi,
yasan tunanin bushiqa ne ke damun sa, dan haka sai ya ce, abba kasan allah, abari ya huce shi
ke kawo raban wani. haka kuma ZURFIN KICI, ba xai kai ka gaci ba. ka fada mata kawai. abba
ya ce hum ,ina tsoron kada ta ce bata sona, dan bansan ina xansa raina ba. ahmad yace daga
ganin yadda take jin kunyanka tana sanka. abba ya kalli ledan da ke dauke da dunkunan su
bushiran, yace ina xatan yau xasuxo amsan kayansu, dan tun jiya nace suxo.ahmad yace to in
sunxo kayi qoqari ka fada mata mana, indai ba ragon namiji kake ba. abba ya tsurama qasa ido
yana tunanin in sunxo mai ce mata? kusan awa biyu sukaje sukai sallan axahar, tungan motan
ta tsaya yasan tasu bushurane. shi kadaine a shagon sauran basu dawo ba. bushura ta shigo
da qannansu da yarsu aisha. ya taresu da faraa, suka gaisa kan bushura na qasa, sam bata iya
kallan abba tela kamar yadda suke kiranshi. Ya tura masu kayansu suka duba sunata murna
dan ya masu wadda sukeso. aisha ta aje masa cikon kudinsa kan table. har sun fita yagadai
baxai iya hakuri ba, yace bushura xo gashi. ta juyo tana dariya taxo. yace bushura inasan na
fada maki wata magana gashi kuna sauri ko? ta kalli motan tace fada min. yace kina sona? ta
xare ido sannan ta ruga da gudu. gabanshi na faduwa, bata tsaya ba sai mota. ya kwantan da
kanshi akan keken yace menene maanan gudun da yarinyannan tayi? ya tambayi kansa, qarfe
uku sunada lecture, amma baya xatan xashi makarantan. ahmad ya dubi abba wanda daga ka
dube shi xakasan yana kin damuwa. yace wai banaga sunxo ba? ko ba motan su bane? shiya
bandawo ba nakuma hana yaran dawowa dan ku sasanta. abba yace um, inaga yarinyannan
gara na haqura, dan bana san insa kaina cikin tunani. ahmad yace ban gane ba, abba yace, to
naga daga tambaya tana sona, saita kwasa da gudu ta shige mota. ahmad yayi yar dariya
sannan yace ,amsan ta baka. tana nufin tana sonka. abba ya harare shi kada ka maidani dan
iska, ina ta magana ta xabga da gudune shine tana sona? yace jeka tambayi manya .yaci gaba
da cewa kaine baka mata magana da hikimaba, ka fito mata kai tsaye baka sakaya ba. abba
yace, kai nifa ka sanni ba ruwana da wata kwana kwana, idan abu yayi min bana kwana, inko
bai min bama haka, ni ba ruwana. Ahmad yace sai xurfin kici ko? da ya aka shawo kanka ka
fada mata,abba ya mike tare da kallan agogo, yace inada lecture. gida ya nufa dan shirin xuwa
makaranta, har yayi kamar ya tambayi ummanshi cewa in ka ce ma mace kana sonta taji kunya
ta gudu wai alamun so ne? sai kuma ya kasa, yana jin nauyi amma in bai samu wata manufa ba
dole yaxo ya tanbaye ta dan baya boye mata komai.bushura yar ahj sale ce kwamishinan gona
na wannan xamani, gidansu yana karkasara. danqareran gida ne ginin xamani, sun san abba
ne sanadin dinki da yayi wa wata qawansu jamila.dinkin yayi matuqan birge su dan haka suka
fara kawo masa dinki, tun ranan da ya fara ganin su bushura ta kwanta mashi a rai. to ashe ita
ma yamata.shiyasa yau daya furta mata take ganin kamar anmata gafara da aljanna.wata
xuciyar tace ,to yanxu da kika gudu in ya xaci baki sansane fa, nan take hankalinta ya tashi har
tana rayawa ga abba can da wata.dan haka taga dolene ta koma gun sa inhar tana sansa. dan
tasha ganin mata na masa tayin kansu in sunxo kawo dinki.nan ta soma tunanin wace dabara
ce xatayi ta fita?saiko ta warware daya siket din kayanta cikin dare.da safe ta nunama
momynsu tace mata telan ya manta bai hada wannanba,dama yace xai gwada nine kafin ya
hada.momy tace direba ne xai kai mashi.bushura tace momx xaifa gwadani ne muje dai xa
kaini.tace to kuje, bushura ta danyi gayunta suka tafi.saidai kash! bata samu abba ba ance
mata yana gida. tace gidan da nisane, aka ce mata babu nisa,dan haka ta sa aka
rakata.tacema direbansu tana xuwa telan na gida.gidan ba nisa. A qofar gidan su abba ta tsaya,
sai ga ummi ta sheqo da gudu tana dawowa daga aike.ta tsaya tana kallan bushura, sannan
tace lafiya?bushura ta dubeta. yauwa abba yana nan?budan bakin ummi sai tace yaje kashi ya
fada a masai.bushura ta dafe qirji, yaushe? ummi tace oho.sai ga abba ya futo sanye cikin
shadda bulu mai duhu yana ta qamshin turare.shawara ya yanke lkcn da yake xaune a shago
kan cewa yaje gidan su bushura,tunda gidan kwamishina ba boyayye bane,suka hada ido da
bushura,ta saki faraa sannan ta dubi ummi,kince ya fada ina? ummi tayi ciki da gudu.ya bita da
kallo sannan ya kalla bishira,me tace maki?bishira tace, ba komai.saidai dariya da maganan
ummin tabata.yace tunda baxaki fada min ba xomuje ki gaida ummana.cikin muryan jan hankali
tace ina jin kunya.ta bude jakanta tace kamanta baka dinke wannan siket dinba.yace
mugani,yaga yadda aka warware shi aka cire xaran da kyau. murmushi yayi dan yasan ya dinka
siket din,kusan shinema na farkon dinki.ya gane yaran nata qila san ganinshi take san yi. Ya
dinke siket din yana cewa"to amma sai dai ayi min izini inzo gida in kawo da kaina in na gama."
tace haba dai,ya za ayi in taso ka?"ya ce,"ba komai,in dai anyi min izini sai inzo," ta ce,"to in
maka kwatance?" ya ce,"a'a huta kada ki bata bakinki,nasan gidanku zanzo anjima bayan
tarawih." ta ce,"to." sai mun zo" tace"ku dawa? ya ce,"abokina mana,kinga zo muje gurin
ummana ku gaisa." Bishira ta bishi cikin jin kunya.tun kafin su shigo daman ummi ta shiga gurin
umman da gudu tace mata"umma ga budurwar yaya Abba." Umma tace budurwa kuma? tace
eh ai zama su shigo.daga nan ta kara kyallawa dakin tsohuwa tana fada mata. Umma dai jim
tayi dan bata da wani burin da ya wuce ta baiwa Abba ummi,kuma da tasan har zai ga wata can
da wuri haka data fada masa kudurinta,sa tay 'ZURFIN CIKI' gami da nauyin baki....... sallamar
Abba ce ta katse ta ta ce,"shigo Abba." ya ce Umma bakuwa ce taxo gaisheki.Umma ta fadada
fara'arta tace to shigo,ba dai surukar tawa bace?" ya ce,"ai ita ce kam" Bishira ta shigo tana
sunne kai,ta gaida umma Umma ta ce,"masha Allah,Allah yasa rabon muce."Abba yana dariya
ya ce,amin ummana."ya dubeta,"tashi ki gaida kakata." suka nufi dakin tsohuwa,umma ta jinjina
kai .tabbas Abba nason yarinyar,in ta dubi yanda yake fara'a da zumudi. a fili ta ce,"Allah yayi
mana zabin alkairi."ummi na kwance kanta na cinyar tsohuwa,sai ta kalli bishira ta tuntsure da
dariya,lokacin da suke gaisawa da tsohuwa. Abba ya ce,"dariyar uban me kike yi?" sai ko ummi
ta sake shekewa da dariya. ya nufota ya suri kafafunta,tsohuwa ta ce haba mai sunan malam
yanxu in bata yi dariya ba kuka zatayi?" ya ce,Bishira tashi muje" Tsohuwa tace to yanmata mun
gode ki gaida magabatan naki,sannan kiyi ta hakuri da halin wannan miskilin." Umma ta
ce,"tsohuwa kodai kishi ne?suka yi sallama,ummi wadda tunda ya shureta ta rigasu fita sai ta
dauki takalmi Bishiran guda daya takai soro (zaure). don haka da suka fito suka shiga nema
ummi ta kule uwar dakin umma tana ta dariya tana lekensu. Abba ya ce,"ummi! ummi!!" taki
amsawa ya nufi waje da niyar dubota don yasan ita ce zata dauki takalmin,sai ga takalmi a
kofar shi. Don haka ya dauko kawai ya dawo ya bata umma ta ce,"ka kaita su gaisa da umman
Bashir." Abba ya ce,"a'a ba yau ba."ya rakata wurin direbansu,kusa da shagonshi sukayi
sallama da alkawarin zai zo washegari. yaje kuma bishira ta fada masa lallai tana sonsa sai dai
tana tunanin iyayenta ko zasu amince? ya ce,to shi dai zai turo magabatansa su nemar masa
izinin zuwa zance kamar yanda yake a shari'a Bishira tace a'a ya bari tunda yanxu shekarar
farko take a babbar sakandare(s.s.1)ba za a bari ya dinga zuwa ba,amma zasu dinga haduwa
gidan yarta dake na'ibawa. Abba baida zabin da ya wuce ya yarda da hakan tunda tace baza a
barta yin tadin ba.sai dai fargabar shi kada nan gaba sunyi zurfi cikin soyayya ace ba za'a bashi
ba. ta ce,"Babana bashi da matsala,amma momy dinmu ce abin tunani."Abba ya ce,"shikenan
Allah ya shige mana gaba." soyayya ce mai karfi ta kullu tsakanin Abba da bishira,wanda har
ummanshi da kanta tasan cewa Abba yana son yarinyar. Domin duk lokacin da zaije gurinta
tana lura da zumudin da yakeyi,kazalikain tace ka gaida surukar tawa, bakinsa baya rufuwa.
Don haka sai ta tattara batun ummi ta aje a gefe addu'a ce kadai bata daina ba.ana sauran
kwana uku sallah.Abba ya siyo fenti yazo da mai fentin nana ak fente gidansu ciki da bai. Da
yamma kuma ya kawo dinkunan su ummi da fati,ummi tasa ihu,sam irin dinkin da ta aro gurin
kawarta Amina ba shi yayi mata ba,ya zai mata dink iri daya da fati? ya ce,"kin isa ki sani in miki
dinkin da kike so?ta ce to ni dai bazan sa ba umma ta rafka salati tana kallon ummi ta ce,"ummi
kina da hankali kuwa? kudi kika biya ko ko Abban sa'anki ne?" tace cikin kuka to ni umma ya zai
min iri daya da fati? ya dubeta a fusace,"in kin bari na dauki kayannan wallahi bazaki sasu ba."
Umma ta ce,"ni da zaka daukesu ma da naso"tsohuwa ta fito ta ce,"saboda me? akan wane
dalili zaka amsar mata kaya?tunda baka mata wanda take so ba sai ka kyaleta." Da hannu
Umma tayi mishi alamar yayi shiru,sannan ya fita waje.Abba ya kada kai ya fita. washe gari
kuma ya shiga da me fenti har cikin gidan Alhaji karami,sahura tana daki lokacin da yake nuna
ma mai fenti guraren da zaya fara. Ta fito daga daki ganin Abba sai ta hade rai sannan ta
ce,"mune kashin baya? ai dama ka bar shi tunda baka mai da mu wani abu ba,mu ne dai baka
so din mahaifanka. Ta dalilinmu zaka shiga aljanna,ba dalilin wasu banzaye ba da sauri ya nufi
hanyar fita waje don baya son yaji zagin da zata yiwa Alhaji da Ummanshi. wannan na cikin
dalilin dayasa baya son zuwa gidan Alhaji Babba da Umma,sune suka ci kashi da fitsarinsa.
suka bashi tarbiya da ilmi,suka ci da shi suka shayar dashi.amma sam basa yi masa abinda
umman Bashir ke masa. haihuwarsa ce kadai su Alhaji babba basu yi ba,sahura tana zuwa har
shago tayi masa rashin mutunci,sannan ta ce ya bata kudi,ta ce ya ba bashir kudi ko ta aiko fati.
Bai taba kin bata ba,amma duk da haka bai tsira daga zagin rashin mutunci ba.ta ce ya tare a
gidan ummanshi komai nashike mata,wai da kuma sam ba haka bane. Umma bata taba
tambayar shi sisi ba,haka nana duk lokacin da ya bata wani abu ko ya sai mata,sai tace ina na
umman Bashir? kaje itama ka bata,in ko bashi da yawa ni naci girma ka bata. Ranar sallar idi
kuwa ummi koda tayi wanka kin saka sabon kayanta tayi sai na bara. Lokacin da zasuje sallar
idi,Abba ya fito daga wanka ya kalleta ina kayanki sabo? ta tura baki"ni baxan sa ba." Yace,"to
zanga wanda zaki bi masallacin,kuma ki kara magana saina fasa bakinki."sai ta wuce kofar
dakin tsohuwa,sannan ta ce,"to ai dai nima nasan hanya,kuma sai naje."ta fada dakin da gudu.
ya bita bata san yaga tsohuwa lokacin da ta shiga wanka ba,bayan fitowarsa.don haka ya ritsa
ta ya kwakkwada mata mari,sannan ya rike mata kunne. zan kara fada ki fada? ta ce,"a'a kayi
hakuri." ya saketa ya wuce,ta zauna tana kuka. misalin karfe hudu na rana ,bishira ta iso
shagon dinkin ita da direba,shagon a rufe.don haka ta ce su karasa gidan. Can dinma baya
nan,amma sai ta fito ta shigj gidan dauke da tire babba cike da kuloli. cikin kunya ta gaida
umma,ta kuma bada a aje masa.umma ta ce,"to ko ina Abba yayi? kila gidan su Ahmad
yaje."umma ta ce,"ke uwar gudu ina yayanki?" ta ce,"nima na ganshi?" karar bude kofarshi suka
ji,ta ce,"leka in shine kice yayi bakuwa.shine kuwa,jin cewa ga bishira ya shigo da zumudi.
Umma tace ka kaita ta gaida umman bashir. yace to, ta fito ta tafi kicin ta bar masu dakin,ashe
ummi tana uwar daki tana jinsu.ya ce,yanxun fa daga na'ibawa na ke,ina ta xumudi in ganki.
tace,na xaci ba xa kaxo ba ne,nace bari inxo ni,dan baxan iya kai dare batare da idanuna
sunganka ba.ummi ta toshe bakinta saboda dariyan da yakesan kufce mata,yace sai inga
kamar bakya sona.bishira tace haba abba, in kace haka bakamin adalci ba.yace to wadannan
kulolinfa me kika kawo min?ta ce bude ka gani.ya bude ya gani yace kai, lalle ashe ni dan
gatankine? tace sosai ma.ya marairece murya yace to bani abincin a baki.ummi daga cikin
dakin tace, la'ilaha illallahu.abba ya miqe da sauri.kafin ya ankara ummi tayi fitan bindiga tsakar
gida tana fadin la'ilaha illallahu,dama yaya abba dan is....umma ta gwabe mata baki,bayan ta
fito daga dakin ahj babba.ummi wadda inta s6a magana ko ana hanata sai ta kai aya.ta dafe
baki,tace maci gaba da fadin,umma to kinji abinda yake ce mata ne? umma ta jefeta da takalmi
tare da cewa,wai baxa kiyi min shuru ba? ummi tace,to fa cemata yayi xai bata abinci a
baki,kuma daman xan nuna maki wani kaset da yake kallo. Abba ya riqe kai tare da cewa ummi
in na kamaki xaki sani, kaset din wa kikaga ina kallo? tace na yan is....da gudu ya bita ,yayin da
umma ta jefa mata murfin kwano,amma duk haka ko da ta fita waje saida tace masa sai na
nuna ma ahj kwalin kaset din.take ya tuna da kwalin kaset din daya boye,wanda ya qwace a
hannun bashir,kaset din tsiraici ne wanda laanannu sukayi.abba cikin takaici yace,kai ummi! kai
ummi!! kinsan allah in kina wasa dani xa karyaki a banxa.ta ce to ba a dakinka na gani ba?yayi
qwafa,allah ya sani ya tsani ummi kamar ya shaqeta ta mutu.sai ya samu kanshi da qin
komawa gidan,kunya da nauyin umma yake ji,yasan dai ba xata kama xancan ummi ba,amma
yasan xuciya da xargi,qila xuciyanta ta xargi wani abu.bashir ya fito daga cikin gidan su abba
yace,yauwa bashir shiga gidanmu kace bishira taxo. Bashir rai bace ya shiga,dan yana jin
haushi ya amsar me kaset.ya shiga umma na qofar kicin xugun tana tunanin halin ummi.bashir
yayi sallama umma ta amsa.yace,abba ne yace in kira bira ne ni yace ne?umma tace gatanan
ciki,taxo bakin qofa ta kalli bishira kanta na qasa tana mamakin ummi.yarinyan sam bata
ji.umma tace kixo yana kira awaje.cikin kunya ta fita, yace da bashir rakata gun ummanka su
gaisa.bashir yayi fara,a antynace ke nan?abba yayi murmushi. bishira ta xauna gaban
ummansu bashir suka gaisa. bashir yace,budurwan abba ce. sahura tace,yau kika taba xuwa
nan unguwan? kanta na qasa tace, xuwana biyu kenan.ta kalli bashir tace kaji ko? amma shine
ko a turo ta nan gidan.nina haifi abba amma an gaje min shi.tace yarinya duba nan.bishira ta
dubeta,ta dafe qirjinta ni na haifi abba nine uwansa.matan gidan can mai gidana ya bada shi a
gunta,da ubansa da maigidan dan wa da qani ne amma sun gaje shi.bani da ikon sashi ko
hanashi amma sun mallakemin shi. da muryan tausayi take maganar. Bashir yace, umma indai
ya aurota xamu samu sauqi.bishira tace kada ki damu, insha allah komai xai warware. tace, to
yan nan na gode.fati ta shigo ta gaidata cikin nutsuwa, bishira tace wannan qanwansa ce?
umma tace eh, ai su ga sakamakon mugunta nan sun haifi yar muguwa mara jin magan. bishira
tace, kai yarinyar bata ji. fati ta ce abba ya ce kixo.sahura tace kinji ko? shifa ko nan gidan baya
qaunan shigo wa.bishira ta miqe ta balle jaka ta ciro sabbim kudi yan ashirin ko irgawa bata
yiba ta bata, tace kinsaya goro.sahura tace harda abin arxiki?to an gode.bashir yace antyna
inane gidanku?tace karkasana gidan kwamishinan gona.bashir ya raxo ido, nako san gidan,lalle
antyna ina qara gaisuwa.bishiratayi dariya.abba na tsaye suka fito,yace mata to ki tafi xanxo
amjima. tace baka kaini dakinka ba.ya girgixa kai, bai dace ba wannan ba mutunci bane,sam
bai kamace yar mutunci suna xuwa dakin samari ba. bishira tace danme? yace sharia bata
amince ba, damin duk lkcn da mutum biyu suka kebe,musamman mace da namuji. Abba yace
na ukun su shedan ne. irin wannan yana haifar da xinace xinace a bayan qasa.tace hakane ta
tafi.abba ya rakata har mota, bashir kuma tamkar maroqi, sai fadi yake allah ya tsare antina ki
sauka lfy.bayan tafiyanta abba bai iya shiga gidan ba tunaninshi daya kada umma ta
xargeshi.dan haka ya nufa gidansu ahmad.ya ba ahmad