Showing 18001 words to 21000 words out of 26460 words
Chapter 7 - ZURFIN CIKI book 1 Complete by halima Abdullahi K Mashi .pdf
ta tambaye bishira,
yace lafiyi lau.yaci gaba da cewa, yau nema xata
soma girki,nace na turo mata ummi tace wai
fati.umma tayi murmushi, sannantace kai ko
yaushe xata so a tura mata ummi umma tace ina
xata so a tura mata ummi? ita fa ba natsuwa
gareta ba.abba yace, duk da haka tafi fati
hanxarin aiki. umma tace,yanxu dai tura mata
fatin.ka ko sai kayan abinci?yace ina fa,yanxu dai
xan je bin wasu yan kudadena.tace ina xuwa
baqar leda ta ciro a cikin adakan suturunta,taxo
ta xauna sannan ta umurce shi da ya xauna.ta
miqa mashi ledan tace,kwance ka gani.abba ya
kwance ledan yana cewa menene a ciki ummana?
kudin da yayi arba da su su suka bashi amsa
yace,umma kudin nan fa?tace gudunmawa ce da
jama'a sukayi ta bani,ka gansu nan.yanxu ka je
ka siyi kayan abinci da su.abba yayi dariya,
sannan ya kullesu ya miqa mata tare da cewa.
Allah ya kyauta in amsan makh kudi, ki boye
abinki. tace bana son muyi ta jan magana
abba,kawai ka riqe kudin nan.muryan tsohuwa ne
ta katse su,inda take cewa yanxu ke suwaiba
hakan da ki ka yi adalci ne? yar gudunmuwar da
ki ka samu kiba mai sunan malam duka, ummin
fa? umma tace,to tsohuwa ummi me xatayi da
kudi yanxun?abba yace kai wannan matan sa
idan ki ya gota misali. Tace kai tafi can,ni rufemin
baki,ke kuma suwaiba da kike cewan haka ba kya
siyan mata yan tukwane da kwanonin nan na yayi
maigida cika duba ne ku ke ce musu ko ci bari
kallo? umma da abba suka sa dariya,tsohuwa ta
sake jin haushi ta ce eh dole ku min dariya tunda
kema kin xama shi,ai sai kiyi ta bashi naki ne ba
nawa ba.umma tace yi haquri tsohuwa, gani nayi
nan gaba muna sa ran abba shi ne xai ma ummi
kayan dakin ma gaba daya tace,me kika ce?tab
mai sunan mlm ne xai yi wa takwara wani abin
axo a gani?shi da ya tsaneta.abba yace,in lkcn
yaxo ke kya yi ma.ta tafa hannu cikin jin
matuqan takaici ta ce,a gayawa mai xuciya ba
mai dukiya ba,dan ko xan mata.ta nufi dakinta
tana fada.umma tace,tashi abba,dauki kudin nan
kaje. yace,wallah umma bari dai in dauka tunda
kin matsa,amma ba xan amsa duka ba.ya qirga
dubu uku,tace ka qara dan kusan dubu tara ne
kudin,yace haka ma ya isa ki adana sauran.tace
shi kenan. daga nan kasuwa ya wuce,ya sai
kayan abinci.bayan ya amso wadansu kudaden
shi ya hada ya kai mata. Sannan ya yi cefanen
kayan miyan rigijif da nama ya aika yaran
shago.dama kafin ya bar layin ya shiga gun
umman bashir ya gaisheta.da tana ta bace bacen
rai,sannan da yace umma ina fati? taje xata taya
bishira aiki ne.sai ta washe baki,tan bandaki.
yace to in ta fito ki tura mata ita.ya fice
abinshi.biyu saura ya iyo gidan,tun a tsakar gidan
yake jin qamshin shinkafa.ya isa kicin din tuni ta
sauke shinkafa sai miya.yace ki xubama yaran
shagona.ya dubi fati da ke yanka latas yace,in
kin gama jamin ruwan wanka a rijiya.tace to.yana
daki yana sa kaya yaji sallamar abokanshi.da
sauri ya fito, suna ta yi masa tsiya ango kasha
gyara, munxo dibar girki. abba ya bude musu
falo,falan yaji jeran samiru abin yayi na xamanin,
ga kujeru suka xauna suna yaba dukiyar da aka
xuba cikin falon.ya fito yace bishira ta saka hijabi
taje su gaisa.ya dauki abinci ya kai musu,sannan
yasa fati takai filet da ruwan sha,shi kuma ya
koma daki dan qarasa saka kaya.a xatam shi xai
samu sunyi nisa da cin abincin amma sai me?
dukkansu su shida kowanne filet din gabansa
shaqe da abinci da nama,ga cokali a
hannunsu,amma kowannansu juya abincin
yake,yace a,a kuci mana kai muke jira ka bude da
addua.tsaki yayi, yasan halin ahmad gun
xolaya,dan haka sai yace muktar kuci abincinku,in
kun bi ta ahmad xai ta bata mana lkc.cokali ya
dauka shima ya xauna kusa da sunusi ya ce mu
ci tare.take ya yatsina fuska tare da dawo da
abincin ya xube shi kan ledar yana tande
harshansa.dan danan gishirin da ya kama masa
harshe ya ragu,cike da kunya ya dubi abokanan
nasa suna ta dariyar da suke gimtse.da farko ya
dubi sunusi,wai gishiri ka qara ne?sunusi ya
ce,qila dai gishirin nan da bakin buhu ta
xufa.muktar yace dubi gaban rigata ni da shegen
kwandayi na tura nama a baki na tauna ya qwace
saboda tsananin qarfi ya dawo ya fado min
jiki.abba ya miqe cikin damuwa ya ce bari in
maku wata miyar. ahmad yace a,a duk yunwa
muka debo, inda yaji da mai a bamu muyi maneji.
abba ya fito xuwa kicin.fati ce xaune da nata
abincin tana ta juya cokalin. Abba yace ina
bishiran?taje daki.ya daga murya ya kirata,ta
amsa sannan taxo.ya dubeta fuska a daure ke
dama ba ki iya abinci ba shi ne ki ka toxarta ni
cikin abokaina?maimakon ki fada min? tace, to ai
fati ce nace tayi miyar, danni bansan yadda a ke
yi ba. haushi ya kama shi.ya dubi fati, ke dama
baki iya komai ba kema?shashasha, gara ki koyi
girki, dan duk macen da bata iya girki ba ba mace
ba ce.ya daka mata tsawa, tashi kije gidan
ummana ki ce ta baki abinci inji ni,ni da abokaina
ne.sallamar yaron shagon shi ne ta katse shi,ya
gaishe su sannan ya ce,naxo daukan abincin.ya
dubi bishira,kina da yaji?tace,eh gashi can cikin
kwalba da ummanka ta aiko min.ya ce,xuba ma
yaran nan yaji da mai.ta ce ai akwai miyar.yace
miyar ai ta xama guba.fati ta dauko abinci cikin
kula xata fita,yace wannan fa?ba aikenki nayi ba?
tace na ummanmu ne xan tafi mata da shi,ita ce
ta ce duk abin da a ka dafa inxo mata da shi, shi
ne yaya bishira ta xuba mata.abba baice qala ba,
sai al-ajabin halin uwarshi ya ke yi. Bishira ta ce,
kawo ita ma a kwashe miyar a xuba mata mai da
yaji. ya daka ma fati tsawa,kai mata haka ni ki
dauko min abinci gun ummana, minti uku na baki
in kin wuce biyar xa ki sani.da gudu ta fita tana
shiga gidansu ta aje bata tsaya yin surutu ba, ta
fita da gudu.dan wake umma tayi,Allah yasa tayi
da yawa,dan haka ta xuba musu ta dora ma fati
ba tare da ta tambeyeta dalilin aikowarshi ba. sai
dai a ranta tana ta saqe saqe tace,qila sun fasa
girkin ne,ko kuma bai kai kayan abincin ba.koda
fati ta kai musu dan waken nan suka baje suka
kwashi dan wake suna santi.bishira tana jiyo
shewarsu.abba na cewa ummana ta iya girki, bari
in xo in sa muku waigi.muktar yace, ka kai
amaryarka ta koyo girki.garzali yace,saboda irin
wannan matsalan kafin in auri yarinya sai na
tabbata ta iya girki.ahmad ya ce daya daga cikin
illar auran yaqan masu kudin nan kenan,
sangartattu ne basu iya komai ba tun da a
gidajensu ba sasu a ke yi ba.ado yace wasu ba
amma wasu suna saka yaransu.
vels / ZURFIN CIKI book 1 part 7
ZURFIN CIKI book 1 part 7
Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:59
Ado yace wasu ba, amma wasu suna saka
yaransu,dan wani abokin wasanmu a kaduna ya
auri yar wani attajiri, ba kaga girki ba kala
kala.abba dai yana ta binsu da ido,har aka yi
kiran sallar la'asar suka fita xuwa masallaci,daga
can xasu wuce gaida surukai.bishirata dinga jin
haushi,wai abokan abba sunxo har gidanta sunci
mata xarafi.ummi ta fito dan xuwa gidan su
amina,domin akwai wata xainab da wai ta musu
gulma xasuje su.kirata har gida su dake ta.suna
xuwa kuwa suka tsaya a waje suna tunanin
yadda xa suyi ta fito,amina ta ce muje mu ce
mun xo gunta ne, inta xo rakiyan mu mu duke ta
mu gudu.haka kuwa suka yi,har ummarta tana ba
su quli quli,ita ga me qawayen yan tana rako su
tun daga soron gidan suka soma dukanta.sai da
ummanta ta fito sannan suka gudu.ta ce yar tata
kin san gidansu?xainab tace,na sani.ummar tata
ta taso ta.su kuwa su ummi suna fitowa sai suka
canxa hanya.amina tace dan allah muje gidan
amaryan abbanku,naji ana ta labarin jeranta an
ce kaya ne na uban gari. . Ummi ta ce,"duk da
son kirgan samirana ban taba zuwa ba,saboda na
kula ita ma yar rainin wayau ce kamar mijinta."
Amina ta ce,"ke dai muje inga samirun da aka ce
jajaye wai masu shida-shida" ummi ta ce,"mu
fara bi ta shagonsa in yana nan to sai muje,in ko
bayanan ba zani ba ya dake ni a banza." duk da
cewa shagon da gidan tsakaninsu da nisa sai da
sukaje suka duba sukaga yana nan,sannan suka
je. gidan shiru sunata sallama,ummi ta nufi wata
kofa ta tura,ta yafito Amina,"zoki gani nan ne
falon."suka kirge samiru tsaf,sannan suka fito. ta
window ummi ta leka nan ta hango bishira kan
gado tana ta bacci,suka je kicin suka leka suka
tura dayan dakin da ba kowa. nan ma sukaga ba
komai ciki,an dai shimfida ledar kasa an sa
manyan robobin ruwa. suka fito,ummi ta
ce,"gaskiya matar nan banza ce,dubi yadda
mukaje tana ta bacci." daga can suka sake zuwa
gidan wata amaryar don kirga samira,sai kusan
magariba sannan ta shiga.umma tana alwala ta
ce,"to tunkiya uwar tumbele,tun yaushe ki ka bar
gidannan sai yanzun kika waiwayo? sai kararki
da jama'a keta kawo min?to na gaji da
halinki,bari Alhaji ya dawo,wato tunda yanzu
babu Abba a gida shi yasa iskancinki ke son yafi
da." tsohuwa ta fito,"suwaiba da a ce ba a
gabana kika haifi takwara ba,to da zance ba yarki
ba ce,ba dama yarinya ta fita wasa?" umma ta
ce,"ban hanata yin wasa ba,amma tayi shi a gida
yawo ne bashi da dadi." tsohuwa ta ce,"a'a karki
wani fada ma Alhaji,ta daina ko takwara?" ummi
ta ce, eh.umma dan haushi ta shige daki ta barsu
anan. lokacin da su Abba suka je gidan
surukanshi an amshe su ba yabo ba fallasa,har
ma da zasu tafi aka basu (uniforms)din bishira na
boko wai ranar monday lallai ta tafi makaranta.
sun zaga gidajan danginta dake kusa,sannan
suka dawo gida.ya sameta tana fushi,shima
shareta yayi don yaji haushi barnar abincin da
tayi masa. dadin dadawa gidan nan yanda ya bar
shi haka ya tadda shi.ita kanta batayi wanka ba
ta kwanta tana ta uban bacci.fita yayi daga
gidan,sai goman dare sannan ya shigo ya rufe
gidan yaja ruwa yaje yayi wanka. sannan ya
shiga dakin,tsayawa yayi yana kallon gadon
mutsu-mutsu,sannan ga kaya nan duk a kai.ita
kuma tana kwance rike da wani littafi tana
karantawa. . Ya ce,"bishira wai me yasa bakya
son kakkabe gadonki? ta dube shi nifa duk na
gajine.tsaki yaja tare da cewa me kikayi da har
kika gaji? bani guri ni in gyara shimfidar zan
kwanta. shine ya kakkabe shimfidar sannan ya
kwanta.duk da ya cike da bukata amma haushi
ya hanashi kulata,sai ma baya da ya juya mata.
Abba yanada tsafta sosai,haka nan ma'abocin
son kamshi ne,duk da gyara gami da tsafta irin
na ummanshi wata ran har cin gyaranta yake
yi.sam baya so yaga ko ina rakwacan,yafi son
komai ya ganshi a muhallinsa. dole kullum shi ke
share gidan ya wanke ban daki,sannan da rana in
ya dawo ya dora abinci. litinin duk makaranta
suka koma daga dogon hutun kirismeti da suka
samu.Abba ya koma kan aikinsa na bautar
kasa.dan haka kusan tare suka fita da bishira ta
wuce makaranta shima ya wuce wurin koyar war
shi. . Ya rigata dawowa gidan,dan haka gajeren
wando ya samu ya shiga tsabtace gidan.sannan
ya dora dafa dukan taliya. uku da minti sha biyar
ta shigo ya dubeta ina kika tsaya? ta ce,ba ko
ina mufa makarantar mu biyu da rabi ake tashin
mu.dan ma na samu direban gidanmu da yazo
daukan kannena shine ya kawo ni. Abba y sake
had'e rai,motar gidanku? Bn baki kud'in mota
ba?Ta ce ka bani, ya ce to bn amnce ki sake
shiga motar gidanku ba. Ta ce,"kan me ? ya
harare ta ba tare d ya bata amsa ba,y nufi kicin
tabi bayanshi d harara,sannan ta shige d'aki. A
ganin Abba sam babu wani sauki da ya samu a
auranshi,nashi ganin wahala ya d'ebo ma
kanshi,kwanciyada ita ne kurum zai ce ya k'aru d
shi acikin auren. Ya shiga gidansu d
sallama,Umma ta amsa tana zaune kan sallaya
bayan ta idar d sallar Isha'i. Ta ce,Abba ba a je
an kwanta ba?ya zauna tare d d'an jan tsaki ta
ce,A'a ha,jikin ko garin? Ya ce,Umma gaskiya ni
abubuwa sun cud'e min,yarinyar nan tunda a
kawo ta sam ban huta ba. Umma ta saki dariya
"ka ji Abba d wani zance,dama ce maka a ka yi
ana bauta d hutu? Aure shi bautane. Ya ce,Tsaya
kiji fa ummata,kinga tun Asubahi in nayo Sallah
zan hau sharar gidan,in shirya in je gurin d nike
koyarwa. In dawo in dafa abnci,sannan in tafi
shago kuma don takaici in na zo kwanciya ni zan
kakka6e shimfid'a,ita bata iya komai ba ashe
daga gidan nasu.Ni fa har ta soma sure min......
"Kai Abba! Umma ta katse shi d sauri, kada in
kuma jin wannan furucin, kana hauka ne?yanzu d
fada min menene matsalarka?in dai abnci ne ka
bari zan diga aiko muku da shi. Ya ce umma ya
ya ma za a yi haka?Tab ai ba zai yi wu ba,Ta dai
zo ta koya sati d lahadi. Umma ta ce,To shi
kenan,tazo din.kayi ta hkr Abba,nasan ka kai ma
d zuciya,don Allah kada ka sake in ji wata
fitina,ka lalla6a matarka kuyi zamnku lfy. Abba
ya ce, To ko da ya sanar d Bishira cewa yana son
taje gurin ummansa ta koyo girki,sai ko ta tuma
ta ce ita ba zata je ba,dama dai gurin umman
Bashir ce, Ya ce,shi kuma gurin ummansa ya
turata,koda Asabar din tazo kin zuwa tayi,shi
kuma sai ya shareta ta ya daina girkinki. Sai dai
yaje gidn ummanshi yaci,hatta ranar litinin d suke
d makaranta bai dafa abncin ba da ya dawo a
galabaice da yunwa ta iso. Bashir ya ce, Ni har
fata nake wata rana 'yar sa' in'sa ta hadu ku
umma,wlh in mata shegen duka. Bishira ta ce,Ni
dai bata isa ba, in ma ita ce ta turo shi dn in
dinga zuwa gidnta to ba zanje ba. Haka suka yi
ta zagin umma,daga bisani Bishira ta mike ta tafi
dn kada ya dawo bata nan. Rashin iya girki ya
kawowa masoyan 2 rashin jutuwa,wanda ko
magana Abba bai cika yi mata ba. In ta zauna
tayi ta kuka tana mmk,me ta mishi ya juya mata
baya dan da nan? Yau kam abn ya yi kamar
kaurace mata ya yi daga dakin baccinta, ya dauki
filo ya tafi falo ya kwanta. Tayi ta kuka. Kasa
jurewa tayi ta mike ta bishi,kwankwasakofar tayi
kusan sau 3 ya ce "Waye?" cikin muryar kuka ta
ce, Ni ce, Abba don Allah ka bude. Ya kunna
wutar falon,sannan ya bude ta shigo ta zauna
kusa d shi, ta ce, Abba wai mi na maka ne ka
tsane ni? ka duba fa ko wata daya ban rufa
ba,kasan dai yadda a ka yi auranmu yanzun in
Mahaifana suka ji dariya za su Min. Amma ba
komai sai biredi ta samu ta k'asuma,d ya tafi
shago sai ta yafa mayafinta ta nufin gidn umman
bashir. koda tai sallama umman tana kan turmi
zaune suna ta ganzar rake ita d su bishir. umman
Abba ce ta aiko musu da shi don rashin Adalci
suna sha suna yi da ita. Suka shiga lale d zuwan
Bishira, ta kalli bashir 'Ina fushi da kai, shine
wato har yanzun ba ka zo ba ko? ya ce, Tab, sau
2 ina zuwa zan shiga gidan sai yaya Abba ya fito
ya ce min kina bacci, na gane nufinshi baya son
ina shiga masa gida,shi yasa na share.Bishira ta
ce Um, wannan Yayan naka halinshi sai shi,
yanzun ma fa fushi yake dani. Umma ta ce," A
kan Me kuma? wai shi dole sai nazo gurin
ummarshi na koyi girki, ai ko nace wlh ba ni
zuwa. Umman bishir ta rafka salati. sannan tace
'Naga ta kaina ni Sahura,kai Allah ya isa
tsakanina d Suwaiba. yanzun kuma ta gama d ni
ke ta sako a gaba, so take ta shiga tsakaninku?'
Abba ya kura mata ido, yasan abn d ta fada
gaskiya ne ya ce "Me na miki to?" ta kalle shi,"Ba
ka ma san abn d kayi min ba?Ta ga daya yanzun
fa kaurace min kayi. Ya ce ba kya gyara
gadonki,ni kuma na gaji d gyarawa. Ta saka tafin
hannunta cikin nashi zo muje in gyara.
Tausayinta ya ji,ya tashi ya bita yana kallonta
duk kakarin d ta yi dn t gyara ta kasa. Sai dai shi
ne ya gyara, Sannan ya janyo ta suka
kwanta.Sam bata d gardama ko nuna gajiyawa a
gurin ba shi hakkinshi na kwanciya. In zai zo sau
nawa ba ya damunta,gurin da ta ke birge shi
kenan. Amma ba wannan ba ne kadai namiji ke
bukata,Musammanirin Abba dan kwalisa. Wata
ranar Jumma'a bayan sun tashi daga mkrntr da
ya ke koyarwa,ya ce da Ummi ta jira shi zaya
aike ta gida. Kudin cefane ya bata ya ce taje ta
sai kayan miya d nama ta kai gidanshi, Sannan
ta tsaya tayi masa miyar tare d yi masa sakwara.
. Shi kuma zai je ya fada ma umma, dn yana son
d dunkunan wata amarya d yake son karasawa
ummi ta zun6uri baki bayan ta amshi kudin ta
wuce tana yankun-kunai, ya ce "Ke!" ta waigo "Zo
nan . ta dawo, Ya kama mata kunne, Kin san
kwana 2 bn ta6a lafiyarki ba ko?to kiyi abn d yau
zaki gwammace ba ki zo duniya ba. ya
rankwashe mata kai, Sannan ta wuce tayi ce
fanan ta nufi gidn Matar gidn tana zaune d kayan
mkrnt a jikinta,,Ummi ta mata Sannu harara ta
zuba ma Ummi, Ummi ko ta rama,sannan ta ce
"Mijinki ya ce in zo in yi mashi sakwara d miya.
"Bishira ta ce, To sai ki koma gidn ubnki ki dauko
tukunya d murhu b dai nawa ba, Ummi ta ce, To
ni dai