Showing 15001 words to 18000 words out of 26460 words
Chapter 6 - ZURFIN CIKI book 1 Complete by halima Abdullahi K Mashi .pdf
kariqa ware ranaku biyu a sati kana hutawa.yayi
yar dariya,ina wani hutu da xanyi a gidan
nan,matsalar ummina kadai ta ishe ni.umma tayi
dariya,sannan tace ai ummi sai addu;a Ta canya
xancan da cewa,af na manta niko yanxu auran
abba yayi wata hudu nangaba?ya ce hudu ne da
yan kwanaki.tace tofa!gashi ni uwarsa banida ko
kobo,bari naxo na kama sana'a. ya tuntsure da
dariya,sannan yace sai yanxu kika san da
sana'a?itama dariyan tayi tace, in ba haka ba ahj
ranar biki ko an kirani bana amsa ba.yace gashi
kuma ke xaki mishi lefe.tace,to na shiga
aljihunka,in yaso in an soma sana'a sai in biya
ka.yasa hannu ya dago fuskanta yace sannu
sarkin wayau.suka sa dariya.yace in san muje
yaga gidajen nan na layin gabanmu,sai ya xaba
guda daya a baiwa masu hayar notice sai a gyara
shi.tace ya xabi na farkon layin dan yafi
kxau.yace amma bashida girma.tace ya ishe shi
daga shi sai matarsa fa?wanda ke cikin gidan ba
mata bixu ne dashi ba?yace to xamuje dai ya
xaba.sannan akoma kan lefe,tace allah ya saka
da alkairi,allah ya kaimu.yace amin.wayanshi
dake caji ta soma ruri,yace dauko min wayar
can.ta miqe tana cewa har naji tsoro,na kasa
sabawa da wayan nan.yace kuma gashi na kusa
bar maki ita. tayi dariyan jin dadi,tana
kallanshi.to ni wama xai dinga kirana?yace ni
mana,bana iya yi miki wata magana in na kira
abba na ce ya kawo maki,sai inga kamar yana
tsaye,inko taki ce dana kira sai ki kebe daga
jama'a muyi hiranmu. tayi dariya, daidai lkcn da
kiran ya sake shigowa,ya daga. ahj buhari ne
wanda ke sarin kaya gun shi daga kaduna.suka
gaisa yace ahj ka kira kan in dauka ta katse.ahj
buhari yace,dama ina san ince maka ne dan allah
gobe xan shigo,kasa ahada min kayan nan da
wuri.yace ba komai xa a hada.bayan sunyi
sallama umma tace ni abin da yake bani al'ajabi
da wayan nan, har kullum yanda xaka kira wani
daga nisan duniya,kuma kuyi xance radau.ahj
yace ci gaba kenan,wata rana ma sai kinga
fasahan data ninka wannan.tace haka ne.abba
yana xaune gaban ahj da safe bayan sun
gaisai,sai ahj yace abba ina ganin da yamma ko
xuwa dare kaje ka duba gidajen nan ka xabi
guda,saboda a ba su notice dan a gyara
didan.yace ahj ba sai naje ba duk wanda aka bani
yayi.ahj yace ummanka tace ka xabi na farkon
layin. cikin murmushi abba yace,ta shi
kenan,nima shina xaba domin duk abinda umma
ta xaba min shine xabina. tuni sahura ta fito da
anko,xaqewanta da nuna isarta akan bikin sai
kace ba dan fari ba. duk dangi sai surutunta ake
yi,har danginta.umma kan cewa tayi anko ba
shine damuwanta ba,dan haka sam bata bi ta
kansu ba.abba a cikin ajin da yake koyarwa,ummi
tana 2n gefe in da yayi mata maxauni a qasa,can
in da ba knwa sakamakon ganowa da yayi in tana
ajin ba a xaman lafiya,sannan babu me ikon xama
a kujeranta.yace,in ma ya sake ganinta ko a wace
kujera ce bas,xai ballata.rubutunda yayi take yi
ranta bace.ya kalli gun datake yace ke!ta dago ta
dube shi,yace xo nan.taje yace,amso min bulala
acan ajin.kafin ta dawo sai da ta duke wata
yarinya ta rugo.nan kuwa yarinyan ta biyo ta har
aji,abba kam daya amshi bulalar saida ya xaneta
tas.sam abba ya sama uni ido ko ta ina,ba
makaranta ba, ba gida ba.dan haka ta matsu yayi
aure ya bar gidan sannan ya gama service dan
shi ya qara gaba. tabbas lkcn auran sa xata yi
party.RFIN CIKI book 1 part 6
ZURFIN CIKI book 1 part 6
Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:56
Tabbas lkcn auran sa xata yi party. Ummi party
xatayi na murnan barin gidan shi.ahj ya ba umma
wayarshi kamar yadda ya fada mata,ya ba abba
ya suya mata layin mtn kamar yadda ya fada
mata.ummi tafi kowa murna da wannan
wayan,domin in umma ta aje takan dauka tayi ta
latse latse,har dai ta iya abubuwa a wayan
saboda ta iya karatu.kwanci tashi bikin abba ya
rage saura yan kwanaki.duk gida biyun sai shirya
shirye suke,mu samman gidan amare saboda yan
mata biyu xasu auran.gidansu abba tuni ahj yasa
an masu fantin gidan biyun,gidan ango kuwa ya
sha gyara da fenti.ahj ya sabunta mishi qofofi da
wundunan gidan, batun lefe kam dama tuni ya ke
sayen xannuwanshi da kadan da kadan yana
kawo ma umma tana adanawa.dan haka ahj
karami yana kawo akwatuna umma ta fito da
kayan dan tasan me xa a qaro.sannan ya yaba
da hankalin abba.wannan ya nuna mishi cewa
abba xai iya riqe gidanshi.lalle sana'an hannu
tana da amfanh ga yayanmu a wannan xamanin
namu.umma tai mashi lissafin sauran abubuwan
da xannuwa da leshi xuwa shadda,tace ahj dan
allah adubo mana masu tsada, Ahj yace suwaiba
xan yi daidai qarfina,ba xan yi qarya ba dan sun
san cewa dana talaka ne,kuma suka ba shi.umma
tace,sai batun abin da xa a ci.yace suwaiba
kenan,saunawa xakimin lissafin kayan abincin?na
xata ma xakice kayan sawanku?umma tace suma
a kawo mana da wuri dan mu dhnka da wuri,ba
abba xan ba c saboda harkokin sun masa
yawa.saura sati uku biki aka kai lefe.hjy xainu dai
unguwa ma ta tafi a ranar,danginta na maigidan
su ne suka amsa.sai yatsina suke tare da raina
kayan da suka duba ma sai um da um suke
cewa,wata tace to an gode fa,tunda taji ta gani
mu menene namu?suka ba da tukuici, nan dai
yan kai lefe suka dawo jiki babu qarfi.koda suka
dawo suka sanar da umma sai tace ku qyale
su.mu dai mun yi daidai qarfinmu.umman bashir
kuwa da qannanta suka kai mata labari cewa,tayi
ina ko xa suyi maraba da kaya?suwaiba ta karbe
mishi kudi bada xuba kayan kirki ba,banga
laifinsu ba.ummi kam sai dibar ma umma kayan
abinci take a boye tana kaiwa gidan maman iman
maqotansu ne,matan suna shiri da ummi, don ita
rayuwar ummi dariya take bata,ta gwado shinkafa
ta kawo,taliya,ta tsiyayo mai,ta ce sauran kayan
miya da magi,har nama debowa zanyi. maman
imam ta ce lallai kawayenki zasu sha party.
ummi ta ce tab ai dole inyi party zan rabu da
alakakai sarkin mugancin duniya. maman imam
ta saka dariya,ummi ta kuma fita da gudu tana
fadina na tuna inda gishiri da maggi suke. daga
gidan amare anzo anga gidan amarya,nan ma sun
tafi suna mita,fadi suke "bishira batayi sa'ar miji
ba,wata ta ce ya aureta ne don kudin ubanta.
koda suka je suka fada ma hajiya zainu fasalin
gidan,daki uku ne duka falle dai dai sai kicin da
bayi a tsakar gida. kanwar zainu ta ce,"kai
gaskiya bishira bata yi dabara ba.hashimu dan
gidan Alhaji mansur ya jima da sanar dani ya
kamun bishira." hajiya zainu ta ce,"shi kadai?ko
yayan abokan babansu nawa ke sonta?tunda taki
tsayawa tayi karatu ta zabi ta auri tela,ba shi
kenan ba?dubi gidan ubanta amma ta zabi zama
a wani gida dakuna jere sai ka ce ajin
primary."lol. suka ce,"kwarai kuwa kamar ajin
makarantar gwamnati."ta ce,"shi kenan ai kaya
dai asai mata daidai tsarin gidanta ba iri daya za
a sai musu da Aisha ba." sun siyo sunje sun jera
komai ras,yanzun kam sai daura aure ya
rage,Abba da abokanansa walima kadai ya shirya.
can gidan ne suke ta bukukuwansu irin ma masu
hali.shi kam dai yasan yan'uwanta ba sonshi
suke ba. sam be je gurin shagalinsu ba. ranar
lahadi aka daura aure,misalin karfe goma na
safe,unguwar kam ta cika da mutane da motoci.
Abba da zugar abokananshi salisu yayan amare
yayi musu jagora cikin gidan. sun gaisa da
mutane sannan suka fito kowa fadi yake."kai
amma angon bishira zankadede dashi
tubarkalla."gashi Abba da iya daukar
wanka,tsafta ce dashi ga son kamshi. KAI MATA
IYAYEN GULMA. Can gidan ango ma anata
shagalin cin abinci, jama'a dangi da makota sa
gudunmawa suke ba umma tana a'a amma sai
ace ta rike sabida ita mutum ce mai kyauta.
umman bashir kam sai takaici take ji,kowa ya
shigo sai dai ya ce mata."Allah ya sanya
alkairi"kawai musamman ta shigo gidan don taga
ko ana ba umman Abba ne. Nan fa na fita ta
koma gida babu ko kunya tana ta masifa, fadi
take "lallai suwaiba,gudunmawar auran dana duk
ita ce ke karbewa? gaskiya naga sai dai amin
Allah sanya alheri a wuce,to da sake,ni na haifi
abuna ta bari sai ta tashi auran wannan
figaggyar yar tata sannan ta amshi bikin." ta
gama fadanta ta matsa,danginta suka soma yi da
ita,suka ce wa zai baki wani abu ke da ko dan
uwanki baki san ki bashi gudunmawa ba bare
kyauta.tsinanni yar rowarki ce taja miki."
kanwarta ta ce,"sahura sai dai ta ci na wani ba
dai aci nata ba,dama irinsu sun cika son banza."
ummi kam anci kwalliya an gayyato kawaye
anata party a gidan maman iman,an kunna rediyo
sai rawa suke yi,kafin a gama partyn an bige da
fada da dambe,da kyar aka rabasu,nan taro ya
watse. da misalin karfe takwas na dare,ango da
abokanshi sun taso sallar isha'i Ahmad ya ce don
Allah ango muje mu rakaka. ya ce,"Allah sai nayi
wanka."mukhtara ya ce,"gidan cunkus da jama'a
zakayi wanka?" Aminu ya ce,"don Allah malam
kazo mu tafi,in ma kifi zaka zama a gidanka."
Abba ya ce,"bari dai ku gani." a zaure suka ci
karo da ummi,ya ce,"ke jeki ki wanke bayi ki kai
mun ruwan wanka." ta sobare baki ta koma ciki
tana fadin. na dai kusan hutawa, masifaff. ta
wanke bayin sannan takai ruwan,yana shiga gidan
dangi sukayo kanshi,ga ango! ga ango!! abokan
wasa suka za na can zamfara suna tayi masa
tsiya. dan gidan ummanshi yau dai za a kwana
wani gidan ba na umman tashi ba.ya dai samu
ya shige wanka. bayan ya fito ya bude
dakinshi,ya shirya cikin wata shadda
mirror,lokacin su ake yayi.ruwan kasa mai duhu.
yasha hula mu hadu a banki ita ma kalar
shaddar,ya feshe jikinshi da kalolin turaruka.ya
shigo cikin gidan yaje kofar dakin umma. ya ce
umman tana nan.aka ce mishi tana dakin
Alhaji,yayi sallama a kofar falon Alhajin basu ji
ba,suna ta hira tsit ya yi lokacin da yaji umman
tana cewa Allah dai ya basu zaman lafiya da
zuri'a tagari. Amma har ga Allah naso Abba ya
auri..... ringing din wayar shi ce ta hana jin kowa
ummanshi ta ce,sai dai muryar Alhajin ya ce
wallahi suwaiba nima tsarina kenan. ahj yace ta
allah ya riga ya shirya ba ita ce matarshi ba.ya
daga wayar,ahmad ina xuwa mana. ba tare da
yaji abinda ahmad din xai fada ba ya katse
kiran,dan yaji haushi.yaso jin wacece iyayansa
suka so ya aura?ya sake doka sallama,suka
amsa.ya shiga ya xauna ya gaishesu,sannanya
dubi umma.dama naxo miki sai da safe ne.ahj da
umma suka yi yar dariya,umma tace to
abba,yanxu dai ka girma,dan allah kyawawan
halayenka dinnan kaci gaba da su.yace na
gode.ahj ma yayi masa nasiha,daga nan ya fita
jikinshi a sanyaye.da muwarsa me yasa umma
bata sanar da shi yarinyar da taso mishi ba
tuntuni?haka dai suka rankaya da abokanansa
dan xuwa dakin amarya. gidan kam tun daga
tsakar gida qamshi ke tashi.sun taradda
qawayenta biyu,ita kam tana lullube kan
gado.nan dai suka sayi baki akayi yan shaqiyanci
tare da barkwanci,sannan qawaye suka yi mata
sallama suka tafi,shima ya raka abokansa. ya
dawo ya xauna bakin gadan yana dubanta, itama
kallonshi take cike da so. sukayi ma juna
murmushi,ya janyo ledan kaxan da suka shigo da
ita. Ya warware takardar,y yago cinya ya mika
mata a baki,"ci,nasan yau kin wuni da yunwa
ko?" ta ce,"na koshi bana jin yunwa ma,ni kam
duk yau banji yunwa ba." ya ce,"ni ma haka,dama
yau bai da ce muci abinci ba."ta dube shi da
alamar tambaya a kwayar idanunta.ya ware
idanunshi. "taron da muka tara ko ina cike da
jama'a." yayi yar dariya sannnan ta bude baki ya
saka mata kazar.ta dan figa.haka yayi ta bata
tare da zuba mata juice a kofi shima yana bata.
ta ce,"to kaima ka ci." ya ce,nima ke zaki
bani."ta sunkuyar da kai don kunya sannan ta
dauka ita ma ta soma bashi. sai da suka yi
dam.sannan ya ce mata kije kiyi alwala kizo muyi
sallah. ta ce ai tun dazun nayi sallah.ya ce
wannan ta ma'aurata ce,zamu gode wa Allah
taare da rokonshi zuri'a tagari,da kuma fatan ya
tsare mu daga sharrin shaidan dama duk abin ki.
Ta fita ta dauro alwala,shi kuma ya kuskure
baki.shine yaja su sallar,raka'a biu sannan sukayi
ta addu'a,shi ne ma yake addu'ar ita kuma tana
cewa amin. bayan sun idar da sallah idar da
sallar,ya yi mata tambayoyi game da addini ta
sanar da shi,yayi mata yan gyare-gyare sannan
suka kwanta. sam Abba be daga kafa ba,a ranar
ya angwance abin shi.don haka yayi kwanan farin
ciki. da asubahi ya dawo masallaci,har lokacin
amarya tana ta shirga bacci ya zauna bakin
gadon yana kallonta.yasa hannunshi a gefen
kumatunta. "sleeping beauty" tayi mika sannan ta
bude ido,ya ce"a tashi ayi sallah ko?gashi sai
kinyi wanka ko?" ta ce,"eh." ya ce, "to tashi ki
gani gari ya soma haske." zani taja ta daura
daura ta nufi waje. da kallo tabi tsakar
gidan,sannan ta dawo dakin Abba.bazan iya jan
ruwa daga cikin rijiya ba. ya fito da sauri yaja
mata sannan yakai mata bandakin,ya dawo yayi
taja yana cika robobin ruwanta.sai da ya cika
mata komai,sannan ya koma dakin. lokacin ta
idar da sallah.ya dauko Alqur'ani mai girma ya
zauna gabanta,ya ce "madam zamuyi karatu." ta
dube shi tareda yatsina fuska,"wallahi bacci
nakeji."ya ce,"daure muyi ko aya biyar ce," ta ce
cikin shagwaba,"ni biyu." ya ce,"to bismillah,mu
fara ta sama ko ta kasa?" ta ce,"ni kam ko ta
ina, don haka sai ya soma mata daga bakara
yana yi tana maimaitawa,aya biyu kusan minti
ashirin ta ce, "zan kwanta." Ya aje kur'ani ya
kmama hannunta,zo muje kicin mu gani me zamu
nema.dan dole ta bishi zuwa kicin din.suka tsaya
suna kallm kayan, tukwane ne zuwa kuloli da
sauran tarkace,sai risho.ta dube shi cikin yanayin
tsausaya ma kanta. tace, sun qi sai min gas
cooker wai gidana ba flate ba ne bai dace da gas
cooker ba. ita ko anti aisha an sai mata, kayan
girkita ma duk yan chaina. tausayinta ya tsirga
ma abba, ya jawo ta jikinshi ya rungume, kada ki
damu bishira, duk abin da a ke sai ma yar gata
xan sai miki, matsawar Allah ya hore min. ya
janyo kwalin risho din ya ciro shi, ya hada yace
xan siyo lagwani da kalanxir kenan ko? tace eh.
ya miqe bari na dawo. tace to. ta nufi daki ta
fada kan gadanta taci gaba da baccinta, shi kam
gidansu ya nufa. tun daga nesa ya hango ahj
babba xai shiga dakin waje, in da aka sauki baqi
maxa, da alama ahjn ya hango shine shi yasa ya
tsaya a bakin qofar. abba yana cike da fara'a ya
rusuna xai gaida ahj shi kuma ya miqa masa
hannu, dan haka sai abban ya kama suka yi
musabaha. ahj yace Alhamdulillahi abbana, ka
xama mutun, sai ayi ta hakuri da rayuwa. abba
ya sunkuyar da kai yana tambayar kanshi ko
manya suna ganewa ne in kayi auratayya da
matanka? ahj ya katse shi da cewa, ya kwanan
iyalin taka? tare suka shiga gun baqin, yana
gaida su ya fito xuwa cikin gidan. yana leqawa
dakin umma bata ciki, sai baqi. wata uwani dake
matsayin abokiyan wasansu tace ango amarya ta
koro ka ne? yace, keni karki dame ni, ina umma
na? umma daga kicin tace, gani nan dana, xo
qyale su uwani. gurinta ya nufa yana cewa,kina
kicin ashe? tace, eh ina hada ma baqi abin kari
ne. yace kalli yanda duk suka yi mana kaca kaca
da gidan,wannan in sun tafi sai kin sha aikin
tsaftace gidan.tace to yana iya?dole in gyara in
sun tafi,ai arxiki ne ma xuwan nasu.abba yayi
dan murmushi,sannanya canxa maganan da
cewa,umma galan din kananxir muke so.tace,ga
ma kananxir din can da ahj ya siyo jarka babba
wai saboda biki.nace yaushe girkin biki xai yiwu
da kananxir?shine na aje shi.sai kadau galan ka
cika.yayi murmushi. Yace kai ahj akwai qoqari,
musamman lkcn bikin nan.umma tayi yar dariya
tare da cewa ko abinci fa baya iya tsayawa
yaci,in na masa magana sai yace bijin da guda
ina yaga ta cin abinci?abba ya girgixa kai,Allah
ya rama muku da mafificin alkairin da kuke
min,yasa ni ma in goya ku kamar yadda kuka
goya ni.tace amin abba ai muma kana yi mana
biyayya Allah yasa albarka a cikin auran, ya baka
yaya masu binka kaima.yace amin. ya isa gida da
kalanxir da lakwani ya samu ta koma bacci,dan
haka ya hada ya dora ruwan xafi ya juye cikin
plaks yaje ya ce ta shi mu karya. tayi juyi tare da
cewa sai an jima,dama tun jiya sun shigo da
biredi da kayan tea,shima sai ya sake
kwanciya.ya mannata jikinshi suka koma
bacci,goma da ishirin wayarsa ta tashe shi da
ruri. ya daga ahj ne ke san ganinsa qarfe sha
biyu.yace,ya sanme shi can kasuwa,ita ma ta
tashi.nan suka karya sannan yayo wanka ya tafi
kiran abba.kaya ne ya ba shi da kudin mota, yace
ya kawo ma baqi yan xamfara da xasu koma gida
yace ka tabbata ka dauki shatar mota har
Zamfara abba ya ce to.sai da ya samu motar
sannan yaje ya loda su suka daga,suna ta
godiya.yau satinsu daya cir umman shi ke kai
masu abinci,sannan ita kuma ya shigo da kayan
marmari,sai kaji ko tsire da balango.abba ya
shirya tsaf cikin qananan kaya xai tafi shago,yace
madam yau fa abinci xaki yi mana,kin san
abokaina su ahmad xasu xo muci abinci,in yaso
daga nan sai mu wuce gaisuwan surukai gidanku
a matsayin kina amarya wanda xaki soma girki
yau, me xaki dafa mana? ta tashi xaune duk abin
da ka ke so.dadi ya rufe shi,kowanne dai ki mana
fatana shine ki birge abokaina.tace an gama.
yace to bari inje xan turo yaran shago da abinci
da cefane tace to, har ya tafi kuma ya dawo
yace, xan biya in turo miki ummi,tace saidai in
fati.yace,ummi tafi fati hanxarin aiki fa.tace eh
nafi son fatin.kamar kullum sai da ya soma shiga
gun ummarshi suka gaisa