Showing 12001 words to 15000 words out of 26460 words
Chapter 5 - ZURFIN CIKI book 1 Complete by halima Abdullahi K Mashi .pdf
sauri ta fita taxo tana
buga gidan tana mashifa.yan baqin
ciki,mahassada,yanka min akuyan xaku yi?san
ummi bata ji ba, dan gidan ba kowa. umma taje
sheka can gidansu,hta kuma tsohuwa taje
gaisuwa n mutuwa nan kusa dasu.saida taga
akuyan ta galabaita sannan ta janyo wata leda ta
daura mata a bindi,sannan ta saketa.akuyan ta
tashi da gudu tayi hanyan fita,tace shegiya gobe
kixo ki bude mana abinci kici.taje ta bude qofar
ta jiyo muryan umman bashir,dan haka sai ta cire
sakatar sannan ta dan sanmata qofan akuya tayi
waje da gudu.saboda ledar da ummi ta qulla
mata,sai take ganin kamar binta ake,dan haka ta
nausa cikin unguwa da gudu.umman bashir na
ganin akuyarta tayi fitan bindiga,sai tabi tana
cewa,ku taremin.ummi ta koma ciki tana
dariya.ita kuma umman bashir daqar ta samu aka
ruqo mata akuyan ta.aka kwance ledan taruqo ta
xuwa gida.sai masifa take, tana isowa qofar
gidan umma na RFIN CIKI book 1 part 5
ZURFIN CIKI book 1 part 5
Posted by Bashir Sani Fesan on 14 Dec 2016 - 21:54
Ita kuma umman bashir daqar ta samu aka ruqo
mata akuyan ta.aka kwance ledan taruqo ta xuwa
gida.sai masifa take, tana isowa qofar gidan
umma na isa. tace yar baqin ciki kun kama min
akuya kun jiqata xaku kashe min,ta ta allah ba
takuba.umma tace akuya kuma wani iri?ni bana
gidan dawowa ta kenan.ta ce kina nan muna
fuka.umma sai ta shige gida,amma duk da haka
sai da umman bashir ta bita har ciki tace sai ta
doke mace akan akuyan ta.umma ta shige daki
can qurya tasamu ummi a kwance,tace ke uwar
yan daukan magana, ke ce kika jiqa mata akuya?
umma tace cinye min abinci tayi.nan abba ya
riske ta tana ta tsine tsine.yace meya faru?tace
kai ja can ka bani guri,dan baka san darajata
ba,banda an raina ni yaya xa'a kama min dabba
a jiqa?in nai magana sai a maidani mahaukaciya
ko haquri baxa a ban ba.abba yace to kiyi haquri
in sha allah baxa a qara ba.tace baxan haqura
ba,tunda inta mutu nike da asara.umma tafito
tace to yanxu ya kike san ayi?ni dai bananan
ummi ce da wannan tsiyan wai ta sameta ta
cinye mata abinci. umma tace kinsan halin ummi
kuma nima haquri nake da ita.tace to ni baxan
iya haqurin ba.umma ta finciko ummi ta hanka da
mata.ta gata na ki rama mata.ta juya cikin daki
ta kama harko kinta.ba kunya ta kama ummi
tana ta jibga.abba takaicin mahaifiyan shi ya cika
mai xuciya,amma bashi da daman cewa ta
bari.shin baxa tai tunani ba takama yar matan da
tariqe mata danta riqon adalci da amana,tana
duka haka? sai data gaji dan kan ta sannan ta
fito.abba ma fita yayi cikin takaici,ummi kuwa
kuwa tayi tayi har tsohuwa ta dawo,ta sameta
xaune tana dirxan kuka. Dama taci karo da abba
a waje tace mai sunan mlm har ka dawo xaka
kuma fita?yace um.tace miskilin banxa saikace
mai ciwon hakori,ta riska ummi tana kuka,tace
umhum daman tunda naga ya fita yana ta
maxurai nasan yaci xalinci.kai na gaji da halin
mai sunan mlm.umma tace,ba ruwanshi.ummi
taqara satin kuka ba umman bashir bace taxo
tayi min duka.meki ka mata?wai din akuyan ta
taxo ta cinyemin abinci,shine na jiqata da
ruwa,shine taxo tamin duka kuma gashi banci
komai ba, ko qala bata ceba,ta juya sai gidan
umman bashir.ta sameta tana sinke kayan
miya.tace ke sahura saboda bakida mutunci shine
xakixo har gaban uwarta ki daka?sahura tace na
daketa,kamme xata jiqa min akuya?tace wane
shegen ne yace ki saki akuyan ki har taje taci
mata abinci?to kashedin ki mara mutunci da baki
san girman nagaba ba.bashir ya fito yace a'a
tsohuwa kidaina xagan mana uwa har cikin
gidanmu.tace iye!kaxone ka nuna min rashin
tarbinyan ka?nan har wata uwa gareka?nanfa sa
in sa ya tsarke a tsakaninsu.ummata juyo su
tarasa yadda xatayi,sai ga abba ya shigo.yauwa
abba shiga gidan can ka lallaso min tsohuwa taje
kasgedi ataba yar gwal dinta.ta dubi ummi tace
duk aka yar marajin can ni naji dadin dukan da
tayi mata,dan dukan algaki tayi.banda xalunci ya
xata kama dabba ta jiqa? abba ya fita ba tare da
yace qala ba. abba na shiga gidan bashir yana
tsigale tsohuwa tankar xai kai mata duka,abba ya
daga hannu ya wanka ma bashir mari,sannan
yace tsohuwa saankace da xaka dunga mata
wannan fadan.ya dubi umman bashir dan allah
kiyi haquri.sannan yaja hannu tsohuwa,shi kuma
bashir yana ta xagin abba yana cewa allah ya
isa. umman bashir ta ce abba tir da hauhuwan ka
tir!tir! kuma gab nake da in dagama ka nono.cak!
abba ya tsaya kalaman mahaifiyan shi sun shi
jeshi,a hankali ya saki hannun tsohuwa batare da
tasan ya tsaya ba.dan sababin da takeyi yaja
hankalinta.ya juyo har gabanta yace dan allah ki
yafemin ki ya femin.ba tareda ya jira amsan ta ba
ya fita. baiji muryan taba amma koda bata ya fe
maiba jikinta yayi sanyi.da yamma bayan su ahj
babba sun dawo kasuwa sai suka shiga dan
gaida tsohuwa.nan ta saka masu kuka suka rude
tare da fadin me aka mata?cikin kuka tace ni
sahura xatai ma rashin mutun ci tare da danta
bashir nan ta koro masu bayanin komai. Ahaji dai
sukai ta bata haquri,ahj qarami yace shi kam dole
ya cimata mutunci daga ita har bashir din.da
suka fito ahji babba ya ce kada gaje ka mata da
tsin hankali,nashihaxaka yi mata shi kuma bashir
ya girmama yayansa.abba kuwa yana fita sai ya
bar layin dan bacinrai,dakin ahmad yaje ya
kwanta duk da cewan ahmad din bayanan.tunani
yake tayi akan mahaifiyanshi,yadda ta runtse ido
da alkairin da umma da ahj suke mata.ahj qarami
cikin damuwa da takaici ya shiga gidansa,da
bashir ya soma yin karo,nan take ya rufeshi da
fada.sahura na ji ta taso cikin mashifa kada ya
xagan mata da,dan ya nemi tare mata
mutunci.ahj yace har wani mutunci ne dake
wanda xai kare maki?to da kinada mutuncin kin
tunkari mahaifiyata ki mata cin xarafi?tace har
gidannan ta shigo saboda na daki yar gwal
dinta,takan wannan wara mutuncin yarinyan xata
xo ta xage ni?umma tace ma ahj babba ka fito
gashi can fa ahj qarami rigima ta kaure
tsakaninshi da umman bashir.da qyar ahj babba
ya kashe wutan,abba da ya dawo yaji hayani ma
mahaifanshi sai ya qara barin layin sai can sha
daya na dare ya dawo ya kwanta,ranan ko abinci
bai ci ba.da safe yana gaban umman shi yana
fada mata kalaman da umman bashir ta masa
jiya,una ta ce ashsha,kai banji dadin wannan
kalaman na sahusa gare ka ba.saidai na gode
daka nemi yafiyanta,sannan ka kiyaye duk abinda
xaisa tayi maka munmunan furuci.dan bakinta
dafine a gareka.kada kaga cewan baka yimata
komai ba,to intayi ma mugun furuci sai
kamaka.yace xan kula,tace yauwa abba.saka
makon binci ke da mahaifin bishira yasa amishi
iri daya da wanda sirikinshi ibrahim yayi
mishi,ma'ana halayan kirki da mutuncin iyayanshi
da shi kanshi yaran.duk dadai ance masa ba
wasu masu hali bane?sai rufin asiri da suke da
shi.wannan bai dameshi ba tunda dai ance mashi
yaran yana neman na kanshi,sannan yana karatu.
to tunda tana sanshi ba ruwan shi. ya kira wayan
cikin gida ya kira hjy sai yaji sallamanta ta turo
qofa.yace yauwa dama ke xan kira.ta dire tire
mai dauke da kayan shayi akai,sannan ta xauna
tana gaishe shi. Ya amsa sannan yace ina jin
gobe masu neman auran bishira zasu je wajen
yaya a jakara. Hajiya zainu ta gyara zama,"ka ce,
bishira ko Aisha? ya ce bishira dai tayi yar dariya
yaushe bishira tayi saurayin da har zai turo? ya
ce,"a'a ba ki sani ba? ta ce,"na dai ji yanzun" ya
ce to na basu izinin turawa tun jiya tunda tana
sonshi babu ruwana da doguwar soyayyar nan
kin sani Hajiya zainu ta hade rai,"amma kana
sane da cewa ss2 zata je ko? ina laifin ta gama
sakandare? Tace ,"gaskiya ranka ya dade ka bar
batun auran bishira." ya dubeta,"kada ki damu
kanki fa.don kin san ba zan canza ba" ta bata
rai,to dan wanene? shima ya daure fuska dan
babanshine.ta mike a fusace ta fita sai dakin su
bishira. Lokacin suka farka daga baccin da suka
koma bayan sallar asubahi.ta ce,"ke bishira,ke ce
kika turo saurayinki gurin dadynku? wai yaushe
ma kika yi saurayin? Aisha tayi zaraf tace, momy
kin ma san wanene? hajiya zainu ta ce,"wanene?"
Aisha ta ce telanmu Abba din nan." Hajiya zainu
ta saka salati Abba tela? tela fa? Aisha ta
ce,"tela kuwa" hajiya zainu ta isa gurin bishira ta
rike mata kunne. "kece kika zabi auran tela? me
ya ci shi kansa bare ya baki? zai iya da
karatunki? wallahi tun wuri kije ki fada ma
dadynku bakya sonshi." Bishira ta ce,"nifa shi
nake so momy."hajiya zainu ta rufeta da duka.
washe gari su Alhaji babba da abokinsa Alhaji
sani,sai makocinsu malam ma'aru suka je
nemawa Abba auran bishira a jakara gidan Alhaji
musa wan mahaifin bishira. an amshesu hannu
biyu,sunyi magana ta fahimta an basu,kuma sun
karba.an yanka sadaki da dukiyar aure,sannan
sunce suna so za'a hada da yarta. Su Alhaji suna
ta godiya nan dai gemu da gemu suka rabu cikin
mutumta juna. Hajiya zainu ta dauki karan tsana
ta dora ma bishira,tunda tayi-tayi cewa ta janye
batun auran Abba taki,ta ce to bazan miki komai
ba.sannan in babu ta sameki kada ki ce kin
sanni,in ki ka zo nan gidan da sunan neman
taimako saina wulakanta ki. Duk bishira dai ta
yarda,nan aka sa rana kusan wata shida. Abba
ya iso kofar shagonsu da sauri don hangen da
yayi gurin ya cika da jama'a,yana zuwa sai yaga
ashe ummi ce tazo wucewa ta taba wani shagon
fale-fale ta taba sai yayi mata shocking. shikenan
ta tsaya tana jiran wa zai zo tasa shima ya
taba,can sai ga wani yaro,tace kai ka iya karatu?
yaron ya ce,"eh" ta ce karya kake in da gaske ne
nuna mun acan.da gudu yaro yaje ya dangwala
dan yatsa a kan A sai ko shocking ya debe shi ya
jefa kwata. Ashe yayan yaron na kallonta sai ko
ya biyota shine ta fallo da gudu ta fada
shagon,shi kuma y ce sai ya duketa. Abba ya
kalleta kallon tsana ya ce,"fito shegiya ya
hankado ma yaron ita ya ce ka mata dukan tsiya
yaron ya ce na hakura ta ci darajarka Abba ya ce
don Allah ka duketa,don wannan bata da wani
amfani daya wuce duka. yaron ya ce,ku dai ku ja
mata kunne don kar taje tasa dan wani a
matsala,ko ma ya rasa ransa,domin shocking zai
yi kisa nan da nan. Abba ya ce dama zai kasheta
ai da munyi murna.ummi ta kalleshi a ranta ta ce
sai kazo ka kashe ni. Bayan kowa ya watse na
nan yasata tsalle kwado. Ahmad abokin shi ya
shigo shagon ya ganta tana ta tsallen kwado ya
ce a'a Abba meye naka nasa mace irin wannan
horon? Abba ya ce kasan Allah da ace yarinyar
nan namiji ce da tuni na zuga an kaita gidan
horon yara,kaini da in kayi kisan kai babu laifi da
sai na ba yarinyar nan gamalan 20 tasha ta
mutu. Ummi cikin kasa-kasa da murya ta ce
nima da zaka mutu a dadina. Ahmad ya ce haba
Abba ya kake irin wannan maganar? ya dubi
ummi tashi ki tafi abinki.ummi taki tashi don
tasan in don Abba ne sai ta tashi ya ce ta sake
sabon lale don haka sai ta ci gaba da tsallan
kwadonta. kuma bata nuna kasalarta domin ya ce
sai taji jiki tukunna zai barta. wannan ya shigo ya
ce Allah sarki ai mata hakuri wannan ya shigo ya
ce don Allah a kyaleta.sai kurum ta saka kuka. da
kyar Ahmad ya shawo kansa har ya ce ta tashi
ta tafi.ya ce kuma inta yarda yazo gida ya samu
tayi wani laifim shi da ita ne.daf da magrib yana
sauri za shi masallaci sai ya ganta da dan tasi
tana kasa shi kuma yana tuko motar a hankali
yana ce mata an kusa gidan tana cewa eh. bata
lura da Abba ba saida ya ce ke ina zaki? da sauri
ta fice da gudu dan tasi yace ke yarinya zo nan.
Abba ya matsa gurin shi ya ce malam lafiya? dan
tasi ya ce yarinyar can ce ta taro ni tun daga
bakin titi.wai an aikota ta kira dan tasi za'a dauki
kaya zuwa wambai. nan na dibo fasinjan cikin
gari ne ma sauke su tare da basu hakuri,to da
mukazo hanya sai tace mun jaki ne za'a dauka
nace jakin lafiya? ya ya za'a iya saka jaki a tasi?
ta ce mun ita dai tashi aka ce mata ta taro,kuma
nayi-nayi ta shigo motar taki. Abba ya ce,kayi
hakuri karya takeyi,kanwata ce.wallahi bata ji.
dan tasi cikin takaici gashi ya sauke fasinjanshi
yajuya ya tafI. Abba ya nufi masallaci yana
kyalkyata dariya.don shi lamarin ummi tsoro ma
ya soma bashi jaki a tasi.kai shima dan tasin
mashiririce ne.banda haka tunda ta furta jaki ai
sai ya kama gabansa. yau bai ma bi ta kanta
ba.don yana sauri yaje gurin masoyiyar sa
bishira. Ummi ta shiga ajinsu na makaranta.kai
tsaye ta nufi kujerarta wadda babu wata yarinyar
data isa ta zauna duk ajin don suna matukar
tsoron ummi. Tun daga lokacin data bigi kirji ta
ce kujerarta ce,kowa ya sallama mata.malamai
ma da suka gaji da rabon fada cewa suka yi a
bar mata kujerar. duk makarantar babu wanda
bai san ummi ba,malamai da dalibai saboda
yawan fadanta da tsokana,har malamai bata bari
ba a tsokana. sun fita fitsari ita da kawarta
Amina,kafin su dawo malamin (social studies)ya
shigo. Amina ta ce ummi dubi har malamin(social
studies)din ya shigo. ummi ta ce,"ina ruwana,ko
wanene ma ni shiga zanyi abuna."Amina ta ce,"in
dai tica hassan ne gara mun juya don sai ya zane
mu." ummi ta ce,"tab ai gara dukanshi da in tafi
gida yanxun wannan mugun yaya Abban ya ci
zalina." sam ummi bata kalli malamin ba,sanda
take takai kujerarta,yayinda Amina ta labe ta
kasa shigowa,kamar cikin mafarki taji muryarshi y
ce,"ke daga ina ki ke?" ta dubi gurin da
sauri,"yaya Abba ne ya hade rai,fuskar nan tashi
babu annuri sai kace mai bada mugun labari. ta
tsorata matuka,ya ce" zo nan kiyi 'kneel down'."
jiki na bari ummi taje ta zube gaban allon.nan
take yayi mata bulala guda goma masu kyau.
take yan ajin suka shiga taitayinsu,don sunga
ummi tsiga tana kuka irin wanda bata taba yinsa
ba.don ko an duketa daurewa takeyi ta kuma
shanye dukan. sannan sabon malami dan bautar
kasa kamar yadda ya gabatar musu da Kansa
daga zuwa yayi wannan duka.lalle dole su
tsorata. ya ce,wuce ki zauna dakikiya mai idon
jaki.wannan kalma ta daga hankalin ummi,domin
taga yan ajin sun guntse dariya. ummi ta koma
kamar ruwa ya cinyeta a cikin ajin duk tsokanarta
ta tsiya,tsunguli wancan,shuri wancan,duk an
samu saukinta. taimako daya Allah yayi mata,duk
da halinta ta da kan daukar karatu.a zaton Abba
bata iya komai ba,tun da basa shiri. don haka
baya ko duba takardunta,islamiya ne yafi tsarata
don tashi hikimar fannin addininta ne dole a
matsa mata ta sani,boko kuma in bata yi ba ta
yiwa kanta. duk rubutun da Abba yayi ummi yake
ta dawowa ya ce ta karanta shi in ko ta mike sai
ta karanta shi tsaf.in da ta dan samu saukin shi
kenan. tun daga wannan ranar ummi alkadarinta
ya soma karyewa gurin yan ajin,domin in suna
fada shh da yazo ba bin ba'asi ita yake horawa.
sannan in ta duki wani kafin ya shigo.daya shigo
za'a fada mishi,don shine ya basu damar cewa
duk wanda ta taba in yazo a fada mishi. duk da
sun gano kanwar shi ce,gashi kuma wani lokaci
tsokanarta suke tunda ya ce mata ummi mai idon
jaki. sam bataji dadin zuwan Abba ba amma
tasha alwashin itama sai ta mishi abinda zaiji
bakin ciki kwatankwacin yadda taji. wata rana
Abba ya siyo wayar sadarwa, lokacin tana farkon
fitowa,yazo da ita gidan yana nuna ma su umma.
nan akayi ta mishi murna umma ta ce,"kai
Abba,kai da zancen aurenka ke karatowa ina kai
ina siyan wannan abar har kusan dubu ashirin ka
ce?" Yace umma amfani kai,kema xan sai miki ai
tunda nan gaba kadan xata sakko.ahj babba dai
yace xaya bani kudi in sayo musu shida ahj
qarami.ummi na wanke wanke tana kallan
su,wayar ta birgeta,irin wanda suke gani a cikin
fina finan indiya, ta xata yan sanda ne kawai
suke riqe irin wannan wayoyin.kai ko na bakin
titin nan da take ganin mutane na bugawa birgeta
yake yi,har ta tuna ranan da sukayi doguwan
tafiya sukaje phone book.suna xuwa suka tarad
ana layi,haka suka koma gyefe saida kowa ya
gama sannan suka shiga sunata latsa latsan
nanbobi suna karawa a kunne.saida wani mutun
yaxo ya kore su,bayan ya dundungure masu kai.
tayi murmushi, sannantace a ranta, allah yasa ya
sai ma umman su,ita ko ta samu abin latsawa.
daya nunama tsohuwa wayan tace shirman
banxa,inba qarya ba da wannan xaka kira wani
daga nesa?yace kn da a saudiyya kike xan kira
ki.ta ja tsaki tayi daki shiko ya fice nana
dariya.cikin satin ahj babba ya ba abba ya hada
masu waya da layi,ahj babba yafi kowa murna da
wayan, saboda shi mata fiyine. Wata safiya abba
ya shiga wanka, umma na kicin tana soya masu
dankalin hausa. zirif ta shige dakin abba tanata
danna danne,da taji motsin bayi sai ta aje ta yi
waje da gudu.saida ta tabbata ya shiga daki sai
tayi xirif da shige gida.lkc da taxo kawo mai abin
kari tasame shi yanata danna wayan,ya dubeta
kinxo kin tabamin waya ko?da sauri tace a,a.yace
munafuka,kece gashi kinyi min delete din duk
numbers din dake cikin wayan, muguwa. tace to
ni na shigone?ya harare ta yace fita, da ace ban
rubuta lambobin na aje ba da yanxun kin min
asara, muguwa kawai. ummi ta fita tana dariyan
mugunta,domin in da abin da tafi so bai wuce
taga bacin ran abba ba,kamar yadda tayi imani
shima burinsa kenan. umma ta lakato man xafi
tana shafama ahj a qafa tana murxawa.yace
yauwa suwaiba kamar kinsan tun daxu yakemin
kwankwatsa.daxidariya tace in dan tamu ne